Skip to content
Part 9 of 13 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Kwanaki bakwai kacal Amma wasila tayi wata irin sauyawa . Farar ta ta Kuma danyacewa Saboda sauyin da ta samu . Tana zaune bakin famfo da Robar man petals tana warware kitson kanta inda dogon gashin kanta ya bayyana ta Soma shafe shi da man petals din tana shafawa inda ta tabbatar da Rashin gyara ba k’aramin taimako yake bayarwa ba wurin kashe mace daga tsaye ba . Ta Dade Rabon ta da shafa petals akan ta in bata manta ba tun yusra na goye sai fa yanzu da taji Lallai sai ta Gyara kanta Sosai ko don ta Kara Samun kudin da take mayata.

Tayi Mamakin yadda gashin nata ya sauka akan kafadar ta tamkar dai an jawo shi ya Kara tsayi.
Ta Soma taje shi tana mamakin yadda ya koma.

Tana safe gashin da mayuka ne yarinyar da ke kunshin lalle a unguwar wacce ta tura zee zee ta Kira mata ta iso ta Soma Zane Mata Jan lallen a farar fatar kafar ta wacce take cike dam ko Babu lalle Abun kallo ce bare Kuma ta Sha Jan lallen sai ga wasila ta fito tamkar wata matar gwamna.

Yusra ta shigo da kayan filawar da ta aike ta siyowa don Alhajin naira ya bukaci ta Yi mishi boga da snacks har ya tura Mata kudi a account din Dubu Hamsin wai na snacks din ne don haka tayi nufin yagar kudi Sosai a Hannun shi don sai ta gigita Mishi Duniya wacce ko nawa ya nema sai ya bata Shiyasa take ta wannan Aikin kwalliyar wacce zata mayar da kudin da ta kashe har ta samu Riba ma

Yusra ta zuba Mata ido Yana Fadin, “Alkur an mama kin zama Mai kyau duk gashin ki ne haka? Dubi kunshin ki Mama mu Banda mu kunshin?

“In Kun shirya kunshin sai ki karbo kudin wurin Uban ku ni dai ai kin San ba biya muku Zanyi ba in ya shirya sai ya biya ayi muku.

Ta Soma hada Kayan snacks din ta yusra tana ta Binta da ido har ta gama ta kwashe Kayan ta tayi daki tana Kiran wayar Yar Sokoto wata mata da take siyar da kayan Mata irin na D’a A.

Yar Sokoton ta iso gidan tana fadin, “Kai Yaushe Rabon Duniya da ayyaraye wasila Amma sautu aka Baki ba ke ce zaki Siya kiyi amfani da su ba ko? Don na San ke Kam kin gama da.

Ta Zubawa wasila Dake fitowa daga d’aki ido Ganin yadda ta koma kamar wata sarauniya yasa tace…
“Masha Allah wasila ko Mai gidan ya samu Wani Aiki ne ya bar telan?

“Bai bar tela ba kallon da kike min kenan na wata gallafirin Duniya wacce tsiya tayiwa dukan kawo WUKA har kina fadar sautu aka bani ? To ni ce zan Siya ki bani Kaya original real one na Siya na Baki kudin ki in nace ki bani bashi ki tsine min sau Dubu d’ari.

“Allah ya Baki Hak’uri Hajiyar birni bari na koma na dauko Miki original din don gaskiya Wanda nazo dasu tsaka tsaki ne Wanda Mata ke iya biya a yanzu saboda yanayi Amma tunda kin shigo garin Haj ta bari ki Gani na koma gida don Dake nake hada hannu bari ma na tabo Anty suby naji in akwai wasu wurin ta ko Badi Atun bukari tunda duk Muna tare da Masu harkar ai kin Sha Kaya masu kyau Haj ta.

Yar Sokoton ta fice fa sauri ko minti Sha Biyar Bata Rufa ba sai gata ta dawo da kayan masu kyau tana nunawa wasila da irin amfanin da sukewa Wanda yasha da Kuma Abinda suke k’arawa.

