Skip to content
Part 26 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Kwanan Saddam Ashirin cif a garin partacout Wanda yayi daidai da kammala iddar Farida har da kwana Biyar. Don haka a wannan satin Sameer ya Shirya tahowa katsina ya tunkari Farida da Maganar Auren KISAN WUTAR da ya Shirya Mata ita da Nazir.

Saddam Kam ya samu abubuwa masu yawa daga sojojin da suke cikin barracks din su Sameer Saboda shakuwar da yayi da mutane a barracks din kowa ya kawo kyauta ya bawa Saddam . Kai hatta da Ogan su Sameer kanal iziddin yayiwa Saddam kyauta ta ban mamaki . Domin kuwa ya bashi kayan sojoji na Yara kala biyar masu dauke da star da jar igiya . Haka Kuma ya bashi gun bindiga ta wasan Yara itama irin ta sojojin ya Kuma bashi mashin na Yara na Roba Mai kakin SOJA sai kuma mota ta Yara itama wadda zai iya shiga ya zagaya itama dai duk Mai dauke da kalar kakin SOJA. Sai tanka ta yaki itama irin ta sojojin duka na Roba wanda Yaro Zaiyi wasa.

Ba Saddam ba hatta Sameer sai da kyautar kanal iziddin ta burge matuka Gaya ya Kuma zube Yana Godiya kamar Babu Gobe inda Kuma kanal din ya dankawa Saddam Wani ambulan Yana bashi hannu sukayi musabaha ya Sumbace shi sukayi sallama

Sameer yayi Mamakin irin son da Yan barracks suka nunawa Saddam. Sai kuma ya ga Rabo ne ya kawo Saddam din shiyasa ya tadawa Uwar sa Bula akan shi Daddy zashi.

Suka taho a mota shi da Saddam Wanda yake ta kallon hanya Kuma duk Abinda ya Gani sai ya tambaya Sameer Kuma ya bashi Amsa har suka iso garin katsina

Farida tana yiwa Hanan wanka Saddam ya shigo Gidan Haj a guje Yana kwala Kiran Mami taho kiga mota ta da jirgi na da aka bani a partacout…

Yana shigowa yayi karo da Uwar sa ya kuma dafe ta Yana kyalkyala Dariya…

Ta Rungume shi tana ganin shi cikin kakin SOJA irin na Uban sa har da jar igiya ga Kuma hular shi an kafa mishi.

Ta Zubawa yaron ido taga yadda ya Kara girma a cikin kwanakin k’asa da wata Daya. Sai Kuma ta tabbatar in dai kulawa ce wurin Uban shi zai zama fiye da haka don ya ganshi ne Ba tare da yayi zaton ganin shi ba.

Haj ta fito tana fadin, “Wai Mai Gidan Kaine ka dawo ?

Saddam ya falle a guje ya Rungume Haj Yana Fadin, “Nine Mana Haj Baki ga motar da aka bani ba har da mashin da jirgi.

“Kai madalla Allah gashi Kuma na ganka har da kakin SOJA ko Ka samu Aikin ne a can?

Ya yi Maza ya ce, “Ban samu ba Amma dai an bani Kaya ga Daddy na Nan waje Yana waya zai shigo mini da su.

Sameer ya shigo idon su ya Hadu da farida wacce taji wata faduwar gaba Mai tsanani ta saukar mata.

Suka Zubawa juna ido inda take Ganin Sameer yayi Mata Wani irin kyau Mai daukar hankali koman shi ya zarce Sanin da tayi mishi.

A Nashi bangaren ma kallon ta yake wata Duniya da Bai sani ba. Ji yake tamkar ya dauke ta su gudu don bai taba Jin Yana son ta ba irin yanzu da tsananin kewa da bege suka lullube shi.

Ta yi karfin halin janye idon ta Daga gareshi yayin da Hanan ta kwace Daga gareta ta nufi Uban ta ya cabe ta Yana dagawa sama Yana sumbatar ta tana Dariya kafin ya Rungume ta Yana Jin Kaunar yarinyar a Ranshi.

