Skip to content
Part 22 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Goggo ta dubi murja tana zaro idon ta waje tana fadin.

“Ni ? Allah ya sauwake murja wallahi ba zan iya hada tafiya da wasila ba don Bak’in ciki kawai zan kwasa Muna tafe ana nuna mu? Ba zan jera da ita ba in taga dama ta biyo bayan mu in ma Bata Gani ba tayi zaman ta ni da ke mun wakilce ta. Ke kinji yadda ake yamad’id’i da yarinyar Nan a kauye kuwa ? To ni Kam in dai da ita zamu tafi sai dai ku tafi ni Kam ba zan iya jerawa da ita ba.

“Kiyi Hak’uri Goggo Yaya zamuyi da wasila ne? Dolen mu ce ADDU A kadai zamuyi Mata Kuma tafiya tare da ita ne zai rage yamad’id’in da Ake Akasin taje ita kad’ai Kuma gara muje a tare da muje mu Biyu ita taje ita kad’ai sai aji Dadin fadar maganganun a Kuma Gane Muma mun ware ta Bama Saka ta a sabga ta haka kowa zai Gane mun kyamace ta.

“To kina ma da tabbaccin tana Gidan tunda ta na da sana ar ta ai kullum kafar ta a waje take.

“Mu biya ta gidan sai mu Gani na Kira wayar ta ne a kashe.

“Ni kam Allah ya sani ba don Raina yaso ba matsa min kikayi murja . Kuma ni duk Abinda Bai Yi min ba da nayi shi sai na samu matsala da shi bana ko shakka a tafiyar nan sai na samo Abinda zai Bata min Rai tunda banji Ina son na jera tafiya da ita . Gidan makoki zamuje inda Bana bukatar kunji kunji to yanzu Kuma gidan makoki Nan aka Fi yawan yamad’id’in magana da kunji kun ji.

“Babu komai sai Alheri Goggo Babu Abinda zai faru sai Alheri in Sha Allah.

Goggo ta Mike tana shafa kwalli a idon ta ba don ta so ba ta yafa gyalen ta Suka fito suka nufi gidan wasila don tafiya Gago ta azziya.

Suna tafe a kafa da yake ta can zasu bi zuwa Tashar mota don haka suna tafe suna Dan taba fira tsakanin murja da Goggo akan Mai Rasuwa malam Yale.

“Ai ke dai murja Allah ya cika mu da Imani Amma wannan Rayuwar abin tsoron ta yawa ne Dashi. Jiya jiya fa bawan Allah Nan malam Yale lafiya Lau ya kwanta ya Kuma wayi gari Amma wai Yana fitowa sallar Asuba ya gurde ya fadi maganar kenan sai dai wata Maganar shi Kam ya tafi ba Kuma zai tab’a dawowa ba sai dai a taswira ko a MAFARKI. Yaushe Mai Imani yake mike kafafun shi har yace Duniya tayi mishi dadin da ya manta waccan tafiyar? Ai sai dai shagalalle.

Katuwar motar da ta dauko wasila ta Mai gemu ta faka bakin sauki venture don sauke wasila inda Goggo tabi motar da kallo tana fadin

“To dubi dai motar Nan murja kullum Kara sabon samfur Ake yaushe Mai dogon Buri zai tuna LAHIRA idan Yana ganin irin wadan Nan motocin.

Goggo tayi saurin datse sauran maganar ta saboda bilhakki take kallon motar da Wanda yake cikin ta inda numfashin ta yake barazanar daukewa Saboda Abinda take gani Mai KAMAR A MAFARKI a wannan mota da take Magana akan ta.

Goggo taja tayi turus ta kasa motsawa idon ta Kur a kan mutum Biyun da suke Cikin motar suna damke da juna tamkar zasuyi Wani Abu.

Anty murja da ke Fadin, “Ai Goggo kowa ya iya allon sa sai ya wanke Allah ma ya bawa maiyi zabi Kabi shi ko Ka karkace abin Yana Nan Rubuce a kundin sakamakon.

Ta juyo Jin Bata ji Goggon ta tanka ba inda ta hango Goggon a can baya don ta Bata rata Mai yawa Bata San Goggon ta coge ganin Abinda Bata San ko meye shi ba.

Ta yuyo tana kallon Abinda Goggon ke mayatar Gani a motar sai kawai taga Abinda Goggo take kallo wato wasila a motar Wani katon Wanda Suke Rik’e da Hannun Juna suna kyalkyala Dariya.

