Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Ina mai bada haƙuri a kan Kuskuren da aka samu wajan da nace Zainab yar asalin jahar Katsina ce a garin Saulawa. ‘Yar asalin jahar Kaduna ce a garin Saulawa Ikara. Duk da na gyara a wasu page ɗin amma an riga da an saki wasu ɗin. Nagode sosai.

Tarba aka masu ta musamman kowa na nuna farin cikinsa da ziyarar da suka kawo masu, a gidan kakarsu Gwaggo Hari suka sauka. da dare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa da miyar taushe ta sha tantaƙwashi da man shanu, “gafarar ku dai masu gida Kuna ciki”?   Wata dattijuwa tayi maganar tana ƙoƙarin kutso kai cikin gidan, gwaggo Hari da take zaune a kan tabarmar kaba tare da su Shahid tana masu tatsuniya suna ta dariya ta kai dubanta ga ƙofar tana faɗin “maraba da Tasalla ƙaraso kin ganni nan tare da mutanena muna shan fira.”

“Ai kam dai barakallah har daga waje ana jiyo dariyar su” ta faɗa tana mai zama akan tabarmar tare da ajiye languna biyu babba da ƙarama da ke a hannunta, Zainab da  Raliya suka gaisheta ta amsa da fara’a tana faɗin

“‘yan mata sannunku da hanya kun zo lafiya,

ya iyayen naku”?

“Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ku” Zainab ta bata amsa,  Tasalla ta nunawa gwaggo Hari abinci a baiwa baƙi, gwaggo Hari ta yita godeya,  cikin ƙasa da murya  Zainab ta ce; “ke ‘yar Nono wai haka ake yi anan kowa yayi ta kawo abinci, tun ina ƙirga kwanun abincin da aka kawo har na gaji” wacce aka kira da ‘yar Nono ta harari Zainab tana faɗin “na faɗa maki ki daina kirana da ‘yar Nono ko?”

“Hahaha haka na ji Gwaggo Hari na kiran ki harda wasu ma ‘yan gidan nan”

“Ai dan ba yanda zanyi ne Allah da za su daku da  sai na dake su ke har kirɓesu sai na yi, ai kinga duk yaran gidan-nan babu mai gigin kirana da hakan, Allah na tsani sunan nan, kawai ki kirani da Ruƙayya”  dariya Raliya tayi tana faɗin  “wai ni kam me yasa ake kiran ki da wannan sunan ne”

“Mtsw! Kawai fa sanda nake yarinya ina son nonon shanu sosai haka zan je wajan nagge idan ana tatsa sai nasa bakina tun ana hanani har aka ƙyaleni shi ne fa aka mayar dani ‘yar nono”

“Ai da ni ce su ‘yar Nagge zan  ce ba ‘yar nono ba” cewar Zainab tana ƙyalƙyalar dariya,  Ruƙayya ta kai mata duka tana faɗin “A’a Naggen ce ma” dukansu suna dariya, ta ɗan tsagaita dariyar kafin daga bisani ta ce “kin tambayeni ɗazun ai dan ba ki saba zuwa bane al’adar karkara kenan a duk sanda baƙo ya zo abokan arziƙi su ta kawo girki iri-iri wasu ma ba dafaffi za su kawo ba shinkafa ɗanya da su nama, idan kin zo irin lokacin da aka yi girbi har wake da sauran cimaka duk kawowa ake”
  “Kai gaskiya al’ada mai matuƙar burgewa” cewar Raliya “wallahi kuwa gwanin sha’awa, Allah ni na ɗauka idan na zo zan mugun takura amma sai naga saɓanin tunanina garin ya mun yanayin wajan gwanin daɗi”

“Sai ma mun fita gobe na nuna maku gari.”

