Haj ta Dube ta cike da Mamaki Ganin HAWAYEn a idon ta tamkar wata yarinya k’arama.
“Ke Kuma fa? Me ya ke faruwa ne kike wannan Kukan?.
Da sauri Farida ta Soma share Hawayen tana Fadin
“Babu Komai Haj.
“A karya ne an tab’a kuka Babu Dalili ne? Ko na Jin Dadi ne ai Yana da Dalili bare da kika zabi boye kanki kiyi shi .
“Wallahi Babu komai Haj kawai dai Wani Abu na tuna .
“Kika tuna? Fito dai a mutum ai ni na gano ki Saboda an Dauki yaran Nan ne kika lafe a nan Kina kuka? Ai sunyi Miki Alfarma ma da kika kawo KAMAR yanzu kina kallon su Amma da sun so tun Lokacin da kikayi Auren ki zasu karbe kayan su .
“Wallahi Haj ba akan Yaran Nan nake kuka ba in ma sun karba Haj ai lalurar su bare ma ba zasu iya Rik’e su ba ko sun karba Dole zasu dawo da su.
“To yanzu na Gano ki in kince ba kukan Yara kike ba kukan anyi Miki kishiya kike? Ni wannan JANHURUN masifar Naku Yana bani Mamaki. Kun Rabu to Ina Ruwan ku da Saka ido akan Abokan Zaman ku? Haka fa yaron Nan Sameer yayi ta huzuni Lokacin Auren ki shine har da kwanciya Asibiti kema daga Zuwa kinji an Daura mishi Aure shine kika zo Nan kika lafe kina kukan munafunci ? Ku Kam shiga uku ta same ku Wallahi ke yanzu Duk kulawar Abdullahi Bata ishe ki ba kina can Inda Baki da Daraja kullum ana zargin ki Amma shine har da Wani kukan munafunci? To ki kaso Auren Mana sai ki koma ku dasa daga inda kuka tsaya .
Farida tayi Shiru ta kasa tsinkawa haj don ji take tamkar Hakan ta faru na kashe Auren don ta komawa Sameer don Bata tab’a Jin kishi irin Wanda take ji yanzu ba dukkan Abinda yayi Mata a baya ya zama tamkat mafarkin sanyi ta manta ko ta juya baya Babu Abinda take hangowa sai faffadan kirjin Sameer da Aisha zata kwanta Akai.
Haj tayi ta Sababi Amma Farida ko tari ta kasa Yi har tayi dakacen Zuwan ta gidan a yau da ta San wannan bak’in cikin zata tsinta da ta Hak’ura da Zuwa tunda Sanyin idaniyar ma su saddam Bata gansu ba bare ko shirmen su ya debe Mata kewa
Ta k’agara Abdullahi ya iso ko su bar Gidan. Ana dab da Kiran sallar magaruba ya iso ta Mike tamkar wacce take akan k’aya tayiwa Haj sallama suka wuce Gida.
A Ranar da aka Daura Auren Sameer Bello ne ya Kira shi ya sanar mishi cewa baba iro yace in ya samu Lokaci yazo satin sama ko Kuwa Nan za a kawo mishi matar tashi?.
“Wai me akeyi ne haka Bello? Da gaske kake an daura min Aure da Aisha? Sai ya hau bellon da masifa tamkar dai shine yayi mishi Auren Nan.
“Ni Nace Ina son wata aisha ne ko kuwa nace Ina da matsalar Auren ne da za ayi min wannan k’arfa k’arfar? To bana so in ma an daure a kwance bana bukata.
“Allah ya baka Hak’uri ni dai baba iro ne yace na fad’a maka in Kuma in Kai mishi wayar ne to bari na Kai mishi sai kuyi magana.
“Ni Nace ka Kai Mishi waya ne? An dai cuce ni Wallahi da wannan Auren ni bance Ina so ba Amma an Wani k’ak’aba mini shi tamkar wahayi Kuma ka fad’a wa baba iron bani da Lokacin zuwa yanzu don bana ma pertercout an tura ni can can wata Uwa Duniya ban Kuma San Ranar da zan dawo .
