Skip to content
Part 27 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Wata gigitar tsawa da Sameer ya dakawa Farida itace ta kusa kurumta Mata dodon kunnen don duk da a waya ne Amma ya kusa ya lalata Mata ji.

“Farida kina Shirin Kashe ni ne? Ta Yaya Wanda ya furta Yana son ki zai iya kawar da Kai daga muradin ZUCIYAR sa bare har ya ce ba zai taba ki ba? Kin kuwa San waye Abdullahi yakubu? Ko Bai furta Yana son ki ba Farida ba zan yafewa kaina ba idan ya Gane min ke har yaji Yana Sha awar ki Farida zan mutu ne Wallahi don Allah ki fahimce ni wannan mutumin yayi Miki waye da yawa.

“To yanzu ya kake so ayi kenan? Idan ba shi din ba fa Akwai yuwuwar a Gane manufar mu Amma shi In ka bari na jawo shi ya shigo ai zan zurma shi ne ba tare da ya San jeka ka ka dawo zanyi ba.

“Ban gamsu da Hakan ba Farida don na San Halin mutumin Nan Farida duk macen da ya Kalli tsakiyar idon ta da maganar Abinda yake so da ita to Bata Isa ta kubce mishi ba don Allah Kar ki yarda ki Kalli idon shi Wallahi Farida Ina ji a jiki na shigowar mutumin Nan a wannan lokacin matsala kawai zai kawo Mana ki sallame shi don Allah Wallahi banji dadin haduwar ku da bawan Allah Nan na San shi na San ko waye shi hatsabibi ne akan Mata kar dai ya kyallo mace sai gashi Farida ya kyallo min ke har Yana shiga layin masu Neman Auren ki Wallahi Duniya ta ta tashi daga zaune ta koma tsaye bari na Nemo Nazir mu tawo don Kuma kin firgita ni.

“Tunda kace na sallame shi ai Kuma na sallame shi sai ku taho da sauri don na San shi da Na ci

“Ko yazo kar ki fito Don ALLAH bana son Yana kallon ki Farida in aka kuskure kika hada ido da shi zakiji Wani Abu akan shi tunda har alfahari yake da Hakan shi sai dai in mace Bata kalle shi ba Amma matukar ta kalle shi to tazo Hannu.

“Babu matsala sai yaushe zaka zo din?

“Nazir din ne baya nan yaje Gida shiyasa kika ga na jima Amma in Naga zai jima Bai dawo ba zan Nemo Wani kawai ai tunda kika fada min Mai gemun Nan ya shigo naji Kuma hankali na ya tashi matukar ba Gani nayi Wani ne ya Aure ki Wanda ni na Saka ba Amma in dai Mutumin nan Yana tsakanin mu Farida na kusa mutuwa.

“Kar ka Damu fa don Allah nace Maka zan sallame shi kayi sauri dai ko Wani ne ka samu sai a tura shi wurin Yaya dauda ayi komai da wuri kawai.

“Yauwa to Na gode take care your self my dear wife.

Suka ajiye wayar Farida kuma Kara maimaita maganar Sameer akan Mai gemu Wanda ta tabbatar Yana da wani Abu Wanda ita da kanta ta San Me gemun Yana da kalaman da suke tsayawa a Rai ko babu komai jiya Ya fada Mata Kalaman da ta kwana tana tuna Su musamman Yaba mata akan tsarin ta da yake burge shi yake Kuma son wasu abubuwa daga gareta . Ita da kanta Taji ko Babu komai ya samu Wani kaso daga zuciyar ta ko Bata Kira Hakan da so ba to zata jima Bata manta shi ba.

A wannan Dare Mai gemu ya Kwana Yana mafarkin Farida musamman Da ya Rungume ta yaji Abinda yake son ji na Game da mace Mai kirji shikenan ya Kara haukace wa ya Kwana Yana faman Ambaton sunan Farida akan kunnen Basma wacce taji shi a magagin bacci har ta wartsske ba shiri ta zuba mishi ido Yana ta Sharar BACCI Bai San Abinda take ba.

