Cikin sheshshek’ar kuka Maryam ta ce “Hajiya fa fushi take yi dani, yanzu idan na gudu zata kuma jin haushi na.”
Hannu biyu Abba ya d’aura a kansa, kafin yace “O my God!! Maryam da wanne yare kike so in yi miki bayani ne?? Ko bayan auren ki da Usman zata ci gaba da jin haushin ki ne, in dai kika auri Usman to kun yi ta janyo fad’a kenan a tsakanin iyayenku har azo a lalata zumuncin…”
A hankali ya matso kusa da ita yace “Nace miki kar ki duba kowa yanzu, just ki duba mu. . .