Ya katse wayar shi ya bar Bello da Yi mishi Dariyar mugunta da irin yadda ya Rufe shi da masifa
Suna Zuwa gida ta Bude wayar ta wacce a yau din Sameer ya wuni akan ta Yana Kira Amma kashe Saboda ta Rufe ta Amma yanzu da tazo taji ya karbi Auren Aisha ita da kanta ne ta Kira shi.
Yana Zaune ya na ta d’acin Rai yaji wayar ta sake daukar tsuwwa ya jawo ta da karfi don yayi zaton Bello ne ya Kuma kiran shi ya fada mishi wata Banzar magana inda yayi nufin durawa Bellon Ashariya sai yaga Farida ce take Kira
Da sauri ya dauka Yana Fadin
“Kina gida ne Farida ko kuwa Yaya kukayi da shi Shegen.
“Kar ka Kuma zagar mini miji Sameer. A Hakan kake son na fito na koma gidan ka Ashe dama duk abinda kake fada min karya ne munafunci ne kana Can kana soyayya da wannan gallafirin Aishar Amma kake son na baro Miji na Mai kauna ta na dawo gareka? Wallahi Nayi kaicon Sanin ka Sameer Kuma Wallahi ba zan tab’a dawo gareka ba tunda kana son matar Nan har yau din Ake fad’a min ka Aure ta to ka Rik’e ta Nima na Rik’e mijina kar ka Kuma tuna ka San ni Wallahi Allah ya Isa mugu macuci.
Sai ta Saka mishi kuka Abinda ya tayar da hankalin sa matuka Gaya Domin kuwa duk Duniya kukan Farida shine tashin hankali a gareshi musamman da ya fuskanci inda kukan nata ya nufa na kishi ne Wanda ba zata iya hada shi da kowace mace ba .
“Saurare ni Mana Farida kiji ? Daina kukan please don Allah Yi Shiru nifa Wallahi tallahi ban ce Ina son yarinyar Nan ba Nima fa sai yanzu Bello yake fada min .
“Me ya Hana to kace baka son ta ta nemi Wani? Kuma ni ai ka San ba zan taba iya zama da wata Mai amsa sunan matar ka ba Kuma Wallahi ka cuce ni tunda naji an Daura Maka Aure nake zazzabi kar ka Kuma tuna ka Sanni ka Rik’e matar ka Nima na Rik’e miji na dama don Kai zanyi tunda Kuma ka nuna min Halin ku na Maza ka tafi can ka kyale ni ko tuna ka Sanni kayi wuta bal bal.
“Tsaya kiji Farida.
“Ka Rik’e koman ka Sameer bana son ji ba zan saurare ka ba na Hak’ura da Kai Wallahi Nima ya zama Dole ka barni nayi Rayuwa ta kaima kaje kayi taka .
Ta yanke wayar ta barshi Yana faman fadin tsaya kiji Farida.
Ta Sauke wayar tana kuka bil hakki Wanda take Jin Bak’in cikin na Neman tafiyar Ruwa da Ruhin ta .
K’arar wayar ne ya farkar da ita taga shine yake Kira tayi maza tayi rejected ya sake kira Nan ma tayi rejected. Kira sama da Ashirin tana yankewa karshe ma sai ta kashe wayar Baki Daya don taga zai Dame ta .
Satin ya shige Sameer Bai zo katsina ba inda haj da Anty Asiya suka yanke shawarar tariyar Aisha . Aka Bude gidan Sameer aka Saka Aisha tare da kayan ta har da na garar ta aka SHIGA sauraren zuwan shi
Tunda Farida ta kashe waya Bai Kuma samun ta a waya ba Abinda ya kawowa Ranshi ta Saka shi black list .
Sati kisan Biyar da faruwar Hakan Farida na cike da damuwa Amma Bata yarda Abdullahi ya Gane ba Babu Abinda ya rage ta Dashi soyayya Mai tsayawa a Rai tare da kulawa ta musamman haka ma Dukkan Abinda take so sai dai in Bata fada mishi ba Amma sai ta same shi.
Basma ta kyalkyale da Dariya tana Rik’e ciki. Lawisa ta Dube ta tana fadin
“Kin hada wata muguntar ne Halan?.