Goggo ta zama mutum mutumi ta kasa motsawa sai kifta idanu take tamkar Yar tsanar Roba..

Ita kuwa murja sai ta Ji tamkar ana ranwa da ita ta Samu ta dafa iccen fal ta tsaya tana ganin Al Amarin Mai KAMAR A MAFARKI a idon ta.

Kudin Da Mai gemu ya dauko ya dankawa wasila wacce ta karbe tana zuge jakar ta ta danna kayan ta ta kuma balle murfin motar ta fito Mai gemu yaja motar shi yayi GABA a guje ya hau titi.

Kamar wacce aka cewa dago kanki ? Sai kawai ta dago kamar wacce taji a jikin ta ana kallon ta sai kawai taga Goggo ta zuba Mata ido Bata ko kiftawa inda Wani tashin hankali ya Saukar Mata Wanda Bata zaci samu a yanzu ba.

Kadan ya Rage ta Kai k’asa lokacin da ta hango Anty murja can dafe da iccen fal duk ita suke kallo sun zuba Mata na mujiya.

Ta zube a Gaban Goggo ta kasa Cewa komai sai b’ari da jikin ta yake don har ga Allah Bata zaci ganin su a wannan lokacin ba.

Goggo ta wuce ta ta nufi murje tana Fadin, “Kaico na da wannan mugun gani da nayi a yau. Ni Kam Ina na kuskure da aka jarrabe ni da wannan kaddarar? Allah ya sani ko musu Mai tsanani ban tab’a Yi da iyaye na ba Amma yau ni ce da wannan muguwar Sakayyar.

“Ki yi Hak’uri don Allah Goggo.

“To in banyi hak’uri ba murja ai da tuni na hadiye ZUCIYA na mutu . In banyi hak’uri ba hauka Zanyi? Kin dai ga hanyar da Yar Uwar ki take bi ko murja? Kin dai ga Abinda Wani Kato yake Mata akan idon ki . Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un ni asmau Allah na tuba Astagfurullah ALLAH na tuba.

Sai Goggo ta fashe da kuka tana Fadin, “Murja sai da nace Miki idan nayi Abinda ban gamsu dashi ba matsala nake Samu Kinga Abinda ya faru ko? Yau Allah ya tona Asirin yarinyar Nan ni da ke munga Abinda take Yi a Duhu.

Anty murja ma idon ta da Ruwan hawaye take duban wasila Amma ta kasa cewa uffan.

“Ni Kam ban tab’a hasaso wannan Al Amarin ba a gareta ba Goggo. Nayi zaton ko kasuwanci take Wanda kafar ta take waje.

“Kasuwanci ne mana Baki ga ya sallame ta da kudin ta ba? Kwanan gida ma ai kasuwanci ne ni Kam tunda Naga tana Saka wannan suturar Mai tsada wadda na tabbatar Mijin ta ba zai iya Siya Mata ita ba Raina ya bani ta Soma bak’ar kasuwar Nan ta Matan Zamani in ta bayar da gishiri aka Bata Manda me ta manta? Ko a so ko a ki waccan yarinyar karuwa ce tun tuni na shinshino Hakan ga Kuma tabbaccin Allah ya gwada Mana.

Goggo ta fada tana share Hawaye a fuskar ta.

Murja ta Mike da kyar tana Fadin, “Hakika wasila tayi min ba zata Goggo Wallahi ban zace ta a haka ba Amma Allah ya ganar da ita…

Goggo ta wuce tana fadin, “Aka Gaya Miki tana Neman shiriyar ne ? To waccan yarinyar Duniya take so Kuma ita ta Saka gaba Bata Neman Ganewa . Wanda yace zai iya hadiyar gatari to a sakar masa kotar gata ga Duniyar Nan Wanda Bai zo cikin ta ba tana Dakon shi bare ita da ta Gane halal da Haram.

Suka wuce Suka bar wasila a Nan ta kasa tashi Babu Abinda ke amsa kuwwa a kunnen ta sai kalaman Sagir, “Tun tuni na fada Miki mama koma me ye kika fara baki fara shi da nasara ba tunda duk Abinda kike lullube sai Allah ya tona Asirin ki da sannu duk Wanda kike Rufewa Allah zai tona Asirin ki suga Abunda kike rufewa.

