Skip to content
Part 21 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Tamkar Wanda aka kwalawa mabugi aka haka Sagir yaji wani matsiyacin duka akan sa wanda yake neman tarwatsa masa kwanya.

Yayi maza ya dafe bango saboda jin ana shirin wurwura shi a maka da kasa.

Wasila da taji Wani matsiyacin firgici da dukan kirji Wanda Bata San Dalilin sa ba sai kawai taga Al Amarin tamkar shiri ko majigi inda ta hangi sagir Dafe da bango idanun shi suna tsiyayar hawaye.

Suna hada ido da Sagir ya saki key din motar a k’asa yayi Maza ya ja jiki ya fice har Yana gabza tuntube ya Kuma kife a kas Yana dauje goshi. Ya Mike da wani irin sauri ya fice inda kukan ya kwace mishi ya fice a guje.

Wasila da taga sagir a bakin kofar tayi maza ta kwace bakin ta da yake Jone da Bakin Mai Naira tana Jin Wani matsiyacin lugude a zuciyar ta inda ta kwace jikin ta tana mayar da numfashi tamkar wacce tayi Gudun fanfalaki.

Mai Naira yabi ta da kallo ganin yadda ta firgici tamkar wata Mai aljanu.

“Waye ka Kira ne yayi maka gyaran mota?
Ta tambaya a rikice.

“Wani yaro ne wani abu ne?

Ta Kuma Rikicewa don ta gama yarda sagir ta Gani da dai tana ganin kamar gizo idon ta yayi Mata Amma yanzu tabbaccin Hakan gare ta.

Ta Dora Hannun ta a kirji tana Shirin FASA kuka Amma kuma ta kasa samun kukan.

Mai Naira ya taso ya Rungume ta Yana shafa fuskar ta Yana murmushi yana fad’in.

“Me ya faru ne Naga duk kin birkice kamar wacce aka tsorata?

Ta kasa Bashi amsa don bil hakki a kidime take. Lallai ta gama muzanta a yau tunda har Allah ya nunawa sagir irin Bak’ar kasuwar da take Yi wane ido gareta na duban yaron?
Duk yadda Mai Naira ya ke cike da ita da barikin shi Bai iya Samun yadda yake so ba Domin kuwa tamkar marar lafiya haka wasila ta koma Babu wani armashi a haduwar ta yau shi yayi kidan sa yayi rawarsa.

Bata taba yin nadamar Abinda takeyi ba irin yau da sagir yagan ta Baki da baki suna Abinda ta tabbatar wa kanta ita da shi zai Hana su Zaman lafiya.

Ta rasa Abinda yake mata Dadi har Suka gama Masha ar su wacce ba zata iya tuna komai a ciki ba.

Mai Naira ya Dube ta Yana Fadin
“Wai me yake damun ki ne gimbiya? Naga yau duk a Rikice kike Babu laka a jikin ki ko Baki da lafiya ne muje Asibiti?

Idon ta ya kada ta juya fuskar ta gefe tana Fadin “Ba ni da lafiya ne.

“Ayya tashi muje Asibiti ai nayi zaton ko ke da Mai gidan ne ince ai yayi Hak’uri Muna ta gurzar mishi abubuwa.

Ya fada Yana gaggaba Dariya ya Mike Yana Fadin “Kinga yaron Nan har yanzu Bai kammala gyaran Nan ba Anya kuwa ya iya gyaran Nan? Har yanzu fa kusan awa biyar Amma Bai k’arasa ba?

Ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya Saka jallabiya ya fita wurin smoli Amma sai ya Tara’s da Babu kowa ga mota Amma Babu yaro Babu Dalilin sa.

Ya duba ya Kuma dubawa Amma Babu kowa
Ya Isa inda Mai Gadin yake Yana tambayar shi yaron da yazo yayi Gyaran mota.

“Ai ya fita tun Dazu Mai Gida inajin ya gama ne.

“Ya fita ka ce? Ya tambaya Yana mamakin to ya akayi ya gama Bai mishi magana ba?

“Ko Wani Abu ya faru ne Mai Gida? Naga fitar yaron tun Dazu na zaci ko an sallame shi ne.

“Ban sallame shi ba makullin motar ma Yana wurin shi Amma ai na San Wanda ya turo shi bari na Kira shi nace ya turo min yaron bana zaton zai tafi da makullin don wani Abu sai dai ko Wani uzuri Mai k’arfi.

Mai Naira ya juya ya koma ciki Yana Fadawa wasila cewar

“Yaron Nan ya gama Amma baya wurin Kuma bai bar makullin motar ba wata Kil Wani uzurin ne ya mayar dashi bari na kira shehu ya turo min shi.