“Allah ya nuna mana” Zainab ta faɗa da murna, daga nan fa suka ɗora sabuwar fira, Ruƙayya jikanyar Gwaggo Hari ce ‘yar babbar ‘yarta, a wajanta take zama. Sai zaga dangi da abokan arziƙi suke duk inda suka je  ana masu sha tara ta arziƙi. Ana saura kwana biyu su tafi, da yamma tana kwance ɗakin Matar Kawunta, Inna Hansa’u ta shigo tana faɗin “Ke ba zaki gidan Baffa   Habu bane?” Ta ɗan ɗago kanta kaɗan tana faɗin “eh kaina ne yake ciyo shi yasa, Raliya da su Shahid dai za su je”

Raliya da take shigowa tare da Ruƙayya ta ce “nifa na faɗa maki idan dai ba za ki ba to nima ba zan je ba”

“Inna ba fa  wani ciyon kai da take kawai tsoro ne ya sa ta ce ba za ta ba tunda taji na ce ƙauyen sai an tsallaka ruwa shi kenan ta ce ba za ta ba, wai tana tsoron shiga kwale-kwale” Ruƙayya ta yi maganar tana mai zama kusa da Zainab aikuwa tana zama tana mintsile ta har sai da tasa ‘yar ƙara daga “faɗar gaskiya sai cin zali!” Murmushi Inna ta yi za ta yi magana ta jiyo Gwaggo hari na ƙwalla mata kira da sauri ta amsa kiran tare da fitowa ɗakin Zainab ta tashi zaune tana faɗin “kai ‘yar Nono Allah ya shiryeki kawai sai ki sani jin kunya”

“Wai dai ba zaki daina kirana da ‘yar Nono ba ko?”

“Anƙi a daina ɗin ke ‘yar Nagge ma zan dinga kiran ki daga yanzu”

“Za ki sani ne yarinya bashi kika ɗauka, kuma Allah ko gobe kika shirga ƙarya nan take zan tona maki asiri”  Zainab ta ce; “idan kin sake ganina ko?  Mu da jibi iwarhaka mun kai garinmu” Raliya ta ce “kun san me Allah har bana so jibi ta zo kamar mu yi zamanmu garin ya mun daɗi”

“Yadda kika san kin shiga zuciyata wallahi, Ruƙaya za muyi kewarki dan Allah kizo mu tafi tare ki ma koma wajanmu da zama kinga shikenan mu zama mu uku ko?” Ta ƙarasa maganar tana kallon Raliya”

“Eh wallahi kawai mu je mu faɗawa Gwaggo Hari” Ruƙayya ta  gyara zamanta tana faɗin

“hum-um ba inda zan je kun manta na faɗa maku a shekarar nan zan gama nima muna da jarabawa, amma in dan kewa kam zanyi kewa harma sai na fi ku” Zainab za ta yi magana Inna ta shigo ɗakin tana faɗin “Zainab ki zo ana sallama da ke a waje” cikin mamaki ta kalle Inna “sallama kuma Inna? Ni wa na sani a garin nan?”

“Idan har baki san su ba ai su sun sanki ki tashi kije daga gidan Baba Haladu aka turo shi”

“Hum-um ni gaskiya ba inda zan je, kawai ban san mutum ba sai ya zo nemana to nayi masa me?”

“Idan kin je za ki ga ko waye kuma ai zuwan da za ki yi ne zai sa ki fahimci dalilin zuwan nasa” shiru ta mata “wai ba za ki tashi ki je ba?”

“Ni fa ba za ni ba” Inna tayi juyen duniya ta je ko gaisawa ne suyi ta kafe Gwaggo Hari ta tsaya daga bakin ƙofa tana faɗa “wai Hansa’u baki faɗa mata ba ne?”

