Cikin nutsuwa ta shirya ta d’auki y’ar k’aramar jaka da wayarta ta fito.
Bata samu Abba a wanann parlourn ba! Dan haka ta sauk’a chan k’asa cikin nutsuwarta.
Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi shi da Sudais wanda shima har ya shirya da alamun ita yake jira.
Har ta sauk’o Abba bai lura ba, yana nan ya dulmiya duniyar tunani, surutun Sudais ne ya d’an dawo da hankalinshi parlourn, daidai nan kamar had’in baki Auwal ya shigo.
Riga da wando ne a jikinshi, rigar maroon mai dogon hannu da black jeans asalin crazy!
Ga wani had’add’en takalmi sau ciki mai mugun kyau black!
D’azu uban gashi ne a kanshi amman yanzu yayi sabon aski an aske gefe da gefe da k’eyar an bar tsakiyan (saman kan) lallausar sumar ta taru a kanannade iya tsakiya sai shek’i take yi, gefe wajen kunnenshi na dama ta sama inda aka aske an sake bi anyi wani style kamar zigzag, asalin farar fatar kan nashi ta baiyyana ta fito da design d’in radau!!
Ga wani bracelet kamar sark’a a hannun daman shi, sannan ya maka wani arnen bak’in glass mai shek’i wanda kana gani kasan mai mugun tsada ne.
Yana shigowa k’amshin turaren shi ya gauraye ko ina. Tafe yake yana danna waya, har ya k’araso cikin parlourn bai ma lura da su Abban ba.
Da Hudan ya fara lura kasancewar ta a tsaye sai kuma sudais wanda ya k’arasa wajenshi da sauri ya ce “Ya Auwal har da wannan wajen nan zaka kai mu ko? Wanda ake sa glass ayi game..”
Dariya yayi ya d’an sa hannunshi akanshi ya hautsina y’ar sumar data d’an tarar mishi ba sosai ba sannan ya ce “Ashe yau za asha ihu kenan”.
Dariya dukkansu suka yi, sannan ya dago ya kalli Huda. Three quarter riga mai fad’i ce a jikinta wadda ta wuce mata har gaba da guiwowinta peach colour, sai pencil trouser white, ta yi mopling da white vail, sai y’a k’aramar white bag d’inta.
Kwalli kad’ai ne a idonta sai d’an pink d’in jam baki data shafa amman tayi masifar kyau! A ranshi yace “Yarinyar akwai kyau kamar aljana” sai dai shi ko sau d’aya bata tab’a burgeshi ba, asalima shi haushin ta yake ji! Ko dan ita tayi sanadiyyar zuwan su Mom da Mammy cell ne, oho!
Duk da ba wani shiri yake yi da Mom d’in tashi ba amman yayi mugun jin zafin abunda aka yi musu ata dalilin y’ar k’aramar Yarinya.
Gyaran muryar da Abba yayi ne ya katse mishi tunani. Bai ma lura da shi ba, sai yanzun.
“Abba ashe kana nan.” Ya fad’a yana d’an murmushi.
A b’angaren Abba kuwa yada yaga ya kafe mishi y’a da ido ne ya sanya yaji kamar ya ce su fasa fitar! Ajiyar zuciya ya sauk’e yayi saurin kawar da tunanin daga zuciyarshi, sannan ya sake kallon Auwal d’in ya ce “Kallo d’aya tak! Duk wani mai isheshen hankali zai yi maka ya fara yi maka zargin gudowa kayi daga gidan mahaukata! Kalli wandon ka kamar wanda aka yi maka gorin kaya, kalla nan” Abban ya mik’e yana nuna mishi wandon da hannunsa kafin ya ce “har cinyarka ana iya hangowa!
Wannan d’an iskan askin shi kuma an hana ka amman naga abun naka gaba yake yi dan na yau ma yafi na kullum! Sai ka ce wani zakara. Harda sark’a a hannu!! Wai ni Auwal mai kake son ka zama ne? Eh??” Ya yi mishi tambayar cikin b’acin rai, bai jira jin amsar shi ba yace “Wallahi ka tabbar ka saisaita wannan d’an iskan askin kafin ku dawo gidan nan inba haka ba kowa sai ya ji kanmu!”
Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ranshi a b’ace. Gabad’aya In ka kalli Auwal ba za ka tab’a kiran shi da musulmi ba, ba abunda yafi b’ata mishi rai kamar sark’ar hannun shi ya lura harda wata sark’a a wuyan shi wadda ta b’uya a cikin rigar kawai shiru yayi masa dan in yaci gaba da kulashi zuciya zata jashi ya fella mishi mari!! Anyi maganan anyi har an gaji amman saboda ya raina mutane sam bai fasa ba.
Auwal kuwa kamar ya had’iye zuciya.
Tunda Abba ya fara fad’a ya had’e rai! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin tijarar da Abban yayi mishi a gaban Yara, don haka ya ja hannun Sudais suka fice ba tare da yabi ta kan Hudan ba. Ganin da tayi ranshi ne a b’ace yasa kawai ta bishi wajen, bata biye sa ba.
Sudais yasa a gaba, amman dake Yaron ya fishi hankali yana ganin Hudan ta taho ya bud’e mata motar shi yayi saurin tsallakawa baya. Kamar zai yi magana sai kuma kawai yayi shiru.
Ko ida rufe murfin motar bata yi ba ya fige ta da azabar gudu. Daman masu gadin tun da suka hango shi ya tada mota suka wangale gate, gudun kar garin saurin bud’ewa idan ya taho yayi gaba da wani! In kuma kayi jinkiri a balbaleka da zage zage! Komin tsufan mutum.
Gudu yake shatatawa kamar zai tashi sama. Hudan duk ta tsure, ta rik’e kujeran da take kai gam! Ta k’ame, yana lura da ita wanda hakan ne ma ya sa ya sake k’arfin gudun nashi.
Ikon Allah ne kawai ya kaisu inda za suje, ita ba sanin munjibur park d’in tayi ba, shiyasa bata gane inda suke ba!
“Fito” Ya ce, yana k’ok’arin bud’e motar ya fita. Sudais ma ya fito daga baya. Tana fitowa tun kafin ta rufe motar gabanta yayi mugun fad’uwa ganin su a police station. Juyowa ta yi tana kallon shi wanda zagayowar shi kenan kafin tayi magana ya ce “Slsu Mom zan nuna miki, halin da suke ciki all because of you! Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta wucewa jikinta sai karkarwa yake yi.
Direct wajen da suke ya nufa, bayan ya amsa gaisuwar police d’in da suka tarar a reception, sannan ya zaunar da Sudais a kan kujerun wajen yace mishi “kar ya kuskura ya tashi, ya jira su a nan”.
Da kyar ta iya k’arasawa wajen!
Tun daga lokacin jikinta ya mutu, yayi wani irin sanyi.
Da kyar ta iya bud’e baki ta gaishe su amman ba wadda ta amsa mata tsakanin Mammy da Mom, Ummi ce wadda take mugun jin jiki ta d’ago da ta kalle ta a hankali ta ce “Lafiya Alhamdulillah.” Sannan ta komar da kanta k’asa ta kwantar.
Wata jakar leda wadda ya shigo da ita yayi saurin mik’a musu, ganin wani police ya taho yasa Mammy tayi saurin b’oyewa a cikin mayafinta, sannan ta ce, “Ka cewa Arshaad inata jiranshi akan maganar mu naji shiru!!
Shekaran jiya da na samu waya nayi mishi more than 20 miss calls amman bai d’auka ba k’arshema kashe wayar yayi! Ka ce nace dan ubanshi shi nake jira in kuma ba zai iya ba to ya daina kashe mini waya kawai ya fito fili ya fad’a min!!”
Hudan kamar ta ce mata ‘ba kashe wayar yayi ba’ don tana gani kamar wannan number da tayi ta kira ranar nan da wayar tana a hannunta ne Mammy take magana akai! Sanann sub’ucewa wayar tayi a hannunta ta fashe. Amman kuma kawai sai tayi shiru ganin yadda ko inda take Mammyn bata kalla ba.