Wani Abu ya soki zuciyar wasila Jin Wai sagir ya tafi mishi da makullin mota Abinda ya Kara tabbatar Mata da dan iska baya son ace Nashi Dan iska ne ta San hakikatan sagir ba zai dauki makullin motar ba.

Mai Naira Yana daukar wayar shi da nufin Kiran shehu ya gangi key din a k’asa Abinda yasa shi Cewa

“Kingan shi ma a k’asa. To ta Yaya Akayi key din yazo Nan ? Kar dai ace yaron yayi Mana magana Muna Saman network bamuji shi ba? Ya fada Yana Duban fuskar wasila wacce ta tabbatar da Hakan akayi Amma ita da wace fuskar zata Fadi Hakan?

Ya Mike ya fita inda motar take ya bude ya shiga ya tashi motar yaji ta Gyaru ta Daina k’arar da take, Ya fito Yana danna lambar shegu Yana kir “Yaya ne Mai Gida gyara yayi ko kuwa akwai Gyara?

“Gyara yayi shehu yaro Kuma yayi bajinta hakikatan sai dai Wani uzuri ya Hana na sallame shi har ya tafi ko akwai account din sa a bani na biya shi kudin Aikin shi?

“Yauwa to don Allah a bani na tura mishi kud’in Aikin shi.

Sai da aka tura mishi account din sai ya tuna shehun ma ya tura mishi lambar shi don haka sai ya danna Mishi Kira Amma har wayar ta tsinke Bai dauka ba ya sake danna Kiran inda yaji muryar sagir din ya dauka Yana sallama inda Mai Naira ya Soma Fadin.

“Smoli Kuma sai ka tafi baka tsaya na sallame ka ba?

“Kayi hak’uri Alh Dole ne yasa na tafiya.

“Dama Nace wata Kil Wani uzurin ya taso Maka Amma yanzu zan tura maka kudin Aikin ka shehu ya tura min account nambar ka yanzu zan tura maka sakon ka na murza mota Naji tayi zan Adana nomber ka ko da zata kama na neme ka.

Ya kashe wayar wasila na Jin su tana hango muzantar da zatayi idan ta hada ido da sagir

Ya sauke wayar daga kunnen shi Yana shiga app don yin transfer yayiwa sagir transfer Dubu Hamsin a account din sa a matsayin kudin Aikin shi.

Sagir
Ya fito daga gidan da ya Kira bakin gida Wanda har ya komawa Ubangiji ba zai tab’a manta Abinda ya Gani da Wanda akayi mishi ba.


Goshin sa da ishe shi da Rad’adi Bai dame shi ba irin Abinda yake gilmawa ta idon shi na haduwar Bakin mahaifiyar shi da wannan hamshakin da sunan watsewa Alhalin ita din tana Rik’e da igiya UKU ta Auren mahaifin sa Amma dubi Abinda taja musu ko ace taja mishi Wanda yake jin da mutuwa yayi Bai ga wannan abun ba da ya fiye mishi afuwa don yasan mutuwa ga musulmi Hutu ne

Ya tsayar da Napep ya SHIGA ya Fadi inda za a kaishi Yana dafe da kanshi Yana Jin yadda zuciyar shi take Shirin tsinkewa saboda Tashin hankalin da yake ciki.

Har suka zo Gida Bai iya Sanin ta hanyar da suka biyo Zuwa gidan ba shi dai ya gansu a kofar gidan su.

Ya fito ya sallami Mai Napep din kudin shi ya wuce cikin Gidan Yana layi tamkar zai Fadi

Ya shiga gidan yana cin karo da Zee Zee wacce ta taho da Gudu ta na mishi oyoyo Amma Ganin goshin sa da jini yasa tace

“Yaya jini a kanka? Bai iya tankawa zee zee ba ya wuce D’akin shi ya kwanta hawaye na bin idon shi Amma duk ba ta su yake ba. Ta Abunda ya Gani a kwayar idon sa ne wai mahaifiya ce tayi hakan Allah ya nunawa Ahalin ta.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un.

Ita kadai yake fada.

Yusra ta shigo D’akin tana Fadin, “Yaya me ya same ka?

Ya boye fuskar shi wacce take kaca kaca da hawaye Amma tuni Zee Zee ta Gano hawayen tana Fadin“Yusra Yaya kuka yake kanshi Kuma da jini.

Sukayi jugum suka kasa tabuka komai.

ISHAQ ya dawo gida inda Zee Zee ta taho tana fadin
“Abba Yaya ya dawo Yana kuka Kuma kanshi da jini…

Ya Dubi bakin yarinyar wacce take fadar maganar kafin ya fita ya nufi D’akin sagir…

A zaune ya same shi ya Dafe Kai ido jajir Yana yararin hawaye…

“Subuhanallahi sagir me ya same ka?
Ya kamo hannun shi Suka fito tsakar gidan Yana Rarrashin shi ..

