Skip to content
Part 18 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Rayuwa ta yiwa Sameer matukar zafi. Al’amarin da yayi matukar shafar Aikin shi don babu nutsuwa a tare da shi.

Damuwa da tunanin gyaran da zai iya samowa ya haddasa mishi ciwon zuciya wanda ya ke shi Daya kwal a gida banda rai da Alkawari da a jiya kam sai dai gawar shi amma da yake rayuwar tana hannun Allah ya samu arzikin ganin wayewar garin inda dole ya kira Bello wanda yaji muryar shi a dame dole ya nufi gidan shi ya kuma same shi R’rai a hannun Allah dole ya dauke shi suka nufi Asibiti inda Kuma aka tura su Asibitin shika na Zaria.

Bello ya Kira Haj Yana fada Mata Sameer Babu lafiya yanzu haka ma an tura su shika Zaria…

A Rude Haj ta Isa Asibitin taga halin da Sameer yake ciki da kuma matsalar shi wacce ta tabbatar rabuwa da matar shi ce ta haddasa mishi hakan har zuciya na kokawa.

Dole Suka wuce shika Zaria ya kuma samu kulawa sosai har ya soma samuwa

Yana Zaune akan Gadon an jingina mishi filo Yana Shan shayin ya Dubi bello Wanda shine yake jinyar shi ya Soma share HAWAYE Yana Fadin

“Bello kaga kaddarar da ta fada mini ko? Amma Anki a fahimce ni sai Fadi Ake wai Auren mu ya kare da Farida bayan ba a cikin Hankali na nayi furucin ba? Yaya Zanyi da Rayuwa ta Bello idan aka Raba ni da Farida? Don Allah ka fahimtar da su na ce na janye sakin Nan Kuma cikin fushi nayi shi shin ba ance Banda sakin da akayi cikin fishi ba? Allah ma ya yafe kuskure Amma shi Dan Adam baya yafewa har Haj na Fadin har Abada ni da Farida bello ban zaci wannan kalmar daga Bakin Haj ba.

Sai ya Soma kuka Abinda yayi matukar bawa Bello mamaki don yayan nashi Akwai taurin zuciya ba dai kaga Hawayen shi a arha ba sai an turxa.

Bello ya dafa shi Yana Fadin “ka yi hak’uri Yaya Sameer zasu fahimta nima kuma zan nemo maka wasu fatawowin a zauren malamai kai dai ka yi Hak’uri har ka samu lafiya kaji fa abinda Dr ya ce zuciyar ka ta Soma kumbura saboda damuwa. Kasan fa damuwa Bata maganin komai Yaya Sameer sai dai ta cutar da lafiya da gangar jiki ayi Hak’uri har muga Abinda Allah Zaiyi ai mutane da yawa Basu fahimci saki da yadda Ake yin shi ba da ance anyi sun kama ga zance ga magana Basu San Akwai Wanda furucin ne kawai ba aikace ba.

“Yauwa Bello kaga Kai ka fahimce ni Akasin sauran mutane da suke Ganin laifi na don Allah Kayi gaggawar samo min fatawar Nan.

Bello ya amsa Yana tausaya mishi . Ya dai bishi da yadda yake so ne Amma matar shi Kam ta Saku sai dai yayi jinyar shi ya gama Amma shi da ita sai taje ga Wani in dai ba a na son cin gyaran wahayi Babu inda Akayi wata magana akan sakin cikin fushi saki duka saki ne koma a me kayi shi matukar dai da hankalin ka ba hauka kayi ba Babu Ruwan Shari a da wani fushin ka.

“Taimaka mini Bello ka kawo mini farida da su Saddam kafin na mutu na Kara Ganin ta.

“Don Allah Yaya Sameer kayi hak’uri ka cire damuwa a Ranka Babu Mai Raba ku da Farida matukar Ina Raye Amma yanzu lafiyar ka nake so ta inganta zuciyar ka fa ta fara kumbura.

“Kayi mini hak’uri Bello in na ga Farida da su Saddam Hankali na zai Kara kwanciya don Allah ka fahimce ni Mana Bello?

