Skip to content
Part 25 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sai dai ko ba komi, ta yi farin ciki, farin cikin kasancewar a yau ta san tana da wani dan matsayi a Faisal, da ya wuce na Ronke Adeyemi. Alkawari na karshe da tayi da zuciyar ta shine bazata sake yin wani abu da zai sosa ran Ya Faisal ba, tunda kuma shima bai son tayi zancen wani (wanda dama ita wasa take) to hakannan zata kari rayuwar ta single ba aure don ma kar tazo auren ransa ya baci.

Ita dai ta kasa gane irin wannan abu, ta kasa gane meke damun dukkannin su? Wannan kishin masifa kamar wasu mata da miji? Suna haukane? Wai shin a duniya akwai wasu ‘ya’yan da suke Uba daya da ke wa junansu irin wannan son?

Cikin wannan dare mai kunshe da tarihin al’amura da dama cikin rayuwar su, daga Faisal har Saratu ba wanda ya rintsa sai juyi a kan gado. Tabbas son junan su ke dawainiya da zuciyoyin su yana yamutsa duk wani tunanin hankali da suka mallaka, wannan wace irin masifa ce?

Daga Faisal har Intisar ba wanda ya taba kawo wannan a ransa ko a mafarki cikin shekarun da suka gabata, sanda take Riyadh har zuwa yankewar karatun ta sai ko yanzu da Shaidan ke neman kaisu ga halaka in har basu yiwa zuciyoyin su linzami ba. To ta yaya?

Ba abinda zasu iya illa daukar gingimemen dutse su danne abinda ke neman tunkudowa daga kirjin su.

Faisal Bello, matashi ne da tashen kuruciya, gami da jin dadin da yake ciki basu sa shi watsi da Addini. Don haka cikin daren ya mike ya gabatar da nafilfili na musamman yana rokon Ubangiji daya daura mishi wannan bala’I da ya yaye mishi, yo bala’I mana? To amma me?

Tamkar ana kara iza wutar so da kaunar Saratu ne a kalbin shi. Ya durkushe bisa sallaya yayi kukan sa mai isar sa, kuka riris kaman ba namiji ba, namijin ma, Da ga Daddy Makarfi, kuka irin wanda rabon sa da yi tun wani duka da aka yi mai yana ajin karshe a sakandire  daya zanawa wata yarinya jarrabawar lissafi, sai ko yau da son Saratu-Intisar ke neman narkar mai da zuciya.

Hukunci na karshe daya yankewa kansa shine yayi nisa da Saratu, nisa ba kadan ba, wanda zai mantar da shi duk wani abu daya shafeta, tunanin ta, rayuwarta da matsayin da take da shi a zuciyar shi, ya tabbatar in har suna tare dole ne watarana  abinda suke fakewa da ‘yan uwantaka  ya bayyana zahiri ga iyaye da ‘yan uwan su da jama’ar duniyar ma bakidaya.

Duk da yasan kasancewa ba tare da Intissar din ba, na nufin rugujewar rayuwar sa gabadaya kuma wani gibi da cike shi ba zai taba yuwuwa ba. Anya zai iya? To in bai yi hakan ba yaya zai yi? Tunda gashi har Goggon su na cewa (da su  abokanen wasa ne da an musu aure), kenan ta fahimci duk fadan da suke takalar junan su duk cikin sigar SO ne? Son ma irin wanda ya fi karfin boyuwa a zuciya aka rasa yadda za’ayi da shi ya fiddo kansa kowa ya gani.

A take ya amince da shawarar da zuciyar shi ta bijiro na tafiya (Birmingham) zurfafa ilmin sa (Masters) amma shi ba zai je soja kamar yadda Daddy ke so ba, ba don komi ba sai don kada ya mutu, ko a harbe shi bai ganewa idon sa wane irin (lucky man) ne zai sami Intisar a matsayin matar aure ba.

Shi kam ina ma ba’a gidan su yake ba? Ina ma shi ba dan Daddy Makarfi ne ba? Ina ma shi dan Wa, ko kanin Daddy ne?

Tunaninnikan da yake tayi kenan marasa kai da gindi har aka yi kiran assalatu a kunnuwansa, ya mike yana layi tamkar bugagge ya sako alwalla ya shiga nafilfilin da bai san iyakar su ba yana rokon mai canza al’amura daya canza mishi da mafi kyau.

Karfe shidda dai-dai na safiyar ranar wadda ta kasance Talata, ya dauki diary din shi yayi wasu rubututtuka masu matukar muhimmanci a gareshi da Saratu, yana yi yana zubar da kwalla tamkar ba Faisal ba, ya hade duk wani abin amfanin shi da yake bukata cikin katuwar trolly ruwan bula mai duhu, ya shirya cikin suit baka da ratsin toka-toka sunyi masifar amsar shi, ya matse wuyan shi da bakin tie ya barwa al’ummar gidan (note) cewa yayi sammakon tafiya ya kama hanyar Ilorin inda yake hidimar kasa.