“Na faɗa mata Inna tana zuwa”  ta dawo ga kallonta ga Zainab  “kinga ki je ku gaisa kawai tafiya za ki yi da kin tafi ba shikenan an rabu lafiya ba, amma yanzu idan kika ƙi tafiya ba Gwaggo Hari ba har Baba Haladu za su yi ma ki faɗa ne” da ƙyar ta rarrasheta ta yarda ta tafi su uku suka fita. Magidanci ne da ba zai haura shekara arba’in da biyu zuwa da huɗu ba, yana zaune a kan tabarma a cikin soron gidan ya tanƙwashe ƙafafunsa yana danne-danne a cikin babbar wayarsa, sanye yake cikin farar shidda mai babban riga, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci shi ɗin mai kuɗi ne domin yanda fatar jikinsa ta kwanta da kuma tsadaddun kayan jikinsa. Sallamarsu ce tasa ya ɗauke idanunsa daga kan wayar ya mayar da su akan ƙofa da murmushi a fuskarsa ya amsa sallamar “sannunku da fitowa” Raliya da Ruƙayya kaɗai suka amsa tare da gaishe shi cikin girmamawa, ita kuma tana daga gefe fuskarta tamau babu annuri, gwaggo Hari ta aiko tana kiransu Ruƙayya za su tafi ta biyo bayansu ɗan aiken ya ce; “cewa ta yi su Yaya Ruƙayya kaɗai ba da ke ba” ta dalla masa harara ta koma ta tsaya su Raliya suka tafi suna ƙumshe dariyarsu. Kallonta ya yi daga ƙasa har sama aransa yana faɗin ‘Masha-Allah’  ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce “ki zauna kar ƙafafunki su yi sanyi.”

“Nan ɗinma ya yi” tayi maganar tana ƙara ɗaure fuska, “shikenan bari na kira gwaggo Hari ɗin na san idan har ita ta yi ma ki magana za ki ji ko?” Tana harararsa ta ƙasan ido ta zauna a kan wani dutse da ya ke ajiye daga ƙofa, murmushi ya yi yana faɗin “ko ke fa, ya gidan da fatan kina lafiya?”

“Lafiya” ta ba shi amsa a taƙaice, gyara zamansa ya yi kafin daga bisani ya ce “am na san ba ki sanni ba domin wannan ne karon farko da kika taɓa ganina, sunana Umar haifaffen garin Saulawa ne ina zaune a cikin Kaduna tare da iyalina, ina ɗan taɓa kasuwanci anan gida da kuma ƙasashen waje, ina da mata ɗaya da ‘ya’ya huɗu” ya yi shiru yana kallonta sam babu annuri a fuskarta hakan bai dame shi ba ya cigaba da faɗin “jiya nazo gaida iyayena kamar yanda na saba gidanmu yana kusa da na Baba Haladu, da yamma naga kun fito gidan tare da waɗanan ƙawayenki ne ko ‘yan’uwa ban dai sani ba” ya ɗan tsahirta kafin ya ci gaba da magana “magana ta gaskiya ina ganinki naji a raina na samu matar aure, hakan yasa banyi ƙasan a gwiwa ba na tambaye ƙanena da a tare muka ga fitowarku ya ke faɗa min kunzo ganin gida ne, hakan yasa na samu Baba na faɗa masa abinda yake a raina ya turoni mu fahimci juna” shiru  yayi yana mai zuba mata idanu ji take kamar ta buɗe baki tayi ta surfa masa zagi ‘kawai tsoho da shi ya rasa wacce zai so sai ita, tabɗijam lallaima ya raina mata wayo wallahi’ ta yi maganar a zuciyarta jin taƙi ta ce da shi komai ya sa ya ce “Zainab kin barni ina ta zuba kin ƙi ki ce komai, ina so na ji idan har kin aminta da ni, ko na ba ki lokaci ki yi tunani?”  ‘tab har wani tunani nake da shi bayan na faɗa ma ka gaskiyar ba ka min ba a ƙara gaba’ afili kuwa cewa tayi.

“Na ji ni ba aure zanyi ba karatu nake” yana murmushi ya ce “In har karatu ne ni ai ban da matsala a kwai ‘yata sai ku cigaba da karatu tare dama kanku zai zo ɗaya” miƙewa tayi tsaye tana yatsinar fuska “me ya faru?”

“Cewa fa ka yi ni sa’ar ‘yarka ce kuma a hakan kake sona zan aure ka?”  Gyaɗa kai tayi kamar ƙadangaruwa “A’a ni gaskiya, kai ni fa ba ma aure zanyi ba” tana gama faɗa ta shige ciki da sauri, murmushi ya yi “da sannu zan shawo kanki, a kwai yarinta a tare da ke.” Waje ya je ya samu wani matashi ya ba shi sayayyar da yayi mata aka shiga da su gidan bayan ya fito ya sallame shi da dubu biyu ya ja mota ya tafi ya bar matashin yana ta godeya.

