Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Ta zu ba ma shi ido tana jiran ta ji me zai faɗa amma ya ma ta shiru, “Malam ka yi shiru”. “Me ki ke so na faɗa ma ki Maryam” gyara zamanta ta yi tana daɗa fuskantar shi ta ce; “tambaya na ke idan taƙi amincewa fa”? “Sai idan ke ma ɗin ba so ki ke ba wannan zai sa ki ba ta ƙwarin gwauwar ta bijire mini wanda hakan tabbas zai sa mu samu matsala da ke domin kuwa kin fi kowa sani kaf duniyar nan ban da iyaye sama da Baba Haladu da kuma gwaggo Hari, dan haka tun da har su ka amince da Alhaji Umar za su ba shi aure ba zan taɓa bijire ma su ba” cikin takaici ta ce; “dama na san a rina tunda naga kana kewaye-kewayen nan na san ƙarshinta cewa za ka yi ka amince, magana ta gaskiya Malam idan har Zainab ta amince ta na so to ni ban da ja sai fatan Alkhairi” ta ɗan sihirta cikin jan numfashi ta ce; “idan kuma bata amince ba gaskiya sai dai a haƙura da maganar nan a bar yarinya ta samu wanda take so sai ayi aure dama duka nawa Zainab ta ke da har za a fara maganar aurenta”.

Tashi ya yi yana ragi kayan jikinsa ya ce; “sai na gani tsakanin ni da ke waye ya ke da iko da ɗiya” “Humm! Malam na sa ni kafini iko da ita amma hakan ba zai sa na ja baki na yi shiru a cutar da yarinya ba, ko mu ai da mu ke iyayenta ba dole a ka mana ba bare kuma ita sannan zamani ya sauya an daina irin wannan auren Malam, bai kamata saboda farin cikin wasu mutanen ka banzarar da farin cikin ‘yarka ba?” “a wajan ki ne ki ke ganin farin cikinta na ke so na banzarar ni dai na san matuƙar ta yi biyayya wa ni ba za ta taɓa taɓewa ba duniya da Lahira In Sha Allah” ranar haka su ka kwana zuciyoyin kowa babu daɗi.

Ta fito cikin shirin makaranta ta samu Mama kichen tana zuba wa Malam ɗumami ta ce; “Mama zan tafi” Mama ta ɗago ta kalleta tana faɗin “har kin shirya kenan, to Allah ya bada sa’a a mayar da himma kinga wannan ce jarabawar ƙarshe kar ki bari damuwa ta sa ki yi asarar wannan shekarar dan naga tun dawowar ku kin kasa sakin ranki” narai-narai ta yi da fuska kamar za ta yi kuka dama an jefa dutsi inda ya ke son sauka “Mama kina ji fa ko yanzu da na je karɓar kuɗin wajan Baba ya ce da mun gama jarabawa kar na tsaya ko ina na dawo gida zanyi baƙo da yamma wai Alhaji Umar zai zo” cikin lallashi Mama ta ce; “kar ki ma sa wannan aranki da yardar Allah ba zan taɓa bari ayi wannan auren ba tunda har ba kya so ki je abin ki ki yi jarabawar ki cikin natsuwa” murmushi Zainab ta yi har cikin ranta taji daɗin kalaman Mama ta sani Mama tunda har ta faɗa tabbas za ta jajirce wajan ganin ta hana auren, cikin ƙwarin gwuawa ta tafi makaranta. Su na dawowa makaranta kaya kawai ta canza ko wanka ba ta yi ba ta tafiyarta gidansu Raliya, su na zaune ɗakin Raliya ta na dannar waya Raliya ta shigo da abinci a filet ta a jiye a gaban Zainab ta zauna ta na faɗin “wai ke da gaske ba za ki bari ku haɗu ba?” Ajiye wayar ta yi gefe ta ɗauki cokali ta fara cin abinci sannan daga bisani ta ce; “to da ke kin ɗauka da wasa na ke?”

“Amma gaskiya Zainab ina jiye ma ki fushin Baba, a ganina ki bi komai a sannu zai fi domin su iyaye lallaɓasu a ke a samu a gama lafiya da su” kallon Raliya ta yi ta ce; “amma dai kin san abin da a ke shirin mini sam babu adalci ko? Ko musulunci bai yarda da irin wannan auren haɗin ba, domin shi aure mutum biyu ke yinsa da zarar ɗaya na so ɗaya baya so tawaya ta shigo a cikin auren, ba za a taɓa samun farin ciki ba, dan haka ni ba zan bari a illata rayuwata ba”.

“Na yarda da duk abinda ki ka faɗa, sai dai ina so ki sani shi Allah ba ruwansa da wannan shi ne ya ce ‘ya’ya su bi iyayensu dan samun rabauta duniya da lahira, koma me ye gaba ka ke dubawa kanka”.

“Hmm amma ai kuma mai ahlari ya na cewa babu biyayya ga abokin halitta a cikin saɓawa Ubangiji” harararta Raliya ta yi ta na faɗin “me ye abin saɓo a cikin aure Sunna ce fa ta Ma’aiki ,(S.A.W)”
“Amma kuma ai Annabi bai ce a gina Sunnarsa a kan ƙiyayya ba ko?”

