Skip to content
Part 64 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishi
sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba!

Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi.

Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina. Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace “In fito ko za ki shigo?”

Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace “Ki fito Ina?
Ina zan shigo?” Turuss! Haka Hudan taja ta tsaya itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace
“Sak’on fa da kika ce za ki bani?”

Cikin rashin fahimta Sakina tace “Wanne sak’o?”

Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyara zuciya tace “Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak’o in zo in karb’a da sauri…”

Cikin katseta a d’an firgice Sakina tace “Hudan yi sauri ki koma gida maza maza yanzun nan!
Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata sun ga yau kuna taro. Yi maza ki koma ciki da sauri
kar ki sake fitowa.”

Da sauri kuwa Hudan ta juya k’irjinta yana dukan uku uku! Har da d’an gudu ta shiga had’awa da shi.

Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse. Haka nan ta wuce kitchen d’in jikinta yana karkarwa tana salati.

Tana shiga taga kamar an fita ta k’ofar baya! Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa.

A hankali ta shiga takawa tana kallon k’ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k’ofar ba a matsa ba!

“Huda”. Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand’a ta kira sunanta.
A mugun tsorace tace “wayyo Allah!!” Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa.

Dariya Ummi tayi kafin tace “Matsoraciya!!! Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan…D’azun Dad yake gaya mana
Granpa although yana fushi da Aslam akan ki amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK
ya bashi kyautar gida da mota a chan.

A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had’in coffee d’in Aslam.

Murmushi Ummi tayi, ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa
“Yauwa coffe d’innan na biyo! Gaba d’aya drinks d’in nasu na yau zak’iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping. Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na.”

A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace “Eh. Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan ajjiye mishi a gefen tray d’in in yana so sai ya k’ara.

Murmushi Ummi tayi sannan tace “To za a zuba min inshaa ne ko sai na jira an fara kai mishi ya d’iba?”
Ta k’arashe tambayar cikin sigar tsokana.

Murmushi mai had’e da y’ar dariya Hudan tayi kafin tace “Haba Ummi”
Tana mai juyawa ta d’auko cup mai d’an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata.
Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace “Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam.”

Sunkuyar da kai Hudan tayi…Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta tayi walwala
shiyasa kawai ta d’an sake suka hau hirar yadda birthday d’in ya kasance, suna hirar tana juye coffe d’in a cikin flask……..

Ummin kuwa daman hakan take so dan ita kunyar Hudan ma take ji akan abunda aka yiwa Sakina yau gashi saboda su Shuraim takanas ta zo shiyasa ta dinga janta da wasa har sai da taga ta d’an sake
tukunna ta shirya bata hak’uri akan abunda ya farun! A lokacin Huda har ta juye ta had’a tray ta d’aura cup da spoon da sugar tana shirin d’auka Ummi tace “Amm Huda iwant to apol….” Kamar an mak’ale ta haka maganar tata ta tsaya cak!

Da sauri Hudan ta ajjiye tray d’in ta nufeta saboda yadda tana juyawa taga Ummin ta damk’i wuyanta kamar zata shak’e kanta sannan ta runtse idanuwanta. Da kyar Ummi ta iya cewa “ya subahanallah!”
Sai kuma ta zube a wajen ta fara tari. “Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Hudan ta ambata a firgice da k’arfi! Sakamokon ganin jini yana fitowa daga bakin Ummi wadda take nan k’asan tiles d’in kitchen d’in kwance tanata tari.

Da sauri ta durk’usa ta hau jijjigata tana “Ummi! Ummi!! Ummiii!!! Abbaaa! ya Aslam!
Ya Arshaad! Ummi ki tashi..”

Kuka take tana ihu tun k’arfin ta dan tun lokacin da ta durk’usa akan Ummin ta ga ta daina motsi sannan jikinta ya sake.

Da gudu ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar fita ta kira jama’a azo a kai Ummi asibiti…Tana gudu tana juyowa tana kallon Ummi bata yi auni ba taji ta fad’a jikin mutum! Da sauri ta d’ago tana kallon Arshaad wanda shima ita d’in yake kallo bakinsa yana d’an rawa da alamun magana yake son yi amman ya kasa.

