Ta zu ba ma shi ido tana jiran ta ji me zai faɗa amma ya ma ta shiru, "Malam ka yi shiru". "Me ki ke so na faɗa ma ki Maryam" gyara zamanta ta yi tana daɗa fuskantar shi ta ce; "tambaya na ke idan taƙi amincewa fa"? "Sai idan ke ma ɗin ba so ki ke ba wannan zai sa ki ba ta ƙwarin gwauwar ta bijire mini wanda hakan tabbas zai sa mu samu matsala da ke domin kuwa kin fi kowa sani kaf duniyar nan ban da iyaye sama da Baba Haladu da. . .