“Na fahimce ka Amma ka San iyayen Farida ba zasu yarda ta taso gari ya gari har Zaria duba ka ba musamman da suka tabbatar akwai soyayya Mai zafi a tsakanin ku ka San iyayen da son kiyaye komai.

“Bari na Kira Hajiyar su zata yarda ai tana fahimta ta bello Ina son Ganin Farida Wallahi.

Ya jawo wayar shi Yana Kiran wayar Haj
Farida da ta samu Sauki tana zaune ta rafka tagumi Babu Abinda take so da Gani irin Sameer Amma da wace fuskar zata ganshi? In Kuma ta ganshi yayi Mata me?

Ta juyo da sauri Saboda Jin Haj tana kama sunan Sameer.

Yana gaishe da Haj Yana kuka Haj ta Soma Rarrashin shi tana fadin.


“Kayi hak’uri Sameer musulmi fa ya kamata ya Dubi hanyar zuwan kaddara a Rayuwar sa don matukar Imanin ka ya Kai to tabbacci hakikatan a jarrabe ka Kuma sai Allah ya na son bawa yake jarraba shi
.

“Nagode Haj mutane sunki fahimta ta sai Cewa suke wai Auren mu ya haramta da Farida Alhalin cikin fushi nayi furucin Nan don Allah Haj ki fahimce ni kar ki ce min ba haka bane irin yadda suke ce Mini. Ya fada Yana shesshekar kuka..

“Sameer sai dai kayi Hak’uri Amma duk Wanda ya fada maka Auren ku da Farida ya kare gaskiya yake fada Maka don Yana son ka ne da Rahamar Ubangiji Amma duk Wani da zaice Maka akwai gyara ko kwaskwarima to ba Mai kaunar ka bane kaima fa kana da sanin ka bakin gwargwado kasan fari ka San Bak’i saki UKU dai tunda aka yi Duniya bamu taba Jin inda aka yi shi aka koma ba sai dai wata kabilar ba ta musulunci ba.

Yayi shiru Yana sauraren Haj yayin da Farida ma ta kasa kunnuwa tana sauraren su Gaban ta Yana Sarawa.

“Kayi hak’uri Sameer Dole na baka Hak’uri Domin kuwa tun Ran Gini tun Ran Zane idan Ubangiji ya kare zaman ku da Farida to Babu da Wani da ya Isa ya dawo Maka da ita. Amma idan Bai yanke zaman ku ba sai kaga ko taje ga Wani ta dawo Kun koma Ina son ka Saka tauhidi a cikin Al Amarin naku.

Wani irin matsiyacin firgici da ya sauka a ZUCIYAR shi Jin Hajiyar na Fadin wai ko Farida taje ga Wanin shi zata dawo . Idan Akwai Abinda ya tsana a maganar Nan shine ace Farida zatayi Wani Aure har ta tare da Wani Mijin wannan shine karshen tashin hankali a gareshi. Sai yanzu ma ne yake auna maganar hajiyar shi da tace Bai fara kishi ba sai Wani ya mallaki Abinda ya kewa kishin . Hakikatan zuwan Farida ga Wani Namijin tamkar kashe kanshi ne . Ta Yaya farida zata Auri Wani a matsayin shi shi ace Wani ne zai maye mishi gurbi.

Da sauri ya Runtse ido Yana fatan Hakan ya zama MAFARKI.

“Allah ta ala yasa Hakan shine Alherin ku damu gaba Daya Sameer kaddara kenan wacce take sauka akan musulmi.

“Na gode Haj Allah Ya kara lafiya don Allah Haj ki yi min wata Alfarma na san za ki yi mini ita Haj Ina nan asibitin Zaria a Shika ba ni da lafiya Ina son kiyi min Alfarma Haj Ina son Naga Farida da su Saddam kafin na bar Duniya Domin kuwa zan Roki Allah idan har Farida ta barni to ya dauki Raina na huta don Allah Haj ki Amince min na turo Bello ya dauke ta Ina son nayi musu kallon karshe.

“Subuhanallahi Sameer me yake damun ka?.
“Zuciya tace take ciwo Haj.

“Allahu yashfeeka Sameer na maka wannan Alfarmar ka turo Bello n yazo ya dauke su Allah ya baka lafiya ka Daina fatan mutuwa Sameer saboda kaddarar Rayuwa baka San lokacin da Ubangiji ya halicce ka ba sai dai ka ganka a cikin Duniya. Haka Kuma idan yaso ya Kira ka baka da Sani.

