Skip to content
Part 29 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

 Baba Yusha U Zaune akan kujerar sa ta rai da rai irin ta mutan da wacce ake linkewa.

Yana Rik’e da Radio Yana kama gidan Radion Nigeria Kaduna don bashi da abin saurare sai Radion Nigeria Kaduna Saboda shirye shiryen su Wanda yake so don a Cewar sa duk Wani Gidan Radio in dai ba Nigeria Kaduna ba shirme suke don Haka a ko yaushe bashi da abin saurare sai Nan.

Baba Yusha U kanin mahaifin su su Farida ne Wanda shine a madadin Uban su a yanzu . Mutum ne Mai zafin gaske sai dai akwai tsage gaskiya Komai d’aci Kuma yana da kirki da zumunci matuka Gaya Amma fa baya daukar wargi akwai zagi da son ya kawo duka Kuma in ya dafi mutum zaiji a jikin shi don haka ake shakkar shi matuka Gaya Amma Kuma Yana fahimta Sosai kawai dai baya son iya Shege da lalata Amma Yana fahimta duk Kuma Abinda kazo da shi zai saurare ka har ya yi maka kokari akan Abinda kake so.

Farida ta iso gidan tana sallama inda matar Baba Yusha U Mai suna Baba Gaji ta Amsawa Farida tana Fadin.

“Kai maraba da Amarya Mai man shanu.

Farida ta Sha mur don ma kar a ga fuskar ta ta zauna tana Gaishe da baba Gaji suka gaisa ta leka d’akin inno dayar matar baba Yusha U suka gaisa itama tana zolayar ta da Amarya Amarya.

Ta dawo Zuwa gindin iccen dirimin da baba Yusha U yake kafa kujera cikin inuwar Yana sauraren Radio ta zube a Gaban shi tana Gaishe shi ya Amsa Yana tambayar mutane gida ta amsa da Duka lafiya Suke. Tayi shiru ta Rasa ta inda zata fara don kwarjinin baba Yusha U ya cika Mata fuska.

Baba Yusha U ya Rage k’arar Radio Yana Kiran inno ta fito Yana Fadin.

“Daukowa Farida Naman Nan ta ci ki Hado Mata da alkubus din ma ni sai na Sha fura.

“A a Baba Nagode Wallahi naci abinci. Ya auno Mata harara Yana Fadin

“Ke tafi can in kinci Abinci ai ba Naman kaza kika ci ba In ma kinci Bai Kai wannan Dadi ba don dahuwar daddawa ne da albasa.

Tuni inno ta dauko Abincin daga D’akin Baba Yusha U ta direwa Farida wacce ta Bude taci kadan ta Rufe tana Fadin,

“Na ci Baba Na gode Allah ya biya.

“To Ameen Amma Baki ci komai ba Farida Yaya Hajiyar ku da sauran Yan Uwan ki?

“Duka lafiya Lau alhamdulillah Baba.

“To madalla Yaya Hidima Kuma abubuwa suna ta tahowa? To Allah ya Saka Albarka Farida ayi ta hak’uri in an sabunta don wannan mijin Naki na yanzu Abdullahi Allah NE yayi Miki sakamakon Alheri da shi don kuwa ya samu yabo da shaida bashi da matsala kuma Nima na yarda tunda Abokin dauda ne ya Kuma bayar da shaida akan shi kuma tunda ya so ki da kuruciya yanzu ma da kika dawo ya Kuma Dawo ya cika masoyi.

“Baba ni fa dama Abinda ya kawo ni kenan bana son mutumin Nan tunda Yana da matar shi ni Kuma bana son Mai Mata Wallahi.

Baba Yusha U ya Dube ta Yana Fadin

“Waye ne ba Kya son ne? Ta yi Maza ta ce, “Shi wannan Abdullahi din don bance Ina son shi ba sai kawai Ji Nayi wai har magana ta kankama to ni bana son shi baba a mayar mishi da kayan shi ni Ina da Wanda nake so zan Kuma turo shi.

“To ya aka yi haka kuma Farida? Ni kuwa ai na San ba za ayi Miki haka ba sai kin yarda Amma dai nafi yarda kice min fasawa kikayi Amma ba kice Baki San da maganar ba.

“To gaskiya Baba na fasa gara kawai na turo Wanda nake so Amma ni baba ai ba zan fito daga wani gidan ba kuma naje wani gidan in da na tabbatar da ni ko wacce zan iske sai daya ta barwa daya gidan.

