Skip to content
Part 3 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Ya Mike cikin mutuwar jiki musamman da ya laluba aljihun shi ya ji Babu komai dama ya San Babu komai sabo da Yi ne wai kuturu da gatsine.

Hankalin sa yayi matukar tashi da ya tuna yanzu ne zai bayar da Abinda za a sarrafawa Yara na Karin kumallo shi kam dama baya Jira in dai yaran sun karya to Alhamdulillah bukata ta biya. K’aramin karfi ne dashi Amma Allah ya hada shi da mace Mai dogon Buri. Wasila Kam in son samu ne a wurin ta wannan Duniyar tayi Mata kad’an sai Kuma gashi Auren su Babu jimawa karayar Arziki ta same shi Al Amuran sukayi wata irin sauyawa Amma wasila Sam Bata Duba Rayuwa da irin sauyin da take Dasu.

Ya Mike Yana fito da sabuwar Rigar shi wacce Baiyi Mata sakawa uku ba. Ya yanke shawarar kaita wurin Yan kasuwar tsaye ya karbo kudin a Siyawa Yara Abun Karin.

Ya zaro shaddar ta gizna ce koriya Mai Daraja wacce Tasha Aikin surfani kasancewar sa tela a yanzu Wanda sai ayi kwanaki bakwai ba a samu Aikin ba sai dai Rufin Asirin Allah kawai

Ya Dubi shaddar wacce yake so ba don Dole ba da Babu yadda za ayi ya kaita ya siyar don ya San ko Rabin kudin ba za a maida mishi ba. Yaji Wani Rashin Dadi a Ranshi Amma Kuma baya son matar tashi ta tunkare shi da Zancen ya bayar da abin yace mata Babu yanzu ne zata hau tijara da Sababi. Gara kawai ya Kai Rigar kasuwa in Allah ya so sai ya nufe shi da samun wacce ta fita ita dukiya dama bakuwa ce. ..

Sagir ya shigo D’akin cikin Shirin tafiya makaranta yaro ne dan shekara Sha uku Amma Mai tunani irin na manya kuma Wanda yake matukar tausayin Uban shi musamman da ya lura da Mamar tasu Bata rage mishi ko na sisi in dai akan kudi ne Bata shayin kowa da Komai zata cashe mishi duk da baya biye Mata. Hasali ma baya tanka Mata sai dai in Abun ya Bata mishi Rai ne zaka idon shi ya kada yayi jajir.

“Abba za ayi maka wanki ne?

Sagir ya tambaya Yana Mika hannu da nufin ya kawo in ya dawo makaranta ya wanke mishi.

“A a sagir ba wanki bane zan fita da ita ne ka shirya ne? “Eh Abba bayar wa zakayi ?

“Zan karbo kudin ta ne don Babu komai a tare Dani Kuma bana son cewa mamar ku Babu don jiya ma bamu kare da Dadi ba saboda ban bayar da komai ba.

Wani Abu ya soki zuciyar sagir yayi kasa da kanshi kafin ya dago Yana Fadin.

“Yanzu ma cewa tayi nazo in ka dama ka Bada Abinda su yusra zasu karya wai jiya ma haka suka kwana Basu ci komai.

Ya Mike da sauri Yana daukar Rigar shaddar Yana sakawa a Leda Yana fad’in, “Ce tayi min hakuri kadan sagir yanzu zan dawo ai ban San Basu ci komai tunda na shigo da garin rogo dama tace sun gaji da cin sa bari naje na Dawo.

Ya dauki ledar ya fice da sauri yayin da hawaye ya kawo a fuskar sagir ya dafe bango ya share Yana tunanin wane irin tunani ne da mahaifiyar sa wacce Sam Bata tausayin Abban su? Ya fice daga D’akin Bai ko koma ta kan mamar su ba ya wuce Abun sa Zuwa makaranta inda yayi fatan Allah yasa a yau garejin da yake koyon gyaran mashin a bashi kudi ya Rik’ewa Abban nasu ya Siya wa su yusrar abinci ba sai ya siyar da kayan shi ba.

A fusace wasila ta Nufo d’akin ishaq din masifa na cin ta ta banko kofar dakin tana Fadin

“Wai haka zaka barmu yanzun ma? Jiya yaran nan sun kwana da yunwa kuma yanzu na turo ayi maka magana ka bawa banza AJIYAR mu?

Ta leko d’akin taga Babu kowa kafin tayi baya tana Fadin

“Wai mutumin Nan fita yayi ya sulale ya bar Gidan ?

Ta dawo ta zauna ta warwaro kudi ta mikawa yusra da Zainab suka wuce makaranta ta zauna tana Dakon isowar ishaq.

ISHAQ

“Sani don Allah duba Kayan Nan Sabbi ne sakawa ta Biyu ko Ruwa ban Kai ta ba don Allah duba ta ka bani Abinda ya kamata.