Ya Isa kofar D’akin Haj ya zube Yana gaishe ta ta Amsa tana tambayar shi Aiki kafin tace

“Sai kaga Saddam kamar daga Sama? “Wallahi kuwa Haj nayi Mamaki matuka Gaya.

“Ai kuka ya Saka ya ki Jin Rarrashi shi a Dole wurin Daddyn Sa zashi Allah ya taimake mu dauda yazo shi ya wuce da shi can Kaduna yace Akwai Wanda zai bawa shi har wurin ka.

“Wallahi Nayi mamaki Haj Amma da na tambaye shi sai yace wai kuka yayiwa Mami sai uncle ya taho Dashi.

“Ai Saddam sarka ne in ya Rikice baya waruwa.

Ya Mike Yana ajiyewa Haj Abinda ya Ruko Mata Yana Rungume da Hanan inda Farida ta wuce D’akin ta tana mishi shimfida ya shiga ya zauna Yana kallon ta tamkar Bai taba Ganin ta ba.

Ta dauko mishi lemu a fridge ta kawo mishi Naman kafar saniya da masa wadda tayi da safe

Ya Soma cin masar Yana kallon ta ita Kuma tana Shirya Hanan Saddam Kam ya cika su da surutu.

Sai da ya gama cin Abincin ya matsa inda take Zaune kan gadon ta Yana kallon ta kallon da yake kashe Mata jiki

“Kinga yadda na koma Farida? Ke Kam naga Baki da damuwa don Naga kin min kyau Sosai Kyan da ban taba Ganin kinyi min shi ba.

“Sameer Allah ne kadai yasan irin damuwar da nake cike da ita . Kaine nake Gani ma kamar baka da damuwa Amma Kuma na San shaidan ne yake kawata mana juna a idanu in Kuma muka biye mishi zamuyi nadama Mai yawa a Rayuwar mu.

“Haka ne Farida Amma yanzu me kike tsara Mana daga gareki?

“Me zan tsara kuwa Sameer Banda nayi ADDU AR zabin Ubangiji? Duk Wani tsari da zamuyi Aikin Banza ne tunda komai ya gama lalacewa.

“Ni nayi Wani tunani Wanda zai kawo Mana karshen komai Ina fatan ki fahimce ni don in aka wuce Haka Farida mutuwa zanyi don na Gane Allah ya hada Rayuwar mu ne ya dunkule ta wuri Daya ni da ke.

“Na Sani Allah yasa kuma mafitar da zata fitar damu ce Amma dai muyi Imani da Allah muyi da kaddarar mu Sameer.

“Ai nayi tunda na yarda aka haramta mini zama Dake Farida aka kasa fahimtar cewa Abinda nayi Nayi shi ne cikin fushi . Yanzu Abinda Kawai na yanke shine na samo Wani na hada ki da shi Auren KISAN WUTA ta yadda zai Sako min ke ba tare da kowa ya Gane Abinda muka shirya ba.

Ta Dube shi da sauri suka Zubawa juna ido kafin ta janye nata idon kwalla na Shirin fita.

“Sameer ba zan iya yarda da wani Namiji ya Kai Hannu a jiki na da sunan shi din mijina ne ba . Babu Namijin da zanyi Hakan da shi bayan Kai kad’ai. Ni Kam na zabi nayi ta zama a gida Amma Maganar nayi wani Aure ba zanyi shi ba Amma na tabbatar da Ranar da ka gaji da Jira na ka Nemi wata matar aka Daura muku Aure to a Ranar ne ni Kuma za a sallaci GAWA ta Saboda kishin matar ka ne zai kashe ni Sameer. Don haka ba zan iya Auren Wani Namiji da sunan na Aure shi ba har ace zan Sauke hakkin Auren da igiya UKU ta daura min ba.

