Skip to content
Part 41 of 71 in the Series So Da Buri by Bulama

Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta! Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya.

Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana. Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama. A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi” Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama.

Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’aga ta, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.”

Da sauri ta d’ago tana goge hawayen da suka k’i tsayawa, da kyar kuwa ta tsaidasu, ta d’an harari Sakina tana murmushi sannan juya tace “ina wuni Mama, ya jikin ki?”

Da murmushi Maman tace, “Alhamdulillah”

Sannan Huda ta juya ta gaida Ummu, wadda itama ta amsa mata cikin kulawa sannan tabce “ya mutanen gidan naku?” A hankali Huda tayi k’asa da kanta tace, “Alhamdulillah”

Sakina ce ta ce “a estate d’in kike? Family house d’in nasu kamar estate ne kowa da kowa ko?”

Numfashi Hudan ta fesar tukun tace “Eh, nan aka kaini da farko, amman yanzu dani da Abba da Daddy da Ya Auwal mun tashi mun koma wani gida a baya. Saboda Granpa ya ce ‘Abba sai dai ya zab’a, ko ni ko su!’.”

Cikin mutuwar jiki Sakina ta ce “shi ne ya zab’e ki kuka tashi?”

Da “eh” ta amsa, kafin ta ce “Har da d’an uwan shi ‘Daddy’ shima muka tashi, sun yi fad’a sosai jiya da Granpa d’in.” Tana shirin sake yin magana Mama ta ce, “Kuka tashi as in how??
To ai yayi ta banza ne, dan ke kam kin zo kenan!! Ya aka yi kika fito? D’azu su Kaka suke gaya mana kalar rashin kunyar da ya yi musu ai! Yanzu haka takardun shiga kotu ake had’awa!…”

Cikin rashin jin dad’i Ummu tace “Mama dan Allah ki daina biyewa su Abba Modu kina k’ara tunzura su!
Kina ji fa bawan Allahn nan har gidansu ya bari, saboda ita!

Ko fa anje kotun nan na fad’a miki bamu da nasara saboda kamar yadda Abba Madun yace d’an uwanshi( Daddy) ya fad’a musu d’azu ‘ko a iya case d’in Baba aka tsaya dole a bashi Hudan!!’ Ballantana kuma idan aka duba yanayin standard of living! Shi (Abba) yana da aikin da zai iya kula da ita ke kuma.” Shiru Ummu tayi ta kasa k’arasawa ganin yanda Maman ta kafeta da idanuwa. Cikin jan numfashi Maman ta ce “Ki k’arasa mana! Ni kuma ba ni da aikin yi, bani da komai ko?.” Sai kuma tace “Bari kiji idan su sun yi amfani da Baba to ni kuma zan yi musu amfani da Granpa! Ai har gara Baba shi bai tab’a korar Huda a gidanshi ba, Granpa fa?” Cikin katseta Ummu ta ce “Amman ai yanzu ko me Granpa yake ji dashi bai isa yayi mata ba! Saboda Abban ma ya d’auketa a kusan shi gabad’aya! Dan haka Kotu ba zata duba wannan bama a matsayin reliable.”

Cikin d’an fad’a Mama ta ce “Wai Ummu kina nufin in barta kenan a wajenshi ko me kike son gaya min?”

Cikin kwantar da murya Ummu tace “ba nufi na kenan ba, ki fahimceni Dan Allah… Maganar shiga kotun ne bana so saboda idan anje mune za muji kunya! Kuma In dai Abba yaga anbashi custody d’inta gaba ld’aya to fa ba lalle ya dinga barinta tana zuwa mana ba!

Mama, Hudan y’a mace ce! Makaranta ma zata shiga yanzu university wanda idan kika kwantar da hankalinki ma wata rana a wajenki za tayi Hutun ta! A hankali a hanakali zaki ga zata iya dawowa wajenki gabad’aya wata rana.
Abunda nake so dake shine yanzu ki barshi (Abba) Zafin zuciya ne kawai yake damunshi. Ni a nawa ganin banga amfanin a shiga kotu anata kace nace ba k’arshe kuma na san mu ne da kunya! Kuma Hudan aure zata yi
nan ba da dad’ewa ba, daga k’arshe fa dole ta bar gabanku gabad’aya daga ke har shi. Dan Allah Mama ki fahimceni ki tayani fahimtar da su Kaka.”

