Safiyar yau zaune nake kan kujera ina wanke-wake, yayin da Adawiyya kuma ke shara tsakar gida bayan kammala wankin bayi da tayi, can gefe kuma Inna Zulai ce tana lissafa mafitai da take sayarwa, sai Gwaggona da ke kai da komowa zuwa madafa kasancewar yauma girki a hannunta yake. Inna Amarya kuwa na ɗaki bata fito ba, dan dama ita uwar ɗaka ce da wuya ka ganta a waje, in dai ba wai ranar girkinta ba ko kuma ya kasance duka iyalan gidan ana zaune a tsakar gida. Baba ne ya fito daga ɗakinsa yana gyara zaman hularsa yake. . .