Skip to content
Part 20 of 23 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

 

 Wasila

Tun da Sukayi haka da ISHAQ wasila taci ganye Wanda ya zarce na baya . Domin kuwa a yau joint Kwana tayi da Mai Naira Wanda ya isheta da Kiran waya. Don haka tayi Shiri na Sosai da kayan Yar Sokoto Wanda ta yarda da ingancin su Domin kuwa suna kawo Mata fire.

Ta fito cikin dogon hijabin ta Wanda ta sakaya matsiyaciyar kwalliyar da ta tayi.

Ta Dubi yusra tana fadin, “Kinga shinkafar can yusra ki debo ki dafa muku don ya kamata ma ace Zuwa yanzu kin iya girki don na huta in yaso idan Uban ku ya dawo ya baku kudin Mai akwai yaji a d’aki sai kuci fara da Mai.

“Ni fa mama ban iya girkin Nan ba wutar ma ban iya hada ta ba bare gawayi.

“Sai ki koya ai ba daga sama ake iyawa ba sai an koya ki zuba kalanzir sai ki buga ashana ki fifita idan ya kama sai ki Dora waccan tukunyar ta tower tafi saurin tafasa ki zuba Ruwa Kofi uku bari na Debo Miki shinkafar.

Ta Debo Mata ta Bata ta fice daga gidan tana sauri.

Mai Naira ya dauke ta Suka wuce inda yace Mata Abuja zashi Kuma tare yake so su wuce

“Ba ka da matsala muje Kawai a yanzu bani da wata fargaba ko sati kake so zamu yi.

Ya kuwa wuce zuwa filin sauka da tashi na malam Umar Musa Yar Adua ya yankar musu tikitin jirgi suka wuce Abuja Zuwan wasila Abuja karo na farko ta ga birnin tarayya Abuja ta Kuma ga gidaje don Mai naira Yana da gida a birnin tarayya Abuja Wani mashahurin gida Mai kama da fadar sarauniya inda suka SHIGA watsewar da suka Saka gaba har suna mantawa da haramcin ta.

Sai da Suka yi Kwanki uku Mai Naira Yana morewa da wasila Abinda yasa yake makale Mata shi kadai yasan Al Amarin da yake samu a tare da ita.

Tun daga wannan Rana yusra take kwamacalar ta da sunan girki haka zata dafa ko ta cika Ruwa ko ta cika gishiri suyi ta sharba ita da Zee Zee wacce Bata jure yunwa acici ce ta Sosai .

Sagir ya Dubi yusra tana ta hada garwashi a kurfoti yace, “Me zaki dafa ne Kuma yusra?

“Ruwan wanka zan dafawa Abba Naga baya wanka da Ruwan Sanyi Kuma in na gama zan dumama Mana taliyar mu.

Sagir yaji Wani Abu Yana tab’a zuciyar shi Dole ya fice ya bar Gidan

Ai kuwa yusra ta dafa Ruwan ta Isa d’akin ishaq tana fadin, “Abba ga Ruwan wanka na dafa Maka.

Ya Mike ya fito Yana Fadin, “Allah yayi Miki Albarka yusra kinji Allah ya azurta ki da zuciya Mai k’ana A da tauhidi Da tsoron Allah ya cire Miki kwadayi da Hangen Duniya.

Sagir ya Isa gidan Anty murja Yana kuka ta fito tana Fadin, “Sagir wa ya mutu Kuma ? Me yake faruwa?

Ya zauna Yana kuka yake fadawa Anty murja halayyar da Uwar su ta dauko.

“Yanzu Anty har mama zata iya watsar da yusra da Zainab ta kama gaban ta Babu Wanda take fadawa ko Abban mu baya sanin inda take Zuwa. Yau fa kwananta UKU bata gida . Dole fa yanzu sai yusra ce ke kwamacalar ta da sunan girki Ranar zee zee kwana tayi zawayi saboda danyen Abincin da taci. Don Allah Anty murja ke kadai ce Mai fada Mata gaskiya Amma ko Goggo na lura mama ta Raina ta ni Kam mama tana shayar Dani Bak’in ciki marar iyaka.

Murja ta Soma share mishi HAWAYEn shi tana Fadin.

“Wallahi ban Sani ba sagir Amma kayi hak’uri idan ta dawo kazo ka fad’a min zanzo na fada Mata gaskiya tunda babu Abinda zaka bawa Dan Uwan ka da ya wuce ka fad’a mishi gaskiya Kuma ni da kaina naga canje canje da yawa ga wasila Amma ban munana Mata zato ba Amma a yanzu Kam Dole akwai ayar tambaya akan ta kayi Hak’uri kayi Mata ADDU A.

Ya Mike Yana Godiya ga Anty murja Yayi Mata sallama ya tafi.