“Zain… Katse ta Zainab ta yi tana faɗin “idan fa damuna za ki yi da zancen nan sai na bar ma ki gidan na ƙara gaba” harararta Raliya ta yi tana faɗin “Allah ya kyauta ma ki to” murya Maman Raliya suka jiyo daga waje ta na faɗin “shiga suna cikin ɗaki” Na’ila ta shigo “lafiya?”

“Baba ne ya ce na zo na kira ki kuma ya ce na faɗa ma ki kar ki kuskura ki bari ƙafarsa ta taku ƙofar gidan nan” cikin jin haushi ta ce; “to na ji ji ki”

“Aunty cewa fa ya yi mu zo tare” cikin masifa ta yunƙuro ta na faɗin “wallahi Na’ila zanci Ub… ta zageta tare da ƙoƙarin kai ma ta duka yarinyar tabar ɗakin da sauri, Zainab ta ja numfashi ta furzar cikin takaici ta ce; “wallahi na san duk Na’ila ce ta faɗa wa Baba ina nan”.

“Kar ki zargi yarinya kin sani Baba ya san kaf unguwar nan babu inda za ki je da ya wuce nan ɗin” Zainab ta yi tsaki ta ce; “gaskiya ni banza ce ma da na tsaya gidan nan dana-sani gidan Aunty Sumayya na je” Raliya ta ce; tsaya surutu har Baban ya zo”.

“Zo ki rakani” Raliya ta ɗan fito da idanu ta ce; “tabɗijam rufani ki saya haka kawai na je ki shuka masa rashin mutunci Baba ya haɗa har ni ya mana wankin babban bargo”. “Ni na ce ma ki rashin mutunci zanyi”
“Halin ki na sani wallahi komai ma yi masa za ki yi ke ɗin” ganin da gaske Raliya ba zuwa za ta yi ba yas ta kama hanya ranta a ɓace ta bar gidan.

Ta shiga suron gidan nasu ta samu yana zaune a kan shimfiɗa ya tanƙwashi ƙafafunsa ya na dannar waya, ta yi turus ita bata ƙarasa shigowa ba ita bata koma baya ba, kamar an ce ya kalle ƙofar shigowa ya ganta a tsaye murmushi ya yi kafin ya ce; “barka da zuwa ran Sarauniya ya daɗi” fuska ta sa ke ɗaurewa kamar bata taɓa dariya ba, “kin tsaya ki ƙarasu mana” gyaran muryar Baba ta jiyo daga cikin gidan hakan ya sa da sauri ta ƙarasa ta zauna gefen tabarmar a tunaninta Baban fitowa zai yi, kanta a ƙasa ta na wasa da ƙasan hijab ɗinta, “da fatan kin wuni lafiya?”.

“Lafiya” ta amsa masa can ƙasan maƙoshi, “Zainab na tambaye ki mana?” Ta gyaɗa masa kai “ba za ki buɗi baki ki yi magana ba sai dai gyaɗa kai, shi kenan tambayar ki zanyi kuma ki ba ni amsa tsakani da Allah” ya gyara zamansa tare da kafeta da idanu sannan daga bisani ya ce; “me ya sa ba kya sona? Shin kinga wani abu ko wata alama da ya ke nuni da ni ɗin mutumin banza ne banda halin da za a soni?” Ɗago kanta ta yi ta kalleshi daga bisani ta kawar da kanta ba tare da ta ce da shi komai ba, “kinyi shiru, ki bani amsa”.

“To ni yaushe ma na sanka bare har na san halayyar ka” ya ce; “tunda hakanne ki bani dama ki sanni sosai kafin ki yanki hukuncin za ki soni ko ba za ki soni ba” kallonsa ta yi ido cikin ido ta ce; “ni fa ka ma daina wannan zancen ba wata dama da zan baka kawai bana so kuma ni ba aure zanyi ba karatu na ke so” murmushi ya yi a zuciyarsa yana jin zallar ƙurciya ce kawai take cinta, ba wai son nasa ne ba ta yi ba shi kansa son bata san shi ba, dole sai ya bi ta sannu a hankali kafin ya samo kanta, ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce; “na faɗa ma ki idan dai karatu ki ke so na ma ki alƙawarin har sai kin buɗe baki da kan ki kin ce min ya ishi ki haka”.

Wani irin haushinsa taji ya rufe mata zuciya shi wani irin mutum ne da baya da fahimta ne, “ki amince dani Zainab za ki yi farin ciki da aurena, zan nuna ma ki so zan ririta ki, zan bambanta ki da sauran ‘yan-uwanki m… Katse masa magana ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu “ya isa haka ni bana son jin duk waɗannan kalaman na ka marar kai bare kuma makama” zuba mata idanu murmushi shimfiɗi a fuskarsa ta ɗora da cewa “kaga ina girmama ka a matsayin ka na babba da a haifi ka haifi ni don Allah don Allah ka fita rayuwata cikin mutunta juna mu rabu ba tare da ka haddasa min matsala a tsakanina da iyayena ba”
“Uhm ba burina kenan ba Zainab sam ba zan zama silar samun matsala a tsakanin ki da mahaifan ki ba, sai dai ina so ki sani son da na ke ma ki bana jin zan iya rayuwa ba tare da ke ba”.

