Skip to content
Part 36 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Hankalin Sagir yayi matukar tashi ganin Goggo ta fashe da kuka tamkar wacce aka dadawa duka ko aka falle ta da Mari.

Goggo kuka share share da hawaye Abinda ya Tayar da Hankalin Sagir Wanda yake jin ko maganar da ya fadawa Goggo ce ta nata Mata Rai har ta Saka ta kuka?

“Don girman ALLAH Goggo kiyi Hak’uri Wallahi ban San magana ta zata Bata Miki Rai ba Wallahi da ban fada Miki ba.

Da sauri Goggo ta Goge idon ta tana fadin.

“Ba Bata min Rai kayi ba sagir kukan Dadi ne nake Wallahi ban ma fa San kukan ya kubuce Mini ba sai da naji kamar fa kuka nake.

Kad’an ya Rage Dariya ta kwacewa sagir Amma sai ya maze Yana kallon Goggo wacce take ta share HAWAYE.

“Ai Sagir Allah ne kadai yasan Dadin da Naji akan wannan maganar wallahi har wallahi tuni na Ambata zanyiwa Uban ka madadi da maimuna Amma sai na tuna Uwar ka Bata bar mishi Abinda zai Kalli Ahalin ta da Kima da Kamala ba sai Naga idan nayi Hakan ba Lallai ishaq Yana muradin Hakan ba kaga na cutar Dashi don in yace duka jinin wasila Basu da kirki ni ce farkon wacce zata gasgata shi Domin kuwa batayi mishi kirkin da zai ga na bayan ta da shi ba. Shiyasa nayi Shiru na bar abin a ZUCIYA ta Amma da yake Allah yaga ZUCIYA ta Alheri nake nufin ISHAQ dashi sai gashi ya cika min fata na.

Wallahi har MAFARKI Nayi an Daura Auren ISHAQ da maimuna Ashe Al Amarin ne Ubangiji zai tabbatar. Hakika sai a yanzu na Gane sau da yawa fatan ALHERI ko Sharrin da Muke nufar Yan Uwan mu da shi shine Ubangiji yake fara saukewa akan mu Domin mu gane ita fata kowace iri ce tare da Mai yin ta Ake tabbata. Da munayiwa junan mu fatan ALHERI Wallahi da Sharri bashi da muhalli a Rayuwar mu Amma sai muke mantawa son kanmu da son muga Wanda Bama so ya wulakanta ko ya tozarta don muyi Dariya Allah ka Hana mu Jin Zafin Wanda yafi mu wata ni I’ma daga Allah muma Allah kayi Mana fiye da ta Wanda muka Gani ya burge mu haka ya kama ta Ake fad’a ba Wai son a fasa kowa ya Rasa ba. Sagir ka fadawa ISHAQ tun tuni nayi wannan tunanin Amma Gudun kar na matsa mishi yasa Nayi Shiru Amma a yanzu Kam na yarda na Amince na bashi maimuna Kuma Ina Mai tabbatar maka da yadda nace haka maimuna zata karba na yarda da ita da Imanin ta har aradu zan iya Sha akan maimuna ba zata tab’a yiwa ISHAQ Wani Abu da zaice kaicon ta ba kaima da kayi wannan tunanin kayi hange Mai kyau sagir Allah ta ala ya Sab’a Halin ku da na Uwar ku.

“Ameen! Ameen Goggo in Sha Allah kuwa zan fada mishi duk yadda kika ce.

“To Alhamdulillah ai ni wannan Al Amarin ni akayiwa tun tuni nake Ganin abin Nan a mafarki na Ashe zai tabbata ni hurera ? Ta Kara Jin jina Al Amarin da mamaki.

Sagir ya Mike Yana Fadin, “Goggo bari na koma ga wannan ki siyi Goro tunda dai Baki yarda na siyo Miki shawarma ba kince Bata da Dadi.

Ta karbi Dubu Dayan da yake Bata tana Fadin, “Kai bar sharwanar nan fanke ya fiye min ita sau Dubu Sagir Allah ya kamawa Rayuwar ka ya baka Rahamomin da suke cikin Duniya da LAHIRA yada yasa Ina da Rabon ganin Auren ka ALLAH yayiwa Uwar ku baiwa da yawa Amma Bata Gode ba? Miji Mai yakana ? Ya’ya masu biyayya duk Bata Gode ba? Allah ya shirye ta ya ganar da ita.

