Skip to content
Part 13 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Shiri mai martaba ke yi sosai babu kama hannun yaro, bikin shalelensa Aliyu haydar ne kawai ya sa gaba yanzu baki ɗaya masarautar Jordhan ta ɗauka, Gobe juma’a da misalin ƙarfe biyu ake ɗaura masa aure.

Tafe yake cikin izza da ƙasaita ƙarasowa, ɓangarensa ya yi, da sauri guards suka shiga gaida shi, cikin hanzari suka matsa mishi hanya ya shiga. Zaune ya tarar da Aaliya ta ƙura wa Tv ido, amma gaba ɗaya ta tafi duniyar tunani. harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana kallonta, fuskarta ta yi fayau jikinsa duk ya yi sanyi gaba ɗaya bata da saƙat, a ƴan kwanakin nan idan har ba barci zata yi ba, ko da yaushe idanuwanta manne da glass.

Wani irin kyau ta yi mishi, sosai dan dama tana da wani irin sihirtaccen kyau mai nutsuwa tare da fisgar zuciya, madaidaicin hancinta ne ya yi matuƙar ɗaukar hankalin shi, da kuma lips ɗinta, ganin hannunta na motsi ya sanya shi saurin janye idanuwansa a kanta, yana jin haushin kansa me yasa ma zai tsaya kallon wata mace haka.

Ba tare da ya yi sallama ko, magana ba ya ƙarasa ya zauna kujerar dake fuskantar tata, sake tamƙe face ɗinshi ya yi, A natse ya dube ta ganin har lokacin bata cikin natsuwarta, tafa hannayensa ya yi da ɗan ƙarfi, Afirgice ta dawo cikin hayyacinta, wurga idanuwanta ta yi kan kyakkyawar fuskarsa da bata gajiya da kallonta, sosai ta ƙura masa idanu tana kallonsa, wani irin shauƙi na fizgarta. ta ma manta da wata damuwar da take ciki.

Gyaran muryar da ya yi ne ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta ƙasa, Invitation cards ne ya miƙo, ya ɗaura da cewa”Ga katin ɗaurin Aurenmu nan, idan Allah ya kaimu gobe misalin ƙarfe biyu za a ɗaura mana aure, ki zama matata..!” cikin sanyin jiki ta amsa masa da to, dan tun bayan da ya zo tambayarta cikakken sunanta ta bai sake dawowa ba. tun jiyan sai yau dan tana ganin kamar ta ɓata mishi rai akan cewa da r yi bata san sunan mahaifinta b, kuma ita bata san wani ɗaura aure ba, imfact ma a koda yaushe tana ƙoƙarin tuna wasu abubuwa, dan Tana ji a jikinta ta manta wasu abubuwa, masu matuƙar muhimmanci a rayuwarta, amma sam ta gaza tuno komai, idan ta tsananta tunani kana ne kawai ke ciwo.

Ƙarar wata ƴar ƙaraurawa ce ta katse mata tunanin da take yi, idonta ta kai kanshi waya ce hannushi yana daddannawa hankali kwanche tamkar bai ji ƙarar ƙaraurawar ba.

Kusan mintuna Goma da faruwar hakan, tun lokacin da aka nemi ison ba a bada ba kuyangar Sarauniya A’isha ta koma ɓangarenta, ta sanar da ita dan dama a faɗa mata da zarar ta nemi ison ta ji shuru, ta dawo ta sanar da ita in yaso ita ta kira Haydar ɗin.

Ɗaukar waya Ammah ta yi, ta dannawa Yarima Aliyu haydar kira, yana ganin Call ɗin ya yi picking ya kara a kunne, ba tare da ya ce komai ba.

A ɗayan ‘bangaren gyaran murya ta yi mishi, sannan ta ce, “Ina son ganinka kai da Aaliyah!.” tana gama faɗar haka ta yi rejecting call ɗin. Slowly ya miƙe ya fara tafiya, a hankali ya motsa laɓɓansa tare da faɗin, “Ammah na son ganinmu, biyoni”. Miƙewa ta yi cikin sanyin jiki ta ɗauki mayafin da ke a jiye ta yafa har kanta kamar yanda ta saba, ta rufe rabin fuskarta.
Gabaɗaya komai cikin sanyi take yin shi, saɓanin da. cikin zafin nama take aiwatar da abu sannan tana da izza sosai da kwarjini, amma yanzu ta zama shiru sosai ba umh ba A’a, komai cikin sanyin jiki take yin shi, tamkar ba Gimbiya Aaliyah ba, komai ya sauya mata, kallo ɗaya zaka yi mata ta baka tausayi.