“Muje” taji muryan Auwal.
A hankali ta ce musu “Sai anjima’”.
Nan ma ba wanda ya kulata sau Ummi dake kwance taga ta d’an d’aga mata kai alamun ok.
Suna fita Mom ta cewa Mammy
“Ni fa gaskiya ko Arshaad ya kawo kud’ad’en nan ba inda zan biki mu fita, maybe ma yaudararki police d’in nan yake shirin yi, dan ba miliyan uku ba gani nake ko miliyan arba’in zaki bashi ba lalle ya iya k’etare umarnin Granpa ba! And in ma ya yarda, ba kya tunanin irin mummunan hukuncin da shi Granpa d’in zai yanke mana muddin yaji labari?”
Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Adama na gaji da halin mutanen nan! Na kawo wuya! Ke dai kawai kamar yadda na fad’a miki ‘ki zuba min ido’ wuyarta kawai mu fita daga nan, dakanshi shi Granpa d’in zai kira mu mu koma gidajenmu. Shi kuma Yahaya wallahi kinji rantsuwar d’an musulmi ko? Sai na gasa mishi aya a hannu! Wai ace mutumin nan ya dawo amman ban isa yazo ya ganni ba?
Hak’uri na ya k’are Adama! Maganar gaskiya na gaji da cin kashin da ake min na gaji!!!” Ta k’arashe maganar tana share kwallar data zubo mata.
Matsowa daff da ita Mom tayi tana magana k’asa k’asa gudun kar Ummi taji, tana cewa “To ki kira maman ki mana, ai kina nan ma ita d’in zata iya yi mana komai”. Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin ta ce “ta ce babu ruwan ta, ranar dana ari wayar ai har ita na kira kin tafi fitsari lokacin, ta ce in yi hak’uri har lokacin daya yanke yayi, ita ba ruwanta waye waye. Ni k’arshe ma kashe wayar na yi dan tsabar bak’in ciki.
“Adama ba abunda yake d’aga min hankali irin maganar nan ta fita wasu suji, duk da shima Granpa d’in na san k’ok’arin b’oyewa yake tayi dan Ina jin wanda yake sa mana ido yana gayawa wani Abokin shi wai ‘kar a had’a mu da kowa Granpa d’in yayi waya yace a ware mu.’ Ina ga yana gudun kar wani ya gane mu ne.
Amman fa kin san zancen duniya ba ya b’uya, wacce irin kunya kike tunanin zamu kwasa idan k’awayenmu suka ji labari?”.
Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e kafin tace
“Shikenan ba damuwa, amman kina da tabbacin ba zata kwab’e mana ba ko?”
D’aga mata kai kawai tayi alamar ‘eh’
Shikenan nima zan gwada yiwa Auwal magana, ina ga maybe ya taimaka, dan
naga kamar abun ya dame shi. In kuma yak’i, to ko sark’ata ce zance ya duba ya d’auki d’aya ya saida sai ya kawo kud’in”. Cewar Mom.
“Allah ya shige mana gaba”Mammy ta ce, daga nan suka ci gaba da maganganunsu, ita kam Ummi tun d’azu bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, ata dalilin allurar da aka yi mata.
Tabbas su Ummi basu kyauta ba amman a nata tunanin bai kamata ayi musu haka ba! Hukuncin yayi yawa kuma abunda akai musu d’in tabbas zai jawo mata bak’in jini a wajen y’ay’ansu ne, besides ita tama yafe musu har k’asan zuciyarta.
Tana wadannan tunanin suka isa munjibir park, sun sha doguwar tafiya ba kad’an ba, ita Huda jikinta ma duk ya fara ciwo.
Parking yayi duk suka fito, sai da ya gama komai ya siyaawa Sudais ice cream d’inshi, ya d’aura shi a lilo tukunna ya dawo inda take tsaye.
Kallonta yayi kafin yace “Ko kema lilon kike son hawa k’atuwa dake??” Kauda kai tayi ta girgiza kai, kawai.
