Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Matashiya ce zaune a  acikin ɗaya daga cikin tsukakkin ɗakunan gidan yari,  tana sanye da kayan gidan yari a jikinta,  ta sa kanta a tsakankanin gwuiwoyinta. Ɗaya matashiyar ce da itama take sanyi da kayan gidan yarin ta ta su daga wajan da take a zaune ta matso dab da ita tasa hannu ta dafa ta tana faɗin “tun ɗazun da aka kawo ki gidan yarin-nan kuka kawai ki ke, shin wane irin laifi kika aikata har kika tsinci kanki a cikin wannan yanayin?”  Ko motsi bata yi ba daga yanda take a zaune  cikin jin haushi ta ce. “koda yake ni miye ma nawa a ciki ai amsar ma a fili take kisan kai kika yi, shi ya kawo ki gidan-nan kamar dai ni ɗinnan, sai dai ban sani ba ko ƙaddararmu iri ɗaya ce?”

Ko ci kanki bata ce da ita ba hakan ya sa ta dawo gefe ta zauna sai dai zuciyarta na azalzalar ta da son jin labarin matashiyar da tun zuwanta kalma ɗaya bata iya jin ta furta ba kuka ne kawai take. Wasu mata da suke sanye da kayan ‘yan sanda irin na masu tsaron gidan yari su biyu suka zo suka buɗe ɗakin “oya-oya a fito a fito lokacin aiki ya yi!”1 Jiki a sanyaye ta miƙe tsaye tana tafiya a hankali domin ko ina na jikinta ciyo ya ke mata ga ƙafafafunta sunyi haushi saboda dukan da tasha a wajan ‘yan-sanda kafin zuwanta nan ɗin kullum sai ta sha duka na fitar hankali, ɗayar tana ganin sun buɗe ƙofa ta falla a guje ta fita dan ta san halinsu ba a masu tafiyar yanga yanzu sai mutum ya sha na jaki da kulaken da su ke hannunsu,  da ƙyar take iya taka ƙafanta ta dinga hanɓararta da ƙafa “ke mu fa ba a mana iskanci anan kina wani tafiyar yanga kamar kina a gidan ubanki!”  Kuka ta fashe da shi yayin da take ta ƙoƙarin ɗaga ƙafafunta  domin yin sauri amma hakan ya gagareta haka su ka sa ta gaba da duka da hantara har zuwa wani babban fili da ya ke ciki da mata ‘yan gidan yari kowa da irin aikin da ya ke, ma su tsaron su suna biye da su da abun bugu kuskure kaɗan su labtawa mutum,  ingiza ƙeyarta suka yi wajan cirar haki da ƙyar ta iya duƙawa tana cira da hannunta suna dukan ta da zagi.

Haƙiƙa rayuwa tattare take da shafukan ƙaddarori wasu takan  zo masu da sauƙi wasu kuma gaunin da take zuwa masu da ita ya wuce misali, ita dai tata ƙaddarar har bata san da wace irin suna zata kira ta da shi ba, mutanen da suke tare da ita su ma suna aikin tausayinta ya cika zuciyarsu, ta kusa da ita ta ɗago ta kalli masu tsaron su  “haba ku kuwa dan Allah ku tausaya mata ku duba yanda ƙafafunta ya yi haushi Allah kaɗai ya san irin azabar da take ji, dukan jikinta a farfashe ya ke da shacin bulala“ laftawa mai maganar bulala ta yi tana faɗa “ke har tausayi kika sani! Banzaye mararsa imani, tana son jikin nata ne za ta je ta aikata rashin imani, maza ku kama aikin gaban ku kar na sake jin waninku ya ce tak!” 

“Kema dai da son janyowa kai wahala waɗannan mutanen ai ba su san Allah ba, babu tausayi a zuciyarsu, kawai idan kika ga suna abunsu kawo na gani ki zuba mau” ta kusa da ita ta yi magana ƙasa-ƙasa.