Ya Mike Yana Amsawa da Ameen Ameen Goggo na tafi. Ta ce, “Ka cewa ISHAQ din Ina son Ganin shi in ya samu dama Yazo muyi magana.

Ya fita Yana fadin in Sha Allah zai fada mishi. Goggo sai murmushi take tana fadin, “Allah Mai iko shiyasa Haihuwa da yawa take da Dadi in wancan ya Bata Maka sai wancan ya wanke Maka Abinda aka Bata maka.

Maimuna kuwa tunda ta fita Daga Gidan take tunanin maganar da Sukayi da sagir. Lallai Allah Mai Rahama ne tabbatacciya Kuma shine yake da hanyoyi da yawa Wanda Hankali ko tunani Bai Isa ya hakaita ba . Yau dai dubi wannan Al Amarin Mai KAMAR A MAFARKI ISHAQ din da ZUCIYA ta kimsa Mata shi da karfin tsiya saboda kawai Goggo ta hada Al Amarin su da sunan comfiering sai kawai taji Gaba Daya Al Amarin ISHAQ ya tsaya mata a zuciya Abinda ta tabbatar in da Hakan Bata faru ba sai dai ta mutu da Mikin ta a ZUCIYA sai ga mafita Daga ALLAH.

Bata iya fahimtar Abinda akayi a makarantar ba har aka taso tana Lissafin Dokin Rano Wanda ko Babu komai dai Wani Abu Mai kama da cikar Buri Yana dab da faruwa.

Tana shigowa Gida Goggo ta Kira ta tana fadin.

“Taho Auta na yanke miki Hukunci Allah yasa ban shiga hakkin ki ba.

“Babu Wani Abu da Zaki zartas a Kaina Goggo ya zamo shiga hakki ko kin shiga ma na yafe Miki Babu ta inda Baki wuce Hakan a gareni ba Goggo.

“Alhamdulillah maimuna Naji yadda kukayi da Sagir Kuma kin San ni a gareni wannan maganar tamkar Wani buri ne da yake ZUCIYA ta Allah ya Amsa . Don haka na amsa mishi maimuna Amma kar ki Cuci kanki Idan kinji Al Amarin Bai kwanta miki ba ki fada min don zan bashi hak’uri ne.

“Wallahi Goggo yadda kike so Dani haka Zakiyi matukar madadin da kikayi Dani kin gamsu Goggo Wallahi Nima na yarda na Amince Allah yasa hakan ya zama Alheri.

Goggo ta Soma matse hawaye tana Fadin, “Allah ya Baki Ya’yan da zasuyi Miki fiye da biyayyar da kikayi min maimuna . Na sani ko wuta nace ki fada Zaki fada Allah ya saukar Miki da Dukkan Rahamomin sa yasa Alheri ne biye bayan Al Amarin Nan.

“Ameen Ameen Goggo ki Daina kuka dukkan Abinda zakiji yayi Miki Dadi ko Rashin Dadi Godewa Allah sai kiga ya Saka Miki k’ana A da juriya.

ISHAQ ya gama sauraren Sagir har ya kare da cewa Goggo tace yaje suyi Magana.

Ya Sauke AJIYAR ZUCIYA Yana Fadin, “In Sha Allah sagir zuwa Dare zanje Kiran Goggo.

Da dare kuwa ishaq ya Isa gidan Goggo maimuna tana d’aki taji zuwan shi Bata dai Ji Abinda suka tauna tsakanin shi da Goggo ba Wanda yaja su har karfe Taran Dare Kafin yayiwa Goggo sallama ya Wuce.

Sai da ya Isa gida ne ya Kira wayar maimuna wacce taji Wani irin naushi a kirji Saboda firgitar da Kiran Nashi ya haifar Mata. Ta danna ma amshin Kiran tana mishi sallama.

“Allah ya taimaki malama ko na tayar da ke daga bacci ne?

“Ban ma kwanta ba Yaya ISHAQ Ina wuni? “Mun wuni lafiya ya makaranta?

“Lafiya Lau ya Aiki?”

“To Alhamdulillah maimuna kinji Sako kamar daga Sama ko?”

“Na ji Yaya ISHAQ”

“To Maimuna ina fatan ban shiga rayuwar ki ba duk da Goggo ta fada min komai Maimuna amma ina tsoron shiga hakkin ki, dukkan abinda kika ji a ranki ki fada min zan fahimce ki maimuna tunda shi Aure da kike Gani na mutum Biyu ne Babu Mai takura Daya akan lallai sai yayi abinda baya so kin Gane?

