Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta, ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita!
“Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine.
Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa! Ta kasa tab’uka komai banda hawaye. . .