“Allah dai ya fitar da mu daga wannan baƙar izaya, ya rabamu da aikin Da-nasani”

“Ami… Dukan da a kai masu ne ya sa ta haɗiye sauran maganar ba tare da ta shiryawa hakan ba. Wuni ta yi ana sanya ta aiki mai matuƙar jigata sai azahar suka je wajan sallah, banɗakunan biyu da a ke zuwa dan yin lalura duk mutane a  tsaye suna bin layi sai hayaniya ake wa na ciki a kan suyi su fito sun daɗe, tana tunanin yadda za tayi babu buta duk an ɗauka wasu na tsaye suna jiran ‘yan uwansu su gama su basu, wacce suke ɗaki ɗaya ce ta tsaya gefenta ta bata wani ƙoƙon roba da ya ke da ruwa  “ga ruwa kuma idan kika ce za ki yi sanya duk wanda ya ke wajan nan sai ya gama lalurarsa ya barki a tsaye”

Miƙa hannu tayi ta karɓa tana takawa a hankali ta ƙarasa wajan layin, ta jima tsaye ƙiris ya rage ta saki  fitsarin a wando dan ba ƙaramin matsuwa ta yi ba, ta zo kan layi kenan ta sa ƙafarta ɗaya ciki ɗaya ƙafar a waje wata ɓukekiya ta zo da sauri ta bangajeta tayi taga-taga za ta fadi ta yi saurin dafa ginin banɗakin matar ta shige ta rufe ƙofar kwanon da har ya fara ɓallewa da kuma tsatsa, wacce take alwala ta ce. “Gara ma ki je can baya ki yi lalurarki a kan ki jira wannan ɓukekiyar jakkar kashi sai ta yi minti talatin bata fito ba kuma babu wanda ya isa yayi magana, idan ka yi magana ta zaune abin banza su kansu hukumomin gidan-nan shakkunta su ke, waɗancan kuma ba nasiha zasu maki ki shiga ba”  bata ce da ita komai ba, ta sake faɗin “ki yi sauri kije tun kan marasa imanin can su zo su ganki a wajan, idan kuma baki gaji da tsayuwar ba sai kiyi ta tsayi”  ta ƙarasa alwala ta bar wajan, bata da mafitar da ya wuce tabi shawarar matar, da sauri ta je baya wajan ƙazanta ga banhaya duk anyi wani ya bushe wani kuma ba a jima da yi ba, da ƙyar ta samu wani wajan da ya fi ɗan sauƙi ta yi fitsari tana gama yin tsalki ta tashi tsaye kenan sai ga ɗaya daga cikin ma su tsaronsu tazo wajan “ke uban waye ya faɗa maki ana fitsari a nan!?” Wuri-wuri da idanunta ta yi “ba tambayar ki nake ba!?”

“Kiyi haƙuri yau na zo baƙuwa ce ni”

“Sannu raɓa kinji, maza duƙa ki gyara filin nan bana son ganin wata ƙazanta a wajan!” Cikin tashin hankali ta ce. “duk kashi ne fa a wajan”

“Sai a ka yi ya idan kashi ne? Maza kisa hannu ki kwashe ki gyara”

“Dan Allah ki yi haƙuri ki ƙyaleni wallahi na maki alƙawarin duk rintsi ba zan sake zuwa wajan… Wani irin duka ta kai mata da icce a kan kunkuminta har sai da ta sunkuya ta sake wata irin ƙara “ba na son musu maza ki yi abinda na sa ki idan kuma ba haka ba yanzu sai na karkarya ƙasusuwan jikin ki, kuma hannu za ki sa ki kwashe!!” Kallon ƙazantar wajan take cike da tashin hankali ta yanda za’a ce mutum mai rai ne zai sa hannu ya kwashe ya gyara wajan, ‘wayyo Allah ƙaddara me ya sa za ki mini  haka me ya sa za ki cilloni cikin wannan mummunan rayuwa?’ a ranta addu’a take Allah ya tasheta daga wannan mummunan mafarkin, ɗaiɗaikun mutanen da su suka yi saura a wajan duk sun tsaya suna kallon su, wasu zuciyoyinsu cike da tausayin ta, wasu kuma dariya su ke suna fadin ai kowa ya so kwana lafiya shi ya so, tsuntsun da ya ja ruwa  shi ruwan kan doka, wacce su ke ɗaki ɗaya ta ce “haba ku kuwa  me yasa kuke mata dariya da yada magana haka, dukanmu ƙaddara ce ta cillomu cikin gidan nan ya kamata kuwa mu so juna, mu tausayawa juna“