Gaban Farida yayi wata matsiyaciyar sarawa saboda Jin hajiya na mishi ADDU AR Allah ya bashi lafiya me yake damun shi ne?

Haj ta aje wayar Farida tana kallon ta, “Sameer ne Babu lafiya wai Yana shika Zaria Ciwon zuciya.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un ta kadu matuka gaya in son samu ne ta nemi izinin haj don tana son Ganin Halin da yake Amma Kuma tana Jin kunya Dole ta kame Baki tana Jin Ciwon Sameer a jikin ta.

“Ki shirya Bellon shi zai zo kuje da Yara ki duba shi.

Ta ji wani sanyi Yana Sauka a zuciyar ta.

Ta shirya ita da su Saddam Bello ya iso ya kwashe su a mota suka nufi Zaria.

Tun a motar Farida take tambayar Bello a wane hali Sameer yake ? Yana cin Abincin? Yana Jin sauki kuwa? Wane ci gaba Ake Samu a Asibitin?

Ya Rasa Amsar da zai Amsa Mata.

Suka iso Zaria inda taga Sameer da irin Ramar da yayi sai gashin fuska da ya Tara.

Suka Zubawa juna ido yayin da Hanan ta Dare jikin Uban ta Saddam Kuma da yaga kanula a hannun shi ya Soma Fadin.

“Daddy baka da lafiya ne? Wannan abun akwai zafi kuwa?

Ya Rungumo Saddam din Yana fidda kwalla yayin da Farida ta zuba mishi idanu Yana Rungumar Ya’yan shi kafin ta Tako tazo Dab da shi ta zaune tana dauke kwallar idon ta.

Tuni Bello ya fita daga D’akin ya Basu wuri
Ya saki Hannun Hanan ya Ruko na farida Yana Kai fuskar shi akan tata Yana fidda kwalla ya Soma Magana.

“Kin ga Halin da Rashin ki ya jefa ni Farida? Kin yarda da Masu son su Raba mu? Nifa Wallahi na janye kalmar Nan don Allah ki fahimtar Dasu.

Ya Sumbaci bakin ta Yana Jin wani irin matsiyacin filing akan ta tamkar Bai taba sanin ta.

Ta Rungume shi Kam a kirjin ta tana kuka tana Fadin.

“Duk Mai kaunar mu Sameer wannan Ranar yaji Mana tsoro. Hakika Babu inda Ake gyaran Auren saki UKU in dai ba gyaran wahayi Ake son ci ba . Ni da Kai Muna son juna Amma sai ka Kasa fahimtar Wani Abu guda Daya har sai da kaddarar tacimmana.

“Ba zan iya Rabuwa da ke ba Farida. Idan Kuma har zan Rasa ki to Allah ya gaggauta daukar numfashi na na bar Duniya.

“Ni Kuma ai ba zan so ka bar Duniyar ka barni ba sai dai kawai mu samu wata mafitar.

Sun jima suna Neman mafitar da zasu jingina da ita Amma Suka kasa samun ta Dole ta Mike da Shirin komawa Gida saboda Ganin yamma ta Soma Amma yace tayi hak’uri zuwa dare bello ya Mika su jaji gidan Yaya dauda su kwana a can.

“Ba zan iya zuwa gidan Yaya dauda ba Sameer. Bani da idon iya duban shi na karanta mishi Auren mu ya mutu don ya jima Yana fada min duk Nisan Zamani matukar dai kana a yadda kake to ga Auren mu can ya mutu me kake so na fada mishi idan nace mishi Kai Nazo Gani a Asibiti saboda zafin kaddarar da ta same mu? Na San Halin sa Yana iya juya maganar ta koma zance.

“Ban gaji da ganin ki ba Farida !

“Sai dai muyi Hak’uri zan dawo Wani Lokacin Ina Maka fatan ALHERI Ubangiji ya baka lafiya Amma kayi kokari ka cire damuwa a Ranka Ina tare da Kai hundred persent

Yana Rik’e da Hanan Yana shafa kanta tare Da Saddam kamar ba zai barsu ba sai da bello yace yamma na Yi fa ya kyale su Suka tafi Yana kallon su idon shi cike da kwalla.