Cikin gidan Gwaggo Hari sai guɗa take tana  faɗin “ikon Allah ashe rabo ne ya kawo ki garin-nan gaskiya yarinya kinyi goshi kin kuwa san waye Alhaji Umar?” Cikin takaici Zainab ta ce “to ni me ya shafeni da ko shi waye ni bana son shi ku ma mayar masa da kayan shi” harararta gwaggo Hari tayi tana faɗin “to idan ba kya son  shi wa ki ke so?”

“Ba wanda nake so, ni karatu zanyi”

“To ba ki isa ba da ke da bokon duk kunci… Ta gunduma mata ashar tana cewa “ko Ubanki Umaru bai isa ya tsallake maganar Yaya Haladu ba bare ke, tunda har ya turo shi na tabbata ya masa don haka babu fashi aure kam anyi angama”

“Tabɗijam sai naga wanda zai min dole to” duka Gwaggo Hari ta kai mata tana faɗin “ja’irar banza ni za ki yi wa rashin kunya? ai kuwa za ki sani, ke wallahi idan kika sa wasa sai na hanaki tafiya a ɗaura auren naga ta tsiya!” Inna Hansa’u ta shiga baiwa Gwaggo Hari haƙuri sai dai ina kamar ƙara zugata take inda take shiga ba a nan take fita ba, Zainab ta wuce fau tana kuka Raliya tabi bayanta tana zuwa kayansu ta fara haɗawa “wai miye haka Zainab don Allah kiyi haƙuri kibi komai a sannu, tunda barin garin za mu yi muna tafiya shikenan amma kinga bai kamata gwaggo na faɗa kina faɗa ba” magana take cikin masifa “dan me zan ja baki na yi shiru, haka kawai ba zan faɗi abin da yake raina ba sai na ja baki na yi shiru a cutar da ni, ni gida zan tafiyata” 
“Gida kuma? Yanzu da yamman nan, don Al… Ta yi saurin taran numfashinta “kinga idan kin tashi ki zo mu tafi idan kuma ba ki tashi ba ni kinga tafiyata” ta faɗa tana mai rufe masu akwatin ta ɗauke mayafinta ta fito Raliya ta ɗauko nata da sauran kayansu tana faɗin “ni kam me zai zaunar da ni dama ai dan ki na zo.”

Tsakar gidan Inna da take ta tausar Gwaggo da take antayowa Zainab zagi ta hango su janye da kayansu da sauri ta taso, Zainab ta kira ƙaramin yaron Inna ɗan shekara takwas “Ibrahim ina su Na’ila?”

“Suna ƙofar gida”

“Yawwa maza je ka kira su, ko ma dai ƙyalesu mu samesu a wajan”

“Zainab ina za ku je da kaya?” Inna tayi tambayar tana mai ƙoƙarin riƙe akwatin, fizgewa Zainab tayi tana faɗin “gidanmu zan tafi”

“Haba ai nan ɗinma  gidan ku ne, kiyi haƙuri ki dawo ku zauna, ita matsala ba da zafi ake warwareta ba, idan aka bi komai da sannu sai kiga an warware matsalar cikin sauƙi,”

Ruƙayya ta ƙaraso wajan tana bata  haƙuri “ke kawai sai ki biyewa faɗan Inna kice za ki tafi gida yanzu da yamman nan, a yanda tsaro yayi ƙaranci”

“Ku daina bata haƙuri yanzu nan zanyi maganin rashin kunyarta ” ta faɗa tana janyo wani babban icce da yake ajiye gefenta tayo kansu, Raliya ta tsorata tana ƙoƙarin janyo Zainab su gudu ɗaki amma ta kafe taƙi tafiya, Ruƙayya ta dubeta “wallahi ki rufawa kanki asiri ki shige ɗaki ki rufe ƙofa  tsab Gwaggo  za ta dake ki da iccen-nan” Inna ta tare gaban Gwaggo Har bangajeta tayi  har sai da tayi taga-taga za ta faɗi Allah dai ya taimaketa bata kai ƙasa ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Su Ne Sila 2Su ne sila 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×