Cikin kuka ta hau juyawa tana nuna mishi Ummi wadda ke nan kwance a k’asa kan tiles!
Sannan ta juya da gudu ta nufi Ummin tana cewa “Harda jini! Tama daina motsi”
tana mugun kuka.

Da kyar Arshaad wanda gaba d’aya ilahirin jikinsa ya d’au karkarwa tun lokacin da ya ga Ummin nan kwance, ya taka ya k’arasa inda Hudan da Ummin suke.

Da sauri ya durk’usa a wajen a mugun rikice yace “Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Kawai kuma sai hawaye ya biyo ta idanunsa.

Da sauri Hudan tace “Ya Arshaad dan Allah kar ka ce ta mutu! Wallahi bata mutu ba!
Bata mutu ba!! Ka kaita asibiti zata farfad’o. Dan Allah ka kaita asibiti. Ummi ki tashi!
Abbbbbaaaa!!!” Ta sake kwala kiran Abba dan taga Arshaad d’in yak’i motsi kwata kwata so ba lalle ya iya tab’uka komai ba, da alamun ya yi mugun firgita da ganin Ummin.

A rikice Aslam ya afko cikin kitchen d’in sanye da bathrobe a jikinsa da alamun ma bai gama wankan ba dan har da y’ar kumfa a gefen kumatunsa.

Ganin Ummi yasa shima ya k’araso ciki da mugun gudu ya durk’usa a inda suke
dai dai nan su Shuraim suma suka k’araso cikin kitchen d’in.

Sai ga Mom itama ta shigo tana cewa “Ife ifen me nake ta ji ne wai hak……?”
Muryarta ce ta katse sakamokon kitchen d’in da taga cike da jama a a nata ihu ana kuka!
Dan su Shuraim suma suna shiga suka yi kanta sukai joining Hudan a kukan. Da sauri ta k’arasa tana cewa “waye ba lafiya ne mai ya far..”Maganarta ce ta katse sakamokon had’a ido da tayi da Aslam! Sanye cikin bathrobe. Da mamaki take kallonsa har da y’ar kunfar sa a gefen fuska, har zata yi masa maganar fitowar dayayi half naked dan bathrobe d’in bata da wani tsayi sosai sai kuma kawai ta shareshi dan jin dalilin kukan da take ji ne priority yanzun. D’auke kanta tayi ta maida inda su Hudan suke durk’ushe….

Dishi dishi ta fara gani sakamokon Ummi da ta gani kwance bakinta duk jini!
A hankali jikinta na mugun karkarwa tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Sai kuma ta tafi luuuuuuu ta sume a wajen…

Sudais da Shuraim ne suka fara k’ok’arin ciccib’ar Ummi dan haka Hudan ma ta sa hannu suka d’auketa.
Aslam yana ganin haka ya bisu a baya duk ya rikice… Da gudu ya wuce su ya shiga d’aki ya d’auko mukullin motarsa ya mik’awa Huda yace “su jira sa” Sannan ya koma ya zura jallabiya mai kauri daman already ya saka boxes a k’asan bathrobe d’in! Ya fito ya bi bayansu.

Yana zuwa ya kunna motar already sun gama shiga suka yi gaba kowa hankalinsa a tashe sai kuka su Hudan suke yi.

Da kyar Arshaad ya iya mik’ewa ya d’auko ruwa a fridge ya shiga yayyafawa Mom. Har ya d’an fara tsorata dan da farko k’in farkawa ta yi, kafin daga baya kuma ta farka a firgice tana salati sai kuma ta tashi ta zauna ta fashe da kuka! Kallon inda taga Ummi d’azun tayi ganin ba kowa sai d’an ragowar jini jinin da aya zuba a k’asa ne yasa a rikice ta juyo tana kallon Arshaad kafin tace “Tana Ina?”

Bai ce mata k’ala ba! Dan kanshi a mugun d’aure yake ‘jini, Ummi, how?’ Sune abubuwan da suka taru suka hautsina mishi kwakwalwa.

Mik’ewa kawai yayi ya wuce d’akinsa ya d’auko key ya cire rigar suite d’in jikinsa ya rage daga long sleeve sai dogon wando da belt, ya fito ko cover shoe d’in k’afarsa bai tsaya chanjawa ba.