Cikin tsananin b’acin rai Maman tace
“Eh!! Ai shiyasa ya turo mata da Arshaad, kuma abunda basu sani ba na riga na gama yanke hukunci ‘In shi kad’ai ne Namiji a duniya to Hudan ba zata auresa ba!’ Wai wanne irin rainin wayo ne ma wannan Abba yake yi wanda kika kasa fahimta??? Kina gani fa yadda muka taso muka sha wahalar rayuwa tare, bai tab’a ko da lek’en ta ba, sai yanzu data zama mutum tukunna shine zai nuna ya santa? Ina ce daa cewa yayi ‘kar ma in fad’a mata sunan shi?’.”

Dafe kai Ummu ta yi tana shirin yin magana Huda tace “Mama da gaske yake tun ranar anan ya fad’a miki ‘bai san da ni ba!’ Kuma da gaske yake.”

Cikin jin haushi Mama tace “k’arya yakeyi!! Na fad’a na sake maimaitawa ‘k’arya yake yi!’ Kin ji mai uba! To nuna min shine ya haife ki kinji Huda, hakan yayi kyau! Wato d’an kwana biyun da kika yi tare dasu har an juya miki tunani akaina ko? Bilkisu kinga irinta ko? Ina kuma ga in na barta ta zauna dasu gabad’aya? Hudan fa ita kad’ai Allah ya ba ni, amman kalli mugu Abba abinda yayi a cikin kwana biyu kawai!!.” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka.

Da sauri Hudan ta hau lallashinta sannan ta fara basu labarin yadda aka yi da Mom da su Ummi da Mammy, har cell d’in da suke ciki a yanzu.

Ummu wani sanyi da proud na Abba take ji, kuma ta sake amincewa zai kula da Huda iya iyawar shi kuma zai yi duk iyakar bakin k’ok’arin shi wajen bata kariya.

Amman wani abun mamaki furr!! Mama tak’i amincewa da zancen tace “Makirci ne suka k’ulla da shi da y’an uwan sa, aka yi komai a gaban Huda dan ta yarda dashi asa ta juya mata baya!” Ba Ummu ba hatta Sakina da Huda da basu da shekaru sosai, sai da suka tsorata da lamarin Mama, ga gaskiya nan ana nuna mata amman ta kafe! Tak’i ji taki gani.. Ummu har ce mata tayi “zata je suyi maganar fahimta ita da Abba, ba sai anje kotu ba! Kawai Huda za ta dinga sati sati a hannunsu, har Allah ya kawo mata miji tayi aure Ma’aana taje Gandu tayi sati d’aya sai ta koma Nasarawa tayi sati daga nan ta sake dawowa Gandu, haka dai.”

Amman nan ma furr!! Mama nace akan ‘attakafur!! Ita sai dai a bata Huda gabad’aya!’ K’arshema cewa tayi “idan Ummun ba zata tsaya mata ba ta daina yi mata kwana kwana kawai ta fito fili ta fad’a! Ta samu ta fara neman wani lawyer d’in, tun kafin lokaci ya k’ure mata.” Da jin hakan ne yasa Ummu taja bakinta tayi shiru bata sake cewa komai ba! Daga nan shiru ya wanzu a wajen.

Hudan ce ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “Ya Jalila ma tana gidan”
Da sauri duk suka zuba mata idanu. Cikin In Ina tace, “Ciki ne ma da ita”
A firgice Sakina ta rafka salati haka ma Ummu, Mama kuwa daman ta riga ta Sani, amman abunda ya bata mamaki shine ‘me take yi a gidan su Abba’.

Ummu ce tace “Me take yi kuma a gidan?”

Shiruuu, Hudan tayi, bata san daliliba amman sai ta kasa ce musu cikin na Arshaad ne kawai tace “itama bata sani ba” Tana goge wani hawaye mai zafi daya zubo mata ba tare data bari sun gani ba, kafin ta k’ara da cewa “A gidansu Ya Auwal dai ta ganta, kuma yanzu da suka tashi, Ya Auwal d’in ya kaita wajen Gwaggo Asabe.”

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace “Sadiya ta cuci Yarinyar nan har abada wallahi…” Cikin sanyin murya Huda tace, “Ummu nace mata ta kwantar da hankalinta zan nema mata mafita, ya za ayi yanzu? Dan wallahi naji tausayinta..”