Sani ya karbi ledar Yana fito da kayan duk da Kyan Dunkin Amma da yake Dan Adam a yau ko nace Nigeria a yau idan aka lura a bukace kake to za a ja ka k’asa tamkar Babu Gobe.

“To Kai ishaq wannan kayan ai kalar tayi bau kasan gayun Yanzu basa son kala irin wannan sun Fi son Mai Duhu yadda Zata jima Bata ga Ruwa ba.

“Sani kasan in ba Dole ba babu Abinda zai sa ka ni fito da sutura ta na siyar . Abinda kaga ya fito Bera daga daga Rami ya fada wuta to Yafi wutar zafi.

“Shiyasa kaji na fada maka haka don kala Mai haske Abokin zama take zama sai ka jima baka shugar ba da Mai Duhu ce da Babu tsaitsayawa zamu buga mu kwashe Amma wannan Kam gaskiya ma ni don saboda Kai ne Kuma kace Abinda ya Koro kusu daga Rami ya fada wuta nasan Abun ya Kai inda ya Kai.

“Ni dai gata Nan ka siya ko nawa ka Siya ka bani kud’in Ina sauri ne gida na Jira na ban sallami Yara ba.

“Dubu uku na Siya ishaq Shima don ba zan iya Cewa ka Kai Wani wuri bane tunda ai ka San da Wani wurin ka nufo ni.

“Haba Sani ko surfanin fa Duhu Hudu da d’ari biyar muke Yin sa bare shaddar yadi uku Dubu Hudu duk yadi itace ka Siya Dubu UKU?

“To ishaq gata Kai gaba kaji idan za a kama yadda na kama nifa in ba Kai bane Kai tsaye nake cewa bana siyan kala Mai haske in kana ganin Akwai cutuwa Kai gaba.

Ya turo mishi ledar kayan bayan ya linke kayan ya mayar.

“Ka dai Kara min Wani Abu don Allah sani na fada maka Dole ce tasa zan Siyar ko zaka Ara min kudin ne ka ajiye min kayan in na Samu na dawo Maka da kud’in ka na karbi kayan?.

“Jingina kenan in zaka k’ara min Wani Abu ai sai na baka Kuma yaushe zaka dawo min da kud’in?

“Kaga mu bar wannan yanzu siyi ka bani kud’in in Rabo nane zan samu kudin na zo na fanshi Kaya na.

“Ka Siyar min a Hakan?

Sani ya tambaya.

“Na Saida Maka sani ya Zanyi?

Ya karbi ledar Yana zura Hannu cikin aljihu Yana fito da kudi Yana Fadin.

“Yo Kai Ashe fa na biya wancan Rigar na manta da na biya kudin su dan acaba kaga Abinda yayi min saura Dubu Daya da d’ari biyar Rik’e su zuwa jibi sai na cika Maka Dubu da d’ari biyar Dinka.

“Haba sani ta Yaya Kuma za ayi haka? Na fa fad’a maka damuwa ta me wannan kud’in zasuyi mini?

“Wallahi zan cika Maka kudin ka jibi jibin Nan ko na yanzu a sallami yaran tukuna ai ba mu San Abinda Allah Zaiyi ba Gaba.

Ya Mika hannu ya karbi kudin cikin sanyin jiki Yana Saka su aljihu ya juya zai tafi yaji an kwala mishi Kira da muryar sagir.

Ya juyo da sauri sai kuwa yaga sagir din Yana sauri ya cimma shi.

“Af baka tafi makarantar ba sagir? Ya fada Yana fito da d’ari biyar Yana nufin Mika mishi sai yaga yaron ya fito da kudi Dubu biyu Yana Fadin.

“Abba kudin da nace Maka Ina zubi ne a garejin mu sune na karbo Maka kar ka Siyar da kayan ka in kana siyarwa Abba zasu Kare ne Kuma baka Dinka wasu ba.

Ya zurawa yaron ido kafin ya ce, “In na karbar Maka kudi sagir Kai Kuma fa? Gara ka Tara ba kace Keke kake so ba? In ka tara Nima Ina fatan na samu cikon da zan cika Maka ka huta tafiyar kasa.

“Ka karba Abba Allah zai kawo Mana hanya Mai sauki in Sha Allah.

Ya karbi kudin ya juya Yana fito da kudin sani ya Mika mishi yace, “Sani kayi hak’uri don Allah kaga Allah ya kawo mafitar da ban zata ba.

“Har ka Saka kudin a cikin aljihu Kuma shine zaka dawo min da su don dai mutane ku Baku San Shari a ba? Ai ciniki ya fada tunda ka Siyar na Kuma karba ka amshi kudi.

“To dama ka biya ni kudin ne ? Ina ce Rabin kudin ka bani? To Allah ya min sutura yaro na yajikai na Kuma gaskiya ya fada min in Ina siyarwa kayan zasu kare ne ban Dinka wasu ba.