“Uhum ai ba banza ba ta Sa nayi Shiru Wani malami na samu jiya jiyan Nan naje wurin shi Kinga Maganin da ya bani yace Hayakin shi Zanyi Ina turarawa suka shaki kamshin sa in Sha Allah Daya zai tsani Daya wata irin tsana da Dole su Rabu Kinga nayi maganin matsala ta dama Saboda ciwo Ake mallakar magani Kuma maganin malamin Nan Wallahi mujjarrab ne tamkar YANKAN WUKA don wacce ta kaini Mata dai Daya Wallahi Mata Tara ta kora daga gidan ta duk kishiyoyin da Mijin ta yake jelen dauko Mata ne shin shegen tamkar anyi mishi wahayin Matan . Na Sha mamaki da ta fada min hakan shine Nima na Roki Arzikin ta Yi min hanyar Ganin malamin Yana can kan tudu to Nima zanje na jaraba idan aka Rabu lawee Yasin har dinner zan hada.
“To Amma ko da Hakan fa sai kin kwantar da Kanki Basma shi yaki Dan zamba ne sai da Dan gari Ake cin Riba kinga inda Hakan ma kikayi ai Babu Mai zargin da Hannun ki a cikin Rabuwar Amma dai ko a haka Farida ta girgiza mata kuka dai Kam ke da kanki Baki San iyakar Wanda kikayi ba don ma Allah ya tsare ki Amma ai da gaki can Asibiti kina bin layin masu hawan jini ko Ciwon zuciya.
Suka kyalkyale da Dariya Basma na Fadin
“Ai kwanciyar aska nayi musu su Duka in da Hankali na ma ya kwanta da har yanzu shegiyar batayi ciki ba shiyasa ma hauka na Bai tashi ba Amma da tayi ciki Kam ai da shiga ukun da zanyi tana da yawa Wallahi don ni kad’ai na San Sirri na .
Lawisa ta Dube ta tana fadin
“To sai kiyi azamar dak’ile wanzar cikin don in kika bari ta fara haihuwa sunan ki sorry don yadda Ake son ta haka ma Ya’yan ta zasu zamo sune gaba da Naki.
“Bama wannan ba lawisa in ta fara da Namiji ko daya tayi ai ni Kuma shikenan mun zama Kai daya da ita.
“To Allah dai ya kyauta Amma fa Aikin Yana nan Amma dai in aka Rabun kin watsa wancan Shirin Wanda zai Kuma tura Miki Wani Bak’in cikin.
“Ai Bama zata haihu ba lawisa ni nake fada Miki hakan .
“A a ke kinji matsalar ki shige makadi da Rawa.
“Shiyasa nace Miki ni kadai nasan Sirri na ke dai bari kome kenan zan sanar da ke Amma yanzu Kam na samo makari in Sha Allah kafin Nan da Rana irin ta yau ta bar Gidan har kayan ma an kwashe.
Farida tana kwance jikin Mai gemu yana tab’a jikin ta wanda yake zafi zauu tun Shekaran jiya take Jin zazzabin Nan ga kasala da take ji Amma dai Bata kawowa Ranta Abinda yake Shirin faruwa ba.
Sai da Suka kwanta a Ranar dare ya Raba zazzabi ya tasar Mata tayi ta sheka Amai haka Abdullahi ya Kwana a kanta washe gari tunda safe ya wuce da ita Asibiti inda Basma Kuma ta Soma turara Hayakin ta Wanda ta gama turare sashin ta kaf kafin ta nufi sashin Farida tana gumbuda Hayakin tana fad’in
“Ai kuwa Uban kuturu ma yayi kad’an Wallahi bare na makaho da ba Gani yake ba in Sha Allah yau dai sai dai a komawa gyatuma a dasa Sabon jawarci don ko ke ko shi sai Daya yaji tamkar ya dannawa Daya WUKA a kirji na ma Fi son shi yaji ya tsane ki don shine Mai Yi kuma sakin Yana Hannun shi .
Ta gama turaren ta fito tana Dariya.
A can Asibiti kuma an gama Duba Farida wacce ciki ne ya bayyana na wata Biyu da sati Daya.
Murnar da Mai gemu yake tamkar Bai tab’a samun haihuwa ba sai Akan Farida. Don haka suka dawo gida Yana fadin Dole ya fidda ta waje ta ga kwararren likita a Duba mishi baby da Kyau .