“Saboda a tare a ka haifimu ba, ko kuma a da can da ba ka sanni ba ba rayuwar ka ke ba” ta faɗa cikin ƙufula tare da miƙwa tsaye, ya buɗe baki zai yi magana ta yi saurin barin wajan ta shiga cikin gida, bin ƙofar ya yi da idanu yana mai saukar da a jiyar zuciya, ina ma zai iya haƙura da ita tabbas da ya barta, bai rasa komai ba bai nemi komai ya rasa a wannan rayuwar ba sai ita ƙaramar yarinya da take so ta ba wa zuciyarsa wahala, kawai sonta ne ya masa wani irin kamun kazar kuku a yanda ya ke jinta a ransa baya tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, fitowar Baba ne ya katse masa tunanin da ya ke bayan sun sake gaisawa Baba ya ce; “ina fatan dai babu wata matsala ko?” Ya yi murmushi cikin ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke ransa ya ce; “a’a Baba ba wata matsala” cikin rashin gamsuwa ya ce; “ka dai ƙara haƙuri da sannu komai zai wuce kamar ba a yi ba, domin a kwai ƙurciya a tare da Zainab”

.”Ba komai Baba na fahimci hakan tabba” sunyi maganu sosai kafin daga bisani ya tashi zai tafi ya ciro kuɗi cikin aljihun rigarsa ya ba Baba kaɗa kai Baba ya yi yana faɗin “a’a kar ka wani wahalar da kanka ko ba ka yi wata hidima ba Zainab matarka ce idan Allah ya nufa”.

“Baba ba domin Zainab na ba ka kuɗin nan ba, ko da Zainab ko ba ma tare da ita ni mai yi ma hidima ne domin duk abu ɗaya ne, dan hakan don Allah ka karɓa” karɓar kuɗin ya yi yana ma sa godiya tare da sa masa albarka, Alhaji Umar ya masa sallama bayan tafiyarsa Baba ya shiga cikin gida.

Tun daga ranar Baba bai sake yi mata zancen Alhaji Umar ba, haka shima bai sake zuwa wajanta ba, hakan ya sanya mata natsuwa a zuciyarta tare da tunanin maganganun da ta masa ya yi zuciya ya haƙura da ita ɗin, bayan kwana biyu da kammala makarantar su ta dawo daga gidan Kakanninta iyayen Mama sai masifa take a ranta daidai kwantar da za ta sadata da gida ta haɗu da Raliya su ka tsaya Raliya ta ce; “daga ina haka?”
“Gidansu Mama na fito ai na biya ta gidanku Mama ta ce min kina gidan Yaya Hafiz”.

“Eh wallahi matarsa Aunty Aisha ce ba tada lafiya shi ne ya ce na je na kama mata aikin gidan dawowata kenan” cikin tausayi ta ce; “Allah sarki Aunty Aisha cikin nan dai ya na ba ta wahala”.

“Ina ma ki ka sani sai kinga yanda ta dawo yanzu gwanin tausayi” suka fara tafiya Zainab ta ce; “Allah sarki Allah ya ba ta lafiya, ni kam har na ji ina ƙara tsoron aure wallahi” cikin dariya Zainab ta ce; “Allah ya shirye ki Zainab ke kullum maganar kenan tsoron aure anya ba namijin aljani ne a tare da ke ba” tana harararta ta ce; “A’a Sarkin aljanu ne tare da ni ƙaruwar namijin aljani”.

“Hahaha mayar da wuƙar ƙawata, wai lafiya ma na ganki kamar ranki a ɓace?” Tsaki ta yi kafin daga bisani ta ce; “mazan nan jarababbu ne wallahi ba dama ka fito sai a dinga taran ka a hanya sai ka ce na fito tallar haja, wani kwai daga ganina yau bina yana mini magiya na tsaya da naga zai dameni kawai na ma sa wankin babban bargo na yi tahuwata”.

“Wallahi ki daina korar samari Zainab ba kyau Allah” kasancewar sun kawo gida hakan yasa komai ba ta ce da Raliya ba ta shige gida, Raliya ta kaɗa kai tare da ƙarasa wa na su gidan. Tana zuwa ta samu Mama zaune tsakar gida a kan kujer ta yi tagumi fuskarta na nuna damuwa, ƙarasawa ta yi gaban Mama tana faɗin “Mama lafiya me ya faru?” Mama ta janye hannunta da ta yi tagumi da shi tana nuna ma ta gefen ɗakin Baba ta kai dubanta wajan da Mama ke nuna ma ta zuciyarta ta bada wani irin sauti dum! Ta ware idanunta tana kallon wajan da matuƙar tsoro da mamaki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Su ne sila 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×