Sai dai ko ba komi, ta yi farin ciki, farin cikin kasancewar a yau ta san tana da wani dan matsayi a Faisal, da ya wuce na Ronke Adeyemi. Alkawari na karshe da tayi da zuciyar ta shine bazata sake yin wani abu da zai sosa ran Ya Faisal ba, tunda kuma shima bai son tayi zancen wani (wanda dama ita wasa take) to hakannan zata kari rayuwar ta single ba aure don ma kar tazo auren ransa ya baci.
Ita dai ta kasa gane irin wannan abu, ta kasa gane meke damun dukkannin su? Wannan kishin masifa kamar wasu. . .
Shukurallaki ya habibaty
Masha Allah sannu da kokari
Allah yasaka da alkhairi
Mun gode
Yaushe za mu samu na 3 din?