“Hihihi ƙaddara ko san rai, ba wata ƙaddara malama duk wanda kika  gani a gidan nan san ransa ne ya kawo shi ihin!”

“Barta  da wani tauhidin ta can, da ta ji me yarinya ta aikata ai da sai ta ta ƙyamace ta da ba za ta so ta ganta a kusa da ita ba bare har wani tausayinta ya shigeta, ɗazun ina jin ma’aikatan gidanan suna maganar laifin da ta aikata da ɗebe mata albarka” shiru ta yi bata iya cewa komai ba, domin dukansu masifaffu ne abu kaɗan zasu hau dukan mutum kafin a karɓeka ka ji jiki,  tsawa mai tsaron nasu ta daka ma su “ku ɓace mini da gani kowa ya kama gaban shi tun kan na waiwayo kanku!” Da sauri suka bar wajan sai wacce suke ɗaki ɗaya da ta laɓe ta gefe tana leƙen yadda matar nan take labtawa matashiyar icce cikin rashin tausayi da imani,  hawaye su ka ciko idanunta,  hango wata daga cikin ma’aikatan ta nufo wajan ya sa ta bar wajan da gudu, yayinda matashiyar ta ke kallon ƙazantar da ba ita ce ta yi ba da ake so asa ta kwasa dole,  wani dukan aka mata da ya sata gantsarewa ta buɗe baki tana ihu da muryarta ko fita ba ta yi, “wallahi idan na ƙirga uku ba ki fara ba sai na maki dukan kawo wuƙa!” Ta ya za ta iya kwasar kashi da hannunta.

Ta tabbatar idan har bata yi aikin nan ba tabbas wahala zata sha bata da mafita da ya wuce ta yi, haka ta dinga kwasa tana kaiwa wajan da aka ajiye babban roban da ake zuba shara tana yi tana kuka, sosai ta galabaita ga tashin zuciya ga duka, tana duƙawa amai ya zo mata ta dinga yunƙurin amai ta kasa aman saboda babu komai a cikinta, gandroba ta ce. “Ni za ki yi wa kissa na iya da irin ku ai”  ta ɗaga abun bugu za ta daketa gandroba da take a can ɗan nesa dasu ta yi magana cikin ɗaga murya “ƙyaleta haka!” Ta matso kusa tana faɗin “ya isa haka ai gobe ba zata ƙara ba dan nasan ta karantu,  maza ki je ki wanke hannayen ki” da ƙyar ta iya yunƙurawa daga sunkuyar da tayi ta bar wajan wani ɗan guntun sabulu ta gani a gindin rizabuwa ta ɗauka ta wanke hannayenta, sam bata wani ji ta gamsu da wanke hannun ba kawai dai ba yanda zata yi ne dan ji take kamar ta yanke hannayen duka, zuwa ta yi ta roƙi gandroba da su bata dama ta yi wanka su bata wasu kayan ta yi sallah, wata irin harara ta dalla ma ta “wato ke ga ki a cikin gidanki iko sai yadda ki ka so yi ko!?”

“Dan Allah ki taimakeni sallah zanyi nayi kwasar najasa jikina ya ɓaci dan Annabi” ta yi maganar cike da magiya, shiru ta mata kamar ba zata amsa mata ba, ba jurewa tsayuwar take ba saboda ciyon da yake jikinta ga tashin zuciya ji take kamar ta zauna a wajan amma ina ta san wani laifin za ta ƙarawa kanta, “shi kenan ina zuwa” gandroba ta faɗa tare da juyawa, jim kaɗan ta dawo ɗauke da wasu kayan  da sabulon wanka  “ga shi kiyi sauri ki fito kafin manyan mu su zo, sannan ki wanke na jikin ki ga omo” da sauri ta karɓa tana mata godiya.