Tun da suka shigo Parlourn take faman lumshe idanuwa, dan sosai daddaɗan ƙamshin da ke tashi a ɗakin ya burgeta kuma ya samar mata da natsuwa, Jakadiyar Ammah ce ta iso inda suke fuskarta cike da fara’a hannuwana ɗauke da faffaɗan tray, dire shi ta yi gabansu sannan ta duƙar da kanta ta ce “Yarima sarauniya na nan tafe, amma ta ce na isar da saƙo gare ka, zaka iya tafiya Gimbiya ce dama take buƙatar gani” ɗaga kai kawai ya yi bai ce komai ba, ya miƙe ya fice.

Ba ta jima ba ta jiyo takun Ammah, cikin nutsuwa ta iso inda Aaliyah take fuskarta cike da Annuri, rungumar juna suka yi ko wanne na sauke ajiyar zuciya. Zaunar da ita Ammah ta yi ta fuskance ta sosai, Har lokacin bata daina sakar mata kyakkyawan murmushi ba.

“Aaliyah!!.” ta kira sunanta, tana kuma tattara dukan natsuwarta gare ta, Cikin sassanyar murya ta amsa, “Na’am Ammah” kamo hannayenta ta yi fuskarta da alamun damuwa kaɗan, ‘Kina Son Aleeyu haydar”? Ba ƙaramar girgiza ta yi ba jin tambayar da ta yi mata, ita bata san wani so ba ma gaba ɗaya.

Ganin ta yi shiru ne ya sanya Amma ɗan taɓa ta kaɗan, Ajiyar zuciya ta sauke baki ɗaya kunya ta kama ta, magana Ammah ta fara mata cikin ƴar damuwa…”Duk da ban san Ainahinki ba kuma ban san daga wace nahiya kika fito ba ina kyautata miki zaton kyawawan ɗabi’u, yana yinki ya burge ni sosai baki da gurɓataccen hali, a iya lurar da na yi cikin waɗannan kwanakin, ina son jin shin ina ƴan’uwanki, kuma kina son ALEEYU HAYDAR? sannan ina son faɗa miki maganganu da dama dangane da wannan masarautar”.

Hawaye ne suka cika idanuwanta, jikinta ya yi sanyi sosai, ganin haka ya sa Ammah shiga cikin yanayin damuwa, “Ki yi haƙuri Ƴ’ata ban san ba zaki ji daɗin tambayar ba shi ke nan, ki yi shiru. kin ji”? da sauri ta girgiza kanta ta ce “Ban sani ba, Ammah ina ji a jikina na manta waɗansu abubuwa masu matuƙar muhimmanci a rayuwata! na kasa tuna komai a koda yaushe ina cikin tunanin Asalina, abu ɗaya na iya tunawa Aaliyah shi ne sunana, bayan haka ban san komai ba…” fashewa ta yi da kuka tana sheshsheka, rarrashinta Ammah take yi, itama baki ɗaya jikinta ya yi sanyi tausayinta ya cika mata zuciya.

Juice mai sanyi ta tsiyaya mata a cup wanda jakadiya ta kawo musu, bayan ta sha ne Ammah ta jata zuwa parlournta, zaunar da ita ta yi cikin dubara take mata bayanai akan Aure da yanda addinin musulunci ya tsara aure, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi zuciyarta ta yi rauni ta kuma ji tana kwaɗayin Addinin.

A GURGUJE…A wannan ranar Aliyu ya sa an gyara ɗayan ɗakin dake ɓangarensa, ya ƙawatu sosai an anan ciki Aaliya zata tare. Ammah ta saka an wanke gashinta anyi mishi gyara na musamman, sai ƙamshi yake yi, uwa uba ga ƙunshin da hannayenta da ƙafafuwanta suka sha, ta haɗu iya haɗuwa ba zaka taɓa iya gane ta ba idan ba farin sani kayi mata ba, Ammah ta gyara ta sosai ta yi mata gyaran jiki sosai abunta ta yi fes gwanin burgewa, ko ina jikinta sai tashin ƙamshi yake…

MANAAJ
Zaune Sanaam take gaban Sarauniya Sarah tana bata magani, yanzu Alhamdulillah jikin ya ɗan yi sauƙi, Me martaba na a gefensu. Sanaam ya umarta da ta kira mishi mai isar a saƙo yama son ya yiwa Ƴan masarutar NAHAAR muhimmin gargaɗi akan abun da Rahash ta tako ta zo ta aikata. Da ƙyar sanaam ta samu ya yi haƙuri, dan ya ɗauki zafi sosai, ficewa ta yi daga ɓangaren bayan ta shawo kanshi.