“Ke Farida kalle ni Nan zanci mutuncin ki Wallahi yanzu Lada waje. Yau saura kwana UKU daurin Auren sai kawai aji wata magana daga gareni ace am fasa ? Don gidan ku har kin Isa kice Baki son Mai Mata ? Duba gidan Nan nawa Mata Biyu ne a cikin sa su me ya Hana wata ta fidda wata? Duka hujjar da kika bani Babu wacce ta Isa Abin a duba Kuma sai da magana ta Kare kike son mayar Dani mutumin wofi Wanda Ahalin sa suka Fi karfin sa ? To ko Abdullahi Yana da aibi Farida shi zan Baki tunda har yanzu da sauran kuruciya akan ki.

“Kayi Hak’uri Baba ka fahimce ni . Su inno ba irin mu bane bana son matar shi taga kamar mijin ta wata tsiya yake a wuri ne ta nemi daga min hanci don ni gaskiya na fada ba son shi nake ba Akwai Wanda nake so shi da Yaya dauda ne Suka kullo wannan munafuncin.

“Daudan ne munafuki Farida? Tayi Maza ta kame Bakin ta don ta San ta zunguro sama da Kara.

“To madalla tashi ki tafi Kuma Aure sai kin Auri Abdullahi mutuniyar banza da take son mayar damu mutanen banza In yaso matar tashi tayi Miki Abinda Zatayi Miki . In don kinga Uwar ki ita kadai a gidan ku ki koma ki tambaye ta ta iske wata kafin ita haka Kuma anyi wata bayan ta don Al Amarin Bai da tsayi ne shiyasa Baki risko Hakan ba Yar nema har kike cika bakin Baki son Mai Mata to ni da ke zanga Mai kahuwa Amma wannan maganar Babu Mai tayar da ita Wallahi.

Sai Farida ta Soma kuka tana Fadin, “don Allah ka fahimce ni mana Baba Yusha U? Kaine fa Uba na da zan nufo kayi min Maganin matsala ta baba Kuma don anga Uba na baya Duniya za ayi ta mini zalunci? Sai ta Soma harba kafafu tana birgima da son tayar da Aljanun karyar ta inda ta Soma kakari da birgima a k’asa tana Neman finciko Baba Yusha U Dake kan kujerar sa.

Inno ce ta taho da sauri tana fadin “Assha kuwa Farida kema kina da wadan Nan mutanen Dama? Kayi hakuri malam a Bata Wanda take so tunda har Ranta Yana Baci haka kar Azo ayi Abinda ba zai kallu ba.

Baba Gaji ma ta fito suka Rufu akan Farida wacce take ta furje furjen yawu su inno da baba Gaji suna Rike ta tana kubuce wa da son nuna musu dai aljanun ne a kanta.

“Malam a Yi Mata tofi a Samu kanta.

“Kai a KUL aka yi mana tofi ba mun ce ba ma so ba? To za a ga abinda zai faru wallahi ba ma son Abdullahi din ba ma kamar muna son shi kuma za ayi Danyen Aiki Wallahi in aka tursasawa God’iyar mu zama da wannan mutumin kowa zai mutu ne.

Baba Yusha U ya Zubawa Farida ido Yana karanto Wani Abu a tare da ita Abinda ya fusata shi matuka Gaya da yaji Abinda take fad’a.

Inno ce tayi kokarin tofawa Farida ADDU AR da tazo Bakin ta da son a Samu ta sauka don taga baba Yusha U Bai ko motsa ba.

Suna ta kici kicin da Farida baba Gaji da inno Wanda Suke ta kokarin danne ta Amma tana Shirin watsar da su.

Basu San ta Ina baba Yusha U ya biyo ba don su dai sun dan Yana zaune dafa an bai motsa ba Amma sai saukar Duka Sukaji Yana Sauka a jikin Farida da shareriyar bulala dorina bari na bari.

Inno da baba Gaji suka ja Baya da sauri baba Yusha U Yana fadin

“Kauce ku bani wuri na Nadi Yan iskan Aljanun karyar yarinyar Nan tunda har ta iya wannan munafuncin to bari naci haka Kazan su don kaniyar su . Ai karyar aljani Dan tsatsunbo don Uban shi da shi da Mai su duk zanci Uwar su ne Kuma Muna jiran mutuwar duk mutanen garin katsina Amma Babu Uban da ya Isa ya Hana yuwuwar Auren Nan haka Dake Farida kin iya wannan makircin na tayar min da aljanun karya ? To Zaki Gane karya Bata da Riba a wuri na Kuma Zaki ji jiki idan kina bawa Yan iskan Aljanun ki Damat tashi a Gaba na ke da su duk zanci haka kazan ku ne.