A parlourn ya tarar da Mom tanata faman safa da marwa. Yanzun ma bai kulata ba ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da sauri suka fice.

Sai da suka shiga motar ya kunna tukunna ya kira Aslam. Shuraim ne ya d’auka, nan yake tambayarsu “suna Ina?” Cikin kuka yace “Basu riga sun k’arasa asibiti ba amman duk wanda suka samu mai kyau nearby nan za su je”

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e daga nan ya katse kiran ya tada motar ya fice daga gidan.

Driving kawai ya hau yi towards asibitin da ya san yana a kusa dasu mai kyau. Kamar had’in baki kuwa
yana shiga ya hango motar Aslam nurses suna d’aura Ummi a akan gado. Yana k’arasawa yayi parking suma suka fito suka d’unguma gaba d’ayansu suka rufa musu baya.

Da kyar aka iya tsayar da su Shuraim da Hudan daga shiga investigation room d’in haka nan suka dawo in banda kuka ba abunda suke yi.

Da sauri Mom ta k’arasa ta jawo Sudais da Shuraim ta rungumesu itama tana kuka.

A hankali Aslam ya k’arasa inda Hudan take tsaye tana kuka, ya juyo da ita ya rungumeta a hankali ya shiga bubbuga bayanta.

Da sauri Arshaad ya tashi ya fita a wajen waya kare a kunnensa. Dad, yana amsa wayar ya fad’a masa halin da ake ciki daga nan ya nemi waje ya zauna a harabar asibitin..

BAYAN MINTUNA TALATIN.
Cirko cirko haka kowa yake tsaye sun cika wajen. Dad Daddy Aslam Abba Mom Mammy Gramma Mommy Arshaad Sudais Shuraim da Hudan! Kowa ka ganshi ka san hankalinsa a tashe yake dan ko zama ba wanda ya iya yi.

K’arar bud’e k’ofar inda aka shiga da ita suka ji, dan haka duk suka juya suka zubawa Likitan da ya fito ido.

Yana kallonsu ya yi saurin sunkuyar da kanshi kafin ya zare glasses d’insa yad’an murza idanunsa sannan ya mayar ya d’ago ya kalli Aslam yace masa “follow me”

A hankali ya zame hannunsa a cikin na Hudan ya bi bayan Likitan..

BAYAN MINTUNA BIYAR.
A hankali Aslam ya bud’e k’ofar office d’in ya fito, kamar wanda aka zarewa laakka a jiki haka yake taku, sai da ya kusan k’arasawa corner da in ya shiga zai gansu tukunna ya zaro wayarsa ya danna kiran Granpa!

Yana karyo kwana suka yo kanshi gaba d’ayansu suka hau tambayarsa. Kallonsu kawai yake yi da waya kare a kunnensa, sai ya bud’e baki kamar zai yi magana sai kuma ya kasa. Jijiyoyin kansa sun yi rud’u rud’u! Gashi idanuwansa sun kad’a sun yi jaaa! Wanda hakan ba k’aramin sake gigita ahalin yayi ba.

Sai da wayar ta kusan katsewa tukunna Granpa ya d’auka! Jin shiru yasa yace “Talk to me Aslam”

A hankali bakinsa na rawa yace “Granpa, its Ummi! Incase you have something to say to her…
Likita yace she has less than 1 hour.”

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”. Shine abunda kowa ya hau maimaiitawa a zuciyarsa dan
k’amewa k’am! Gaba d’ayansu suka yi kamar an d’auke musu numfashi haka wajen yayi tsit!.

A hankali kukan Gramma ya fara tashi followed by na Mom da Mommy sai su Sudais da Huda…
Tashi d’aya kuma sai wajen ya hautsine! Masu hawaye nayi masu kururuwar kuka ma suna yi.

Da kyar Abba ya iya k’arasawa ya dafa Aslam yace “What happened to her?”
Jikinsa yana mugun karkarwa. A hankali da kyar ya iya cewa “poision ta sha!
Ya tsinkamata gaba d’aya hanjinta. The Doctors where even shocked! Ta yadda take numfashi har yanzu.”

A rikice Abba yace “Poison kuma? How? A ina? Wa ya bata poision?”