Kalaman yaron ne kawai suke zagaye kwanyar ta yau dai ga shi Dukkan Wanda take jiwa kunya sun ganta da Abunda take boyewa.

Goggo? Anty Murja? Sagir? Ba ta da sauran kima a idon su ALLAH daya kawai zata ce su yarda da ita.

Taji wata irin muzanta don Kuma a yanzu Bata da sauran kima a idon Goggon bare Kuma Anty Murja.

Ta Mike da kyar tana Jin Jiri na Shirin Maka ta da k’asa Amma Abun haushi da mamaki maimakon taji tana son Daina abubuwan da suke jefa ta a damuwa sai taji Bata kamar tana bari don haka a yau din ma kwana daya ne Biyu ta girgije daga wannan alhinin ta koma harkar ta.

Kwana UKU ISHAQ Yana Samun dunkunan Wanda a kalla zaiyi na Dubu biyar zuwa wucewa . A yau Kam Wani costumers din sa ne ya kawo mishi Wani babban mutum zaiyi mishi dinki cikin sauri Wanda yake son Zuwa Gobe saboda Yana Hidima.

ISHAQ ya karbi mutumin da alkawarin cikawa gobe in Sha Allah inda mutumin ya bashi advance na Dubu Ashirin ya ce idan ya gama sai ya cika mishi kud’in shi .

ISHAQ ya Dubi kudin Wanda ko su kadai sun Isa su biya shi kudin duka dunkunan kala biyar Kuma wasu ma haka Nan yayi su Babu Aiki sai wasu da ya gwada mishi irin Aikin da zaiyi mishi na computer.

ISHAQ ya kama Dunkin cike da karsashi da son yau in Sha Allah ba zai kwanta ba sai ya gama su Duka biyar din.

Yana cikin Aikin Wani makocin shi ya zo da kajin agric Wanda aka yanka har Gida takwas Yana fadawa ISHAQ sun kasa ne yasa ya yanka Mai siye yake so ya samu yayi mishi Sauki ko Hudu ne ye Siya shi Kuma ya Kai Rabin gida.

ISHAQ yace nawa ne kudin su Hudun? Ya Rage mishi Sosai ishaq ya bashi kudin shi Kuma ya ka aka gyaro mishi.

Wani takaici ya kama ishaq don sanin bashi da Mai gyara Mishi kajin Nan yusra dai ba iya dafa su tayi ba bare ta gyara musu Dole ya yanke kaiwa Goggo da Inna suwaiba in yaso ya bawa yusra daya ta dafa musu ita da Zainab.

Haka ya dauki kajin ya aikawa Goggo daya ya aikawa Inna suwaiba Biyu wacce take itace Uwar Rukon shi kasancewar ta kanwar mahaifiyar sa don shi Kam Bai san Uwa da Uban sa ba sai Inna suwaiba da mijin ta.

Don haka ya Bata kaji biyu Goggo daya dayar Kuma ya kawowa yusra ta hada kurfotin gawayi ta Dora Nama.

Ya sha mamaki da yaga yadda ta dafe kazar Tasha yaji da albasa har Yana tambayar da me da me ta zuba a girkin? Ta Soma fada mishi tafarnuwa da citta ta Kuma Saka albasa.

“Wa ya fada Miki Hakan ne Yusra? Ta ce, “Ai Abba yanzu na Fara iya girki Nan gidan su hamida nake shiga idan tana yin girkin Ina kallon ta Kuma in mama tana gida Ina tambayar ta yadda ake yi.

“To Amma kiyi a Hankali kar ki kone.

“Ai Ranar ma siraci ya bugar min Hannu sai da nayi kuka kaga wurin har yanzu bai bace ba
Ta fada tana nuna Mishi inda siracin ya tab’a ta.

Washe gari ya kammala Aikin Mutumin Nan duka ya Kira wayar shi ya fada mishi ya gama yace ya kawo mishi su a wata hotel Dake kan titin IBB Way kan hanyar zuwa kofar kaura.

“In kazo sai ka kira ni.

Ya amsa Yana hada Kayan ya gage su da dutsin guga ya Saka leda yayi silin su ya Karbi mashin din makocin sa ya nufi Albustan.

Yana zuwa Albustan aka daga mishi kofar get ya wuce ciki daidai da Mai Naira na Saukowa daga Saman benen shi da wasila wacce take biye a bayan shi tana Kara gyara fuskar ta da hodar da take hannun ta.