“Na sani Nima Kuma Kin San ba zan yarda da kowaye mijin ya taba ki ba . Don haka a can pertercout na samu Wani yaro na da ya yarda da Dukkan sharudana Kuma na Sanar dashi bana son kowace irin alaka ta shiga tsakanin ku Asali ma Auren kawai nake so Al Ummar su shaida ana yin kwanaki kadan ya Sako min ke ya Kuma yarda don yace min shi ana dab da bikin shi ma Amma dai har za ayi komai a gama bamu samu matsala ba . Zan Kuma biya shi kudin Aikin sa don haka Goyon bayan ki kawai nake so In yaso zan kawo shi ku ga juna Amma ki Saka a Ranki Babu wani Abu da zai shiga tsakanin ku wata Kil ma ganin da Zakiyi mishi a Nan shine na farko Kuma na karshe don Yana girmama ni Kuma na tabbatar da ba Zaiyi Daya Daga cikin Abinda na gindaya mishi ba don Haka kiyi Hak’uri na sani ni kadai kika yarda da wannan Rayuwar Nima ba zan iya yin ta da wata da ba ke ba.

Ta sharce hawaye tana Fadin

Zan iya yarda da Hakan Amma ko da Auren na jeka anyi ne ba kowane zan iya yarda da Hakan ba don zan Bata Maka record ne akan ko da tuna na Auri Wani ba Kai ba ne. Kai kadai nake iya Amsa sunan matar ka ba Wani da in na tuna Hakan ba ma Raina ya Baci.

“Babu matsala idan na kawo shi kika ga Baiyi Miki ba kiyi min Magana zan sauya shi da wani tunda Aikin kudi ne Kuma Biyan su za ayi ai sai yadda kike so madam. Ya fada Yana daga mata gira

Suka Zubawa juna ido kafin ya Ruko fuska ta Yana hadawa da tashi fuskar ya shiga sumbatar Bakin ta Suna mayar da numfashi tayi k’arfin Halin janye fuskar ta don ta tabbatar da in aka wuce Hakan Dole a samu matsala.

Ya tashi da nufin tafiya Gida don baije ko gidan Haj ba Nan kawai yayiwa tsinke

Ya fito Yana yiwa Haj sallama ya fice bayan ya direwwa Saddam tarin kayan Arzikin Da ya Samo

Haj ta ganshi ya zo a wannan lokacin kusan wata Biyu da doriya Bai Kuma waiwayar gida ba.

“Kai wata Sabon Gani Mai gida Ashe talaka Yana ganin ka? Haj ta fada cike da zolaya.

Ya zauna a gaban ta Yana Gaishe ta tana Amsawa da tambayar shi Aiki duk ya amsa duka lafiya Lau.

“To Alhamdulillah ai da Naga kwanaki da yawa baka zo ba sai na Kira wayar ka don naji ko lafiya sai na Samu wayar a kashe sai na tuna fa haushin mu kake ji.

“A a Wallahi Haj ko Ina Jin haushin kowa ai Banda ke wallahi Aiki ne kawai ya Rik’e ni.

“Ai da kazo ma kaji Alherin da Muke nufin Yi maka na tabbata ko Ina cikin Wanda kake jiwa haushi zaka wanke ni kayi min Godiya don nasan zaka so wannan Alherin da nake Shirin karba Maka.

“Haj wane irin Alheri ne wannan ? Na tabbatar da ba Zaki taba so min Abinda ba Alheri bane.

“Kwarai kuwa duk Wani Wanda zai so ka da Alheri Sameer ya biyo baya na don haka Naga Da ka zauna cikin wannan kuncin na Rashin Farida muka yi magana da Asiya akan kawai a baka Aisha ta maye Maka gurbin Farida.

“A a Haj kar ayi haka Wallahi bana so.

