Ina mai bada haƙuri a kan Kuskuren da aka samu wajan da nace Zainab yar asalin jahar Katsina ce a garin Saulawa. ‘Yar asalin jahar Kaduna ce a garin Saulawa Ikara. Duk da na gyara a wasu page ɗin amma an riga da an saki wasu ɗin. Nagode sosai.
Tarba aka masu ta musamman kowa na nuna farin cikinsa da ziyarar da suka kawo masu, a gidan kakarsu Gwaggo Hari suka sauka. da dare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa da miyar taushe ta sha tantaƙwashi da man shanu, "gafarar ku dai masu. . .