ISHAQ ya nutsa Yana tunanin yanzu Al Amarin wasila har ya Kai ta kwana Bata gida . Sai gashi ta shayar da shi mamaki tayi kwana uku Bata Dawo ba inda yaji Lallai ya zama Dole ya sauwakewa wasila Auren shi don zai zama kayan laifin da zata dauko Shima ta sammasa Amma idan ya sauwake mata sai taci ganyen ta da kyau . Amma Kuma Yana Jin kunyar Goggo Amma Kuma Goggo ma ba zata iya yarda da Abinda zai cutar da shi ba.

Motar da Mai gemu ya bawa wasila kasuwa ta Saka ta ta siyar da Zuba kud’in a account din ta don ta San Bata Isa murza sitiyarin mota tana a haka ba sai dai na GABA.

Al Amarin wasila da Yan iskan ta yaci gaba da gudana yau wannan ya dauka gobe wannan ya dauka.

A yau Kam ta wayi gari da Alamun bayyanar ciki a tare da ita don haka Bata tsaya ba ta nufi Asibiti . Sai dai magani ta karbo don Bai Isa zubarwa ba.

Kan kace me? Laulayi Mai tsanani ya same ta ta Soma jinya don ita Bata boye laulayi da ta fara shi zai nuna ta.

Al Amarin ya ishe ishaq ya Rasa yadda zaiyi da wasila wacce ya gama Gane hanyar da take bi. Don haka Bai tsaya komai ba ya Rattaba Mata Saki Daya ya linke ya ajiye Amma Kuma sai Kunyar Ya’yan ta ta Rufe shi . Da wace fuskar zai Dube su? Sai ya ajiye takardar ya kasa Bata don ya gama Gane Abinda wasila take so kenan ya sake ta. In ya sake ta gobarar titi a jos kenan . Amma damuwar shi sagir da yusra da Zainab su nemi Uwar su ace ya sake ta shine Abinda yake damuwar shi. Amma Kuma Yana Bak’in cikin laulayin da yake ganin tanayi Wanda ya san a waje ta kwaso abinta.

Tana cikin laulayin ya dauko Anty murja suka zi gidan a tare Yana nunawa murja halin da wasila take ciki na laulayi.

“Murja ke na kafa shaida Kinga Halin da wasila take ciki to na gaji da Abinda take . Idan ta Kuma zubar da wani cikin a gida na zan jawo magana don Naji Dalilin ta na Zubar da ciki don haka ki Bata magana.

Wasila ta Mike daga kwancen da take bakin ta cike da yawu tana Fadin.

“Ai kuwa kazo inda za ayi magana tunda abin naka Sharri ne Wallahi dama na jima da gajiya na gaji da gantalallen Auren ka tunda har kana zargi na.

“Ba shi kadai yake zargin ki ba har Dani Nan !
Cewar Anty murja.

Ta juyo idon ta akan Anty murja tana Fadin
“Har da ke a cikin masu zargi na murja? Ta fada tana dafe kirji.

“Ba ke ba murja hatta da sagir Wanda ta tsuguna ta Haifa na Gane zargin ta yake ni Kam Ina tsoron Ranar da Zaki Saka ni magana don zan fito da komai ne Kuma da kike cewa kin Gaji da Aure na ai ke kinfi kowa Sanin nafi ki gajiya Amma har yanzu Baki zo inda zanyi magana ba.

Wasila ta koma ta Zauna tana kuka tana Fadin
“Ban yi mamaki ba Murja yau ke ce kike fadar wannan maganar a inda Ake son na wulakanta.

“In kinyi mamakin ma ai kin so ki yaudari kanki ne kawai . Kuma tuni Allah Ya nunawa Dubu Abinda kike lullube wa. Kuma tafiyar da kikayi har kika kwana uku bakya Gida sagir yaje gida na da kukan shi yana fada min kin bar Gida kwana uku Baki dawo ba Ina kika je? Kwanaki Goggo ta fada min kin shirya karyar zuwa Gago amma aka Samu Baki Je ba. Wasila Al Amarin ki ya Soma bayyana a idon Wanda kike nufin yaudara . Ke kuwa me kike so cikin Duniya da har kika wulakanta Aure da Haihuwa haka ? Wasila na fahimce ki Wallahi Duniya tana Fada Miki karya har kina Neman ki halaka.

“Abinda ya fada Miki kenan? Sharrin da ISHAQ yayi Min kenan a wurin ki?

“Ni ISHAQ Bai ce min komai ba akan ki gara ki Kalli Hakan daga gareni nice na ke zargin Hakan.