RAHASH-FIRAISH
Sun tattauna sosai dangane da abun da yake buƙata, ta yi alƙawarin kawo mishi Aaliyah, daga ƙarshe sun Yanke hukuncin sanya wata ƙwayar cuta da zata haifar da annoba ga MAYUN ƙasar.

A babban magudanar ruwan na ƙasar baki ɗaya da yake chan bayan wani tsauni, Ƙwayar cutar zata narke cikin ruwan, ta bi ko wane ruwa da yake ƙasar, cutar zata gauraye ko’ina sannan duk wanda ya yi amfani da ruwan, zai samu ƙarfin iko ya kasance ba shi ke sarrafa ƙwaƙwalwarshi ba, Ba ko wane wani ƙarfin sihiri zai yi aiki ga mayun ba, zasu samu linkin ba linkin ɗin ƙarfinsu.

Ko wane maye zai fara kisan gilla ƘASAR YALAAZ zata rikice da kashe-kashen juna babu wanda zai iya dakatar da hakan, sai LAILAH! Idan kuma ana buƙatar hakan Aaliyah zata ziyarce ta.

Bayan gama wannan shirin sun yanke hukuncin Saka ƙwayar cutar tsakiyar dare, dan kafin gari ya waye komai zai baiyyana, dan haka Aaliya zata bincika ta kuma kawo kanta cikin sauƙi, garesu.

DARE!!
Tafiya sarauniya Halsha suke yi, ita da Tazaan cikin mugun daren, wata doguwar kibiya ce golden colour, ke tafiya kan iska suna bin bayan kibiyar, abun da zai baka mamaki, sam babu alamun wani babu abun da kake ji face kukan tsuntsaye, tafiya suka yi ba ta wasa ba har suka fara doso wani daji, in da suke saka sn za a samu masaniya, dangane da sarƙar da zata kaika izuwa tekun jazaal.

SAHASH-KUNJAM
Tafiya suke yi bisa doki ɗaya, Sahash ce farko sai sarauniya kunjam, gudu suke yi na fitar hankali, duk inda suka bari wata muguwar ƙura ke tashi, Gudu ne suke faman yi ba na wasa ba, wasu bukkoki suka fara wucewa, da dogayen itace, kukan tsuntsaye da na wasu ƙananun halittu sai tashi ya ke, gaba ɗaya duhu ne gurin amma duk da haka tafiyar tasu bata tsaya ba, Wani guri mai kama da ƙorama suka fara hangowa, an kunna wuta tana ci sosai da itace, fau fau wutar ke fallatsi.

Ja suka yi, suka tsaya nesa da wutar kaɗan sannan suka sauko, daga bisa dokin juyawa suka yi da baya baya, suka fara takawa izuwa inda ɗumin wutar mai zafin gaske ke matuƙar ratsa gurin, kawunansa a ƙasa suka isa inda wani ƙaton halitta ke zaune kansa a ƙasa idanuwansa a rufe, ya miƙe ƙafafuwansa, hannayensa ma ya miƙe su saman iska.

Wata kalar dariya ya fara mai rikitar da ƙwaƙwalwa, wawakeken bakinsa, na fitar da hayaƙi, dariyar da ya ke yi ta isa ta sanya zuciyar Bil’adama bugawa, cikin ƙanƙanin lokaci, gaba ɗaya gurin amsawa yake yi da sautin dariyarsa mai tsananin firgitarwa.
Lokaci ɗaya ya dakata da dariyar ya ɗaure fuska jikinsa ya fara, tsatstsagewa hayaƙi na fitowa, ya ɗaure fuskarsa tamau, wata gigitacciyar tsawa ya daka musu ta hanyar faɗin “Ku ƙaraso!” jiki na ɓari suka ƙarasa suka zauna, cikin ɗarɗar sarauniya Kunjam ta buɗe baki zata yi magana, da ƙer ta iya fesar da numfashi tsabar ruɗu, wasu kalar idanuwa ne da shi ya buɗe farrr haske ya bayyana golden ɗin ƙwayar idonsa ce ta yi matuƙar Razanar da su fiye da tunanin mai tunani.