Murmushi ya yi kafin ya ce
“ta kwancen, ita ce wacce aka saki Mamanki a dalilinta! Matar Abbanki har a yanzu.”
Ta ji zafin maganar amman ta share shi kawai.
“Wadda ta ba ni sak’o kuma, na san daga maganar da tayi mini kin fahimci Mahaifiyar Arshaad da Aaima ce!
D’ayar kuma Mom d’i ta ce! Ummi, ko dan su Sudais da kike pretending kina so, ya kamata ki tausaya mata.
Mammy kuwa ko Arshaad ya kauda kai saboda son da yake yi miki, to ina tausaya miki in Aaima ta dawo dan sam ba za kiji dad’i ba at all.
Mom d’ina kuwa, to be sincere ba ma wani shiri da ita, but blood is thick!
And you should know me by now
I’m capable of anything..
Huda! All you need to do Is talk to your stubborn father ya san abun yi. Idan ba haka ba kuma Wallahi! Ni kaina ina jin tsoron abunda zan yi miki!…
A matsayin ki na so called cousin d’ina ya sanya nayi deciding in ba ki warning first akan in aiwatar da abunda nayi niyya akanki kai tsaye.
Idan kika yi min abunda nake so to kin tsira. In kuma kika yi taurin kai! To fa gaskiya i can’t save you from me.
Lastly, kar ki kuskura kiyi mentioning cell d’in da kika je yau, to anyone.”
Ya k’arashe maganar yana kallon cikin idonta. Da sauri tayi k’asa da kanta. Tabbas ta hango b’acin rai a cikin idanuwanshi, gashi har colour d’insu ya soma chanza wa.
Bud’e baki yayi zai yi magana yaji an dafa shi ta baya. Kafin ya juya ita ta zagayo gabanshi ta tsaya tsakanin shi da Huda.
Murmushi ya yi kafin ya ce “Har kin iso?” Yayi maganan yana mai rik’o waist d’inta ya d’an jawota jikinshi.
Yadda Huda ta zabura zaka d’auka ita aka janyo..
D’an jaa da baya budurwar tayi ta d’an juyo tana kallon Hudan kafin ta ce
“Who’s she??” Ta yi masa tambayar ba tare da ta kalleshi ba, da dan alamun ɓacin rai a fuskarta.
Murmushi yayi kafin yace “Relax! She’s just a cousin, daga k’auye tazo shine Daddy ya ce In kawota ta ga gari.”
Ture hannunshi da yake rik’e da waist d’inta tayi, har yanzu idonta nakan Hudan wadda ita ma ta kasa d’auke idanunta akan su tana kallon ikon Allah, budurwar tace “Cousin and more, ha?”
Dariya sosai yayi this time around kafin ya matso da fuskarshi dede tata tukun yace “If she’s cousin and more would I do dis in front of her?” Ya k’arashe maganan da kissing lips d’inta lightly.
Da sauri Hudan ta bar wajen tana had’a hanya.
Kujerun data gani a gefe chan taje ta zauna tana haki tana istighfari.
A chaan wajen su Auwal kuwa murmushin jin dad’i budurwar tayi sannan suka shiga sabgogin gabansu.
A tap d’in wajen tayi alwala, wasu mata manya ta gani da darduma sun shinfida k’atuwa suna zazzaune ga kuloli alamun picnic suka fito, dan haka ta k’arasa tayi musu sallama tace
“Dan Allah tana so za tayi sallah”. Da fara’a suka tarbeta suka matsa mata d’ayar ta fiddo hijabi a jakanta ta bata.
Bayan ta idar suka yi mata tayin abinci, gorar ruwa kawai ta d’auka ta sha ta yi musu godiya a wajen ta ci gaba da zamanta a wajen, tana hango Sudais yana ta wasan shi, can gefe kuma Auwal da budurwar shi an cika musu gaba da kayan kwalama kala kala amman ita ko ruwan sha ya kasa bata. Ganin bata da abunyi yasa ta bud’e wayarta ta hau karatunta ragowar ruwan da ta sha d’an mitsitsi ta rage ta tofa a ciki.
