Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta! Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya.
Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana. Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama. A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you. . .