Wasila ta shigo Gidan a matukar kunya ce jikin ta a Sanyaye inda Kuma tayi karo da sagir da ishaq Wanda yake faman Rarrashi…

“Abba ka yafe mini Amma zan bar garin Nan ba zan iya zama a garin Nan ba.

Ya fada Yana fashewa da kuka Abinda ya tab’a zuciyar wasila.

“Ba zai yuwu ba sagir in ka bar garin Nan kaje Ina? Kaine bangon jinginar Yan Uwan ka wace Rayuwa kake so suyi bayan Basu da kowa daga ni sai Kai?.

“Don Allah don ANNABI Abba kar ka Hana ni tafiya in ka Hana ni tafiya zan mutu ne ZUCIYA ta ba zata iya daukar abubuwan Nan ba wallahi . Don Allah ka Saka mini Albarka Amma zan tafi ne inda Babu Wanda ya Sanni nayi Rayuwa ta a can.

“Ba zan iya barin ka ka tafi ba sagir Dukkan Arzikin bawa mafifici shine Wanda ya samu a cikin k’asar su Kuma garin su . Kayi hak’uri da dukkan kaddarar da Rayuwa ta kamfata ta Mika Maka in Sha Allah bayan tsanani Sauki ne bayan shi . Allah yayi maka Maganin damuwar ka ya kawo maka Rahama Mai yawa a Cikin Rayuwar ka.

“Ameen Abba Amma to kayi min Afuwa na bar Gidan Nan na koma kauye wurin su Inna suwaiba.

“Sagir ta Yaya zaka iya wannan Rayuwar? Wai anyi Maka Wani Abu ne a gidan Nan da kake son kaurace mishi ?

“Abbakar ka tambaye ni don Allah! Amma ba na son Ina Bude idona Ina ganin mamar mu Wallahi ..Wallahi Abba bana son Ganin ta ban taba yin kaicon kasancewa ta Ahalin ta ba sai a yau don Allah Abba kar ka tambaye ni komai.

Wasila ta Soma zubar da hawaye Domin kuwa taji shigar wannan maganar a zuciyar ta Kuma ta San da gaske sagir yake.

“Kar ka sake furta wannan maganar sagir kaji na fada maka. Iyaye duk lalacewar su Basu da madadi Wallahi Kuma ko hauka suke sunan su Yana Nan a iyaye ko da Kuwa kafurai ne ba a bujire musu kar na Kuma Jin ka aibata mahaifiyar ka baka da wacce ta fita duk Duniya ko da Kuwa nine tana Gaba Dani a girman matsayi da hakki.

Wasila ta wuce su tana Jin wata irin muzanta tana lullubeta.

Sagir kuka yake tamkar Ranshi zai fita ya kasa cewa komai har ishaq ya gama Yi mishi nasihar ya sallame shi ya wuce d’aki

Ya kasa kwanciya ya kasa zama. Ya Rasa Abinda Zaiyi. Amma dai ya tabbatar da ba zai iya tsallake Umarnin Uban sa ba. Don haka sai ya fito ya nufi D’akin wasila wacce take Zaune cike da Rudani.

Tana ganin ya shigo ta kuma Rikicewa
Ya zube a Gaban ta Yana Fadin.
“Mama tunda kika haife ni na tab’a shayar Dake Wani Bak’in ciki Wanda ya taba zuciyar ki tun daga haihuwa ta kawo yau din?

Tayi shiru ta kasa tanka mishi
“Yanzu mama hanyar da kika Zaba kenan? Kin kuwa San axabar da akewa Wanda yayi wancan Al Amarin da Auren shi? A yau da kin Kai Abba kotu akan ya sauwake miki auren shi da Banga laifin ki ba Akasin Abinda idanu na Suka nuna mini. Wallahi ban tab’a dandanar Bak’in ciki a Rayuwa ta irin Abinda na Gani ba. Da na San zanga Abinda na Gani da na Roki Allah ya dauki Rayuwa ta Banga Hakan ba. Ni ba zance ki Daina Abinda kike ba Amma Ina Mai tabbatar Miki Baki da nasara a cikin sa tunda ta ko Ina kika fara sai an nunawa Wanda kike lullube wa Abinda kike . Nayi Miki ADDU A mama nayi nasiha Amma duk Baki ji ba to ni kam zan barki da ALLAH Wallahi duk abinda kike son samu ba Zaki tab’a samun shi ba tunda kika ci Amanar Allah kika ci ta Aure. Amma Ina Rokon Ubangiji ya tsare Miki yusra da Zainab don in Suka dauki hanyar da kika dauka Wallahi da kinji na mutu to Bak’in ciki ne ya kashe ni Kuma ba zan yafe Miki ba har a gaban Allah sai yayi Mana hisabi . Kuma ni ba zan taba tona Asirin ki ga kowa ba da Sannu dukkan Wanda kike Rufewa Allah zai Bude mishi ya Gani kamar yadda ya bude mini . Da kin Gane tun farko nace Miki abinda kika fara baki fara shi da nasara ba tunda kinyi Kuma an tona Asirin ki da kin bari da Allah ya azurta ki ta inda Bakiyi zato ba to mama ALLAH ya taimake ki Abban mu Kuma da kika wulakanta kika wulakanta mishi Aure Zaki ga ta inda ALLAH zai yi mishi sakamakon da Baki zata ba . Kowa yayi na gari akan sa yake Gani ni Kam na fita hakkin haihuwa ni ban Damu da a fita nawa hakkin ba Allah ne zai fidda min In dai kin cuce ni mama Allah ya shirya ki in har kina son shiriyar.