Sai da aka fara kiraye kirayen sallar Magrib tukunna taga ya taso.
Yana tasowa ta mik’e ta hau sallarta dan ta lura In suka kama hanya yanzu sai sun kusan 40min suna tafiya.
Takaici, kamar ya kifa mata mari haka yaji, ba yadda ya iya shima yaje yayi alwalla yayi iya magribar d’in daya tarar maza sunyi jam’i suna yi.
Tare suka jero da budurwar da Sudais da yaje ya d’auko, suka nufo ta.
Sallama da godiya ta yiwa matan da suma suke ta shirin tashi, ta rik’e hannun Sudais wanda ya iso gareta da sauri suka nufi inda suka yi parking.
Sai da ya k’araso ya bud’e motar tukunna suka shiga. Ita da Sudais suka zauna a baya shi da budurwar suka zauna a gaba. Sai da suka biya wani gida a lamido crescent flat mai kyau suka ajjiyeta tukunna suka wuce. Abunda ya d’aurewa Hudan kai shine shi Auwal d’inne ya bawa budurwar makullan gidan!
Ita dai ba tayi magana ba, ta yi shiru kawai tana mamakin shi. Ko da ya ce wani ya koma gaba, Sudais ta matsawa ya tsallaka.
A gajiye suka isa gida yana ajjiye su yayi reverse ya sake fita.
A parlourn ta tarar da Arshaad
,wanda suna dawowa daga kai Amarya ya had’u da Aslam cikin hira yake gaya mishi ‘Hudan sun fita munjibir da Auwal!’ Ko wanka kasa yi yayi ya taho gidan. Yana tunanin bin bayan su kenan suka shigo.
Ajiyar zuciyar daya sauk’e lokacin da suka shigo sai da taji, sarai ta lura dashi amman ta d’auke kai tayi wucewarta ganin yadda ta bawa iska ajiyarshi kuwa hakan yayi mugun bak’anta mishi rai! At least in tana jin haushinshi ai ko darajar kallo ya ci ace ya samu.
Sai da ta raka Sudais d’akin shi tukunna ta nufi side d’inta.
Tana shiga parlourn ta saki jakarta ta tafi da gudu tana ihun murna. Rungume juna suka yi suna dariya kafin tace “tun yaushe kika zo?”
Dariya itama Sakina tayi tace
“D’azu Abba yaje da kanshi ya d’auko ni hala ke kikayi mishi kwatance ko?”
“Eh” tace tana sake hugging d’inta, sannan ta jata suka nufi bedroom.
“Ma shaa Allah, Ubangiji mai zamani”
Sakina ta ce.
Sannan tace “gaskiya wajen nan ya burgeni Huda, over!! Ina tunanin had’uwar parlourn ashe bedroom d’in har ya fishi? “ Murmushi Hudan tayi tace “Ni kuma duk toilet d’in yafi burgeni” da sauri Sakina ta ce “muje In gani” ta fad’a tana cire hijab d’in jikinta dake nan har k’asa.
Suna shiga nan itama ta ce “gaskiya kam toilet d’in duk yafi had’uwa”
Haka nan suka taru suka dinga hauka, daga su kunna wannan sai su kashe wannan, wani abun ma ba iyawa suka yi ba da karambani suka koya. Babu abunda yafi burge Sakina irin closet dan haka ta fito wajen tana kuma setawa Hudan zaman kayanta kafin ta fito a wanka.
Bata wani dad’e ba ta fito a wankan
tana fitowa ta ce “itama ta shiga tayi wanka sai ta chanja kayan jikinta, lace d’in zai yi mata nauyi dan garin ana zafi sosai”. Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ni fa daga ni sai hand bag d’ina nazo, Ummu da hanani zuwa tayi fa, sai da Baba ya bud’e mata wuta! Amman tace wai gobe da safe in dawo, har na d’auko kaya set uku ta ce wai In na tafi da kaya ba zan dawo da wuri ba! Shi kuma Baba ya ce tunda Abba ne da kansa ya rok’esa to sai lokacin da kika saba da nan d’in tukunna zan koma!