Da sauri Mama ta ce, “Wacce mafitar za ki nema mata?? Me ye naki a cikin lamarin ciki, iye?” Ta k’arashe maganar cikin fad’a! Sannan taci gaba
“Kin san Allah Huda babu ruwan ki a cikin lamarin nan, mafita Sadiya ta nema mata, wannan maganar tafi k’arfin ki kar inji kar in gani! Ballanta a tsunduma ki a cikin lamarin a yi miki bak’in fenti ke daman mai bak’in jini a idonsu…”

Hawayen Hudan ne ya k’aru, ta sa hannu ta shiga gogewa. Ita kad’ai ta san kalar tuk’uk’in da zuciyarta take yi mata, kawai tunowa da lamarin cikin da tayi and tana mamakin masifar da Maman nata ta koya.”

Ummu ce tace mata “kin dai ji ko Huda? Ki bita da addua kawai, Sadiya ta fiki sanin kalar taimakon da zata yi mata, ba ruwan ki! Dan yanzu za a goga miki fenti taki sai tafi ta kowa tsami!” Cikin katseta Mama tace
“Ai gashi irin tarbiyyar Abban da kuke magana akai!! Yanzu kamar Hudan har tana shiga lamarin ciki tana alk’awarin zata nemawa mutum mafita sai ka ce wata nurse??!”

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace “Ki kwantar da hankalinki, ai taji abunda muka ce mata ko Huda?
Besides ai basa tare ma yanzu, naji tace tana wajen Gwaggo Asabe ko?
Wacece Gwaggo Asaben?”

Nan Hudan tace “k’anwar Mommy ce” Sannan ta basu labarin halin da Mommyn take ciki. Kaf a labaran da Huda tazo da su na Mommy ne kawai ya girgiza Mama. Ta ji ba dad’i sosai, gashi ta san matar sun d’an saba dan haka tayi ta jimami, ga shima Aslam wanda dukda kalar rashin kirkin da yayi mata ranar amman har yanzu tana jinsa har cikin ranta.

Kamar ance ta kalli wayar Sakina da message ya shigo yanzu ta d’anyi haske! Wayar na nan akan cinyarta don haka ta samu damar ganin time
Mamakine ya kamata dan har ta shafe wajen awa d’aya da minti ashirin a wajen. Cikin k’arfin hali ta d’an kwanta a jikin Maman, bayan kamar minti uku ta mik’e ta cewa Sakina “tazo ta rakata taje tayi fitsari.”

Kamar kuwa Mama ta sani dan tashi d’aya ta fara k’ok’arin mik’ewa tace “bari ta rakata da kanta!”

Da kyar Ummu ta lallab’ata, ta hak’ura ta koma ta zauna. Daga nan Sakina ta gyara mayafinta suka rik’e hannu suka yi gaba. Har suka fita daga wajen tana d’an juyowa tana satar kallon inda su Maman suke tun kafin suje waje ta fashe da kuka mara sauti suna fita harabar asibitin ta sake shi mai sauti ya fito, da sauri Sakina wadda tun d’azu take ta ce mata “ba fa nan bane hanyar toilet d’in” amman tayi mata shiru sai janta kawai take yi
ta ce “Lafiya Huda mai ya faru kuma?”

Waige waige ta hau yi, chaan ta hango motar Abba da suka yi parking d’azu! Daman bata yi tunanin zai tafi ba.
Bata b’oyewa Sakina ba, nan ta fad’a mata komai akan yadda suka shirya da Abban nata.

D’an k’ura mata ido Sakina tayi…Chaan! Tace “yanzu sai yaushe kuma?
Anyways kinga dai 30 minutes ya baki yanzu kuwa kin kusan awa d’aya ma. Ki kunna wayarki kawai za muyi magana. Mai yasa kika kashe ko kwacewa aka yi?”

A hankali tace “Charger ne babu.
Amman d’azu na siya a online an kawo har na ma jona Ina so ya cika ne kafin In kunna.”

“Ok za muyi waya muje in rakaki”

Hannun ta Hudan ta ruk’o kafin tace “Sakina kina ganin Mama ba zata ji haushina ba? Me za kice mata idan kin koma ciki?”

Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e sannan tace “Haushin ki kam za taji, ba d’aya bama kuwa! Kuma yau Allah yasa ta bar Ummu ta rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!.

Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.” Rau rau Huda tayi da idanu.

A hankali Sakina tayi murmushi tace
“Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?”

A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina, daidai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen.

Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshi ba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye.

Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu
(wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai! Har gidansa ma suka je suka yi mishi godiya. Yana ta yaba alkhairin mutumin, shiyasa da Arshaad ya rok’e sa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’.
Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba don yaga sun san mutunci
kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a daidaita komai! Amma Arshaad ya ce
baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal .
Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban…To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in tukun a samu a daidai sai shi kuma Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!)

Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta. Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa, kallon Abban take yi tana sake maimaitawa! Tana ji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin!
Duk da cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai.. Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai nuna tsufa ba kamar dai Mama, Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba.

Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”.

Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan suka yi exchanging numbers suka yiwa juna sallama.

Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta.

Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan tasan yadda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata.

Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi.

Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai, har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos. Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i dangin su ice cream da milk shake da pizza.

A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.”

Godiya tayi masa, daga nan suka kama hanya, yana ta d’an janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park” Kamar zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai. A haka suka karasa gida.

Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.”

Kamar yadda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a
Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take! Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu. Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi, duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba! Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka. Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina
Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gabad’aya dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayi shi gobe!.
Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta.

Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?”
“Eh” ta bata amsa. “Waye ya mayar da ke?” “Abba” ta sake bata amsa. “Daman tare kuka zo?” “Eh!”

“Tam! Sai da safe.”

Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran.

A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba!
K’arshema dena shiga tayi. Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi, kiran sallar farko ta farka.

Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah. Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu.
Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya! Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe. Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e. Tana bud’ewa taga ashe ragowar kayantane na jiya aka kawo/ Cikin girmamawa maid d’in ta gaidata sanann ta hau shigo mata da kayan leda leda. Godiya Huda tayi mata bayan ta gama, ta juya ta fita. Ita kuma ta tura k’ofar taja kayan zuwa bedroom.

Tana gama ajjiyewa a closet
ta fito kenan ta zauna akan gado Abba ya shigo cikin jallabiya mai k’aramin hannu rik’e da hannun Sudais wanda shima yake sanye cikin kayan bacci.
Da sauri Sudais d’in yazo ya rungumeta sannan yace “Abba just told us that you are our big sister, i’m so glad that we’ve a big sister” Ya k’arashe maganar yana sake hugging d’inta.

Murmushi tayi itama tayi hugging nashi back kafin tace “I’m so glad to have cute brothers too.”

Da sauri ya d’ago ya ce “Monday idan anje school zan gayawa Ashraf da Sultan da Kareem nima nayi big sister, dariya suke yi min kullum suna tsokanata! Yanzu kema ki ce Abba ya kaiki school d’inmu a sakaki a ss2 dan Allah so that i can come and see you during break time just like they do, and also…” Abba ne ya dafa kanshi yana dariya, kafin yace “Sudais wai har yanzu baka san ka girma ba?
Ya kamata fa ace ka daina wannan shirmen And Big sis ta gama secondary ai, kar kayi mata adduar komawa baya mana. School d’in su Aaima zata tafi, ko?” Yayi maganar yana kallonta yana murmushi. D’an zamowa tayi ta gaida shi, a hankali ya amsa yana mai dafa kanta yana kallon idonta da tashi d’aya ya fahimci ta ci kuka.

A kan Kujerar gefen gadon ya zauna yana kallonta kafin yace “Me ya saki kuka? Mama kike son sake gani?”.
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “ina jin ba dad’i ne akan abunda nayi mata jiya, Ummu ta kira ni nace mata mun dawo, inaga haushi suka ji dan I’ve been calling them since last night amman ba wanda ya amsa.”
Ta k’arashe maganar tana sakin kuka.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “A kawo miki Sakina? Ku zauna tare?” Da sauri ta d’ago tana kallonshi, sai kuma ta hau d’aga kai tana share hawayenta.

Murmushi yayi kafin ya ce “Ok, but no more crying, in ba haka ba in fasa.”
Da sauri ta cigaba da goge hawayenta, da kyar kuwa ta samu suka tsaya.

Abba bai kira Baban Sakina ba sai da ya sakata tayi murmushi kala uku! Sudais yana taya shi da yi mata cakulkuli.

Bayan sun gaisa ya tambaye shi akan “Dan Allah ya bar Sakina ta zo ta d’anyi kwana biyu da su tunda basu fara school ba yanzun, maybe Hudan ta d’an sake in ta ganta.”

Nauyi da kunyar Abban ne suka hana shi yi masa musu dan haka yace “yanzu an sallami Mama ne suna kwashe kaya, amma zuwa anjima in shaa Allah zai kawota. Ya tura mishi adress kawai.” Godiya yayi sannan ya kashe wayar, ya tura mishi da adress d’in.

Yaji dad’in yadda ta saki ranta sosai.
Cikin murna ta tambaye shi “me zata dafa?” Murmushi kawai yayi yace mata “koma me ne in ta dafa yayi”

Kafin ya tambayeta adress d’in su Sakina, tayi mishi kwatance,
daga nan suka fita shi da Sudais.

