Skip to content
Part 33 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Farida ta fice daga sashin Basma Abdullahi ya rufa mata baya suka fice tare yana kara Rarrashin Faridar akan wulakancin da Basma tayi mata.

Basma tayi mutuwar tsaye ganin a yanzun ma da Ranar take tata yabi bayan ta…Bak’in ciki tamkar zatayi bindiga take ji. Ba fa Banza ba taji ta tsani Mai irin sunan matar Nan Ashe Gudun kaddarar da tayi guzurin tassheta ne tayi . Ta zaci fiye da haka akan Faridar Nan Amma Bata zaci hadiyar Bak’in ciki irin wannan ba.

Bata kuma Ganin Abdullahi ba sai dab magaruba Abinda Kuma ta tabbatar Yana can sashin Farida don ta leko yafi sau d’ari tana hango motar shi Bai fita ba Alamar dai Yana can wurin Faridar

Ya shigo fuskar shi a daure tamau don da gaske haukan Basma akan Farida ya Fara isar sa.

Ta dire mishi kwanonin Abincin Yayi Maza ya dakatar da ita ta hanyar cewa ta kwashe baya ci a koshe yake. Tayi tsaye tana kallon shi cike da Bak’in ciki tamkar ta dauko wuka ta kashe Faridar Nan take ji don ta gama Gane ta Soma mayar Mata da Rayuwa daga sama zuwa kasa. Ki Zauna Basma Ina da magana da ke Wani irin Abu ya tokare Mata zuciya tana kallon shi cike da Bak’in ciki har tana Jin Wani yaji yaji a idon ta kamar ba zata Zauna ba sai Kuma ta zauna ….”Basma Ina son na Kara jaddada Miki Zaman lafiya kawai nake so Dake ba hauka ko tashin hankali ba. Ki sani ban Auri Farida ba fa don ba sake ta ke da kanki kin San Ina son ta to ki Sani dukkan Wani Abu na Tashin hankali da tozarci ba zai wanzar da komai ba sai Rudani don haka nake so ki kawar da komai daga zuciyar ki ki kalli Farida Yar Uwar ki wacce Zaki so ko don ni na kawo ta . Amma ke yanzu saboda Allah Zaki iya Cewa ga Abinda tayi Miki Wanda yasa kikayi Mata wannan wulakancin? To bana so gaskiya bana son Wani Abu Akasin zaman lafiya da girmama juna Wallahi tallahi idan Farida ce naga zatayi Mika haka duk yadda nake son ta Dole ne na tursasa Mata Yi Miki biyayya Amma ke da kike Babba kina Zubar da girman ki ba Dole ta take girman ta wuce ba? To anyi na farko anyi na karshe iyakar ki da ita gaisuwar mutunci ke da ita ko ni da na hada ku waye yake da tabbaccin Ganin Gobe? Idan na mutu Dole ke da Farida kowace ta kama gaban ta tunda Wanda ya hada din ya Kuma Raba don haka idan na Isa ne Zaki dauki maganar da na fada Miki idan kuwa kince kina nan a yadda kike to Ina Mai tabbatar Miki da Wahala kawai Zaki Sha

“Wallahi Babu Wanda Isa ya Saka ni son yarinyar Nan Abdullahi kar ma kace zaka tallata Mini son ta don yadda na tsani matar ka ban tsani mutuwa ta haka ba shiyasa na tsinewa mijin ta da ya sake ta don na san sakin Auren ta da yayi wata kofar balaki ce ya bude min gata Nan Kuma Ina gani don haka Daina tallata min ita Wallahi Banga ta yadda za ayi na iya son wannan kayan wofin ba don na Gane ita da numfashi na gware suke tana kokari fincike min shi Bata da banbanci da mutuwa ta tunda gashi a Ranar girki na ma kana nanuke da ita Abincin ma a can Kaci ai Wallahi wuta bal bal.

“Baki sani ba Dukkan Abinda kike tunani Farida Bata yarda na shiga hakkin ki komai zata tuna min da ke Amma abubuwan da kike ne suke bani haushi har naji ba zan saurare ki ba don wannan haukan da kike Wallahi ba burge ni yake ba Basma . Na Fi son naga kin kwantar da hankalin ki sai na kalle ki a mace wacce ta waye ta Kuma san Rayuwa. In kumayi ta shakkar Shirun ki don ban San Abinda zai biyo baya ba idan kikayi shiru . Amma kin kasa kawar da Kai bare kiyi kawaici kiga Ina Al Amarin zai je komai sai kice sai kinyi hauka kin Saka harkar jahilci.to ki sani Wallahi babu Abinda Zaki iya Hanawa Kuma Kara fita Raina kike Wallahi Ina kallon ki a wata mace marar kima idona Wannan kalmar ta Kara fita Ranshi take itace tayi Mata tsayuwar mashi a ZUCIYA har taji kwalla na bin idon ta Amma Bak’in ciki ya Hana Mata iya tankawa…A haka suka kwana ya juya bayan shi Bai Kuma bi ta kanta ba duk kayan Matan da ta daddaka da son Lallai sai ya Gane ba finta komai Farida tayi ba Amma sai ta Gane da gaske yake ta Soma fita Ranshi dinKuka ta Saka mishi irin kukan Nan na kissa musamman a turaka Amma ko juyawa baiyi ba ya kyale ta har tayi ta Gaji sai leka fuskar shi tayi taga Yana baccin sa sadidan.Haka yayi Mata kwana Biyun ta Babu wani Abu da ya gitta a tsakanin su shi Yana gabas ita Kuma tana yamma.