Wani irin matsiyacin Duka na zuciya da kwanyar kayi suka Rufarwa ISHAQ har ya kasa dauke idon shi daga wasila wacce ga Alama Bata San Allah yayi Ruwan Halittar sa a wurin ba.

Sai da suka fito farfajiyar hotel din inda katuwar motar Mai Naira take shi Kuma ISHAQ Yana tsaye dab da mashin din da yazo dashi.

Idon shi Kur akan wasila gaban shi na tsananta Sarawa Yana kallon wasila dake biye bayan mutumin tana gyara fuska.

Bata kula da Wanda yake tsaye ba mota kawai ta Bude ta shiga tana Kara gyara fuskar ta inda ISHAQ ya dauko ledar Kayan jikin shi a sanyaye Yana Jin wani Abu Yana yawo da shi a sama.

“Barka da yamma Alhaji,

Muryar ishaq ta daki dodon kunnen wasila wacce kokon hodar da yake Hannun ta ya subuce ya Fadi Saboda firgitar da muryar da taji ta haddasa mata.

Mai Naira da ya bude motar ya shiga Yana Fadin, “Masha Allah malam ISHAQ haka nake son mutum Mai alkawari a fada a cika in Sha Allah kuwa tunda kana da alkawari zaka ga mutanen da zan hada ka dasu Wanda zaka Samu Alheri in dai ka Rik’e alkawari.

Wasila ta zuro kanta inda taga ishaq wanda Shima ya kalle ta tayi k’asa da kanta tana Jin wace irin Rashin nasara ce da ita wacce sagir ya Soma Nuna Mata Amma Bata iya Ganin ta a lokacin ba sai yanzu?

Mai Naira ya Soma Duba dunkunan ya Kuma Yaba don sunyi matuka ya kuma Yaba Sosai inda ya jawo dash bon din gaban motar ya fito da rafar Dubu Hamsin ya mikawa ISHAQ Yana fad’in.

“Rike wannan malam ISHAQ sai na kawo maka Wani Aikin.

“A a Ranka ya Dade ai ka Bada Dubu Ashirin a farko to ba sai ka cika ba ma Na gode.

“A a malam ISHAQ ka Rik’e ni bana Jin tsada irin tela ya Bata min lokaci akan Rashin alkawari don haka Rik’e Babu komai Nagode.

Jiki a Sanyaye ishaq ya karbi kudin Yana Godiya yayin da wasila ke Jin tamkar ta fasa k’asa ta nutse.

“Nagode Sosai Ranka ya Dade Allah ya Kara sutura

Wasila da ta dago kanta tana kallon shi da son taga irin karbar da yake Mata sai Tasha Mamaki don sai yace Mata Ina wuni?

Ta kasa Amsawa Mai naira na fadin, “Kyale madam yau kamshi take Sha min ko kuwa Wani ne ya Bata Mata Rai?

ISHAQ yayi mishi sallama ya tayar da mashin din sa ya fice a guje inda wasila tabi bayan shi da kallo har ya bacewa ganin ta tana Jin hakikatan akwai ta inda ta kuskure Wanda Al Amarin ta ya zama Babu Sirri Kuma matukar tace Bata gyara ba to hatta Zainab k’aramar yarta sai an bankada mata laluben Sirrin ta. Yanzu idan ISHAQ ya je ya fadawa Goggo inda ya Ganta meye ba zai faru ba? Wane irin bacin suna ne ba zai same ta ba? Ya zama Dole ta dauki mataki akan ishaq tun Bai Kuma fallasawa Duniya Halin da take ba.

Ta Yaya zata iya daukar matakin? Zuciyar ta ta tambaye ta sai kawai taga mafita ta kashe Bakin tsanyar ta hanyar kawar da ISHAQ daga Duniya kafin ya furta Abinda ya Gani.

Gawa Dubu ! Taji zuciyar ta na anbata Mata.

Ta yi murmushi tana hango yadda zata Yi da gawa dubun wacce zata yi mata maganin ishaq din in ya mace weye zai fadawa Abinda ya Gani? Ai sai dai ya fadawa Yan can barzahun ba dai na DUNIYA ba.

Don haka Mai Naira Yana ajiye ta ta siyo maganin bera dan china wanda ake cewa gawa dubu ta nufi gida.

<< Tana Kasa Tana Dabo 21Tana Kasa Tana Dabo 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.