Wata gigitar tsawa da Sameer ya dakawa Farida itace ta kusa kurumta Mata dodon kunnen don duk da a waya ne Amma ya kusa ya lalata Mata ji.
"Farida kina Shirin Kashe ni ne? Ta Yaya Wanda ya furta Yana son ki zai iya kawar da Kai daga muradin ZUCIYAR sa bare har ya ce ba zai taba ki ba? Kin kuwa San waye Abdullahi yakubu? Ko Bai furta Yana son ki ba Farida ba zan yafewa kaina ba idan ya Gane min ke har yaji Yana Sha awar ki Farida zan mutu ne Wallahi don Allah ki fahimce ni. . .