Me Yasa?
01.
Da sunan Rabbi Sarki mai kowa,
Al-Ƙaliƙu Allah Kai ka yi kowa,
Salati gun manzo na ninkawa,
Sahabu ba zan bari ba ko yaya.
02.
Me yasa ne ya jama'a, me yasa ne?
Me yasa yau muke yin yaudara ne?
Me yasa wai muke cin amana ne?
Me yasa ne, ya jama'a me yasa ne?
03.
Me yasa yau soyayya ba ta gaske?
Me yasa gaskiya duk muka take?
Me yasa an bar ƙaunar ga ta gaske. . .