Ya yi ta nadar Farida da bulala duk yadda Baba Gaji ds inno suka so karbar ta baba Yusha U Bai yarda ba sai da ya tabbatar da ta Daku don tuni ya Rik’e ta Yana nada Yana maganganu akan ta ita da Aljanun ta.

A guje Farida ta arce daga gidan inno tana Dariya tana Fadin

“Kai lallai sai a jinjinawa dan yau da iya Shege wai Mai aljannu ce take neman matsera Kuma kinji ta shiru taji bulaliya wai Uwar gulma tayi cikin Shege tace sai kuka ji mu shiru.

Baba Gaji ta Rik’e Baki tana Fadin,

“Wannan yarinya da kwazo take don Allah waye zaice ba aljanun gaske bane ? Kiji yadda take niyar watsar damu ni kuwa na daddage sai tofe ta nake da ayatul kursiyyu Ashe Ashe ja ira ta San tsiyar da ta Shirya ni ko ta Yaya ma malam din ya Gano makircin ta ?

“Haba inno wannan yarinyar duka duka a nawa take da har zan kasa Gane Abinda take nufi? Ai ko ban Shekara d’ari ba na kwana Dubu tunda naga take taken ta na Gane iya Shege ne abin Nata ai ba gashi an Sauke Mata aljanun da suke kanta ba? Kinga Bata ko Ko iya tsayawa daukar takalmin ta ba.

Inno tayi Dariya tana Fadin, “Zan bita da shi har Gida ai tunda dai ta sauka ai shikenan.

Farida tana fita daga Gidan baba Yusha U hijabin ta a Hannu kafa Babu ko takalmi ta tare Napep Allah ya taimake ta Bata manto Yar POS din tata ba ta taho tana shafa jikin ta Wanda yayi burdin duka duk ya fito mata a jiki.

Haj taga shigowar Farida Babu ko takalmi ta bita da kallo ganin sangalalin hannun ta da shacin kwanciyar bulala yasa Haj ta Yi murmushi tana Fadin, “Yaya an dace?

Farida ta fasa kuka tana Fadin, “Wallahi ba a dace ba dubi dukan da yayi min Haj daga kawai nace bana son Mai Mata har yake buga mini misali da shi wai Mata Biyu ne dashi kema da na Gani ke Daya kin Tara’s da wata Kuma wata ta Tara’s da ke ni Ina Ruwa na da wannan lissafin ba ku kukaji kuka Gani ba?

Haj ta kyalkyale da Dariya tana Fadin, “Wannan misalin da ya Baki kuwa Darasi ne mai yawa a ciki in kika baje shi a faifai zaki samu na dauka kuka haka zancen yake babu wai Babu in ke…

“Nifa Haj Wallahi da gaske nake bana son Auren mutumin Nan ko an daura shi Kuma za a warware shi.

“Ai yanzu kuma sai ki nufi dauda ku kare ta kalau da shi nifa ai sai yadda kike do iyaka ta Dake wadan Nan. Ta nuna idanun ta.

Da dare ta Kira Sameer tace ya Kai Wanda Suka zo tare wurin baba Yusha U yace ita ta turo shi.

Ai kuwa suka nufi gidan baba Yusha U Mustafa ya Karanta mishi Abinda ya kawo shi wai Farida ce ta turo shi Neman Auren ta.

Baba Yusha U Kam ya fusata ya fatattaki Mustafa Wanda ya fice a guje daga gidan baba Yusha U ya biyo shi Yana masifa Yana JANHURU haka Mustafa ya koma Yana fadawa Sameer yadda baba Yusha U ya fatattake shi.

Baba Yusha U ya shiga gida ya dauki wayar shi ya Kira dauda ya fada mishi Abinda ya faru tsakanin shi da Farida don haka ya shirya daura Auren ta a Gobe da Asubar fari don haka yace ya turo mishi Ango Abdullahi Wanda ya sauka a garin katsina dauda ya Kira shi yace yaje baba Yusha U Yana son Ganin shi.

Ai kuwa a Daren ya Nemo Goro ya Kuma Sanar da magabatan sa akayi gangamin daurin Aure Wanda aka Daura da Asuba bayan an sallame sallar Asuba.