Bata tsinke da Al Amarin Nashi ba sai da taji wayar ta na tsuwwa ta duba taga shine yake Kira ta share Kiran yayi ta Kira Bata dauka ba sai Jin shigowar Sako tayi taja wayar tana dubawa inda taga Abdullahi ne ya tura mata gajeren Sako na cewa yanzu jirgin su zai tashi shine ya Kira ta don ya sanar da ita sun wuce shi da Farida hutun amarci.

A haukace ta Mike jikin ta Yana kyarma tana Aikin me har akayi Hakan? Da sauri ta Figo key din mota ta fice Zuwa filin jirgin don Wallahi ba zata yarda ba sai dai ayi Uwar watsi a filin jirgin Nan.

Aka Bude mata kofar get ta fice a guje ta nufi Filin jirgin inda tana zuwa jirgin Yana Soma motsawa Yana gudun da zai Daga Sama tana kallo jirgin ya cira zuwa Zuwa samaniya tabi shi da kallo idon ta taf da hawaye.

Taja motar Zuwa gidan lawisa.

Lawisa ta zuba Mata ido tana ganin yadda ta koma tamkar wacce ta tashi daga jinya.


Ta kyalkyale da Dariya tana kame Baki Alamar tsayar da Dariyar ta


“Har na zama abin Dariya lawisa?

“Wallahi kin zama abin Dariya Basma . Wai ni Kam ma kina bacci kuwa? A dai yadda na ganki ban zaci kina cin Abincin kirki ba don gaki nan kin Soma fita hayyacin ki.


Basma ta soma share HAWAYE tana Fadin


“Ni na kawo kaina shiyasa kike min kowane irin wulakanci lawisa.


“Abin ki ne yake da mamaki da haushi Basma sai kace akan ki aka fara KISHIYA don Allah? Yanzu Kuma da na ganki wurjanjan in da zan ce me ya faru sai kice min Farida? Wai ke baki ma iya Yar kissar Nan ta auna hankali ba? Bini bini sai kin kwaso kin taho wurjanjan? Ko da yake hawayen naki ne suke da yawa Amma ki sani Wallahi tallahi Zaki zama ALLAH SARKI duk Ranar da kishiyar ki ta Gane kina Mata kuka don Ina mai tabbatar Miki da gaki can Asibiti kina bin layin masu ciwon zuciya. Kwata kwata Basma kina Neman haukavewa akan kishiyar Nan Taki . Wai Baki da wani Abun Yi ne da Zaki mayar da Hankalin ki a can? Wallahi kin Soma bani HAUSHI haba don Allah.


“Lawisa wai don ba ayi miki kishiyar Nan kinji balakin da yake ciki bane?

“Wallahi ko anyi mini ita Basma Ina ganin koma wacece aka Auro Bata Kai na Damu da Al Amarin ta ba in ma na damun to Akwai hanyar da Zanyi maganin Abun Amma ke tamkar dai ace ce Miki akayi Basma Ajalin ki ya gabato ko Kuma za a sake ki wai kin San Wani Namijin ma baya son mace tayi ta haukan kishi akan Auren sa? Da Zakiyi Shiru wallahi sai an koma ana Jin shakkar Shirun ki don ba a San me kike shiryawa ba? Amma Lokacin da kike wannan haukan Wani daga nan yake Jin ya tsane ki Wallahi Amma shiru ai girma ne don ba a San me kake sakawa ba?


“Koma dai meye lawisa ai ni Naga Abinda na Gani yanzu duba waya ta Nan kiga sakon da ya tura min wai sun tafi honey month.

Ta mikawa lawisa wayar ta Karanta tana Fadin

“In nice ke zan mayar mishi replay da ADDU AR fatan su dawo lafiya Ina Mai tabbatar Miki har suje su dawo kina a Ranshi da tunanin me kike nufi ? Don kin barshi a Duhu Amma kin tashi kina tijara in tashi ZUCIYAR tazo a wuya Anya ba za ayi Danyen Aiki ba? To ki dawo Hankalin ki Basma ko da sun Bata Miki kar ki yarda su Gane kin fusata Wallahi da haka Ake cin Riba Basma ko magani kikeyi Wallahi sai kin kwantar da Kai Zaki ga biyan bukata ba Wai komai tsaitsaye ba.