Wanka tayi ta sa wani silk gown, A shape, colour d’in emerald green, an d’anyi kwalliya ta k’asan k’irjin da igiya mai stones ya zagaye, daga gefe ta gaban an tufkeshi yayi kmr ribbon babba. Bai matsetaba kuma bai yi mata ruwa ba dai dai jikinta, tayi
masifar yin kyau, ta gyara gashinta ta tufke a k’eyarta sannan ta d’auko d’ankwali kayan ta nad’a wanda kasancewarshi k’arami, yasa ta d’anyi normal d’aurin kai dashi ta kuma bi da edges d’in dankwalin ta kan gashin data tufke ta sake zagayewa da shi d’ankwalin. Sannan ta d’auki turare ta fesa duk a cikin kayan da tayi order jiya. Tayi kyau sosai kuwa abunta.

Wayarta ta d’auko ta kira Ummu still bata d’auka ba, Sakina kuma a kashe.
Jiki a mace haka ta sauk’a ta shiga kitchen.

Ga mamakinta har an gama breakfast, maid d’in jiya da wani shima da uniform a jikinsa irin nata (maid d’in),
Sun gama hada komai, kuloli wajen uku, kitchen d’in sai tashin k’amshi yake yi. Sai da ta k’araso tsakiyar kitchen d’in tukunna suka lura da ita, kamar zasu kifa haka suka hau gaidata cikin girmamawa. Ita kam kunya da mamaki ma da kyar suka barta ta amsa.

Ta riga tayi niyyar yiwa Abba girki shiyasa ta tambaye su me suka dafa?
To dai d’ayan abincin ita kam ba ma ta sanshi ba kuma bata tab’a ganinshi ba ma, sai shawarma a d’ayan kulan, farfesun kayan ciki kuma a d’ayan, sai ruwan zafi a flask ga mai buk’ata.
A hankali cikin nutsuwarta ta k’arasa ta bud’e inda suka nuna mata a matsayin store d’in ta shiga. Babu abinda babu a ciki, dan haka ta d’auko, dankali kad’an da kwai da Mayonnais da su albasa sai su green beans da
macaroni. Sun so su tayata aikin amman tak’i, da kanta ta had’a mishi potatoe salad mai d’ankaran dad’i da kyau! A dining d’in taje ta ajjiye bayan ta juye a cooler.

Tana shirin barin wajen Auwal ya shigo. Suna had’a ido da shi ya b’ata rai! Fuskarnan tamau haka ya nufo dinning d’in.

ita dai Huda ta lura kwata kwata wannan baya k’aunarta ya tsaneta!
A hankali ta gaidashi amman kamar wanda take magana da dutse ko kallon inda take bai yi ba! Kujera kawai yaja ya zauna ya hau had’a tea.

D’aga sagaggun k’afafunta tayi ta fara takawa don barin wajen daidai Abba yana sauk’owa, bata ma lura dashi ba sai da ta kusan tsakiyan falon suka yi kicib’is! Murmushi yayi ya dafa kanta sannan ya ce “har an gama girkin?”

Itama murmushin ta mayar mishi tace
“Eh” “Ok, mu je.” Ya ce sannan ya kama hannunta suka juya.

Suna zuwa Auwal ya mik’e ya gaidashi, cikin kulawa Abban ya amsa mishi sannan ya cewa Huda “kun gaisa da yayan naki?” A hankali ta d’aga kai alamar ‘eh’ Harararta yayi sannan yace “Daddy ne yace kuzo muyi breakfast.”

“Ok” Abban yace sannan ya cewa Huda taje taga ko su Shuraim sun gama shiryawa. Har ta juya taji yace
“Ina abincin da kika dafa?” Da sauri taje ta d’auko kular ta mik’a mishi, karb’a yayi sannan ya mik’awa Auwal yace masa “fara yin gaba da wannan, gamu nan zuwa.”

A k’afar bene ta had’u da Yaran dan haka suka juya tare.

Suna k’arasowa parlourn suma suka wuce side d’in Daddy.

Ita dai tana mamakin tou wanchan uban abincin, da aka dafa musu waye zai ci!? Kasa hak’ura tayi ta cewa Abban “Ko ta koma ta d’auko kulolin chan, masu aikin fa sun yi girki”.

Murmushi yayi ya ce mata “Karta damu anjima da yamma idan anyi na sadaka za a had’a a kai tare da wanchan d’in.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 40So Da Buri 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×