D’agowa yayi ya na kallon Hudan yana son tambayar ta ‘ya aka yi?’ Ganin yadda gaba d’aya hankalin jama’ar wajen ya koma kanta ne ya sa kawai ya d’auke kai. A hankali yace “Ihun Hudan kawai na ji, ina
zuwa na ganta tana tarin jini. Ba mu san a ina ta sha ba.”

Da sauri Mammy ta matso tana matsar hawaye tace. “Ta ya zaka ce baka san a ina ta sha ba!?
Ga wadda za ku tambaya nan?” Tayi maganar tana nuna Hudan.

Cikin karkarwar jiki Hudan tace “Ban san a ina ta sha ba”

Dasauri cikin katseta tace “Ai tare kuke! Dan haka dole kinga ta sha wani abun.”

Cikin rashin fahimta Hudan tace “Ina cikin had’awa Ya Aslam coffe ta zo tace zata sha, sai
na zuba mata a cup. That was the only thing da naga ta sha daganan ta fara tar……….”
Shiruuu, tayi ta kasa k’arasawa sai kuma a rikice ta d’ago tana kallon Mammy wadda ita ma itan take kallo kafin ta matso kusa da ita tace “Hudan we all know ba kya k’aunar Aslam!!!

Da kika zo kashe shi kika san kin yi poisioning coffe d’insa! Me ye laifin Ummi da zaki had’a har da ita ki bari ta sha?”

Cikin tsananin tashin hankali Hudan take kallonta zata yi magana Mammyn ta katse ta ta hanyar sake cewa
“Ko jifan tsuntsu biyu kike son yi da dutse d’aya? Because it’s obvious yanzu babu abunda zai sake shiga tsakanin Maryam da Abba!”

Wani kalar kuka da Hudan take yi sai da ta kusan shid’ewa!

Zata yi magana Mammy ta sake cewa “Wachche irin zuciya ce da ke Hudan? Na tabbatar idan kika rok’i Aslam kika ce ya sakeki tsaf z……..”

Da mugun k’arfi Aslam wanda ya zo iya wuya yace “Mammy!!!” Wanda gaba d’ayansu sai da suka razana! Kowa ya d’auke wuta……..

A hankali Abba wanda tun lokacin da Mammy ta fara magana ya runtse idanuwan ya bud’e ya kamo hannun Aslam yace “Za a iya ganinta ko?”

Sai da ya d’an dedeta kansa tukunna yace “Eh” ba tare da ya kalleshi ba
dan wani kalar kallon kallo suke yiwa juna shi da Mammy wanda da ace Mammyn ta san kallon da Aslam d’in yake yi mata to daa ba zata yarda ta bar kwayar idanunta a cikin nasa ba.

D’akin da aka shiga da ita sanda aka kawota nan Abba ya shiga dan basu ga lokacin da aka fito da ita ba.

Sai a sannan Mommy ta matso ta jaa hannun Aslam suka fice daga wajen gaba d’aya.

Suna fita Mammy ta sake juyowa kan Hudan a karo na biyu tace “Yau wallahi mai kwatar ki a hannuna sai Allah, kin san ya Ummi take a wajena kuwa……”

Banda kallon Mammy ba abunda Mom take yi tana wani irin kuka, so take tayi magana amman ta ma kasa.

Cikin fushi Mammy ta yi kan Huda kamar zata shak’ota.

Damk’ar hannunta d’in da Dad yayi ne ya sa ta juyo tana kallonsa! Ba tare da ya kalleta ba
ya jaa hannunta da mugun k’arfi ya fita da ita. Sai da ya sakata a mota ya cewa driver ya maida ta gida tukunna ya juya ya koma ciki ba tare da ya bi takan bak’ak’en maganganun da take jefa mishi ba.

Mammy kamar zata mutu haka ta ji, wato bashi da time d’in da zai yi mata magana sai in zai wulak’antata sannan a gaban mutane ko kuma in ba su kad’ai bane to ya kan kulata. Gashi yanzu Arshaad shima ya fara, tsabar wulak’anci ga ta ga shi amman iya gaisuwace kawai take shiga tsakaninsu, d’azu taje d’akinsa har sau biyu baya nan a na ukun kuwa da tayi sa a yana nan tana shiga ya mik’e ya fita ya barta kamar ba uwar da ta tsugunna ta haifesa ba, bama fa ta san ya dawo ba sai a gidan kawai ta ganshi! Takaici da b’acin rai kamar ta d’aura hannu aka tayi ta kurma ihu……..