Ta kwana cike da Bak’in cikin wannan Farida da ta kasa Raba mijin nata da son ta duk da tazarar da ta shata Rata a tsakanin su tana can gidan Wani mijin Amma Bai huta da begen ta ba.( A sanin da Basma tayi kenan Bata San Farida tana Nan a kasuwa ba har Mijin nata ya Soma tayawa Abinda bamu sani ba dai shin ko za a sallama mishi?)

Washegari Yana zaune sanye da jallabiya Yana waya akan wasu kudi da zai canja suna cinikin Abinda za a bashi yayin da Basma mace Mai kyau da gayu doguwar mace mai aji Amma Kuma wasu ne suke Ganin ta Kai mace Amma ita da kanta ta san a wurin mijin ta ba kowa bace ita tunda ta jima da sanin farar mace Bata burge Bata burge shi .haka Yana son mace Mai cikar kirji Kuma ba doguwa ba Kuma ba gajera ba don Haka ta shiga fafutukar Shaye Shayen magungunan da suke ciko da kirji . Ta Kuma Yi da na sanin kasancewar ta farar mace wacce mafi yawan Mazan suka Fi so Amma a bangaren mijin ta shi farar mace Bata burge shi yafi son wankan tarwada Amma Kuma Babu Damar ta koma wankan tarwadar Domin kuwa farin ne kawai Ake iya samu Amma waccan kalar Babu dama wai SATA LAHIRA a kawo Duniya a siyar don haka dole Basma ta Hak’ura da canjin launin fata Amma maganin cikar kirji har yau masu magungunan Basu Daina cin kudin ta ba Kuma itama Bata Hak’ura ba duk inda taji Mai maganin cikar kirji zata Siya duk tsadar sa kuwa. Amma fata kam tana Nan a farar ta ba Damar komawa wankan tarwada. Don a Duniya idan Akwai Abinda Basma take so to Abdullahi ne shiyasa duk mace Mai sunan Farida ta tsane ta ko da Kuwa jaririya ce matukar Taji sunan ta Farida to ta kuwa tsane ta Kenan Kuma bil hakki da gaskiya take tsanar ba don komai ba kuwa sai don Mai sunan ta da mijin ta yake mutuwar so har Gobe kuwa Bata huta ba…

Tana ta kokarin hada mishi abin break bayan ya gama wayar ya dube ta tana ta aje mishi kayan break din har ta gama ta Soma hada mishi ya dauka Yana Kai kofin shayin a Baki ya bude flat din dankali da agada Yana ci inda Basma take Zaune da Ya’yan ta Biyu Najwa da Nabeela suna Kari cike da wata irin cima ta Mai akwai Kuma daula wacce Ubangiji kan azurta Wanda ya so ya huta har talaka bawan Allah idan ya ga irin waccan daular yayi ta fatan Allah ka bani na samu.

Ya gama Karin Yana Duban Basma Yana Fadin, “Farida hada min Ruwan wanka da Allah ana Jira na …

“Am sorry Basma Yi Hak’uri da Allah bakin ne ya kubce.

Basma ta zuba mishi ido cike da wani irin Bak’in ciki tana kin tamkar ta tashi ta mangare shi.

“Wulakancin Nan ya Fara Isa ta Abdul . Haka fa jiya ka ishe ni da kiraye kirayen sunan wata banza wai Farida yanzu Kuma ido na ganin ido kana hada ni da ita. Ni ba gara ka Kira ni da sunan cioma ko ingozi ba akan wannan tsinannen sunan?

“Yi Hak’uri Basma zuciya ta na wurin Faridar ne ai kin San ba zanyi Miki Hakan don wulakanci ba haba my sweety derling?

Ya fada Yana Rungume ta Yana Kai fuskar shi a kirjin ta Abinda ya Dan sanyaya Mata Rai kenan Amma bata tanka ba ta wuce zuwa hada mishi Ruwan wankan ta fito tana d’aci.

Yayi murmushi ya wuce toilet din Yana mamakin dabin da zai hada s gidan shi matukar Farida ta shigo Gidan Nan kwanciyar hankalin Basma Kuma ya Kare.

Ya fito cikin shaddar gizna Camel color wacce ta karbe shi matuka Gaya kasancewar sa fari tas Kuma sai ya Dora hula zanna bukar coffee brown ya fito fes Masha Allah.

