Skip to content
Part 16 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Cikin sheshshek’ar kuka Maryam ta ce “Hajiya fa fushi take yi dani, yanzu idan na gudu zata kuma jin haushi na.”

Hannu biyu Abba ya d’aura a kansa, kafin yace “O my God!! Maryam da wanne yare kike so in yi miki bayani ne?? Ko bayan auren ki da Usman zata ci gaba da jin haushin ki ne, in dai kika auri Usman to kun yi ta janyo fad’a kenan a tsakanin iyayenku har azo a lalata zumuncin…”

A hankali ya matso kusa da ita yace “Nace miki kar ki duba kowa yanzu, just ki duba mu biyu kawai, and trust me! Please Maryam, this is the right thing to do…”

Cikin share hawaye tace “Abbana fa?”

“Abban ki ya riga ya zab’a miki ni, so Abbanki ba zai ji haushin komai ba, this is his choice Maryama. Itama Hajiyan blackmailing d’inta aka yi, sannan kunyan Baaba Talatu take ji shiyasa amman da zarar mun yi aure idan taga kina cikin farin ciki tuni zata manta da komai! Burin ko wacce uwa taga farin cikin Y’arta. Maryam i assure you Usman cannot give you the happiness you deserve!.” Ya k’arashe maganar kamar zai fashe da kuka..

Shiru, tayi tana tunani. Tabbas duk abinda Abba ya fad’a haka ne sannan ta yarda dashi d’ari bisa d’ari!

Cikin katse mata tunani a hankali taji yace “mu je, idan komai ya d’an lafa na yi miki alk’awari zamu dawo mu bawa su Hajiya hak’uri, na san zata hak’ura in sha Allah. Abba kuwa na san shi kam farin ciki ma zai yi, dan mun yi abunda ake k’ok’arin hanasa, wanda hakan shine zab’in shi.”

Na tabbatar idan mijin Innarku ya zo ba zai bari a d’aura aurenmu ba, kuma Inna da kanta kin ji tace ba zata tab’a bari muyi aure ba, wanda na tabbatar Abba ba zai tab’a iya shallake umarnin su ba.”

Cike da gamsuwa da maganganunsa Maryam ta hau d’aga kai alamar amincewa kafin ta ce, “Amman zamu dawo anjima mu gansu, ko iya Abba ne shi kad’ai, na san ya san yadda zai yi ya lallab’a Hajiya Shuwa watakila ta hak’ura, ka yi mini wannan alk’awarin?”.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce “Nayi miki! Amman nima kiyi mini alk’awari idan mun gama ganinsu, anjiman zamu wuce, saboda ina so in yin nesa da mahaifina ko da na wata d’aya ne. Ba zan iya fuskantar shi a yanzu ba, dan ban san hukuncin da zai yanke mini ba.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Na yarda!.”

A hankali ya ce “Ahamdulillah”sannan ya juya ya bud’e mata gaban mota.

Har ta wuce ta shiga, ta zauna sai kuma ta juyo ta kalle shi, yana shirin rufe mata k’ofar ta ce “Abba, kana ganin ba matsala?” Murmushi yayi sannan ya ce “Yes Maryam, in shaa Allah, just trust me please..”

“Na yi, amma dan Allah kar ka sa in yi da na sani” Murmushi ya yi yace “i promise, I won’t!”.

Sai da ya juyo ya shiga, ya tada motar tukunna idanunta suka sauk’a akan Sadiya wadda take tsaye a k’ofar gidansu gabad’aya hankalinta yana a kansu.

Tafiya mai d’an nisa sukayi dan Maryam kam kanta har ya juye abunka da wadda bata fita sosai, tana cikin y’an kalle-kallenta suka iso wani tafkeken masallaci a d’an gaba kad’an akwai hotel.

Wuce masallacin suka yi ya shiga cikin hotel d’in wanda ya gaji da had’uwa ga securities ta koina, ya nemi waje yayi parking.

Babu yadda bai yi da ita akan ta fito ta shiga cikin hotel d’in saboda shi yana so ya je ya samu limamin yayi mishi bayanin komai, kuma akwai y’an shirye-shiryen da yake so ya fara so zai kama mata d’aki ita d’aya shi kuma ya fara preparations amman tak’i tace “ita a mota zata jiras hi har yaje ya dawo”, haka nan ba yadda ya iya ya kunna mata AC ya bata mukullin ya kwashi abubuwan da zai buk’ata.