A kwance ya ganta da oxygen da wasu na’urori tana janyo numfashi da kyar! A hankali ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanta yace “Ummi”. Sai kuma wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarshi. A hankali ta shiga bud’e idanunta. Tun tana ganinsa dishi dishi har ta d’an fara ganinsa sosai dan haka ta fara k’ok’arin mik’ewa. Da sauri yace “Nooo.. Stay still” Sai kuma ya juya ya janyo wani stool ya zauna a kai ya kama hannunta ya rik’e.

A hankali ta d’an jaa oxygen d’in k’asa, tace “Naji Likitan yana cewa poision na sha ko?
Wai hanjina sun tsitstsinke.” A hankali Abba ya kawar da kansa yayi amfani da free hand d’insa ya share hawayen fuskarsa kafin ya juyo yace “You are going to be okay”

Murmushi ta yi a hankali tace “K’arya fa ba halin ka bane Abba”

This time around kuka ne ya kufce masa…A hankali ya kamo hannunta ya d’ago ya kai setin bakinsa yayi kissing hannun cikin kuka yace “Ki yi hak’uri Ummi. Dan Allah ki yi hak’uri. Na nuna miki k’iyayya,
ni kaina naji ina jin haushin kaina ballantana ke.”

Murmushi tayi a hankali tace “Ko sau d’aya ban tab’a jin haushin abunda kake min ba Abba
remember tun muna Yara na sha gaya maka ‘ko menene idan kayi burgeni yake yi’
dan haka kar kayi tunanin na rik’e ka a zuciyata! Zuciyata iya kar k’aunarka da tsananin son ka ta sani
bata san wani abu akasa sin haka ba” Ta k’arashe maganar tana d’an murmushi.

Kuka ne sosai ya kufcewa Abba.

A hankali take d’an matsar hannunsa wanda yake rik’e da nata tace “Good bye Abba,
ka kulamin da su Shuraim dan Allah, har da Hudata itama ka cigaba da kula min da y’ay’ana.”

Cikin tsananin kuka yace “Ummi ki yi shiru. Fad’ar Likita ba fad’ar Ubangiji bace ba. Ki yi shiru da waennan maganganun dan Allah.”

A hankali tace “Lokacina yayi! Tun ba yau ba na fara jin hakan a jikina.”
Shiruu ta d’anyi kafin ta lumshe idanunta ta bud’e a hankali tana ganin dishi dishi tace
“Ina takaicin Ba zaka dinga tunani a matsayin masoyiyarka ba bayan raina! Sai dai
a matsayin wadda ta sanya rayuwarka a k’unci ta saka ka tunani da bak’in ciki. Da ace za a bani chance d’in da zan iya komawa farko to da na fita a rayuwarka kayi farin ciki daga farkonta har k’arshe.”

Cikin katseta yace “Ummi mun wuce wannan wajen, na fad’a miki na riga na yafe miki na manta da komai.
Ba zan tab’a tunoki a matsayin wadda ta sanya rayuwata k’unci ba sai a matsayin ki na matata! Amaryata!
Uwar y’ay’ana! K’anwata sannan masoyiyata wadda take tsananin so na.” A hankali ya matso da bakinsa ya d’aura a kan goshinta yayi kissing yana kuka ya d’an d’ago yana kallon idonta yace “I love you, Zainab”

Wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata, a hankali tace “Now I’ll have a nice nap!
In sha Allah. Thank you.”

Kasa ci gaba da zaman yayi dan haka ya mik’e da sauri ya fita a d’akin yana kuka sosai.

Yana fita Hudan Shuraim da Sudais suka shigo. Tana jin kukan su ta fahimci sune suka shigo
dan zuwa yanzu ba sosai take gani ba. A hankali ta bud’e musu hannuwanta alamun su je gareta. Da sauri kuwa suka nufeta suna zuwa tayi hugging d’insu gaba d’aya….

A hankali suka cikata suka matsa gefe suna kuka. Cikin kuka Huda tace “Ummi wallahi ban san poison bane ba”. A hankali Ummin ta katseta ta hanyar cewa, “Shhh”.

