Skip to content
Part 5 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

A Ina?

 01. 

Da sunan Rabbana sarki, kaine mai duniya

Salati mai yawa, da jinjina bisa gaskiya 

Ga Sayyadi Muhammadu, Manzona mai gaskiya

Asahabu ka sa duka, da duk malamanmu gaba ɗaya

Da musulmai mu duka, ka ɗora mu a turbar gaskiya.

02.

Jama’a ga tambaya, a ina ake raba dukiya?

Ina daɗa tambaya, a ina ake ba da duniya?

Shin ku jama’a a ga tambaya, waye ne mai duniya?

Shin ko kun shina a ina ake samun duniya?

Allah Al-Ƙaliƙu, tabbas kaine mai duniya.

03.

Ya ku al’umma, a ina ake samun ilimi?

Wai ku jama’a, ya ake gane jahili?

Ya ku matasan mu, a ina kuke babin ilimi?

Ya ku matayenmu, a ina kuke babin ladabi?

Allah Al-Musawwiru, ka ƙare mu da ilimi.

04. 

A ina muke yau, ina muka baro kuma ina za mu je?

Su waye mu, a ya muke yau kuma yaya za mu zama?

A ina muka kwana, ina za mu tashi a fantsama?

A ina ne wai, ake ce wa kuma ake bai wa?

Allah Al-jabbaru, ka tsare mu daga shan wuya.

05.

A ina muka bar iliminin mu, a ina muka bar tarihinmu?

A ina muka bar al’adunmu, a ina muka bar kirkinmu? 

A ina muka bar zumuncinmu, a ina muka bar koyarwar mu?

A ina muka bar tarbiyyar mu, a ina muka bar soyayyar mu?

Allah As-Salamu, ka kawo sauƙi a cikin lamurra.

06. 

Wai ina soyayyar nan, ta junanmu take ne? 

Wai ina kishin nan, na junanmu yake ne? 

Wai ina martabar nan, ta junanmu take ne? 

Wai ina ƙimar nan, ta junanmu take ne? 

Allah Ya Hayyu, ka tsare mu da sharrin zamani. 

07.

Ya Ikwani ga tambaya, a ina matsalar take ne? 

Ya al’umma ga tambaya, a ina tufkar take ne? 

Ina warwarar t, da ita saƙar take ne? 

A ina sauƙin da solution, da maslahar take ne? 

Allah ya sattaru, sauƙi dai duka naka ne. 

08.

Allahu ka agaje mu, ka sa sauƙi a lamurranmu 

Ka sa shiriya a zukatan mu, da son juna a tsakanin mu 

Mu zamo tamkar mutan da, dodon ayaba ko kadada 

A lahira mu sam tsira, dukkan mu cikin aljanna 

Allah Al-Muminu, ikon komai duka naka ne. 

09.

Haiman ne ke tambaya, a ina muke ne?

Shin mun shina ko a’a, ina za mu je?

Yau sha ɗaya ga wata, wata ta bakwai ina za mu je?

Shekarar dubu, biyu da biyu sai kuma ina?

Ya zuljalalu, ka iya mana Allah masani.

<< Tambaya 4Tambaya 6 >>

1 thought on “Tambaya 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.