Yana Rik’e da kum k’arami Yana sharce gashin gemun shi Basma ta karbi Kum din tana gyara Mishi.

“Kinga na manta an bani Sako jiya na manta?

“Wane irin Sako ? Cewar Basma wacce tayi tambayar tana kallon shi.

“Farida ta na hadu da ita jiya tace na gaishe ki da Yara wai Auren ta ya mutu.

“Ai in Sha Allah Abdul sai tayi zawarcin ta a can Amma Kai da ita Kam SAI A LAHIRA in Sha Allah ma mijin ta zai mayar da ita yau ko Gobe kaga kunyi Hannun Riga yadda kake mayatar matar Nan itama haka take mayatar ka Amma in Sha Allah iyakar Abinda zakuyi kenan.

Ta ajiye mishi kum din ta wuce ta barshi Nan yana Binta da kallo kafin ya dage kafadar sa ya dauki kum din sa ya fice Yana Kara tada gemun shi.

Kai tsaye ya ja motar shi zuwa filin jirgin sauka da tashi na Malam Umar Musa Yar Adua tun jiya yayi biking flaying zuwa Kaduna don da gaske yake son Farida don haka ya yanke zuwa Kaduna ya samu dauda suyi magana.

Karfe goma na safe Yana cikin garin kaduna ya dauki drop zuwa jaji har kofar gidan dauda ya Kuma Kira wayar shi ya sanar mishi Yana kofar gidan shi.

Tuni kuwa aka isar da dauda falon Saukar Baki aka Kuma cika shi da kayan tarba hatta Anty lubna sai da ta zo suka gaisa tana fadin.

“Ikon Allah Abdul Kai kuwa sai tenuwa tenuwa Ake ganin ka? Bana ko shakka da Hannun Farida a tafiyar nan.

Ya kyalkyale da Dariya yana fadin

“Ba ki yi murya ba matar SOJA ke kin San in ba Farida ba ai Babu Abinda ya Isa na watsar da Neman kudi na na tafi yawo…

Dauda ya shigo Yana Fadin, “Lubna me na fada Miki ? Wannan Dan iskan sai kin Gan shi a Kaduna Kinga kuwa ga shi ya bayyana.

“Ai kuwa gashi na Gani Amma kuwa wanna karon zan Goya mishi baya gaskiya tunda ya nuna so daya tak yake Yi yaje ya Dawo Nima na shirya.

Suka cafke Hannu juna shi da dauda inda Anty lubna ta fita ta Basu wuri Mai gemu ya Duka Yana Fadin

“Ai ni yanzu kafafu na duka a k’as Yaya dauda Gani gaban ka Allah ya sani ba da wasa Nazo ba a jiya na GANA da Farida ta Kuma tabbatar min da bata da magana sai wacce ka zartas a kanta ni Kuma na San ko ba Kaine Mai bayar da Farida ba dauda zaka iya shiga gaba ka Nemo min don haka Ina Neman amincewar ka Farida ta tabbatar min ta Amince Dani Kuma Kai din komai kayi a gareta daidai ne to a tausaya min ka San dai Halin da na kasance akan ta Lokacin da na Rasa ta a farko yaya dauda.

“Kai kar ka yaudare ni kaji Dan iskan karshen Duniya cire min wannan Yayan ta yaudara ka Kira ni dauda na yafi Maka kaji ko.

“Ai kaima ka San a yanzu ba zan iya Kiran ka dauda gatsau ba sai bayan na amshe Farida ne zan koma Kiran ka daudan ka.

Sukayi Dariya suna cafkewa Dauda ya dube shi Yana Fadin.

“Abdul ko da can ma ka San Ni Nafi kowa son ka da Farida sai dai kawai Wanda ta kawo tace shi take so shine na Bata Wanda take so saboda na san inda mahaifin mu na Raye ba zai tab’a Yi Mata Dole ba sai Abinda take so kasancewar ta ita Daya mace a cikin mu Shiyasa ban matsa da lallai sai ta Aure ka ba Amma yanzu in dai zan Yankee Hukunci kamar yadda tace sai nace Maka na Bata auren Farida duk lokacin da kaji ka shirya za a yi Hidima tunda ta gama iddar ta Kuma Nima zan fi son Hakan ace tana gama idda tayi Aure ko don mijin ta ya Gane sai Wani ya aje Wani yake dauka.