Farida tana zaune tana Jan carbi bayan ta gama sallar Asuba tana tunanin ko Yaya su Sameer suka kare da wancan Dan sababin baba Yusha U? Sai kawai taji sallamar baba Yusha U shi da babban Dan sa basiru sun shigo Gidan gaban farida ya Sara ta Kuma lafewa a D’akin sai Haj taji tana Amsa musu ta Kuma fita suka gaisa baba Yusha U ya bawa Haj goro Yana Fadin.

“Ga Goron daurin Auren yarinyar Nan marar mutunci ba kula Bata San girma ba shiyasa ta Gaya min ta fasa Auren nan har tana turo min Yan iska gida na to Auren da Abdullahi ya kullu ta huta tura min wasu Kuma a yau din Nan zatayi tariya don na fadawa Abdullahi yazo anjima in ta kintsa ya dauke ta ya Kai gidan shi idan tana da wata bidi a da ta shirya sai tayi ta can gidan shi Amma ya nemi Alfarmar a Bata lokaci tayi Shiri nan dai Zuwa Gobe ta tattara kayan ta bar Gidan Nan in Kuma ba haka ba za ayi maimai.

Haj ta Yi murmushi tana Fadin, “An gama Yusha U Allah ya Kara girma ai wannan yarinyar ma barta kawai naga ta dawo jiki a kumbure nace madalla dai.

“Eh wai aljanu ta tayar min har da Hawa bori ni Kuma nace ai na iya sauke aljanu da dan tsatsunbo da malam Alhaji da su Sha ka labe Babu wanda ban iya saukewa ba sai gata a guje tana Neman matsera Babu ko bankwana kin Kara jin rangal rangal wai Mai kalangu ya fada Rijiya? Ni Anya Babu wani Abu tsakanin yarinyar Nan da tsohon mijin ta ma?”

Ya kare da tambayar Hajiya wacce tace, “Ba zance Babu ba kuwa Amma Hakan da akayi Yusha U Wallahi yayi min daidai kaga in ma akwai yanzu sai su hakurkurtat da juna.

“Kar ki sake ki barta ta wuce gobe Bata bar Gidan Nan ba don ban yarda da su ba don basiru yace min har da tsohon mijin nata a jiya da na fafaki Shegen da ta turo min yace har da shi ya Gani a motar su shiyasa Naga gara kawai ta bar Gidan Nan ya huta ganin ta don naji Akwai wani a tsakanin su to zanga Mai kahuwa tsakanin ni da su ni da Abdullahin ma ya barni ai Babu wani shirin da zata tsaya Yi tsohuwar mai Yaya Biyu meye na wani shiri ita ba budurwa ba? Amma goben ma zan leko gidan nagani idan Bata tafi ba.

Wani matsiyacin lugude ya karade zuciyar Farida Jin an daura Auren su da Mai gemu shikenan sun SHIGA UKU ita da Sameer.

Ta Mike tana ganin Jiri ta lalubo wayar ta tana Kiran wayar Sameer Wanda ya taho zuwa gidan don jiya dai kam baiyi bacci ba Yana tunanin korar da baba Yusha U yayi musu duk da shi Yana cikin mota Amma yadda yaga Mustafa ya auno a guje ya tabbatar mishi da ba lafiya ba.

Baba Yusha U yayiwa Haj sallama wacce take cewa su tsaya su Karya Amma yace furar shi na can da ita yake karyawa kafin Rana ta take yaci zazafen shi Amma Baya karyawa da farar safiya.

Sukayi sallama Haj na Fadin a gaishe da inno da Gaji suka fice.

A bakin kofar gidan ne Sameer ya fito mota zai shigo Sukayi kicibus da baba Yusha U wanda Sameer ya zube Yana gaishe shi ya Amsa Yana fadin.

“Daurin Auren kuka zo ne SOJA? Ai Kun yaushe hannu ana fitowa aka Daura shi, A rude Sameer ya dubi baba Yusha U Yana fadin.

“Baba daurin Auren wa akayi yanzu ? Ni bani da Labari ma.

“Au Farida Bata gayyace ka daurin Auren ta ba? Ai kuwa ungo Goron daurin Auren ta da Abdullahi na zaci ta fada Maka ne sai a Taya ta fatan Ubangjji ya sa har karshen numfashi SHIGA tana ciki kuyiwa juna fatan Alheri.

Cewar baba Wanda ya wuce abin shi don ya San ya gama Kai Sameer kwano musamman ma irin firgitar da yaga ya yi.

<< Tana Ƙasa Tana Dabo 28Tana Kasa Tana Dabo 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.