“Kai kai SubhanalLah! Inna lafiya”? Kawo Sani ya yi maganar tare da ƙarasuwa da sassarfa duk da gudun da ya yi sai da Inna ta yi nasarar kai mata duka, hannunta ta kai wajan kare fuskarta da a ka kaiwa harin dukan hakan ya sa a ka sameta ahannun dakakkiyar zuciya ce ga Zainab duk da azaban dukan da taji motsi ba ta yi ba za ta kai mata na biyun Kawo Sani ya yi saurin riƙi iccen cikin tashin hankali ya ce;
“SubhanalLah Inna mene ne haka duka da icce irin wannan wani irin laifi ne ta yi haka” cikin kunmfar baki Inna ta ce; “Sani sakar min iccen nan na ce ka sakar min iccen! yarinyar banza marar tarbiya wato haka Umaru ya ma ki taki tarbiyar raina manya ko”? Inna ce taja Zainab tana tirjewa tana komai haka taja ta ta ƙarfi su ka shiga ɗaki tana ma ta faɗan kafiyar da take da shi, da ƙyar kawo Sani ya lallashi Inna ta yi shiru da faɗan da take su ka zauna a inda ta tasu ya ke tambayarta abinda ya faru tana gama kuromasa bayani ya girgiza kai yana faɗin “a’a fa Inna daga ke har Kawo Haladu ba ku yi gaskiya ba yarinyar nan ta fi ku gaskiya, daga zuwa ganin gida sai ku kawo ma ta miji ba ku sani ba ko tana da wanda ta ke so ko kuma shi Yaya Umaru yana da wanda ya yi wa alƙawari, sannan kuma ba lallashi ba ban baki sai duka. Katsi shi ta yi da faɗin “to Babana ai sai ka zo ka dakeni ba wai ka min faɗa ba inaga sai nafi gane na yi rashin gaskiyar ko” ta ƙarasa maganar tana mai bashi baya tana faɗin “maza ka dakeni” murmushi ya yi yana gyaɗa kai ya ce; “Allah ya huce zuciyarki Inna, amma dai dan Allah a bar maganar nan ku bari a rabu lafiya kar ta zo ta ji ba za ta sake zuwa ba ko tsanar garin”.
“Ta tsanemu ma ƙaruwar ta tsani gari, kaga Sani tashi ka bar wajan-nan tun kan na sauke a kan ka” tashi ya yi jiki a sanyayi ya tafi ɗakin matarsa ya samu dukansu sunyi cirko-cirko suna kallon Zainab da lallashin duniya taƙi ji kuka take tana faɗin ita ba za ta kwana ba yau za ta tafi Kafancan, samun waje ya yi ya zauna cikin lallashi ya ce; “kinga Zainab zaman ki ko tafiyar ki ba shi ne zai sa a ɗaura auren da wanda ki ke ikirarin ba kya so ba, ki yi haƙuri idan Allah ya kai mana rai gobe idan ma sammako ki ke so sai mu tafi na kai ko har gida kinji ko”? Ba yanda ta iya domin tana jin nauyinsa ba za ta iya masa musu ba dole ta bar tafiyar sai washe-gari. Da dare Baba Haladu ya zo gidan ya tasa ta gaba da lallashi a cikin ɗakin gwaggo Hari ya ce; “haba Amaryata mene ne abin damuwa daga ya zo ya ce yana sonki duk sai ki bi ki tashi hankalin ki um haka a ke”? Cikin turo baki ta ce;
“Gwaggo Hari ce ta ce wai ko bana so dole sai anyi auren to kawai daga zuwa sai a wani laƙama min auren tsohu kuma ni na ce ne aure zanyi” murmushi ya yi irin nasu na manya kafin daga bisani ya ce; “idan shi ya ma ki tsofa ba kya so ai shi kenan ni sai a ɗaura dani kinga na fi shi yarinta ko” ya yi maganar cikin zolaya da sauri ta kalleshi cikin yarinta ta ce; “tabɗijam ahakanne ka fi shi yarinta kalle gashin ka duk furfura har gemon ka kuma fatan ka duk ta yi irin na tsofaffi kuma a hakan ka fi shi ai shi ya ma fi ka yarinta” dariya ya yi yana faɗin “ja’ira kuma ki ke kiran shi da tsoho ga bakin ki nan ya faɗi gaskiya ai, ina laifin wanda ya so ka sannan Umar ai ba wasu shekaru ne da shi ba, daman zuwan da na yi na tambayi Baban ki an maki miji ya ce a’a dan haka kinga faɗuwa ta zo daidai da zama ko”? Ya ƙarasa maganar da tambaya yana mai zuba mata idanu, cikin rashin tsoro ta ce; “ni fa bana son shi ku ma daina ɓata yawon bakin ku a kan maganar nan”
“To idan ba kya son shi wa ki ke so”? “Ni kowa ban so karatu zanyi” ransa ya fara ɓaci cikin faɗa ya ce; “karatun za ki aura kenan”? Ta masa shiru “tambayar ki na ke kin min shiru” kanta ta mayar gefe tana kallon ƙofa gwaggo Hari ta ce; “ai na faɗa maka Yaya yarinyar nan sam ba ta da kunya Umaru ya mata rainon turawa”
“Ni ai ta san ko Ubanta bai isa ya min rashin kunya ba bare har ‘yar da ya haifa ta min, tunda abin hakanne zai zo ya sameni ai” ya miƙe tsaye yana faɗin “ki shirya Alhaji Umar zai wuce da ku dan da yau zai koma ya fasa zai jira ku gobe sai ku shirya da wuri ya wuce da ku”.
