Matashiya ce zaune a acikin ɗaya daga cikin tsukakkin ɗakunan gidan yari, tana sanye da kayan gidan yari a jikinta, ta sa kanta a tsakankanin gwuiwoyinta. Ɗaya matashiyar ce da itama take sanyi da kayan gidan yarin ta ta su daga wajan da take a zaune ta matso dab da ita tasa hannu ta dafa ta tana faɗin “tun ɗazun da aka kawo ki gidan yarin-nan kuka kawai ki ke, shin wane irin laifi kika aikata har kika tsinci kanki a cikin wannan yanayin?” Ko motsi bata yi ba daga yanda take a zaune cikin jin haushi ta. . .