Tunda Faisal ya tafi Ilorin ko waya bai yiwa kowa ba har tsayin watanni ukku cif, Daddyn na yi mai cuku-cukun tafiya Unibersity of Birmingham dake UK inda zai hado MSc dinsa wata kila ma har Ph D. Admission din bai fito ba sai a watan Mayu daga can ya tafi ko sallama bai zowa kowa ba, alhalin su Najib duk suna zuwa gida a duk karshen wata.

Hajiya ta damu sosai.  A watan Najib, Bello, Yasir. Nasir da Faruk suka sami aiki a garin Enugu inda suka yi bautar kasa, aiyuka kuwa masu gwabi (tsoka), shi Najib a (Petroleum Refinery) na Enugu, Bello (mai sunan Daddy) a kanfanin Inshora, Yasir da Nasir a NITEL sai Faruk a bankin (Inland) da gidajen zama da motocin hawa da komi.

Sai gidan ya dade sai su Idris kananan dake makaranta suma basu faya zuwa ba sabida suna shekarar karshe karatun yayi masu zafi sosai.

Haka kawai Intisar ta rika jin ranta na baci kamar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? Sai da Faisal ya cika watanni ukku cif yana karatu a Birmingham Daddy ya kira Hajiya yace da ita Faisal fa ya zarce UK yin M Sc din sa, in ya ga dama bayan shekaru biyun ya dawo, in yaso kuma ya zarce har Ph D ba zai takura mishi ba.

Brigadier na girmama Faisal duk cikin ‘ya’yan sa a sabili da abubuwa guda biyu: juriya da karfin zuciya.

Faisal ne a duk cikin ‘ya’yan sa zai ce mai yayi abu yayi koda ransa baya so, sannan duk cikin ‘ya’yan sa ba mai hakuri, nutsuwa da sanyin ran Faisal, yana da daukan komi na rayuwa da sauki, (sabanin Ameenu mai zafafawa akan al’amuransa).

Don haka duk abinda Faisal din ke so yana kokarin yaga yayi mishi, in har bai fi karfin sa ba, baya son ya bata masa ko kadan kamar yadda shima yake mai biyayya da zuciya, gangar jiki da duk abinda ya mallaka yaron baya da kwaramniya ko kadan kwatankwacin su Najib, hakannan kome zai yi in ka auna sai kaga hikima a ciki, baya yin abu kai tsaye sai ya tabbatar yana da hujja na yin hakan.
Don haka ko kadan bai damu da makudan kudaden da ya narkarwa Faisal yayi M. Sc a turai ba, shi dai burin sa ya sanya shi farin ciki kamar yadda yake sanya shi a kullum

Hajiya ta gunduma ashar ji kake abu kazan uban nan…don me Daddyn bai gaya mata ba sai bayan ya tafi, kan me ba’a shawara da ita kan harkokin ‘ya’yan ta  sai kace ba ita ta haife su ba?

Ta tsuguna ta haifo dan a cikin ta a ce Saratu ce mai tsara mishi yadda take so? Yace tayi hakuri kada ta dauki hakki, Saratu bata ma sani ba balle ‘yar ta.

Faisal dai dan sa ne, kuma shi ya roke shi alfarmar baya son kowa yasan zai tafi, sai bayan ya tafin, tace ai don ya san zata hana ne shi yasa ya hana a gaya mata, duk an tarwatsa mata ‘ya’ya cikin duniya an hana mata jin dumin su, alhalin ba’a san yadda tayi ta haifo kayan ta ba, ba komi yasa Daddyn yake barin su suna tafiyar ba sai don bai son ta ji dumin abinta, yana bakin ciki don matar sa bata da su a fake da karatu, to wane irin karatu ne da bai isa a yi shi a nan cikin kasarmu da manyan jami’o’in da mu ke da su ba?

Ko su da basu yi ba karatun ba wani abu ya ragu a jikin su? Daddy Makarfi sai yayi dariya ya kamo hannun ‘yar rigimar yace

“bai ragu ba kam, amma ai gaki nan kina abu kamar rudaddiyar tsohuwa ko ni nan na fiki wayewa.”a kara kuluwa ta fige hannunta ta nufi kofa tana kunkunin Daddy ya gaya mata magana don ya nuna mata matar shi na aikin banki, har ita za’a gayawa wayewa, ita da take fita kasashen duniya saro zinarai take ciniki da matan manyan kasa bakidaya aikin kawai, ta sani dai baya shawara da ita kan harkar ‘ya’yan ta, to dai ita ce uwar su, wanna sunan (Nafi Uwar su Aminu) ba zai taba canzawa ba, kuma da tsohuwar zuma ake magani  haka duk warin daddawar, ita ta gyara miyar (tana nufin  ita da bata yi karatun ba, ita ce ta tallafi gidan a sanda aka garkame shi a kurkuku ba masu karatun bokon ba), fiye da wannan ma matsayin ta na mahaifiyar su ya dace a dinga neman yardarta  kamin zartar da komi a kan su koda karatun ne. 