Wallahi tun d’azu jikina a sanyaye yake, Mama ma bata san na taho ba, dan Ummu tace ba ta san da wanne ido zata kalle ta ta fad’a mata ba!
Shine ma dalilinta na hanani zuwa tun farko daman.”
Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce “Ranar dana tafi ya aka yi? Ina ta kiran Ummu bata d’auka.”
“Hmm! Mama ce ta rikita kowa wai Abba ya aiko an sace ki! Amman har yanzu a haka su Ummu suka barta basu gaya mata ke kika tafi da kan ki ba saboda kar taji haushin mu, kawai dai ance mata kina nan d’in so ta kwantar da hankalinta tunda kina wajen Mahaifinki ne ba wani mugun hannu ba.”
Hawaye Hudan ta goge kafin tace “Sakina wallahi ni ban san ya zan yi ba” ta fad’a tana fashewa da kuka, rungumeta Sakina tayi kafin tace “wallahi Huda ni kaina abun nan yana daure min kai, sai ka rasa ina zaka tsaya, gabad’aya ni kaina i’m confused, ballantana kuma ke. Mu yi ta addua kawai ki kwantar da hankalinki, kinji?Please”.
Hawayenta ta goge jikinta duk yayi sanyi, sannan ta d’an d’aga kanta
a hankali kafin ta cewa Sakinan “ki je kiyi wanka sai ki sa kayana Inner wears kuma ina da sababbi suma, muyi sauri dan na san yanzu Abba zai fara kira, lokacin dinner yayi.”
Hijab d’inta wanda ta ajjiye a bedroom Hudan ta fita ta d’auko ta wuce ta sa a washing machine ta fito ta bata towel,
Ita ta tayata wankin dan sai da ta tayata ma shanya kayan data cire suka wanke d’in tukun ta fito ta barta dan tayi wankan.
Sallah ta tarar Hudan tana yi lokacin da ta fito dan haka itama ta nemi hijab ta tayar da sallar. Sauranta izu d’aya a izu goman daya kamata tayi, dan haka ta hau karatu bayan ta idar. Tana idarwa tayi addua ta tofa ta had’e ruwan d’azu data shigo dashi dana d’akin waje d’aya! Da mamaki Sakina ta kalle ta kafin ta tambayeta
Bayani ta hau yi mata a kan ‘na maman Aslam ne wanda ta basu labarinta.’ “Allah sarki Allah ya bata lafiya, abun tausayi wallahi” Sakinan ta ce.
Kayan bacci dukkansu suka sanya, sai suka d’aura hijabai a sama, sannan suka sauk’a dan Abba har ya kirata kamar yadda tayi tsammani.
Sai da ta lek’a d’akin su Sudais, ganin basa nan yasa suka nufi k’asan.
Har Aslam suka tarar a dining d’in da Arshaad amman yanzu ya chanja kaya wanda hakan ke nuni da wanka yaje yayo.
Yaji tahowa amman bai d’ago ba, dan babu abunda yake sosa mishi zuciya irin yadda ko kallon inda yake bata yi.
Sai da suka k’araso tukun Abba yace “a’a inyee! Yau ga annuri a fuskar princess, duk a dalilin Sakina, irin wannan murmushi haka?!” Ya fad’a yana murmushi kafin ya ce “bismillah ku zauna mana”
A hankali suka fara k’ok’arin jan kujera…Yana shirin d’agowa ya ga da gaske Sakinan ce jin abunda Abba yace, yaji tace “Ya Arshaad Ina wuni.”
Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai kuma ya fara murmushi ya ce “Lafiya, Alhamdulillah. Ashe ke ce da kanki!
Welcome, ya gida?”
“Alhamdulillah” ta ce kafin ta d’an turo baki ta ce “Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma baka yi ba”. Dariya yayi kafin yace
“Hankalina baya wajen ne, sorry”
Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba! Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba.
Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam. Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban,
but yanzu kam tagani itama! “Tubarakallah!” Ta fad’a a k’asan ranta.
Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko? Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..”
Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da ake wa Huda, suga yadda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta”. Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta! Ita fa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki.
A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna ya ce “lafiya” da d’an mitsitsin bakin shi.
Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba. “Ouch” ta ce, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba za ki gaida shi ba???” Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta! Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace “Wallahi ko ki gaishe shi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!” Daidai nan wayar Abba tayi k’ara. Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiwu yayi ignoring ba.
Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da suka ji suka juyo suna kallonsu. Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu!
Ganin da Huda tayi Sakina ba zata hak’ura ba yasa ta juya, kujera biyu ne tsakaninta da Arshaad d’in dan haka ta d’an kalle shi tace “ina wuni”. Sai da ya sake tamke fuska tukun yace “Lafiya”
Yana jin haushi a ranshi, wato gaisuwar ma sai ta ga dama zata yi, kuma shine na k’arshe! Har su Sudais sai da ta gama kulawa tukunna shine last!
Tashi Sakina tayi daga kan kujerarta ta dawo ta gefen Hudan side d’in da Arshaad yake ta zauna kafin ta ce
“Am i missing something here???”
Tayi musu maganar tana juyowa ta kalli wannan ta kalli wannan.
“Eat!” Arshaad ya ce sannan yaci gaba da cin abincin shi. Dawowar da Abba yayi ne ya katse mata maganganun da suka taso mata don haka tayi shiru.
Luckily aka sake kiran Abba a waya dan haka ya mik’e ya ce “bara ya shiga wajen Daddy”.
Ba a jima ba Aslam shima ya mik’e, da sauri Hudan ta mik’e ta mik’a mishi Goron ruwan hannunta Opposite yau ma suke dan haka ya kalle ta ya ce
“thank you!” a hankali yana kallonta.
Bata san daliliba! Dan kwata-kwata sam sai ta kasa janye idanunta daga nashi. Tunda Mama ta kawota duniya ko a tv bata tab’a ganin kwayar ido mai kyan nashi ba! Shape d’in Idon kansa abun son ka kalla ne! Komai na idanun nasa masu kyau ne. Ita kam wata rana zata tambaye shi ‘me yake shafawa eyelid d’insa?’ Dan wani haskene yake fitowa daga wajen.
Duk da yadda zuciyarta ta tsananta bugu hakan bai sanyata ta d’auke idanunta daga kansa ba kuma bai sanya ta sakar mishi robar ruwan da ta mik’a masa ba!
“GOOD NIGHT Sakina!!”.
Suka ji Arshaad ya fad’a da d’an k’arfi!
Da sauri Aslam ya yi firgigit, ya janye robar da mugun k’arfi, sannan ya juya yayi hanyar fita. Har ya fice daga parlourn bai yarda ya sake juyowa ba.
Hudan ita kam kunya ce gabad’aya ta lullub’eta.. Ashe har Arshaad da Sakina sun mik’e su shuraim kuma suna shirin fara hawa bene ita bata ma sani ba!.
Yana shirin barin wajen Sakina tace “pls mana” tana d’an karkartar da wuyanta.
Murmushi yayi ya ce “she’s busy rn, let it go kawai.”
A hankali Sakina ta ce “Plss” tana had’e hannuwanta biyu waje d’aya alamun rok’o. Ajiyar zuciya ya sauk’e ya d’an ja ya tsaya.
Hudan na ganin wucewar su Shuraim sama ta juya itama zata bar wajen. Hannu Sakina tasa ta rik’eta.
Ba tare data juyo ta kalleta ba tace
“Sakin mani hannu plss, bacci nake ji”
Jin abunda tace ya sake tunzura shi
don haka kawai ya fice fuuu!! Ko sauraron Sakina bai sake yi ba.
Haushi Sakina taji ta saki mata hannu suka haura sama. Har suka shafa addua suka kwanta suka ja bargo ba wadda ta yiwa y’ar uwarta magana.