Suka dawo gida Yana Rungume da Farida wacce amai yake Wahalar wa.
“Babu inda zan fita Farida kina a wannan Halin zan tsaya na tarairaye ki nayi Miki duk abinda kike so yadda muka ji Dadin mu a tare yanzu ma da Laulayin nan ya zo ni da ke ne derling.
Ya Zaunar da ita Yana tambayar me take so a kawo Mata? Tace tea take so Mai Karanfani da citta da lemun tsami.
“Yanzu kuwa bari na je na Samu Basma ta hada Miki shi .
Ya fita da sauri ya samu Basma ta hakimce yace.
“Tashi da Allah Basma hadawa kanwar ki tea Mai Karanfani da citta da lemun tsami yanzu daga Asibiti muke Bata da lafiya Muna zuwa akace ciki ne da ita kinga Rabon Nabeela ta samu Yan kanne shekara Tara ke Baki sake ba Kinga ai Dole mu Taya juna FARIN CIKI.
Wani irin matsiyacin Duka da ya naushi zuciyar ta kadan ya Rage ta fado daga kujerar ta Dube shi tana Fadin
“Ciki fa kace? Ta fada a tsorace.
“Tashi da Allah ki Dora Mata shayin Nan Amai take tayi Bata iya cin komai .
Basma da taji kamar ta watsa mishi Ashar itace ma Mai dafawa matar shi kayan Laulayi? Sai kuma ta tuna TARKON da ta ke fatan ya kama tunda ga Wani garnakakin na ciki ya Kuma bullowa .
Haka ta bawa kanta magana ta shiga kitchen ta hada mishi Ruwan shayin inda tayi ta nadamar da Bata karbo Wani magani da zata Zubawa Faridar a cikin Abinda zata ci ba . Don har Malamin sai da yace zai bata magani ta zuba mata Amma tace Bata da hanyar Bata wani Abu taci sai gashi yau ta Samu wannan Damar Amma Kuma ba Rabo.
Tana Zaune cike da Bak’in ciki tana cizon yatsa da hango Wani katon kalubale da take hangowa.
Bata tashi daga inda take ba ya Kuma dawowa yace tayiwa Farida wainagirar fulawa da manja ya kuma addaba Mata duk da Bak’in cikin da yake dafa zuciyar ta haka ta Mike ta shiga kitchen Yana Kuma tsaye Yana kallon ta Tayi wainar ta bashi ya fice Yana Mata Godiya inda take nadamar shirin da ta Yi da Farida da tana Nan a yadda take na adawa da ita da shi da kanshi ba zai nufo ta da wannan Aikin na Rainin hankali ba.
A Ranar tayiwa Farida girki yafi kala bakwai da anyi wannan zai dawo yace mata tace Bata son wannan kaza take so taimaka kiyi mata Basma. Haka zai Saka ta Gaba Wani Abun ma Yana Taya ta Yin shi har a gama ya dauka ya Kai Mata.
Yana fita Basma ta fashe da kuka tana Fadin
“Yau ni na SHIGA UKU wane irin Bak’in ciki ne wannan ne? Ya zama Dole ta komawa malamin can ta samo maganin da zata ambamawa Farida a.m cikin Abinci a zubar da cikin Kuma a Raba ta da gidan fun yanzu ma kenan Yana ta wannan b’are b’aren Ina ga Kuma cikin ya tsufa ai kuma har wanka cewa Zaiyi sai anyi mata.
Sai dai har a dare Basma bata huta ba tana ta Aikin bautawa Farida sai da tayi bacci ne ta huta shi Kuma Yana Rungume da ita Yana shafa cikin ta.
Da safe Basma ta shirya Mata miyar yakuwa da dafaffiyar fatar Ganda ta Kai mata har sashin ta tana Duba jikin ta tana mata fatan Allah ya Raba lafiya
Ta Cewa Abdullahi zata leka gidan su ta ga mahaifiyar ta yace to Tayi sauri ta dawo don Kar Farida ta nemi Wani Abu bata Nan.
Da haka ta fito Kai tsaye ta wuce wurin Malam da yake Can kan tudun fulani a k’aramar Hukumar b’atagarawa.