Shi kansa Daddy ya san ya bata mata kuma tana da ‘yar gaskiyar ta sai yayi ta lallashin ta, yana nuna mata menene don Faisal ya tafi Turai? Ita da kullum take hantara da kyarar shi ai jin dadin ta ne, sai tayi murmushi ta huce, ta fi kowa farin ciki.

Tafiyar Faisal… na nufin al’amura masu muhimmanci a gareta, tafiyar Faisal… na nufin farin cikin ta, farin ciki ba daya ba, ba biyu ba hakannan ba uku ba, tafiyar Faisal… na nufin cikar dadadden burin ta.

Ko ba komi, Intisar za tayi bakin ciki, watakila har yayi sanadiyyar katse duk wani farin cikin rayuwar da take ciki a yanzu. Ita ko mai farin ciki ce da duk wani bakin cikin su Saratu a rayuwa.

Saratu da Saratu zasu daina amfana da dan ta, zasu daina morar sa wanda wannan ba karamin nakasu bane ga rayuwar Intisar kuma cigaba ga wani specific (kayyadaddden) kudurin ta a gaba, wanda bai wuce na raba Saratu Da Saratu da duk wani farin ciki dake cikin rayuwar duniya.

Sai tayi murmushi ta sawa abun albarka, tace da Daddy Allah yasa kada shi ya mancesu, ya guje su ya nisancesu tamkar Al’ameen.

Daga Intisar har Antin ta sun ji tafiyar Faisal ne kamar daga sama. A falo Anti Saratu tayi ta kakabin abin Intisar na jin ta bata ce komi ba, hakannan bata juyo ba domin a lokacin tana wasa ne da kwamfutar antin tana ‘game’ din ‘Mabis Beacon’. Ashe wannan shine trauma din da take sunsune tun watannin baya; Rabuwa Da Ya Faisal!

Idon ta suka yi rau-rau sai kwalla suka zubo masu zafin gaske, tasa bayan hannun ta ta share da sauri don kar Anti ta gani. Antin ta zauna shirim, cikin ‘leather seat’ din da suka yiwa falon kawanya tace

“Saratu shine ko ki gaya mun Yayan naki zai tafi Birmingham?”

Da Antin ta san kunci da tukukin dake nukurkusar zuciyar wannan baiwar Allah, hakika da bata yi mata wannan tambayar ba, amma Anti ce, bai yiwuwa ta kyaleta duk yadda taso yin hakan, duk kuma irin rashin son maganarta a lokacin, tace

“Mamar mu babu abinda zan iya boye miki, in da ya gaya min zai tafi, abinda na sani kawai shine brother is in love (yana cikin soyayya) amma yace wai ba zai taba iya auren yarinyar ba, nake jin abinda yasa ya bar gida kenan.

Amma ni ce shaidar cewa Ya Faisal ya tsani karatu ‘abroad (kasar waje)”.

Anti tayi jugum, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar tafiyar Faisal ya taba zuciyar ta, fiye da zaton Hajiya, ya takaita farin cikinta, fiye da yadda Hajiyar ta kintata a zuciyar ta, ta ce,

“Oh ni Saratu! Ban da abun Faisal maiyasa ba zai fadi ba, sai ya bar kasar? Bana jin ko diyar wanene a garin nan da Babanku ba zai iya aura mishi ba. Allah to ya sa hakan shine mafi alkhairi.”

Da daddare tayi shirin kwanciyar barci kamar yadda ta saba amma me? Idanuwanta sun ce basu san wannan ba. Tayi kukan ta mai isar ta, da ta kasa gane musabbabin sa.

Ba zata ce son Faisal take ba, don bata san ma hakikanin menene son ba.  Amma da tayi tsam da ranta ta fahimci kishin yarinyar da ta sa Faisal barin Nijeriya ne!

Haushin tafiyar sa ya shafe kewar sa, mafi rinjaye shine irin matukar sabon da su kai da juna.

Akwai wani kebantaccen al’amari game da Faisal a tare da ita, da ita kanta bata san menene ba. Abinda zata iya cewa shine Faisal, wani mutum ne precious wato (mai darajja) da kima agareta da muhimmancin sa da kimar sa ya zarta na kowa in ka dauke Daddy da Mamarta. Kenan mancewa da shi a tarihin rayuwar ta ko barin tunanin sa, wani abu ne da ba zai taba kasancewa ba!!!

Mu karasa a littafi na uku, Takorin ku ce.Wa billahi taufeek!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 24Siradin Rayuwa 26 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×