“Lawisa ni kadai nasan Yaya nake Jin Faridar Nan a Raina. Wallahi zan iya kashe yarinyar Nan har kiyama . Anyi min Rashin Adalci da yawa lawisa ba Zaki Gane ba. Tunda fa yarinyar Nan ta shigo Gidan Nan yake nanuke da ita. Aikin kwana uku da Ake bawa bazawara ita kwana bakwai ya Bata Kuma ban Isa nayi magana ba sai ya nuna min ta Fi ni a wurin shi har wani wulakanci yayi min a gaban ta karshe Aikin kwana biyu na ma haka ya kare Yana min wulakanci ko fuskar sa ban Gani ba

“To ai kinji sakin layin da kikeyi . Ke yanzu in aka barki Zaki iya kashe ta kenan?

“Wallahi zan iya lawisa.

“To gara dai ki koyi boye Abu a Ranki ki Kuma Daina fito na fito da Al Amarin su kiyi kamar Baki San sunayi ba ko maganar ta ya kawo Miki ki saurare shi kawai kar ko tanka mishi bare kice Wani Abu akan ta . Ki zama tamkar sakarai akan su iyakar ki da ita gaisuwa Kuma kar ki yarda ki aibata ta a Gaban shi ko da Kuwa tayi Miki Abinda Zaki sanar dashi din ne Ina Mai tabbatar Miki idan kika kawar da kanki akan su Wallahi sai sunji shakar ki don zasu dauka kina shirya musu Wani Abu ne ta haka ne zaki yak’e su ba tare da sun kula ba Kuma ta haka Zaki fidda ta Daga gidan cikin Sauki. In kikayi Hak’uri kwana nawa ne an gama amarcin?

“Ni fa da gaske nake lawisa har malamai zan iya shiga don a fidda min matar nan daga gida na

“To malaman Zaki shiga Haj sai kin kwantar da Kai ni Ina so ki Gane Wani Abu Daya Basma ki nunawa Abdullahi da ita kanta Faridar Basa gaban ki ta hanyar mayar da su gefe kiyi Abinda yake Gaban ki kar ki yarda Al Amarin su ya tayar Miki da Hankali bare kice Zakiyi musu Magana duk iskancin ta sai ta Ji shakkar ki amma idan kina haka Ina girma a Nan? Ai zata Raina ki ne bare Kuma mijin nata Yana kama Mata. Ki Rik’e girman ki ki Kuma nuna kema mace ce ko Baki mallaki Abinda take da shi ba Wallahi kema kina da Abinda Bata da shi Kuma fa Basma ki Rik’e a Ranki matukar dai da gaske son ta to itace matsalar sa a Rayuwa ai Abinda kake so shi ke baka Wahala don haka ni dai shawara ta ki kame ki nuna kema mace ce wacce ta San Abinda take kar ki bari Wani Abu na Tashin hankali ya Kuma faruwa da ke ki nuna musu Baki da wata matsala da su bare in kin dubga musu wata tsiyar su zarge ki shi fa yak’i sai da zamba ta yadda ko kinyi abin su karyata Cewa ba ke bace

Lawisa ta amsa tana kada kanta don ta shurya wata mugunta a yanzu ta tsinci wani makirci Wanda zata shirya Kuma Dole ya Bada ma ana.

Ta Dubi lawisa tana kyalkyalewa da Dariya har da kurma Wani Uban ihu tana Fadin


“Wallahi na yarda da ke laweee shiyasa Ake son zama da yan Duniya gashi kin Gano min Abinda na kasa Ganewa Kuma Nima yanzu na kulla Wani MAKIRCI Wanda zai cinye hadiye Abdullahi shi da tsinanniyar gallafirin matar tashi Yasin Wani SHEGEN bom zan Dana ki barni idan ya tashi zan zo na Sanar miki ai Kuma na dauki Darasi da laccar ki Wallahi sai sun Gane ko a cikin tandu akwai gabas.

Sukayi shewa ita da lawisa suka Tara suna Dariya lawisa tana Fadin

“Yanzu Zaki zama mace Mai aji irin Matan Nan da ake Kira manyan Mata ai Basma kissa itace mace Wallahi mace Babu kisaa ai ta zama gardiya Wallahi Amma ta Ruwan Sanyi ake dafa KISHIYA ta tahu fiye da ace wuta aka Saka ta.

“Ai fa anzo wurin lawee Wallahi kin Dora ni hanya Kuma Zaki Yi mamakin irin gadar Zaren da zan murzawa matsiyata sai kin yarda na Fi su makirci ba honey month ba su tafi life month a Shekara Dubu Ina Nan a guda Daya tak Kuma za a dawo a same ni ai har kyauta sai nayi Miki Haj ta Wannan laccar Taki sai na biyata yasin makirci Kuma salamun salamun zasu Gane nafi su Sharri Wallahi.

<< Tana Kasa Tana Dabo 32Tana Kasa Tana Dabo 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.