Tun bayan dawowar su ɗaki take a dunƙule waje ɗaya kamar dunƙulen dawo, wani irin sanyi take ji, ga zogin zuciya, idan ta rufe idanunta abubuwa da yawa su ke dawo mata a cikin idanunta kamar a yanzu su ke faruwa, tashi ta yi ta zauna ta jingina bayanta ga  kusurwar ɗakin, ta ruƙunƙume jikinta  sam bata so ta rufe idanunta da suke dawo mata da hoton abinda ya gabata tangaram kamar a yanzu ne suke faruwa. Damuwa ta gama shiga lungu da saƙo na zuciyarta yayin da  ƙwaƙwalwarta take dab da tarwatsewa saboda tunani,   “Zainab”!! Zabura tayi tana ƙara har sai da ta gaura kanta da bango cikin firgici  Safiya da take bacci ta miƙe  “ke lafiya me ya faru”? Buɗe idanunta ta yi ganin wacce take gabanta  ajiyar zuciya tayi  tare da komawa ta zauna, itama matashiyar ta zauna dab da ita  “ko mafarki kika yi?”  Shiru ta yi tana gyaɗa kanta domin ita bata ma san ya zata kiran abun ba ta dai san ba bacci ta ke ba to mafarki ake ba a cikin bacci ba?”

Ta fahimci ba amsa za ta ba ta ba hakan ya sa ba ta sake tambayarta ba sai cewa ta yi “Allah ya kyauta amma ki sa wa zuciyarki natsuwa damuwa ko kuka ba sa sauya kaifin ƙaddara face ƙarawa kai wata lalurar, kiyi ƙoƙarin sabawa da rayuwar da kika tsinci kanki a ciki kawai shi ne mafitar ki” tana gama faɗa ta koma ta kwanta duk da kwanciyar ba daɗi ga sauro ga rashin wadataccen wuri da zaka samu ka miƙe jikin ka sosai. Bata iya rintsawa ba a zaune ta kwana zuciyarta da jikinta ko wanne da irin ciyon da ya ke cikin sa.

Washe-gari suka fito wajan aiki sai dai da ƙyar ta iya kaiwa babban filin ta zube a wajan, Safiya da suke tare tayi saurin duƙawa tana faɗin “SubhanalLah sannu” gandroba ta kai mata duka ko motsi ta kasa yi, ta kai hannu ta fizgota taji jikinta ya yi rau zafi sosai kamar wuta, “ke Safiya ba ta da lafiya ne?”
  “Ban sani ba  amma dai na jita cikin dare tana ta kakari na tambayeta kuma ta mini shiru” 

Gandroba ta fita zuwa wajan manyan hukumomin gidan,  cikin girmamawa ta ce.

“Yallaɓai wacce aka kawo jiya tana can a kwance bata da lafiya sosai kuma” ajiye fayel ɗin da yake hannun shi ya yi yana faɗin “yarinyar da aka kawo da safe ya ma sunanta” macen da take a zaune gefe ta ce. “Sunanta Zainab”

“Oh na gane” wayar office ya ɗauka ya kira bayan yayi magana ya kalli abokiyar aikin shi “Naja  ku je  ku kaita asibitin cikin gidan nan”

“Yallaɓai da ƙyar fa idan za ta iya tafiya ga asibitin da ɗan tafiya”

“Ok. Isa direba ya ɗauke ku da mota ya kai ku”

Tashi ta yi tsaye tana faɗin “ok Yallaɓai.”