Da wata kalar Rikitacciyar muryarsa ya soma magana, ƙasar gurin har girgiza take, “Ba sai kun faɗi me ke tafe daku ba, na sani. domin son cikar burinku akwai buƙatar kawo jinin yarinyar”. da sauri suka shiga jinjina kai, kafin cikin tsawa ya ce ‘Ku je ku kawo yanzu, a gabatar da aiki….!” Yana ƙarasa maganar ya bugi ƙasar gurin, sarauniya da Sahash suka ɓace ɓat, dariya ya fara babu ƙaƙƙautawa.

FIRAISH-RAHASH
Tsaye suke bayan wani ƙaton tsauni, daga ita har Firaish ko wannensu sanye yake da tufafin da aka yi da fatar kare, wani ƙaramin ƙoƙo ne hannunsa, yana hura mashi iska. Rufe idanuwanshi ya yi ya fara karanto wasu irin dalasimai, da ƙarfin gaske kamar haka, ‘SAFFAR, SAFFAR, DAFFAR, DAFFAR, MAFFAR, RAFFAR!!.’ haka yake ta ambato tare da kuma kalaman tsafinsu, Iska ce ta fara kaɗawa da ƙarfin gaske dunƙullen hayaƙi ya fara taruwa, ƙasar gurin ta soma rugurgutse, tsuntsaye suka soma tashi sama da kukansu.

Wani ƙaton aljanni ya baiyana gabansu da wata kalar suffa mai tsoratarwa, zubewa ƙasa suka yi alamun ban girma, dagon yatsansa ya sanya da ya kai girman ƙafafun sarauniya Rahash, ƙoƙo ya miƙo masa cike da girmamawa shi kuma ya karɓe shi, daga hannunshi ya ɓace…

ALEEYERH.
Cikin barci ta soma ganin Sanaam cikin wani irin hali tana kiran sunanta, da ƙer muryarta ke fita tsananin wahaltuwa, Tsoho Arar kwanche gefe an soke da wuƙa a saitin zuciyarshi, jini na fita daga jikinsa, idanuwansa sun lumshe, da ƙyar ya fitar da numfashi.

Gefe ɗaya kuma sarauniya Saraah mahaifiyarta ce ke kiran sunanta, bakinta na fitar da jini, fuskarta ta yi jajir, fatar jikinta kamar ta ƙone, ”Aaleeyah! Aaleeyah!! YALAAZ muna buƙatar taimakonki, Ke ce zaki iya dakatar da faruwar…,” ba ta ƙarasa ba aka ɓalle ƴar’kofar karan da suke ciki, MAYU ne suka soma shigowa a jere ko wane jikinsa ya chanza fuskarshi ta saɓule, bakinsu jaɓa-jaɓa da jini, kafin su yi wani yunƙuri mayun sun daddaɓe su, da ƙarfi Suke furta, ‘Aleeyerh!!..’

A gigice ta farka daga barcin, ta saka dukkan hannayenta ta dafe kanta, jikinta sai tsuma yake, a jik’e sharkaf da zufa.

YALAAZ
Babban bala’in da suka fara fuskanta,,,duk wani maye da ya yi amfani da ruwan sai ya juye ya fito, ya fara farmakar ɗauwansa.

Masarautun sun rikice Annobar ta addabi kowa, tashin hankalin da sanaam ta shiga Babu wanda ya san adadinshi. jikinta ya yi wani irin sanyi zuciyarta ta karye.

Fadawa, hadimai, bayi ko wanne ya rikiɗe ya zama kamar HORROR! ga wani baƙin hayaƙi da ke fitowa daga madubin ɗakinta, Cikin kerma ta shirya ta ɗauki madubinta.

Baiyana ta yi a bukkar TSOHO ARAR kwance ta tarar da shi, wuƙa soke a gefen zuciyarsa, bukkar tasa kamar an ƙona ta, komai kacha kacha, da gudu ta ƙarasa inda ya ke. kuka sosai ta fara tana jijjiga shi baki ɗaya jikinshi ya tsattsage jini na zuba ta hanci da baki.
Cikin wata irin raunatacciyar murya da bata fita, sabo da tsantsar azaba ya ce “Kiiii…je, ki nemo Aaleeyah…,!!” banko ƙofar da Horror ɗin mayin suka yi ne, suka dunfaro su cikin zafin nama, hakan ya sanya ta soma ja da baya jiki na rawa.

<< Sirrina 11Sirrina 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×