Sai da yaje wajen Limamin suka tattauna sannan ya fito ya tari motar haya ya shiga aikin gabanshi.

Sai wajajen 12 tukunna ya dawo Maryam har tayi bacci ta tashi ga tsoro ga yunwa, yana zuwa ya kwankwasa, da kyar ta iya bud’e k’ofar ya shigo mata da abinci sannan yace bara yaje yayi Sallah idan an idar zai zo su wuce.

Haka kuwa aka yi sai wajen 2:00pm. Time d’in masallacin kowa an watse tukunna ya dawo.

Yana zuwa ya sa key sannan ya umarce ta da ta koma baya, bayan ta koma ya tada motar yaja suka isa bakin masallaci.

Wani dattijo cikin alkyabba da rawani suka tsaya suka d’auka a bakin masallacin sannan suka hau titi, basu yi wani tafiya mai nisa ba suka gangara kan hanya suka shiga wani layi, a bakin wani gida suka yi horn aka bud’e gate d’in suka shiga. Bayan sunyi parking sun fito Dattijon ya nuna musu babban parlourn gidan yace wa mai gadi “ya kai su gurin Hajiya” Shi kuma ya nufi parlourn bak’i dan yana da bak’i.

Matar mai kirki sosai bayan sun gaisa ta dinga yi musu hira aka kawo musu abinci kala-kala, Maryam kam fitsari ne yake neman yi mata illa ga Abba a wajen balle ta ce zata yi fitsari, Allah ya taimaketa matar ta shiga tambayarta “ko tayi sallah?” Da sauri ta mik’e tana cewa “a’a”

Nan ta nuna mata d’aki ta shiga, sai da tayi sallah tukunna ta fito suna cikin cin abinci wannan dattijon ya shigo.

Sake gaisawa suka yi kafin ya juya ga matar tashi ya ce ne “Yakubu ne k’anin Yahaya, kin ganesa ai ko” Da mamaki matar take kallonshi, nan ta hau yi mishi tsiya tana cewa “baya ziyara.”

Gyaran muryar da dattijon ya yi ne ya katse su, sannan ya kalli Abba ya ce “nayi waya da Yahaya yanzu ya tabbatar mini da abunda ka fad’a min d’azu, ya ce tare kuka je dashi jiya. Amman ni da zaku bi ta shawarata da ko Mahaifinta ko wani d’an uwanta a samu a wajen tukunna, ina ganin hakan zai fi, ko?”.

A hankali cikin girmamawa Abba ya hau yi mishi bayanin komai, sai a yanzu matar take fahimtar ba amarya da ango bane ba yet.

Bayan ya kai aya ne dattijon ya sauk’e ajiyar zuciya sannan cike da gamsuwa da zancen nasa ya ce “ai shikenan!! In dai maza sun riga sun gama magana batun mata ba biye shi ake yi ba.”

Bai gama rufe baki ba wasu magidanta responsible su uku suka shigo, d’auke da huhunan goro da packs d’in alawowi.

Zama d’ayan ya yi sannan ya ce “Akaramakallahu barka da rana ga sak’on da kace in taho dashi nan.” Amsashi yayi sannan yayi mishi nuni da su ajjiye.

Bayan sun ajjiye an gaggaisa anan yake shaida musu “Aure za a d’aura, za su yi shaida”. Nan suka amince.
Limaminne ya umarci Yakubu da “ya kawo sadaki.” Kamar jira yake, nan ya zaro dubu talatin a aljihun shi, a take aka gudanar da duk abunda ya kamata, Yakubu ya yiwa kanshi wakili, limamin nan kuma ya yiwa Maryama.

A take a falon aka d’aura auren Ykubu Umar Farouk Mai Turare Da Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu talatin.

Aka raba goro da alaawa a y’an falon sannan aka kwashe ragowar domin rabawa In an fita masallaci dan har an fara kiraye-kirayen sallar la’asar.

A gidan suka yi har sallar Magriba, matar mai kirki tanata nan nan da Maryam, ita dai Maryam Alla-Alla take su tafi dan ta k’agu su koma gida, duk da yadda gabanta ke ta fad’uwa amman dai tana so taje ta tunkare su a tura ta k’are!.

Suna idar da Sallar Magrib d’in wani Yaro ya shigo d’akin da alamun d’an matar ne ya ce “wai ance Maryam ta fito zasu tafi.”