“Yanzu Dama Dan Uwan ka zai nema Maka JANHURUN masifa murja? A duk Duniya Ashe Dan Uwan ka shi yake zama makiyin ka? To Wallahi murja ba zan yarda da wannan yarfen da kikayi min ba Dama ana Shirin kunyata ni kinzo kina sunce min zani a kasuwa.

“Ki kaini Kara kotu sai ki nemi hakkin ki . Ni Kuma a yanzu zanje na dauko Goggo tazo taji irin ta asar da kike Yi a gidan Auren ki Kinga sai mu hade a kotu kawai tunda ma ba Zaki yarda ba ai ni hake so.

Murja ta Mike ta fice daga gidan ta nufi gidan Goggo inda ta fadawa Goggo kuka tana Fadin

“Goggo wasila tana Shirin kunya ta mu a garin Nan na shiga uku Goggo wasila ta dauko hanyar lalacewa a zage ta Kuma Muma tajaza mana zagi.

Goggo ta aje masakin da ta kinkima jikin ta Yana bari tana salati da taslimi tana Fadin

“Me Kuma ya faru murja?

Ta Mike tana zama don sauran kad’an ta Kai k’asa saboda firgita.

“Goggo wasila tana Neman Saka mu a bakin Duniya. Wai fa kiji kwana UKU Bata Gida sai da sagir yazo yana kuka Yana Rokon nayi Mata magana ta Daina fitar da take ko don su yusra. Ban San ta dawo ba sai da ishaq yazo ya dauke ni muka je gidan tana kwance tana Laulayi Goggo shine ishaq ya ce shaida zai kafa ni in ta kuma zubar da cikin shine fa take ta tijara har tana Fadin wai ta Gaji da Auren shi tunda Yana zargin ta ni Kuma nace Nima Nan zargin ta nake tun da ga Abinda ya faru shine fa tace wai nayi Mata yarfe ni Kuma nace sai na dauko ki don kiga komai

Goggo ta Mike jikin ta Yana ciri ta dauko mayafin ta ta ce.


“Tashi mu tafi gidan murja ba ke ba ni kaina Ina tsoron faruwar Wani Abu akan wasila don na tsorata da ita.

Suka iso gidan Suka samu wasila tana ta kuka wai murja taci mutuncin ta akan idon ISHAQ.

Goggo ta Dube ta tana fadin, “Kinga ni ma nan Wallahi Ina zargin ki wasila don haka kar ki Wani tsaya Rufe mini don Allah ya sani ba zan bari ki cuci yaron Nan ba.

“Dubi irin suturun da kike sakawa Wanda ni da ke mun San mijin ki ba ya iya Siya Miki su saboda Bashi da karfin daukar nauyin ki. Dubi yadda kike Wani maiko ke da kanki don Allah bakiji kina tuhumar kanki ba? To hakika ni ma idan Kika sake na Gane Abinda Nike zargi a tare da ke to ni da ke wata Kil dai SAI A LAHIRA don kin min bazata Kuma Babu Abinda zance Miki illa na barki da Allah. ! Ina kikaje har kika kwana UKU? A wancan Lokacin kin yaudare ni da Cewa Gago kika je yanzu Kuma bindawa kika je ko? To na barki da Allah idan kin cuci yaron Nan ishaq Allah ne zai saka mishi ke kuma duk Abinda kika Zaba za a barki da shi Amma Nima Nan Wallahi Ina zargin ki da Bak’ar kasuwar Matan Zamani in kin tashi Kai murja kotu sai ki hada ni don Nima a watse nake kallon ki Wallahi Babu ko Riga don kin gama tsiraita kanki ta yadda zan ganki zugidir.

Haka Goggo ta fice tana fyace majina da gefen zanin ta murja na Bata hak’uri.

Ko a kwalar Rigar wasila don ciki Kam ga shi can ta Zubar ko ba komai ai zai kashe mata kasuwa ne don haka sati Sha Biyu taje Asibiti aka burke Mata cikin Nan ta dawo gida abinta

Tana kuma samun sauki ta koma harkar ta don Zuwan da tayi Abuja ta hadu da wata gogaggiya a Wani store wai ita Shama don haka ita da Shama sun dinke tif da Taya inda Shama ke Kara Gogar da ita yadda Ake wanke Maza.

Ranar da ta fita ita da gemu Wanda yake tsegumi akan Rashin Hawa mota don shi Kam Yana son yaga tana hawa mota Amma Kuma tana tsoron Abinda zaije ya Dawo musamman yanzu da aka zura mata ido.

Ta Dubi motar da Mai gemu ya sauya wata katuwar mota ta shiga taro tana Fadin,

“Gaskiya kana Jin Dadin ka Alhaji na wannan kwano ya burge ni.

