Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishisannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba!
Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi.
Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina. Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace “In fito ko za ki shigo?”
Da mamaki Sakina ta zare. . .