Ai kuwa zumbur!! Haka ta mik’e har matar har tana tsokanarta, ita dai tayi mata godiya ta kimtsa suka fito tare da matar.

Y’ar guntuwar nasiha mai ratsa jiki Limamin nan ya yi musu sannan yai musu fatan alkhairi suka mik’e suka yiwa juna sallama suka nufi k’ofar fita daga parlourn.

Abba ne a gaba sai Maryam wadda ke bi mishi baya bumper to bumper, goshi da k’irjinta ne taji sun bugu da gadon bayan shi sakamakon burkin da ya jaa ya tsaya chak! Lokaci guda, yak’i ya yi gaba yak’i yayi baya.

Daga yadda yake tsaye za ka iya ganin yadda jikinsa yake karkarwa sannan duk ya rikice tashi d’aya!

Magana yake son yi amman sai ya hau in ina sam ya gagara furta ko da kalma d’aya mai ma’ana.

Bata dawo daga mamakin abinda ya firgita Abba haka lokaci d’aya ba taji an d’auke shi da wani mahaukaciin marin da saida ya kai ga kaiwa k’asa ya tsugunna a gurin.

Tsugunnawar da yayi ne ya bata damar ganin mutumin da yake gaban su ya tare k’ofar, kana ganinshi ba sai an fad’a maka ba ka san shine Mahaifin Abba, dogo ne sosai fari k’al kyakkyawa yana mugun kama da Abba da Yayanshi da suka zo tare jiya, sai dai shi ya d’an manyanta, kana gansinshi kaga tsohon dattijo.

Muryarshi ce ta dawo da ita daga nazarin data tafi jin ya daka wata uwar tsawa yana cewa “Out of my way! stupid boy!!!”.

Maryam ba da ita ake ba amman da sauri ta matsa ta koma bayan matar gidan da itama duk ta rikice ta b’uya.

Shima Abba da sauri ya tashi ya matsa yana shafa marin da aka yi mishi.

Cike da k’asaita mahaifin nasu ya k’araso cikin parlourn yayan Abba da wasu maza biyu suna binshi a baya, sai kuma wani Yaro matashi da kayan sojoji a jikinshi.

Kujera inda wannan Limamin yake tsaye ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya, ko takalmin shi bai cire ba haka ya shigo mishi tsarkakakken falon da shi.

A hankali limamin ya d’an zauna akan tumtum d’in kan kafet sannan yace
“Barka da dare Daddie!”. Batare da ya amsa shi ba ya ce “Did u just got them married??.”

Cike da kwarin guiwa ya ce mishi “Na’aam.” Gyara zaman shi ya yi ya fuskance shi da kyau kafin ya ce
“D’ahiru you know I can sue you right??”. Wannan karon murmushi Limamin ya yi, kafin ya ce “A tsarinka zaka iya suing d’ina, amman a musulunce ba zaka iya ba, dan Yahaya ma magabacin shine, dan haka kuwa kaga ba zaka iya suing d’i na ba!.

Baya ga haka, Abba iya shi kad’ai ya isa yiwa kanshi wakili…”

“I’ll get back to you later.”Shine kawai abinda Granpa ya ce dashi cikin katse shi, sannan ya mik’e ya isa gaban Abba ya tsaya.

Hannunshi ya mik’a baya alamun yana so a mik’o mishi wani abun, da sauri Daniel ya zaro wasu takardu da international passport ya mik’o mishi.

Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya ce “Abba, d’azu da Dahiru ya kira Yayanku muna tare! Jiya na bawa Yayan naka sak’o nace ya fad’a maka, ashe bai gaya maka ba, right?”

Bai jira jin amsar shi ba ya cigaba “I’m really disappointed in you, and bana so inyi punishing d’inka harshly which is why I’m doing this…Take this!”

Yayi maganar yana mai mik’a mishi passport d’in hannun shi.

