Kwanaki bakwai kacal Amma wasila tayi wata irin sauyawa . Farar ta ta Kuma danyacewa Saboda sauyin da ta samu . Tana zaune bakin famfo da Robar man petals tana warware kitson kanta inda dogon gashin kanta ya bayyana ta Soma shafe shi da man petals din tana shafawa inda ta tabbatar da Rashin gyara ba k'aramin taimako yake bayarwa ba wurin kashe mace daga tsaye ba . Ta Dade Rabon ta da shafa petals akan ta in bata manta ba tun yusra na goye sai fa yanzu da taji Lallai sai ta Gyara kanta Sosai ko don ta Kara Samun kudin. . .