“Haka ne Amma Yaya ISHAQ Goggo ce ta fara Raya Hakan a Ranta don idan Akwai Wanda yayi FARIN CIKI da Al Amarin Nan to Goggo ce ni Kuma na yarda na Amince ikon Goggo ce duk yadda take so Dani Haka Zatayi idan tace ba Aure ta bayar Dani gareka ba kyauta ta baka ni Wallahi na bayu bare Kuma Aure ta Baka ni tana son na maye Maka gurbin Anty wasila don ta shafe maka Bak’in cikin da aka darsawa zuciyar ka Wallahi bani da abin cewa akan maganar Goggo.

“Nagode maimuna Amma kiyi Hak’uri ni din bani da Komai.

“Ba Wani Abu da yake tare da Kai ne abin duba na ba Yaya ISHAQ illah Kai din kanka Wani Abu da yake tare da Kai Lokaci ne kuskure ne Babba Duban Abinda mutum yake dashi yayin mu Amala don wannan abin Duban Bai bar yau da gobe ba bare Matan da suke son Namiji don kudin sa Wallahi kuskure ne idan abin da kikeyiwa ya kare shikenan?

“Gaskiya ne malama Nagode yaushe zan zo mu Gaisa to ?”

“Duk lokacin da ka samu Dama Amma Banda Wanda nake makaranta.”

“To Nagode zan iya ce Miki I love you?”

Ta yi Maza ta ce

“A a Yaya ISHAQ Ina jin kunyar ka fa”

“Ni Kuma ai na Riga na fada sai ki dawo min da kalama ta in ba Zaki karba ba.”

“In ce me to?”

“Ki ce ga I love you din ka”

“To ga I love you din ka Yaya ISHAQ.

“Kinga nayi Miki wayo kin maida martani.

Suka kyalkyale da Dariya sun juma suna fira wacce su Duka sukayi Mamakin kansu kafin Sukayi sallama cike da wani irin shauki.

Kan kace me? Soyayya Mai tsayawa a Rai ta wanzu tsakanin maimuna da ISHAQ inda aka tsayar da Ranar Auren su watanni Biyu masu Zuwa.

Tuni Kuma ishaq ya SHIGA gyara gidan shi Wanda akayiwa kwaskwarima wacce ta mayar dashi sabo dal aka Zuba abubuwan da Babu su a baya don a yanzu Kam har da Soma ta Ruwa ga Kuma inverter ta wuta an jona. Kai abubuwa da yawa ISHAQ ya zuba su a gidan Nan inda kafin Lokaci akayi fenti aka saka interlock a gidan har zuwa bakin kofar wacce aka sakawa kyauren get itama har Nan an Zuba interlock yayin da gefe da gefen bangon kofar get din aka dasa fulawowi masu fitar da fure kala kala.

Anty murja da take ta Neman layin wayar wasila don tunda ta tafi basuyi magana ba sai fa yanzu da take son fesa Mata Auren ISHAQ da maimuna don ta san dole za ta ji bakin ciki Amma ta kasa samun layin Dole ta Hak’ura.

Al’amarin ISHAQ kuwa Dole ya bawa Al Umma mamaki Domin kuwa a yanzu Allah yayi mishi wata irin daukaka Domin kuwa a yanzu shagon huluna daban aka Bude shi Babu Had’i da turare yayin da na turaren ma daban haka na takalma Suma daban sai Wanda yake Dunki a ciki shaguna Hudu Ras duk na ISHAQ kuma kowane ka shiga zaka Tara’s ana ta shiga da fita ana harkar Arziki inda ISHAQ ya gayyato Abokan sa ya Saka su a cikin dukiyar shi Wanda ya tabbatar da Amanar su Kuma a haka sukayi komai a Bude duk bayan wata UKU suke lissafi ya fidda musu hakkin su Suma suka Rik’e Amana.

Kayan da ya hadawa maimuna a matsayin lefe kowa yayi Mamaki musamman maimuna wacce Bata San da zaman yadda Rayuwar ISHAQ din ta sauya ba Amma sai tayi mishi ADDU AR Allah ya Kara sutura.

