Murmushi Arshaad ya yi kafin a hankali yace “Ummi, na same ku lafiya?”
Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi.
“Alhamdulillah” tace, sannan ta d’aura da cewa “where have you been?”.
Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali ya ce “Bara in d’an huta”. Ya fad’i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi! Gabanta ne taji yad’an buga! Gashi babu damar ta. . .