“Tabɗijam! wallahi ni ba wani gardi da zan bi a motarsa shi ya kawo mu bare ya mayar damu ni ba zan bishi ba” ta faɗa tare da miƙewa tabar ɗakin a fusace dukan su suka bita da idanu “lallai yarinyar nan ashe hakan ta ke”
“Ai Yaya fiye da hakan ma sai ta ma ba zanyi mamaki ba ni da ɗazun kamar mu daku sai da Sani ya zo ya shiga tsakani”
“Allah ya kyauta, aure ne kam anyi an gama yaron kirki ga kuɗi Allah ya ba shi ka yi aure inda za ka huta wani na ka ya huta ta ce ba hakan ba saboda rashin sanin ciyon kai irin na yaran yanzu”.
Hakan ya tafi yana jajjada wa Gwaggo Hari ta sa su shirya da wuri dan Alhaji Umar ya ce sammako zai yi.
*****
Yanda taga rana haka taga dare sam ta kasa yin bacci a matuƙar ƙuntaci take jinta kuka ta kwana yi Ruƙayya da Raliya sunyi rarrashin duniya amma fau taƙi yin shiru har bacci ya yi awon gaba da su suka barta ita kaɗai tana tufka da warwara, tana jin an fara kiran farko na asuba ta ta shi su Raliya da Na’ila, suna idar da Sallah ta ce tafiya ta tashi Inna ta ce; “tunda ba tashin hankali bane Zainab ki bari ku yi wanka ku karya sai ku tafi”
“Idan mun je gida duk za mu yi” ta bata amsa fuska a ɗaure, kawo da dawowarsa masallaci kenan ya ce; “har yanzun dai kinƙi ki sassauta wa zuciyar ki ko Zainab” shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta “shi kenan bari na fito mu tafi tun da kin dage yanzun za a tafi” Gwaggo Hari da ta fito banɗaki ta ce; “ƙyaleta Sani ba inda za ka je ai ta san wa zai kai su idan ba za ta iya jira ba sai ta tafi da ƙafa” ta kalle su Raliya ta ce; “Raliya ku yi zaman ku ku yi shirin ku a natsi za a zo a ɗauke ko” jan kayanta tayi ta fita Raliya ta yi wuri-wuri da idanu ita kam da ta sani ba za ta zo wannan ganin gidan da ya ƙare da fitina da tashin hankali ba, Kawo Sani ya bi bayan Zainab Gwaggo ta kira shi tana faɗa “bana ce ka ƙyaleta ba” “haba Yaya kawo su ya yi cikin aminci ya bar mana amana kuma yanzu saboda wani abu na rashin fahimta ya shigo sai mu barta ta tafi ita kaɗai sam hakan bai kamata ba gaskiya wannan ba daidai bane” ya yi maganar ciki da nuna rashin jin daɗinsa, ya yi saurin fita su Raliya suka bi bayan shi.
Suna zuwa motar Alhaji Umar su ka samu a ƙofar gidan shi kuma yana gaban Zainab yana lallashinta a kan ta yarda ya wuce da su ta buga kai ga ƙasa ba za ta shiga motar ba, Gwaggo ta fito akai akai ta ƙi shiga motar ganin Gwaggo na shirin kai mata duka ya yi saurin shiga tsakani yana faɗin “a’a a yi haƙuri dai Gwaggo, tunda ba za ta shiga ba bari kawai na tafi” ya buɗe mota ya ɗauko kuɗi masu yawa ya ba Gwaggo ya ce su yi kuɗin mota jiki na rawa gwaggo ta karɓi kuɗin tana masa addu’a da sa masa albarka, jiki a sanyayi ya shiga mota ya bar ƙofar gidan. Haka su ka tafi zuciyar kowa ba daɗi kuɗin da ya bayar Gwaggo ta raba biyu ta ɗauki rabi taba Kawo Sani Rabin tace su yi na mota abinda ya rage ya ba Uban Zainab.
