Anya Kuwa?
01.
Da sunan Jalla sarki
Wannan da ya yo musaki
Shi yai kare da gwanki
Yai shanu har da awaki
Allah gwani, Allah gwani.
02.
Dubu dubun salati
Ga abban nan na Fati
Hasken sa ya wuce fenti
Ya zarce duk mai kanti
Tarin daraja ku ji.
03.
Jama’a ga tambayata
Ko da mai ban amsar ta
Ku ɗan bi gari ku yayata
A sam mai ban amsar ta
A cikin gari, ku yi agaji.
04.
Al’umma duk mun canza
Yankan juna tamkar reza
Goyon masara sai geza
Gugar zana ake gurza
Anya kuwa, anya kuwa?
05.
Samari babu ɗa’a
‘Yan mata babu kunya
Tsoffi sam babu girma
‘Yan yara babu gobe
Anya kuwa, anya kuwa?
06.
Anya kuwa mun shirya?
Ta ina wai za a fara?
Anya kuwa za mu tsira?
Anya ko mun hau hanya?
Anya kuwa, anya kuwa?
07.
Yankan juna da ƙarfe
Ƙarya, ƙazafi da yarfe
Zunɗe, zagi da jefe
Munafunci da ƙage
Anya kuwa, anya kuwa?
08.
Hanya kuwa muna duba?
Anya kuwa muna lura?
Koko sai in an ɓara?
Sannan ne za mu farga?
Anya kuwa, anya kuwa?
09.
Cin amana muna yi
Ga zalunci duk muna yi
Tausan juna ba ma yi
Hassada ta hana mu yi
Anya kuwa, anya kuwa?
10.
Halan ko mun manta
Da ƙangin nan na bauta?
Halan ko mun manta
Da azabar nan ta wuta?
Anya kuwa, anya kuwa?
11.
Alƙawari ya ƙare
Ɓawon ladabi ya ɓare
Tarbiyya duk ta zube
Rigar kunya tuni mun tuɓe
Anya kuwa, anya kuwa?
12.
Tsirin tsibirin laifuka
Tashin zunubin hankaka
Kai ɗan uwa kama kanka
Mutuwa na zuwa kanka
Allah kuwa, Allah kuwa.
13.
Anya kuwa ko mun shirya
Zaman ƙabari da hali?
Jama’a ta ko mun shirya
Neman tuba, gyaran hali?
Anya kuwa, anya kuwa?
14.
Dukiyar mu haɗa da ‘ya’ya
Mataye har da ‘ya’ya
Gidaje har da gona
Lahira za mu kai wa?
Anya kuwa, anya kuwa?
15.
Ku yi nazari da duba
Akan dukkan tambayata
Amsar lallai da zurfi
In mun duba ba mu gaji ba
Za mu ƙaru dai.
16
Jamilu nake suna
Haiman ko laƙabina
Abdulrahman Babana
Hauwa’u ce Ummina
Allah gwani, Allah gwani.
17.
Yau Talata da rana
Watan bakwai da rana
Shekarar dubu biyuna
Da biyu cif babu kwana
Bisa adadi, bisa adadi.
Anya kuwa dai?