Ranar Monday a makaranta da malami a ajin su amma Walida ta damu Hamida tana taɓa ta idan ta waiwayo sai ta nuna mata wani abu a wayarta, Hamida ta gaji ta ce “Ki bari mana Walida.”
Karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna ita da malamin ya taso har zuwa inda suke ya tambayi Hamida surutun me take masa yana cikin aji sai ta yi shiru.
Tambayoyi ya cigaba da yi mata cikin harshen turanci duk da ta soma ji amma ba ta iya mayarwa sai ta mishi shiru, hakan kuma ya harzuƙa shi sai ya ɗauke ta da mari! Wata irin wuta ta ga ta gilma ta idonta sai ta fashe da kuka.
Ya koma wurin zamansa tare da nadama da ya ji ta rufe shi sanin ƴayan masu garin ne a sch ɗin ba a dukan su.
Kafin a tashi fuskar Hamida ta yi fushi wurin idon ya kumbura, a haka ta koma gida hankalin Gwoggo Indo ya tashi sai fada take wurin wata Nurse maƙociyarsu ta kai ta ta ba ta magani.
Ta so Hamidar ta kwanta kar ta je Islamiya amma ta ƙi ta ce za ta je za su bayar da hadda.
Gwoggon ta ce “Ke kika dage kina son wata boko ga shi nan za su sabauta miki ido.
Ban da Yallabai ya kai ki ai da kin gama zuwa, mutum sai ka ce ya sha maganin ƙarfe daga mari fuska ta kumbure?
Hamida ta ɗago kumburarren idon “Don Allah Gwoggo ki daina ce mishi Yallabai.
Ta karyar da kai “Ya zama dole ai Hamida, duk wanda kika gani a nan ƙarƙashin su yake.
Ta gama sanya unifoam dinta ta dauki jakar makarantar ta ce wa Gwoggo da Aina sai ta dawo.
Ko tashi ba a yi ba idonta ya ishe ta da raɗaɗi ga shi tana jin kamar zazzaɓi zai rufe ta dole ta ce wa malamin ba ta da lafiya za ta gida.
Ta lallaɓo ta ta kamo hanya horn ta ji a bayan ta ba ta waiwaya ba sai ta matsa jin an ƙara danna mata shi sai ta waiwaya Abdurrashid ta gani “Shigo mu je.” muryarsa ta ratsa dodon kunnenta ta zagaya ta buɗe ta shiga sai da ta zauna ya ja motar ta ce mishi “Ina wuni? Bai amsa ba tambayar ta ya yi “Me ya samu fuskarki? Shiru ta yi daga haka shi ma bai kuma magana ba, suna isa budewa ta yi ta fita shi ma ya fito da jakarta da ta baro a motar.
Sallama kawai ya yi ya shiga gidan ma’aikatan Gwoggo su biyu ke zaune ƙarƙashin bishiya suka gaishe shi cikin girmamawa, a kofar shiga falon Gwoggo ya kuma wata sallamar ita ta amsa don tana tsaye kan Hamida wadda da shigowar ta ta zube kan two sitter ko hijab din ba ta cire ba.
“Shigo Yallabai. In ji Gwoggo ya shigo ya ce “Wai lafiya take kuwa? Ta ce “Ina fa lafiya. Ta kwashe labarin marin da malami ya yi mata ta ba shi, kai kawai yake jinjinawa bai ce komai ba daga bisani ya ce “Ku shirya Gwoggo mu je Hospital a duba ta.” ta ce “To. Bayan ita har da Aina suka fito daidai lokacin Malam Buhari ya shigo suka gaisa da Abdurrashid Gwoggo ta yi masa bayanin inda za su ya yi Allah shi kyauta tare da musu fatan dawowa lafiya.
Hamida Gwoggo ta tura ta shiga gaba suka zauna baya ita da Aina.
Babu mai magana a motar har suka isa barrak din Sojoji da ke Janguza ganin Sojoji ya sa Hamida ƙara duƙunƙunewa cikin hijabinta don a duniya ba abin da take tsoro sama da Soja ko da ya yi parking din ma sojojin ne suka zo suka buɗe, yana fitowa kuma suka sara mishi.