Kan kace me? aka shiga Hidimar Biki gadan gadan ISHAQ yayi Rawar Gani Sosai ya Kuma yiwa Goggo Hidima ita kanta tana ta mamakin hidimar da yayi har Allah ya kaddara dauruwar Auren su Wanda akayi ta sauke Al Kur ani Mai girma duk ba a tsinke da Al Amarin ba sai da aka Sadar da Amarya maimuna a gidan ISHAQ aka Tara’s da gyaran da akayiwa gidan Wanda ya baiwa kowa Mamaki.

Anyi walima itama cikin tsarin addinin musulunci itama Babu wata bidi a sai karatun Al Kur ani Mai girma tare da wa azi karshe Akayi ADDU OI masu yawa na Neman zaman lafiya tare da Kore Dukkan Wani shaidani da zai shigo cikin Al Amarin su.

Wasila Zaune bayan ta fito daga wanka a D’akin honorable Gona Wanda ta mayar da gidan shi kamar gidan Auren ta Shima Kuma Yana sakar Mata kudi na ban mamaki.

Ta gama Shirin ta na Zuwa gidan Shama don a yau din satin ta shida a gidan honorable Gona wanda ya killace ta wai don ma kar taje ga Wani Namijin.

Ya Saka Direban shi ya kaita Gida can garki gidan Shama

Tana sauka motar ta Kunna wayar ta wacce take a kashe tsayin Lokaci inda tana kunnawa sakonni sukayi ta shigowa wayar ta Bata tsaya duba su ba ta shiga gidan Shama ta sheko Aguje tana Rungume ta inda take mata Oyoyo tana Rik’e Jakarta wacce take cike da kudade ta Bude tana ganin kudaden kwance a ciki shama ta zaro ido tana zama tana Fadin.

“Matar nan Allah ya Baki jari a tare da ke baki Siya don ki saida ba Baki kasa jiran Mai dauka ba sai dai kawai kiji saukar karafan banki Allah ya maida mu a danshin ki.

Wayar Wasila dake hannun ta tana duba sakonnin da suka shigo wasu na kamfanin MTN wasu Kuma da wasu lambobin inda taga lambar Anty murja wacce ta Aiko mata da Sako tayi saurin Bude sakon inda taga Abinda sakon ya ke magana wai Auren maimuna da ISHAQ.

Wani irin matsiyacin Duka da taji ya daki ZUCIYAR ta shine ya Saka ta mikewa tsaye tana dafe da kirji cike da tashin hankali tana maimaita karanta Sakon Wanda take ganin shi tamkar a mafarki wai wace maimunar ma Ake magana tukuna? Wane ISHAQ din?

Idon ta cike taf da kwalla ta Soma tsiyayar zufa inda Shama taga tashin hankalin da ta shiga ta dafa kafadar ta tana fadin.

“Wai me ye naga duk kin wani firgice ? Ko mutuwa aka yi ne?”

“Gara mutuwa Shama da Abunda nake Gani a yanzu. Wai kanwa ta ce da Auren tsohon mijina ? Sau Kuma ta fashe da kuka tana Jin Wani matsiyacin Bak’in ciki Yana shirin keta zuciyar ta musamman da take hango ISHAQ a matsayin mijin maimuna kanwar ta Bata taba zaton Jin Abinda take ji a zuciyar ta irin haka ba meye ma Abinda yake damuwar ta?”

Kukan ta ya bawa Shama mamaki ta kame Baki cike da wani irin mamaki tana fad’in.

“Wai akan Auren ne kike wannan kukan ko kuwa dai Wani Abun ne daban? Yayi Auren shi in ma kanwar ki ce ya Aura ai Ina Ganin kamar ke aka taimaka ko Babu komai ai zata kula miki da shi ta yadda Zaki iya zuwa gidan kigan shi Akasin idan wata ce ba wacce Zaki iya tunkara gidan ba Kuma ko ba komai ai Ya’yan ki zasu samu gata Akasin ace matar Uba suka Samu Amma yanzu ai ba matar Uba suka Samu ba sai dai Uwa gaba Daya.

Wani irin kallon kinci haka Kazan ki wasila tayiwa Shama tana Fadin.

“Amma dai Shama Allah Ya tsine Miki Albarka sau fin Dubu Ashirin Wallahi ta Yaya kike min wannan banzar maganar? Ya Ina Nuna Miki Abinda nake ji a ZUCIYA ta kina min Wani Arashi Mai kama da kina Jira na don Uban ki?”

<< Tana Kasa Tana Dabo 35Tana Kasa Tana Dabo 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.