Jiki a mace Abba yasa hannu ya karb’a, passport d’inshi ne da wasu takardun da bai gama dubawa ya gano na menene ba muryar Mahaifin nashi tasa ya maida hankalin shi gareshi jin yana cewa,

“Ga passport d’inka, nayi k’ok’ari wajen ganin na had’a har da na amaryar taka in yi muku tare, amman sai na fahimci ita d’in y’ar gidan talakawa ce bata tab’a fita koina ba, so wannan aikin kane yanzu za ka yishi, tunda kaika kwaso ta. Na baka 5 hours ka bar k’asar nan! Ba na son ganin ka…ba zan iya zama a country d’aya da kai ba. Abba ko labari idan ka ji zanje k’asar da kake, to ka tabbatar ka bar wajen ko kuma duk yadda zaka yi to ka tabbata ba mu had’u ba. I don’t think zan iya yafe maka laifin da kayi min sannan ba na son in yi punishing naka harshly kuma na san indai Ina ganin fuskarka ko kuma kana kusa dani to tabbas zan yi maka abunda ba zaka tab’a mantawa ba. So, as you can see I’m doing my very best to stay calm! All I want from u shine ‘wannan ya zama last time da idona zai ga naka!! You want freedom right? Kana so kayi abinda kake so ka auri wadda kake so ko? Well, Abba ga freedom nan! I’m giving it to you. Idan ka kuskura muka had’u, ko kak’i barin k’asar nan, u pretty much know wat I’m capable of! Dan wallahi i promise sai nayi making life d’inka a living hell!! Ka yi addua In iya yafe abinda kayi mini kafin in mutu, maybe I can forgive and call u back.”

Har ya juya zai fita, sai kuma ya dawo ya zo inda su Maryam suke ya tsaya, cikin kakkausar murya yace “Maryam!” Maryam jikinta har tsuma yake yi, cikin sake b’oyewa a bayan matar liman kamar zai daketa ne, tace “Naa ‘aa mm.” Cike da tsana yake kallonta kafin yace “D’a na kikeso ko?

A kanshi kika bar iyayenki kika gudo kika aure ko? Well congratulations to you, da shigowa familyn MT! But let me assure you! Wallahi karnukan family d’ina sai sun fiki daraja! Sannan ko bayan raina ban amince Y’ay’anki suyi bearing family name d’ina ba

Kuma ina so ki sani, zan iya yafewa Abba kamar yadda na fad’a amman ke kam ni da ke karki kuskura ki bari muga juna suma kuma Y’ay’anki haka, ba na so su zo ko kusa da inda nake ma talkless of mu had’u da su. Idan kika kiyaye wannan watak’ilan ki zauna lafiya, idan kuwa baki kiyaye ba to kinga mahaifinki da mahaifiyarki da wannan k’anwar taki, I’ll make sure na kullesu a prison d’in da ko kusa dashi baki isa zuwa ba ballantana ma kiyi tunanin fito dasu, this is my promise to you!!”

Yana gama fad’in haka ya bawa Daniel umarnin ‘ya kai Maryam da Abba suyi preparations d’in tafiya sannan ya ajjiye su a airport, within 5 hours!’. Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, yana mai yiwa Limamin alk’awarin dawowa idan ya samu lokacinshi, dan ba zai barshi haka ba wallahi!

Kuka Maryam ta dinga yi kamar ranta zai fita. Tsoro gaba d’aya duk ya rufeta!! Tayaya za a ce babu ita babu family d’in Mijinta wadanda sune garkuwar y’ay’anta?? Da wanne dangin y’ay’anta za suyi tutiya idan sun taso? dan ba a ado da dangi d’aya!

Daman Abba ya san haka mahaifinshi yake amman shine bai sanar mata ba?? Tukunnan ma taya za a fara tunanin barin ta k’asar nan har abada?? Dan in har lissafinta ya bata daidai ana nufin ita da Abban zasu tafi.

Wadannan al’amura da tunanin ne suka kuma hargitsa ta, ta dinga rusa kuka ko sauraronsu Abba da suke ta bata hak’uri bata yi… Daniel ne ya d’an rankwafo kan Abba yayi gyaran murya sannan ya nuna mishi agogon hannunshi, harararshi Abban yayi sannan ya mik’e ya fita Daniel d’in yabi bayan shi suka hau shirye shirye gadan-gadan.

Bai sha wahalar yi mata passport ba, daman yana da k’aramin hotonta daya cira a file tun suna makaranta, amman da aka zo kan visa ba k’aramin wahala ya sha ba, duk inda yaje ‘embassy’s d’in Kano’ sai ace visar gari dole sai mutum ya jira. Da kyar ya samu Yayanshi ya kulashi dan shima duk ya tsorace kar Mahaifin nasu ya juyo kanshi. Nacin da Abban ya dinga yi masa ne yasa ya amsa wayar da cook d’in gidan yake ta rok’on shi ya karb’a, yana karb’a Abba ya kwararo mishi abubuwan da yake da buk’ata.
Da kyar da taimakon sa da taimakon kuma wani baban Abokinsa Maryam ta samu visiting visar Madina, amman shima sai nan da 7 days jirgin zai tashi kuma a Lagos, gashi sauran 1 hour 5 hours d’in da aka bashi ya cika.