Suna isa Raliya ta shiga gidansu su kuma suka shiga gida Kawo Sani ya tsaya ɗakin Yayanta da ya ke suro, Mama ta ganta ta yi wani iri ta koma gefe ta zauna ta yi shiru ajiye wa su Shahid abinci ta yi tana faɗin “Shahid ɗauki ka kaiwa kawonku abinci, bayan fitar Shahid ta zauna gefen Zainab tana faɗin “ba ki da lafiya ne” kamar mai jira ta fashe da kuka tare da kwantuwa jikin Mama “SubhanalLah lafiya me ya faru ina Raliya ne Allah ya sa ba wani abin ya samu ‘yar mutane ba”? Kuka kawai take ta kasa cewa da ita komai “wai ba za ki faɗa min abinda ya faru bane”? Ta yi ma ta tambayar cikin tsawa, Na’ila ta matso kusa da Mama tana faɗin “Mama ita da su Gwaggo Hari ne… Tana gama faɗawa Mama Murmushi Mama ta yi tana faɗin “to ke daga magana sai ki bi ki tashi hankalin ki su ne su ka haifi ki da za su tsayar ma ki da mijin aure ” cikin shagwaɓa ta ce; “Mama nuna wa fa su ke su suke da iko da Baba dan haka ko ina so ko ban so sai anyi auren”.
“Kinga ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai ma ki dole, ko Baban ki ba zai ma ki dole ba bare kuma su da kakanne ne ba iyaye ba” maganar Mama ya sa ta ɗan ji sanyi a ranta har taci abinci ta yi wanka.
Da dare bayan sun shige bacci Baba ya shigo ɗakin Mama ya samu tana kwance yana ɗan bubbuga ƙafarta ya ce; “Maryam ko kinyi bacci”? Tana juye da miƙa ta ce; “eh to yanzu ya ɗan fara ɗaukata” ta tashi zaune tana gyara kallabin kanta ta ce; “Malam yau kam ka daɗi ba ka shigo gida ba”.
Zama ya yi gefen gadon kafin daga bisani ya ce; “wallahi kuwa bayan na raka Sani tasha na biya wajan Alhaji Abu shi ne fa ya nemi da na masa rakiya sai yanzu mu ka dawo ya ajiyeni a ƙofar gida sannan ya wuce nasa gidan” saukowa ta yi daga kan gadon “ina za ki je”
“Zan ɗauko ma abinci ne”.
“Dawo ki zauna munci abinci a can, ki zauna magana na ke so mu yi” komawa ta yi ta zauna gefen shi, “na san Zainab ta faɗa ma ki yanda su ka yi da mutan gida ko?”
“Eh ta zo tana ta ƙunci na tambaye ta shi ne Na’ila take faɗa min abinda ya faru”.
“To Baba dai ya aiko Sani ya faɗa min kuma munyi magana da shi ta waya Alhaji Umar na neman auren Zainab, na san Alhaji Umar sani ba na wasa ba bai da wata makusa da za a ce ba za a so haɗa zuri’a da shi ba” jin ya yi shiru ya sa Mama kallonsa cikin mamaki ta ce; “to me ka ke nufi da hakan”?
“So na ke ki lallashi Zainab ta amince da auren nan, sanin kanki ne Baba Haladu shi kaɗai ne uba da ya rage min a cikin iyaye maza ba zan iya musu ko kawar da kai a kan duk wata alfarma da zai nema a wajena ba” cikin hanzari Mama ta ce; “amma na yi mamakin jin hakan daga gare ka malam auren dole fa ka ke so ka yi wa ‘yar ka”. “Yaushe na faɗa maki hakan”?
“Maganganun ka ne su ka nuna abinda ka ke so ka yi, ni ba zan ce kar ka bi maganar Baba ba, amma maganar gaskiya aure irin wannan na haɗi tuni aka daina yin irinsa zamani ya canza Malam abar yarinya ta samu z… Katse ma ta maganar ya yi yana faɗin “kinga Maryam ki fahimcini cewa fa na yi ki lallasheta ta amince bayan hakan ban ce da ke komai ba bare ki ja min dogon zance”.
“Uhm shikenan na ji zan ma ta magana, amma idan ta tsaya a kan bakanta na ba ta so fa”? Ta yi tambayar tana mai zuba masa idanu.