“Amma kuwa in kace baka son Aisha ka zama butulu Kuma har asiya ta karbi maganar da muhimanci Kai Kuma yanzu kace ba haka ba? Me kake nufi to ? Zakayi ta zama haka Babu Aure ko kuwa zakayi ta jiran Wanda zai Auri Farida ya mutu ko ya Sako Maka ita Duk kana gefe? To karya kake Wallahi Sameer mun gama magana da Asiya baka isa kuma kace ba haka ba hakkkin ka ne a Sanar Maka na Kuma fada Maka Amma Hidima ka bar Mana tunda Aisha jawara ce ni da Asiya ma mun Isa mu kama mu kawo maka ita gidan ka.

“Haj ki fahimce ni don Allah Kar kiyi min haka ba Wai bana son Aisha bane Amma gaskiya ba zan iya zaman Aure da ita ba Kuma ni a yanzu bana bukatar na sake shiga Rudani don Allah Haj a bar maganar Nan Wallahi bana son ta.

“Kaga tashi ka tafi na sallame ka ba HAUSHIn mu dama kake ji ba? To ka Kara Jin Wani haushin namu a yanzu in an kawo maka Aisha ka Rubuta Mata takardar saki a Ranar da aka kawo maka ita k’arewar Rashin so kenan.

Duk yadda yaso Haj ta fahimce shi ta kasa fahimtar shi a lurar da yayi ma sun gama shirin su ko da Bai zo ba za a iya aike mishi da Amarya can Inda ya ke don haka yaga lallai ana Shirin dama mishi lissafi ta Ina Ake son ya Kai wata aisha wacce Babu inda Bai sani a jikin ta ba? Bayan tayi Aure taje Gidan mijin ta har da Ya’yan ta uku mijin ya Rasu shine yanzu suke Neman k’ak’aba mishi ita da k’arfin tsiya don haka kwanan shi Biyu a katsina ya juya bayan yayiwa Haj sallama wacce take Fadin Saboda maganar auren da tayi mishi ce yasa ya koma to duk zai gama tsallen shi ya dawo.

Cikin satin da yazo katsina ya Kuma shirya musu tafiya shi da Nazir don ya Gane in ba sauri yayi ya mayar da Farida to Haj taxa k’ak’aba mishi Aisha Abinda Kuma ya tabbatar da zai nesan ta shi da Farida matukar Taji ya Auri Aisha zata barshi bari Kuma na har Abada.

Suka iso katsina shi da Nazir Wanda ya Sha Wanka irin na sukari ya Kuma kira Farida ya fada Mata ga Nazir Nan don in yace Suzo tare Asiri zai Tonu don haka ya kawo Nazir din har kofar gidan shi Kuma ya juya.

Farida ta fito ta tarbi Nazir Wanda tun a kallon farko taji baiyi Mata ba Kuma Bata Wani Bata lokaci ba ta sallame shi bayan sun Gaisa ya Kara kora Mata Bayanin da ta Sani sai tace yaje zata yiwa Sameer din bayani da haka sukayi sallama bayan ya taba Abinda ta kawo mishi shi Kuma ya Bata kyautar turare Suka yi sallama.

Sai da Nazir ya koma ya fadawa Sameer duk yadda Sukayi kafin ya Kira ta ta Kuma fada mishi ba zata iya Auren wannan yaron Da ya turo ba Hakan Nan Baiyi mata ba sai dai ya samo Wani.

Da haka suka koma pertercout Ran Sameer a bace Amma a haka ya Soma Shirin Neman Wani har yayi nasarar da suka daidaita ya Kuma taho da shi inda yake sanar Mata ya samo wani Amma ta daure tunda abin Nan ba zama za ayi ba kar tace Shima Baiyi Mata ba shi Kam Yana cikin matsala Wallahi jan lokacin ma Yana Kara jefa shi a matsala duk da Bai sanar Mata Al Amarin da yake Gidan su ba na k’ak’aba mishi Aisha da Ake Shirin Yi.

<< Tana Kasa Tana Dabo 26Tana Kasa Tana Dabo 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.