Hamida ta maƙale ta ƙi fitowa Gwoggo da ta san dawan garin ta matsa ta kamo ta maƙaleta ta yi ta rufe idanuwanta da taimakon Gwoggo ta riƙa takawa, Abdurrashid da ya ri ga ya yi nisa ya waiwayo don ganin suna biye da shi ai kuwa nesa ya hango su Gwoggo na rike da ita ya tsaya suka ƙaraso Yaya Gwoggo ko jikin ne? “Ai tsoron sojoji take mutumniyar taka. Gwoggo ta fadi fara’a kwance saman fuskarta, kai ya girgiza bai yi magana ba ya wuce suka cigaba da bin sa duk kuma inda ya wuce sojojin da ke shawagi sai sun sara mishi.
Da suka shiga wata Dr Maria ya tambaya a ka ce mishi ta fita ya kira ta a waya ta ce ba ta yi nisa ba ya ɗan jira ta.
Wani Office ya buɗe ya ce su shigo ya yi ma su Gwoggo tayin wurin zama kafin ya fita ya ce yana zuwa.
“Anya Gwoggo ba soja ba ne? Aina ta raɗa wa Gwoggo karaf kuma sai a kunnen Hamida ai kam ta buɗe ido rayau tana ware su cikin Office din, ganin yadda ta razana ya sa Gwoggo Indo ta ce “Kai da ƙyar dai don ni dai tunda nake wurin nan ban taba ji ba.
Abdurrashid ya dawo tare da likitar ita ma soja ce cikin faran -faran ta duba Hamida sai da wani Soja ya je ya sawo magungunan da ta rubuta suka miƙe don tafiya nan ma Hamida na maƙale jikin Gwoggo da ta ga Abdurrashid ya tsaya kawai yana duban su ta yi yar dariya “Ai wannan ban taɓa ganin me shegen tsoron sojoji da allura irinta ba, shi ya sa na gode wa Allah da ba allura da kuka za ta zauna share share tana yi mana.
Hamida sai taɓa Gwoggo take jin tonon sililin da take mata.
Da ya sauke su wucewa ya yi. A falo suka yada zango Gwoggo sai yamutsa magungunan da ta ce Aina ta kawo ruwa take “Wai sai tsurar magani kawai, ba dan abin maƙulashe da za ka saya wa budurwarka ba ta da lafiya? Ni wallahi ina ce yau sayayyar da zai mana kafin mu shigo gidan nan sai ya cika boot.” Aina ta fito da ruwan ta ba ta ta daga kan Hamida “Tashi ki sha to. Shan ta yi ta koma ta kwanta.
Cikin hukuncin Allah zuwa safiya ta yi garau fuskar ma ta rage kumburi idon ya washe, Gwoggo Indo ta ce ta bar makarantar sai ta warware zuwan Malam Adamu sai ta ba Gwoggo hakuri ita kuma gudun kar Abdurrashid ya ji ita ta hana sai ta kyale ta.
Walida sai ba ta hakuri take da aka fita break kan dukan da ta janyo mata.
Hamida dai ta girgiza kai wani yaro ya same su ya ce ana neman Hamida a Office din principal, suka fita tare da Walida sai da suka kusa isa ta tsaya ta ce za ta jira ta anan.
Sai ta ƙarasa mutum biyar ta samu cikin Office din principal da mataimakiyarsa sai Maths teacher ɗinsu sai Abdurrashid tsaye jikin bango hannayensa harde a kirji fuskarsa ba alamar ya taɓa dariya ganin wandon da ke jikinsa na Sojoji ya sa hantar cikin Hamida kaɗawa. Ta gaishe su sai ta tsuguna principal ya nemi ta faɗi abin da ya faru har teacher ɗinsu ya mare ta.
Ta fadi amma ba ta fadi waya Walida ke nuna mata ba, sai shi principal din ne ya ce “Amma mu a binciken mu waya kika zo da ita Jikinta ya ƙara daukar rawa tana girgiza kai ta ce ita ba ta zo da waya ba.
Principal ya maida duban sa ga Abdurrashid hakuri ya yi ta ba shi suna taya shi ya dubi Hamida ya ce ta je waje ta jira shi a mota.
Bayan fitar tata kuma bala’i ya yi sosai kan aka kuskura aka maimaita dukan ta ba zai tafi haka ba zai ɗauki mataki. Karatu ya turo ta ba a nemi nakasa mata ido ba.
Su dai hakuri suke ta bayar wa ya fita Office din, a jikin motar ya hango ta sai ya isa sai da ya shiga ya ce ta shigo ita ma fadan ya yi mata kan ta fara wasa da karatunta, ina wayar da a ka ce an gan ta da ita? Ta rantse masa ita ba ta da waya.