Sai da ta ga ta d’anyi shiru sannan tace “Magana d’aya zuwa biyu nake so in gaya muku…
Ku had’a kanku ku so junanku ku rik’e zumunci a duk inda kuke ku rik’e amana
dan Allah sannan kar ku cuci wani..”

A hankali Granpa ya turo k’ofar ya shigo. Idanuwanshi sun yi jajawur!
Tun lokacin da Gramma ta fad’a mishi ta fito sam sai ya gagara sukuni
shiyasa shima kawai ya yanke shawarar zuwa asibitin. Yana hanya ma lokacin da Aslam ya kira shi ya fad’a mishi abunda Likita yace. Da kyar ya taka da y’ar sandarshi ya k’arasa bakin gadon.
Inda Abba ya tashi nan ya zauna tukun a hankali yace “Ummi”

Juyowa ta yi sanann ta d’an d’ago hannunta tana k’ok’arin kama nasa.
A hankali ya kamo hannun nata da nashi hannayen duka biyu ya rik’e.

Inda su Shuraim suke a tsaye yanzu tun shigowar Granpa ta d’an kalla kafin tace “ku bamu guri”.

Har sun juya za su fita suka ji tace “Allah yayi muku albarka”
Sai da suka juyo gaba d’ayansu tukunna suka ce “Ameen Ummi”
Sannan suka juya suka fita suna wani irin kuka.

A hankali ta maida idonta inda take Jin Granpa tace
“Daddie, dama inada niyyar bada sak’o a baka koda ace baka zo ba.
Na gode kuma naji dad’in zuwanka.

Maganata ta farko. Itace Godiya! Kasancewar ka Uncle kuma Uba a gareni
Is one of the luckiest thing da kuma nake alfahari da a rayuwata.

Tun tasowata har kawo yanzu bana jin akwai abunda na tab’a nema na rasa shi, baka
rage ni da komai ba akoda yaushe k’ok’ari kawai kake yi kaga nayi dariya na samu abunda nake so!
Na gode kwarai Daddie bana jin aduniyar nan a kwai d’iyar da tayi sa’ar samun uba mai tsananin kaunarta kamar ni.”

Runtse hannunta da yake a cikin nashi hannayen yayi hawaye ya fara sintiri akan tsohuwar fuskarshi.

A hankali dan muryarta tayi low zuwa yanzu ta ci gaba da magana “Sai magana ta biyu
Shawara ce zan baka! Iyaye da manya suna ganin kamr duk abunda babba yayi shine dai dai
alhalin wasu lokutan wani babban yana yin abunda ko d’an shekara tara ba zai aikata ba saboda ya san ba dede bane ba amman tsoro da fargabar gayawa wannan babban gaskiya sai a sanya ido ayi shiru a nad’e hannu a koma gefe a taru ayita tafka b’arna!” Shiruu, ta d’anyi tana k’ok’arin jawo numfashi kafin tace
“Same thing da yake going a estate d’inmu kenan Ka yi hak’uri da abunda zan fad’a yanzu. Kai da kanka da hannunka ka hargitsa estate d’innan wanda yanzu abunda ya faru yau yasa na tabbatar da hakan kuma inajin takaicin rashin sanin k’arshen wannan bala’i da musiba da ta shigo mana ko kuma ince muke ciki tsundum ba tare da mun sani ba. Granpa dan Allah dan Annabi the first thing da zan rok’eka shine
ka daina nuna bambanci! Yanzu ni ba a maganata amman in baka tashi ka tsaya ka gyara tsagwaran bambancin da kake nunawa a tsakanin Aslam Auwal da Arshaad ba to akwai matsala babba!.

Ba ni da tantama bani da shakku akan Aslam akaso ayi poisioning yau ni kuma na sha ba tare da na sani ba!
Ban ce Arshaad ko Auwal bane ba amman dai na san dole a cikin estate d’in mu ne wanda na tabbatar ata dalilin kyautar gidan da kayi mishi ne da kuma ragowar abubuwan da kake tayi tun haihuwarshi har kawo yanzu, sannan ina so ka san wallahi tallahi ba Huda bace ba”. Numfashinta da ya fara sark’e wa ne yasa ta yi shiru ta hau kokawar janyowa.