A fusace sani ya mayar da Hannu cikin aljihu ya fito da kudi tari ya zaro Dubu da d’ari biyar ya mikowa ishaq.

“Gasu in don ban cika ba ne zaka jawo min kauli da ba adi.

ISHAQ yayi murmushi yana fad’in, “Yanzu sani da kana da kudin Nan Amma kace sai jibi zaka cika min? To na fasa siyar da kayan Nan Dubu uku dai to ga Dubu biyu na samu Allah ya min sutura Haihuwa tayi min Rana ko a yanzu.

Da fushin ZUCIYA sani ya fige kudin ya jawo ledar ya Miko mishi Yana fadin “Gobe ma Rana ce Ina Nan zaka zo ka kawo min wasu kayan Wallahi ba zan Siya ba tunda baka San Shari a ba.

ISHAQ ya karbi kayan shi Suka wuce shi da sagir Wanda ya cire d’ari uku ya bashi yace ya hau mashin ya Isa makaranta kar ya makara saura Kuma yayi break..

Ya shigo Gidan da garin masara da kayan Miya har da icce, Wasila ta Dube shi tana Fadin
“Kuma saboda Allah saboda Yaran sun kwana da yunwa sai su dawo a nufe su da tuwo ?

“Shi ya samu bani da Abinda yafi wannan din . Don Allah don ANNABI ki rika Yi min Kara akan Abinda kika ga na kawo shi ke gare Ni Nafi ki son naga Kuna samun Abinda kuke so don Baki duba ZUCIYA ta kika ga yadda nake ji ba.

Ta Mike da littafin Hausa Wanda take karantawa ta wuce d’aki don a Rayuwar wasila mijin littafi Yana burge ta Kuma matar Nobel take son zama shiyasa ta kasa zama lafiya a gidan mijin ta.

Bata bari ya dire zancen sa ba ta bar mishi wurin Bata Kuma waiwayar kayan da ya ajiye ba sai da ta gama karanta littafin ta ta Kuma samo hanyar da zata zama matar Nobel a cikin littafin da ta gama karantawa Wanda ya zamo maganin matsalar ta tamkar ma magani Tasha akan zazzabin ta don ta karanto inda jarumar littafin take son samun kudin shiga sai taga an nuna tanayin shiga ta daukar hankalin Maza tana siyar da wani Abu Wanda zai Kuma jawo Hankalin Maza akan ta sai taga ta dace ta samo Wani da ya Fara sauke Mata kyautar Dubu d’ari. Don haka da sauri wasila ta Mike tana warwaro kudi a Jakarta ta Kuma Hado kayan snacks da boga har da shawarma. Kan kace me ? Ta hau Aikin snacks tayi kaca kaca in da ta bar garin da ishaq ya dire Mata Bata ma Kuma tunawa da su ba har ta kammala toye toyen ta don hakikatan gwana ce a fannin kayan filawa.

Ta fada Bandakin ta sullo wanka tamkar Zata sauya fatar jikin ta . Ta fito tana Nemo wasu body hog na karshen adaka Wanda ta tabbatar da in ta Saka su tayi babban tarko sai dai tana tunanin ta yadda Zata iya fita da kayan . Sai ta tuna yadda jarumar littafin tayi ta zura hijabi in taje majalisar alhazawan birni sai ta cire.

Tana Gaban mirror tana faman shafa kwalliyar da ta jima Bata Yi irin ta ba sai ga ta a yau har da budada turare ta kuwa fito tamkar wankar inji dama Abu ga farar fata tuni ta fito Ras da ita.

Ta zurma hijabin ta ta Kuma zube kayan filawar da ta toya a mazubi Mai ban Sha awa kafin ta ta Saka Dan yalolon gyale a Jakarta ta fice ta kulle gidan ta nutsa gari yawon bin inda Maza alhazawan birni suke kafa majalisa inda ta fara yada zango inda su Sameer suke zama Shan shayin Yar buta ta Kuma fidda dogon hijabin ta ta Saka Jaka ta Kuma yafa gyalen ta inda ta Kai musu tallar kayan da take siyarwa Kuma Sameer da Alhajin naira suka karbi nomber ta bayan sun suyi boga da shawarma. Sai gata da Dubu Hamsin Alhajin naira ya Bata shi kuwa Sameer account ya karba yace zai tura Mata kudi Kuma zai Kira ta . Shine fa ya Kira ta washe gari inda yaso kawo ta gidan shi Amma aka Samu Akasin ranar aka Samu matsala joint din Bai samu haduwa ba shine fa yanzu da ya kasa samun relief ya fito Zuwa majalisar don haduwa da wasilar wacce kasuwa ta Budewa.

<< Tana Kasa Tana Dabo 3Tana Kasa Tana Dabo 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×