Satin shi Daya a Asibitin aka sallame shi ya koma gida ya samu Sauki Sosai har ya koma bakin Aiki amma fa cike yake da Rashin kwanciyar hankali kullum burin shi ya Samo hanyar da zai mayar da Auren su da Farida.

A cikin wannan tsukun ne Kuma ya samu Wani malamin Yoruba a garin partacout Wanda ya kaiwa kukan shi ya Kuma bashi fatawar da yake son samu . Don haka wannan week End din da ya zo katsina sai ya samu Farida da wannan maganar wadda duk week End Idan zai zo siyayya tamkar akan su ita da Yara albashin Nashi yake karewa.

“Ban gamsu da wannan fatawar ba Sameer. Ni da Kai musulmi ne mun San Babu wata fatawar da ta Bada wannan Damar ga Auren saki UKU wai ayi wannan Abun..

“Kar ki fara kawo min matsala in kika bani Dama sauran mutane Babu Wanda ya Isa yace ba haka ba idan kika fara kawo min matsala to dama da yawan su ba so Suke mu komawa Auren mu ba ke kadai ce Dama ta Kuma tabbatacci na.

Tayi shuru ta kasa tankawa don ta San kadan ya ke Jira ayi Uwar watsi.

Da haka ya yiwa Haj sallama ya wuce Amma Farida tana Jin tsoron fadawa Haj Abinda ya fada don ita da kanta ta san gaskiya Kuma wannan fatawar akwai coge a cikin ta son zuciya ne kawai aka fada mishi shi Kuma da yake a Wuya yake sai ya yarda da Hakan.

Haj ta kira ta tana fada Mata Abinda take Gani akan yawan zaryar da Sameer yake Mata.

“Kar ki sake naji ko na Gani na Soma gajiya da zaryar Nan Farida idan Kuma Ya’yan shi yakewa to ki Mika mishi su ke Kam idda kike Bai kamata ya Rik’a zuwa Yana shige Miki ba in Wani Abu ne ya fadawa Yan Uwan ki ko ya fada mini Amma na gaji da wannan zaryar bana Kuma son ta kinji na fada Miki kar ki bari na Kuma Ganin shi a gidan Nan ki sallame shi in ma kece kike Kiran shi to a Hak’ura Haka anyi na Allah anyi na ANNABI Babu kare bin damo ba komawa dai zakuyi to Banga Dalilin wannan binbini ba.

Kuka take tamkar wacce aka dadawa duka saboda Jin abinda Haj take fada Mata ita ta Yaya zata iya fadawa Sameer ya Daina Zuwa gidan su ? Ta Yaya zata iya fuskantar shi da wannan maganar? A cikin kwanakin Nan Babu Abinda yake Ranta irin Sameer tana Jin Wani Abu akan shi Wanda Bata tabaji ba. Ta Yaya zata iya Rayuwa Babu Sameer a Duniyar ta ?

Haj ta Zuba Mata ido tana kallon ta ganin kukan ta tamkar wacce tayiwa Abinda yafi magana ciwo Amma take mata wannan kukan?

“Ki tashi daga gabana tun baki yi kukan Mai Dalili ba Wallahi sakarai Jaka marar tunani halan kema kina son ce min mijin ki kike so ? To karya kuke Wallahi ni da ku ne duk ku gama zagaye zagayen ku fito fili kuyi magana Amma har yanzu Bakuyi magana ba don na gama Gane kema kina da magana a cikin Bakin ki to ba Dani ba gadar makwatai in ku akwai wani Abu akan ku ni da sauran mutane da Hankalin mu in ku Kun haukace . Kuma mu Muna da Sanin Shari a in ku shaidan ya kada muku gangar sa.

Ta Mike tana share HAWAYE ta nufi D’akin ta tana gursheken kuka Wanda take ji tamkar Zata mace Babu Abinda take hangowa sai Rabuwar su da Sameer ta Yaya zata iya jure Rashin sa a tare da ita ?

<< Tana Kasa Tana Dabo 17Tana Kasa Tana Dabo 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×