“Wannan motar zan mayar da ita ne a sake min don an Rufe mini tana da matsala yanzu haka Ina jin k’arar da ta ke Amma baccin haka da na Baki ita don Naga kin taba ta ni Kuma Abinda zan burge ki nake so.

Ta yi murmushi tana Fadin “Ni fa ai kullum burge ni kakeyi mota Kuma ba yanzu ba ka bari in na tashi taka mota zan yi maka magana.

Suna karya kwana shiga gidan shakatawar Mai gemu motar Nan ta Soma Kara kit kit kit har tsaya cik.

“Kinga matsalar da nake Gaya Miki ko? Yanzu Dole sai na Nemo Mai gyara sabuwar mota ace sai ka hada ta da Mai gyara?

Ya fito itama ta fito tana fadin, “Gaskiya gara a sake Maka wata wata Kil angulu ne da kan zabo akayi mata tsohuwa ce aka fanfa ta…

Suka wuce cikin Gidan Yana zaro wayar shi Yana Kiran garejin da suke mishi gyara.

“Shehu injiniya ya kake ? Don Allah ka zo motar nan ta Kuma tsayawa Wallahi ni Kam zan mayar da ita a sake min bana Jin wuya don Allah kazo guesy house Dina Dake Ring road ka gyara min ita.

“Mai gida Wallahi bana gari Amma bari na turo Maka smoli ya duba Maka ita ya iya Aiki Babu karya don shine magaji na ko Bana nan ka kawo gyara ka Bashi zai gyara ta kamar ni Nayi…

“Ok to ba matsala ka tura min shi ai na kula Yana da Hankali Kuma baya wasa a Aiki..

“Bari na tura maka lambar shi don in yazo ya Kira ka.

Shehu ya turo lambar smoli ya kuma Kira shi ya kwatanta mishi inda zai je yayi Gyara

Sagir Wanda Ake cewa smoli a garejin su ya fito da kayan Aiki ya nufi Ring road inda Oga shehu ya kwatanta mishi. Ya na zuwa kuwa ya Kira wayar shi ya fada mishi yazo.

Da sauri Mai gemu ya fito ya samu sagir Wanda ya zube Yana gaishe shi ya fada mishi shine Wanda Oga shehu ya turo zai duba motar.

“Yauwa dan smoli karbi key din ka kunna kaji yadda takeyi sai ka Gano kan ciwon.

Sagir ya karbi key din Yana tayar da motar yaji yadda take Yi ya fito ya kwance kayan Aikin da yazo da su ya bude gaban motar ya Soma Aikin shi Mai gemu Kuma ya bar mishi key din yace idan ya gama yayi mishi magana a ciki

Ya juya ya koma ciki shi Kuma sagir ya Soma Aikin shi inda ya gano matsalar tuni Kuma ya Soma gwada kokarin shi da Hikimar da Ubangiji ya bashi.

Cikin k’asa da awa Daya da Rabi ya kammala ya koma cikin motar ya tashi motar yaji ta sauya daga k’arar da take ta Asali har Wani jijjiga take.

Ya fito ya sake komawa gaban motar ya tab’o Wani wurin sai da yaji yayi mishi yadda yeke so kafin ya koma ya sake tashin motar ya tabbatar da tayi daidai kafin ya kashe ya fito Yana Rik’e da key din motar ya nufi kofar da yaga Alh ya fito.

Wasila da ta fito daga wanka bayan an kawo musu abin tabawa ta shiga wanka ta fito daure da tawul a kugun ta yayin da manyan cinyoyin ta Suka bayyana jajir ga tudun kirjin ta da Shima kusan Rabi yake a waje.

Ta zauna ta jawo jakar ta wacce take cike da kayan shafa ta Soma shafe jikin ta da kayan kamshi inda me gemu Shima ya fito daga wankan ya Ganta cinyoyin ta sun bayyana ya K’araso ya Duka dab da ita Yana Kai Hannu akan cinyoyin ta Yana shafawa har ya Rungumo ta Yana Kai bakin shi a bakin ta Suka hade suna kissing din juna tamkar wasu mayu Abinda zamu iya Kira azal ko tsautsayi Wanda ya kawo yaro sagir bawan Allah Rabon yayi mugun gani.

Yayi ta sallama a kofar Amma Bai ji an amsa ba ya Kuma yin sallama sama da sau biyar har dai ya yanke shawarar shiga ya Kuma shiga inda Al Amarin ya zamo mishi KAMAR A MAFARKI ya hango mahaifiyar tashi Rungume a jikin wannan hamshakin mutum bakin su a hade Kuma sunce sai Dan tawul daure a kugun su Wanda bashi da maraba da Babu Al Amarin da ya yi matukar gigita shi ya kusa zarar da numfashin sa.

<< Tana Kasa Tana Dabo 19Tana Kasa Tana Dabo 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×