Da sauri ya shiga nema musu wani ticket d’in daga Kano zuwa Lagos. Aka yi sa’a kuwa ya samu da wuri, zai tashi in the next 20 minutes, a lokacin sauran 15 minutes time d’in da Mahaifinsa ya basu ya cika.

A gurguje suka samu suka k’araso gidan Limamin shi da Daniel wanda yake ta binshi a baya yana nuna mishi agogo duk bayan minti talatin, Abba ji yake kamar ya shek’e sa amman kuma sanin da yayi ba laifinshi bane shima saka shi akayi kuma bai isa ya hukuntashiba yasa kawai ya rabu da shi.

Yana shigowa a gurguje suka had’u da Limam suka nufi d’akin da Maryam take.

Ai anan kuwa ta birkice!! Ta dinga kuka tace “wallahi babu inda zata je, idan ma zata tafi tou sai taje taga su Shuwa tayi musu sallama sun saka mata albarka.”

Tabbas sun san ta fisu gaskiya ata koina amman zuwa unguwar su Shuwa ma kad’ai sai ya d’auki minti ashiri bare dawowa, nan kuwa suna kusa sosai da airport. Daga Liman har Abba hadda ma matar Liman d’in duk sun rikice rok’on Maryam kawai suke suna lallab’ata suna mata nasiha akan tayi hak’uri ta bi mijinta su tafi watarana sa dawo, amman fur tak’i!!.

Daniel ne yayi knocking ya shigo, har Abba zai yi mishi masifa dan ya ishesa! Sai yaga ya mik’o mishi envelope. Sai da yasa hannu ya karb’a sannan Daniel d’in yace “driver d’in Daddie ne ya kawo yanzun nan yace wai a baka.”

Jikin Abba har rawa yake yi haka yasa hannu ya zaro takardar ya fara karantawa.

“Sauran minti goma jirginku ya tashi, yanzu munzo wucewa na sake ganin motar Daniel a k’ofar gidan Liman, which means baka tafi ba and still kuna ma gidan, jirginku zai tashi in the next 10 minutes, I know maybe nan da 7 minutes zaku iya isa airport, which means zaku k’ara 2 minutes akan time d’ina. Already daman d’azu mun tafi da motarka, tunda ni na siya maka!

Kayanka da credentials d’inka da Yahaya ya had’a maka suna boot d’in motar Daniel. Ina umartarka da ka bawa Daniel atms d’inka da komai na kadara ya taho mini da su. If u like ku ci gaba da wasting time, and I’ll not hasitate to keep punishing u. Ina sane da duk wani single movement d’inka.”

Kawai gani sukayi Abba ya durk’usa a gaban Maryam ya kama hannayenta duka biyu ya fashe da kuka, cikin kukan yake rok’onta yana “Dan Allah dan Annabi Maryama ki tashi mu tafi yanzu shine abu mafi amfani, duk tirjiyarki a k’arshe tafiya zamu yi. Wannan b’ata lokacin da muke yi baki san abubuwan da kike janyo mini ba, zamu dawo idan nayi settling I promise!!!”

Kuka yake yi kamar k’aramin Yaro, hakan yasa Liman shima ya ci gaba da lallab’ata tare da yi mata zazzafar nasiha mai ratsa jiki. Jikinta duk yayi sanyi hakan yasa tace “zata tafi amman sai yayi mata alk’awarin zasu dawo very soon, kuma hadda su Liman za aje a bawa su Shuwa hak’uri.”

Duk suka amince hakan yasa suka mik’e da sauri suka yi hanyar fita, su Liman suna ta binsu da fatan alkhairi haka suka shiga mota suka tafi, sai sauri suke yi, dan tuni lokaci yayi.! Allah ne ma ya taimakemusu aka d’an samu delay da tuni sunyi missing flight d’insu. A gurguje ya had’a duk wani abun da Granpa yace ya bada.

Ya bawa Daniel d’in ya ce “ya bashi” sannan suka hau layi.

Sai da Daniel ya tabbatar yaga tashin girjinsu tukunna ya juya ya koma mota ya nufi gida
da tunani barkatai a ransa.

       

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 15So Da Buri 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×