Da sauri Granpa ya mik’e ya fara kiran “Doctor!!”

Ruk’o hannunshi tayi tace “One last thing abunda nake so abunda idan kayi min zan ji dad’i shine
Granpa dan girman Allah da manzonsa ka yi hak’uri ka daure ka yarda sannan ka taimaka wa Abba ya maida Maryam! Ka yi accepting d’inta ita da Huda. Dan Allah Granpa sannan ka tayani neman yafiyar mutum uku Maryam Aisha da Huda! Although na san su Maryam sun yafe min amman Ina buk’atar ka sake nema min yafiyarsu”Tana gama fad’in haka numfashinta ya fara sama maganar ma da take son sake yi ta sark’e harshenta ya fara fidda maganar da ba ita ba! Da sauri Granpa ya sake cewa
“Doctor!!” Da k’arfi yana zubarda hawaye da k’ok’arin barin wajen amman sai yaji still ta sake rik’e hannunshi tak’i saki. Juyowa yayi suka had’a ido yaga yadda idanuwanta suke shirin k’afewa tana ta
faman kokawa da numfashinta! Da sauri ya k’arasa yayi cupping fuskarta yana kallon idonta yace
“Ashhadu allailaha illallah”

A hankali tace

“Ashhadu allailaha illallah” Wani kuka ne ya taho mishi yanayi yace “Wa ashhadu anna muhammadrasulullah” Cikin jan numfashi da kyar tace “Wa ashhadu anna muhammadrasulullah” Daidai nan Doctor nurse da ragowar ahalin MT gaba d’aya suka shigo d’akin ata dalilin kiran Doctor d’in da Granpa yayi. Cikin tsananin kuka dan har idanuwanta sun k’afe yace
“Salllallahu alaihi wa sallam”

A hankali yaji ta maimaita daga nan dip! Komai nata ya tsaya ta chak! Ta daina k’ok’arin janyo numfashin da take ta faman yi yana wahalar da ita. K’arar naurar da aka jojjona mata shima ya chanja.

Kifawa Granpa yayi abkanta yana tsananin kukan da rabonshi da yi tun ranar da Yaya da Doctor suka rasu. A hankali Likitan ya k’araso ya hau dudduba ta, chaan! Ya d’ago agogon hannunsa ya duba kafin ya juya ya kalla nurse d’in da suka shigo tare yace mata “Time of death! 1:30am”.

Kuka gaba d’ayansu suka saka lokaci guda, babu mai lallashin wani.

A hankali nurse d’in tace “su d’an bata guri zata gyarata ta saka mata auduga kar iska ya shiga kafin zuwa gobe tunda ta san dole zatayi kwanan keso”

A waje suka samu Arshaad da Aslam suna zaune kowa yayi jugum. Daman tunda suka ji Granpa ya kwala kiran Doctor sun san menene shiyasa ma suka k’i shiga yanzu kuma fitowar su kowa yana kuka ya sake tabbatar musu.

Da sauri Aslam ya mik’e ya fice a wajen haka shima Arshaad d’in dan basu san wa za su fara lallashi ba! Kowa ka ganshi kuka yake yi masu hawaye nayi hatta Granpa ya kasa tsaida hawayensa.

Cikin mintuna 15 nurse d’in ta fito ta mik’a musu kayanta da ta saka a box tace
“An gama. Saura rufe bill, daga nan su wuce da ita” A take Dad ya bita ya gama komai har file
sanann ya dawo suka turata kanainaye cikin farin bedsheet har mota shi da Daddy, su Mommy da Mom suka shigar da ita suna kuka.

Mom ce ta zauna a baya ta d’aura kan ta a kan cinyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.

Mommy kuma a gaba Dad yana tuk’i, a haa suka kama hanyar MT..

Aslam shi ya ja su Huda da Shuraim da Abba Arshaad kuma suka tafi tare da Daddy
Granpa kuma driver d’in da ya kawoshi ya maida shi tare da Gramma.

A hanya Granpa bai bari sun k’arasa ba ya kira Abba yace mishi “dan Allah a wuce da ita estate idan ba damuwa”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 63So Da Buri 66 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×