Ya sallame ta bayan ya ba ta ledoji masu ɗauke da irin sayayyar da ya yi mata kwanaki.
Lokacin da ta koma har an koma class da aka tashi Walida ta so bin ta ita dai ba ta so ba don boren da take so ta yi wa Gwoggo idan ta koma gida Allah kuma ya taimake ta Walidar ta ce ta fasa ta tuna za ta wani biki.
Da ta koma gida kamar kullum ba ta samu kowa ba sai Malam Buhari da ya shigo tana shigowa. Ta ci abinci ta yi sallah sai ta koma tsakar gida a karkashin bishiya tana tsifar kanta.
Ta yi nisa Gwoggo da Aina suka shigo ciki ciki ta yi musu sannu har sun shiga ciki Aina ta fito “Me ya faru na ga ranki a ɓace? Ta tambaye ta ƙara ɓata rai sai kuma ta fashe da kuka ganin haka Aina ta shiga yankawa Gwoggo Indo kira ta fito a ruɗe ɗankwalinta a hannu “Me ya faru? Ta tambaya sai Hamida ta kuma rushewa da kuka suka kamata suna tambayar abin da ya same ta “Ni wallahi Gwoggo kar ya ƙara zuwa wurina soja ne, ni ban son Sojoji gwoggo.”
gwoggo ta ce ta yi shiru wa ya gaya mata soja ne? ta ce yau da wandon Sojoji ya zf o makarantarmu.”
Sakinta kawai ta yi ta shiga ciki ta saɓo
mayafinta “Ki kwantar da hankalinki yanzu za ni gidan Mariya mijinta shi ke kula da shukoki a gidan Shehu Bello, ita ma shekarun baya an ce ta taɓa musu aiki ta san komai na gidan.
Ta sa kai ta bar gidan. Tsakanin su ba wani nisa sosai ta yi sa’a ta same ta ba ta daɗe da shigowa gidan ba ta je unguwa, sai da aka yi mata maraba suka gaisa Gwoggo ta ce “Wurin ki na zo Mariya wata tambaya nake son yi miki.” ta gyara zama “Allah ya sa na sani.” “Wani ƙarin haske nake nema game da gidan Shehu Bello wai tilon ɗansa soja ne? Ta yi dan murmushi “Ƙwarai likita ne amma na Sojoji. Ta gyara zama don uwar zance ce “Ai lokacin da mahaifiyarsa na raye shi Abdul ɗin ita na yi wa aiki, har garinsu Adamawa take zuwa da ni, ita ce uwar ɗakina mace mai matuƙar kirki da mutunci, rana ɗaya aka aura mishi su da Uwargidansa ta yanzu ita Allah ya ba ta Abdurrashid ita kuma Haj Mariya an ce ta dai taɓa yi ba rai.
Bayan rasuwarta aka ba shi ƙanwarta Aunty Karima da yake ƙannenta duk mata ne su biyar mahaifiyarsu ta haifa ko shi Abdul da rasuwar mahaifiyarsa kakar ta dage sai ya koma wurinta uban kuma ya kasa ba ta sai ya ce a ba shi Karima lokacin tana budurwa in yaso sai ta riƙe Abdul ɗin don ya gane ba ta gamsu da riƙon da kishiyar uwar za ta yi mishi ba, shekarun Abdul din sha biyar lokacin mafari kenan na bar aiki gidan.
Gwoggo Indo ta yi ajiyar zuciya “Allah sarki Allah ya jiƙanta, ni ma ɗazu nake ji wai soja ne, tunda nake wurin nan ban taɓa sani ba, shi ne na ce ai ko na tambayi Mariya ita ta san komai na gidan.
Goggo Indo ta miƙe. Ta ce ta tsaya don Allah a zubo mata dambu da ɗanta ya shigo yana ci, ta ce ta gode ta wuce gida.
Tana shiga falonta a sanyaye ta ajiye mayafi ganin duk sun zubo mata ido Aina da Hamida, ta isa kusa da Hamida ta zauna “Ki kwantar da hankalinki kin ji ‘yar ɗiyata ba wani abu.” “Sojan ne ko Gwoggo? Ta tambaya tana duban fuskarta don ta ga yanayin da za ta nuna.
“Likita ne na Sojoji, don haka kin ga shi ba ruwan shi da Sojoji, likita ne.
Nan dai ta yi ta mata dabara har ta haƙura.
I like reading