“Ai ni yanzu ma in kace na kawo Goro ka daura Mana Aure Yaya dauda zanyi Hakan Amma Kuma idan kace sai anyi shiri ba zanji Komai ba tunda ka yarda ka bani Auren ai magana ta Kare Kuma.

“Dole na je na Sanar da Haj komai Abdul in yaso Abinda tace sai na Sanar Maka Amma na San daga Haj ma ba zaka samu tazgaro ba tunda itama tana yin ka.

Sun jima suna fira har zuwa lokacin da ya tashi da nufin tafiya ya dauko shi a mota har filin jirgin ya sauke shi sai da jirgin ya tashi kafin ya juya.

Yana Sauka a katsina ya dauki motar shi da ya bari a Nan ya nufi wurin Farida wacce Bata ji tayi nadamar zuwan shi ba kamar yadda Sameer ya gargade ta.

Ta fito mishi da kujera ya Zauna Yana kallon ta ta Dube shi Suka Zubawa juna ido inda ta ga Wani Abu a kwayar idon shi Wanda taji Yana fuzgar ta. Ta kawar da kanta.

“Nifa kallon Nan naka Yana tsorata ni don Allah ka bari.

“Ta Yaya ba zan kalle ki na more ba Farida? Abin da zan kalla fa gare ki Baki San ni ba kowace mace nake kallo ba sai waccce na San tana da abinda zan kalla.

“Ya Gida ya Aiki?

“Duka lafiya Lau alhamdulillah yanzu fa daga wurin dauda nake Farida ya amshi magana ta da Hannu bibiyu Yaya me kike Gani a kan yadda zamu Shirya A’amarin auren mu?”

Wata matsiyaciyar faduwar gaba da ta sauko mata har tana Jin kanta Yana Sarawa me yake Shirin faruwa da ita? Maganar har taje ga Yaya dauda Kuma ya Aminta ya yarda? Lallai akwai tashin hankali a cikin Alamarin Nan.

“Uhum Amarya Sha Guda banji me kika ce ba?

“Yanzu har ka samu Yaya dauda da wannan maganar Abdul?

“To me zan Jira Farida? Na matsu ne ace an shafa fatiha tazo Naga Amarya ta a D’akin da MAFARKI na ya Sha hasko min Farida.

“To ka bani Dan Lokaci kadan muyi magana da Haj itama ka San Dole naji ta Bakin ta kar muyi gaggawa a cikin Al Amarin.

“Me zamu Jira ne Farida ? Ai Ina ganin Babu wani Abu da bamu sani a tsakanin mu ba bare ace fahimtar juna zamuyi na sanki kin san ni . Amma Kuma kina da gaskiya Dole kina bukatar shiri na baki kwanaki UKU yayi Miki ai ko?

“Yayi kad’an gaskiya.

“To na Baki Biyar kinga kafin wata biyar din sai dai maganar daurin Auren mu.

Suna Zaune Yana Mata fira cikin kalaman shi na Nuna kauna da bege tare da Yaba mata akan son ya kasance tare da ita tuni Kuma ya samu Dora zuciyar ta akan Abinda yake son dorawa har taji Wani Abu akan shi da son ta burge shi ko don wadan CAn kalaman masu toho da zuciya suji lallai inda Ake yin su din ma mai matsayi ne kawai ke iya samun Hakan.

Suna Rabuwa da Abdul ta Kira wayar Sameer a Rikice tana fadin

“Wai har yanzu fa shuru Sameer Babu Kai Babu nazir din? Wallahi an kusa yin tuntube don Allah kayi sauri ana dab da samun matsala fa Wallahi.

“Ba za a Samu matsala ba Farida wallahi nazir har yanzu Bai dawo ba Amma na samu Wani Gobe goben Nan zamu shigo KT ke dai ki sallami Mai gemun Nan.

“To sai kunzo din Amma Wallahi sai munyi da gaske don ana dab da samun matsala fa.

<< Tana Kasa Tana Dabo 25Tana Ƙasa Tana Dabo 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.