Safiya ta so ta bi su aka hanata, ba dan ranta yaso ba ta haƙura, haka kawai taji yarinyar a ranta, da kuma tausayinta, haka ta bi ayarin masu aiki aranta tana mai addu’ar Allah ya ba ta lafiya. Zainab addu’a take Allah ya ɗauke rayuwarta ta huta da wannan baƙar rayuwar mai cike da baƙin ciki marar misaltuwa.  Tunda suka isa asibitin bayan Dr Mansur ya gama dubata ya  bata gado aka sa mata ruwan jiki da wasu allurai, ba a jima ba bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Naja ta kalle Dr Mansur da ya gama ɗura mata ruwa  “Dr me ya ke damunta ne?”

“Tana da malaria, sannan kuma ga yunwar da taci ƙarfinta,  ga jininta ya hau duk da ba sosai jinin ya hau ba, ba mamaki akwai abinda take tunani ko kuma rashin bacci ne ya haifar mata da hakan”

“Tunani ai na banza ne Dr Mansur idan har kana tsoron tsintar kanka a cikin irin wannan yanayin ba zaka sa kanka aikin da-na-sani ba da bin zuciya da za ta kai mutum ga hawa dokin halaka”

“Allah ya kyauta, bari na rubuta magani sai a karɓo mata” ya ce da Nurse ta biyo shi ta karɓi takardar magani ta kawo masu, bayan sun fita Naja ta dube Gandrobar “ki zauna da ita, ni zan koma gun aiki idan an kawo takardar magani sai ki karɓo”

“To a sauka lafiya.”

Ba ta farka ba sai gab da magarib ta farka, tana buɗe idanunta ta ganta kwance akan gadon asibiti, ‘me yasa mutuwa bata ɗauke ta ba, me yasa zata barta ta dinga azabtuwa da wannan rayuwar da bata da amfani a wajanta’ maganar Gandroba ce ta dawo da ita daga tunanin da take  “kin farka kenan bari na je na kira likita ya zo ya duba ki ya bamu sallama na gaji da zaman asibitin nan wallahi” tayi maganar tana tashi daga kan kujera bayan fitar ta Zainab ta tashi da ƙyar ta zauna tare da jingina bayanta da ƙarfen gadon, kallon ruwan da ake ƙara mata ta yi  saura kaɗan su ƙare, lumshe idanunta ta yi,   idanunta suka fara dawo mata da abinda ya gabata a baya.

“Zainab kina ina ne”? Fitowa ta yi daga uwar ɗakin tana yatsina fuska “ga ni miye kake wani yi min kiran mafarauta?”  Murmushi yayi kafin ya ce. “Allah ya ba ki haƙuri mai tagwayen suna, yanzu dai taimaka kizo mu je ɗakina kiga wani abun” kawar da kanta tayi gefe tana shan ƙamshi “ko miye nuna min a nan ɗin”

“Haba ki dai zo ki gani Please” ya yi maganar cikin magiya, “ba fa inda za ni” ya kai hannunsa ya janyo mata hannu ta fizge da ƙarfi tana faɗin “wallahi na faɗama ka daina gigin taɓa min jikina”! Ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “miye dan na taɓa jikin ki ba nawa ba ne, sadaki fa na biya”

“Shikenan ka sake taɓani ɗin ka gani!” riƙe kansa yayi  “wai ke miye matsalarki ne Zainab, ke a wajanki abu baya wucewa ne?”  Ya matsa dab da ita zai janyota jikinsa ta yi saurin gaucewa tana ɗaga murya “wallahi idan ka yi gigin sake taɓani zan kashe ka!!”

“Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un Zainab kisa ƙanen nawa ne za ki kashe Zainab!”