Ya tashi ya fice ya barta da buguwar zuciyar Amma Kuma a Ranta Bata ji kamar zata bari ba don a satin Nan ma Shama ta Kira ta zuwa Abuja don Akwai Wanda zata hada ta dashi.

Shama kam aikin ta kenan hada Masha a da Zina . Kawaliya ce ta bugawa a jarida don haka duk inda taga mace Mai kyau da Dirin jiki yanzu ne zata dafe Mata da son hada alaka da ita har ta yaudare ta zuwa ga alhazawan birni masu son watsewa ko da Kuwa mace bata da Ra ayin Hakan sai shama ta kwadaita Mata harkar .

Don haka washe gari ma wasila ta fice Zuwa birnin tarayya Abuja suka hade da Shama wacce ta hada ta da Wani babban mutum Dan majalisar wakilai ne Mai wakiltar birnin kebbi Amma Yana da gida a Abuja don haka tuni Shama ta Mika wasila gareshi don tun Ranar da suka hadun Shama tayi hotuna da wasila Hikimar ta don ta nunawa yan barikin mutanen ta kalar fuskar wasila .sai kuwa gashi tayi babban kamu har mutum UKU suka Rola wasila Amma dai za a Fi Samun hatsi wurin Dan majalisar wakilai don haka da shi cinikin ya fada shiyasa ta gayyaci wasila Zuwa birnin tarayya Abuja.

Bata baro Abuja ba sai da tayi sati cur ta Kuma dawo da manyan kudade na ban mamaki inda Shama ke zuga ta akan ta Kai k’arar mijin ta ya sauwake mata Auren shi ta Dawo birnin tarayya Abuja inda zata Gane Mazan Abuja ba Daya suke Da sauran game garin Mazan ba. In ana Dara fidda Uwa Ake in tana son mallakar kud’i sai tayi da gaske in Kuma ba haka ba tana ji tana Gani ayi Babu ita ta dai ga yadda mazan Abuja ke sakin Dalar amurka tamkar yayin dawa.

Da wannan hudubar wasila ta baro birnin tarayya Abuja ta Dawo katsina cike da kwadayi da Burin mallakar kud’i a Rayuwar ta .

Sai ya zamo a yanzu Bata Faye haduwa da Mai Naira ko Mai gemu ba tafi bayar da karfi a garin Abuja don yanzu Bata sati Bata taka Abuja ba.

Saboda ganin wannan harkar yasa taje Asibiti aka k’ak’aba Mata Robar Nan unplug ta Hana daukar ciki a Hannu ta huta da Zullumin samun ciki Kuma wannan din duk hudubar Shama ne don ita ta Gogar da ita da kayan gyara da Kuma mayuka na shafa . Sai ya zamo yanzu Kam suffar wasila ta fita irin fitar Nan ta wankan sukari ta Kuma tafasa ta kone Bata tsoron kauri.

Don Haka a yanzu Babu Abinda ke gaban ta irin ta samu takardar sakin Auren ta ta balle zuwa Abuja don ta sakata ta Wala yadda take so Amma Kuma ta Rasa ta hanyar da zata iya karbar takardar Domin kuwa a yanzu tafi shakkar sagir da Goggo akan ishaq akaran kanshi . Sai ta ga Babu ta yadda za ayi ta Samu Hakan sai ta hanyar kullawa ISHAQ din wani katoton Sharri wanda zasu dire a Gaban kuliya manta sabo ta nemi sakin Auren ta a Gaban alkali don Haka sai tayi murmushi tana Fadin.

<< Tana Kasa Tana Dabo 20Tana Kasa Tana Dabo 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×