Dukansu kallon ƙofar shigowa falon suka yi Hajiya Laila ce take a tsaye bakin ƙofa hannu a gaba tana kallonsu da matuƙar tsoro “eh ɗin idan kuma kina musu ki sa shi gwada hakan” ta murguɗa baki ta juya ta shige ɗaki. “Ai ba tafiya zaki yi ba dawowa za ki yi ki sake faɗan abinda kika faɗa marar mutunci marar kunyar banza!” Zata bi bayanta yayi saurin shan gabanta ya karyar da kai “Aunty Laila Dan Allah ki ƙyaleta ɓacin rai ne kawai da yarinta ya ke damunta”

“Dalla can ai tun farko ba yadda bamu yi da kai ba a kan kar ka auri yarinyar nan amma baƙin nacinka ya sa kaje ka auro mana ita, yanzu  ga shi nan tana gasa ma aya a hannu, hadda ikirarin kisa to wallahi dole mu shigo da hukuma ciki domin a yi wa lamarin tufka”

“Oh Aunty Laila kema dai kin san faɗa kawai take yi babu yadda za a yi ta aikata”
“Tunda ta furta tabbas abinda ya ke  zuciyarta ne ta fito da shi fili munafuka fito!” Ya sake shan gabanta yana mata magiya a kan tabar maganar, da ƙyar ya iya shawo kanta ta tafi tare da sa ta ɗaukar mashi alƙawarin ba zata faɗawa mahaifiyarsu ba. Duk abinda suke faɗa tana jikin ƙofa tana sauraronsu tana jin fitar Hajiya Laila tayiwa ƙofarta key ta je ta kwanta zuciyarta na mata suya, ba ƙaramin haushin Alhaji Umar take ji ba… Shigowar Dr ne tare da Gandroba ne ya dawo da ita daga  tunanin da take, Dr ya tsaya daga gefenta “sannu ko” kai kawai ta gyaɗa mashi tana  sa bayan ɗaya hannun tana goge hawayen da ya ke fuskarta, “ya jikin na ki? Kina jin wani ciyo a jikin ki”? ‘To ita me zata ce da shi komaima tana ji miye ne ma bata ji’ dafa kan gadon ya yi yana faɗin “Zainab  ba wata damuwa ne”?  Tsawa Gandroba ta daka mata  “ke ba za ki ba tambayar ki ake ba!?” Hawayen da take ƙoƙarin mayarwa ne suka shiga zarya a fuskarta cikin rawar murya  “eh a’a” ɗaga mata hannu ya yi  “shikenan ya isa idan kin samu natsuwa sai kiyi magana, kema ba’a yiwa marar lafiya haka” ya cire mata ruwan yana faɗin za ki iya tashi ki yi wanka da sallah idan anyi isha kafin na tafi gida zan zo na sake ɗaura maki wasu ruwan”

“Au likita ai na ɗauka sallamar mu zaka yi” kallonta yayi a ransa yana ji kamar ya maketa ‘saboda ba ‘yarta ba ce shiyasa take so a sallamesu a wannan yanayin’ “A’a, ba yau ba” ya bata amsa a taƙaice yayi ficewarshi , takaici ne ya rufe mata zuciya, ta dinga harararta ita dai komai bata iya cewa da ita ba sai tashi da tayi za ta bude kofa ta fita  “gidan Ubanwa kuma za ki je?”

“Banɗaki”

“To dawo ga shi anan” ta nuna mata, ta shiga.

Bayan sallah isha ya turo Nurse ta sake sa mata ruwan jiki, Gandroba anan inda tayi isha ta ɓingire da bacci,  Zainab na jin babu motsin kowa ta fizgi kalular dake hannunta ta cire ruwan ba ta damu da jinin da ke fita a hannunta ba, a hankali ta sauko daga kan gadon tana kallon   Gandroba baccinta take harda minshari, ta ciro wata igiya mai ɗan tsayi da tagani tun shigarta banɗaki ta ɓoye cikin jikinta bayan ta kashe fanka ta janyo kujerar roba ta taka ta ɗaura igiyar a jikin fankan kamar yanda ta gani a wani Film ɗin India tasa a kanta ta ɗaure rufe idanunta  aranta tana jin kashe kanta shi ne kaɗai mafita dan ba ta ga amfanin rayuwarta ba. Ta sa ƙafa ta ture kujerar nan take ta fara wutsil-wutsil da kakarin mutuwa.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Su Ne Sila 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×