Wasila ta zabi masu Kyau ta biya Yar Sokoton kud’in ta Wanda Yar Sokoton take ta mamaki don taji kudi masu kauri Wanda Bata zaci fitar su daga wasilar ba. Ta nuna Mata yadda Ake amfani Dasu da na Sha da na matsawa da tsuguno. Wasila tace tana fadin idan taga yadda take so zata Kuma Kiran ta. Sukayi sallama da Yar Sokoton ta wuce.

Tun a Nan wasila ta Soma Shan magungunan da Wanda Ake matsawa da Wanda Ake tsuguno duk ta Yi ita da kanta Taji sauyin a tare da ita Wanda ta tabbatar kayan masu kyau ne.

Tuni ta sulla wanka tana fitowa ta Kira wayar Alhajin naira tace ga snacks din sa zai Aiko a karba mishi ne?

Yayi murmushi Yana Fadin, “Taimake ni Mana kizo na ganki dama Ina son haduwar mu don kwana Nan kin barni da Zullumi nace ko dai dama kin San Abinda kika hada min ne?

Tayi murmushi tana fadin

“Gaskiya ba zaka ganni ba don ni Kam kudi nake so Wallahi to Ina da wurin zuwa sai dai zan bar Sakon snacks din ka a gida sai ka Aiko ka Amsa.

“Zan siye Lokacin ki gaba daya Yan Mata ko ya Kai nawa kiyi mishi tsadar tsiya na biya ai Ina da kudin siyen komai Kika ce don bar ni a inda Zan barki Ba Dole na Nemo ki Yan Mata ke dai fada min inda zan same ki.

“Ina da wurin zuwa yau din da kayi hak’uri dai ko zuwa jibi ne zan same ka.

“Shin nawa aka Baki ne da Zaki haramta min wannan Daren? Ko nawa kika karba zan linka na sake linkawa na Baki in dai kin dauke ni da muhimancin da kika fada to Gani Nan tafe daidai sabon titi kusa da Sauki venture sai ki fito mu Hadu.

“To ka bani minti talatin don Ina Shiri ne.

“Na Kara Miki Wani talatin din girman ki ne .

Ya fada Yana sakar Mata sumba da wani irin Salo na Yan bariki.

Tana cikin yarfa kwalliyar ne Kuma ishaq ya shigo Gidan inda taji wani Abu Mai kama da fargaba Amma da yake ta Soma siyar da Imanin ta wa wulakantacciyar Riba sai ta maza taci Gaba da Shirin ta inda ya shigo D’akin Yana aje Mata shinkafar da ya iso da ita sai ya iske yadda matar tashi ta zama tamkar wacce aka Saka inji ya wanke ta.

Ya zuba Mata ido Yana kallon ta tamkar ba ita ba. Abinda ya Soma ji ne yasa ya fice Daga d’akin don Rabon Da ya ga wasila a D’akin shi ko daidai da gyaran shimfidar sa ba zai iya tunawa ba bare ace tazo turaka . Da ya nuna mata kuskuren ta ma yasha mamakin Abinda ya fito bakin ta don haka sai ya zuba Mata ido Bai Kuma Kiran ta turakar tashi ba. Ita Kuma Bata Kuma Zuwa ba ko da wasa don haka a yanzu da ya Ganta cikin wannan kwalliyar sai wani Abu ya tab’a zuciyar shi Amma ya maze yayi ta azumin shi na litinin da alhamis.

Ta gama Shirin ta ta zurma hijabin ta ta fita tana Fada mishi zata je Asibiti wai an kwantar da murja kanwar ta a Asibiti.

Bata tsaya jiran Amsar shi ta Amincewa ko Rashin Amincewar ba ta fice da kayan snacks din ta inda ta nufi Bakin sauki inda ta iske motar Alhajin naira ta Kuma shuge ya Ja suka bar wurin.

Hotel ya dire ta Yana kare Mata kallo don hakikatan Bai taba kare mata kallo irin yau da take sauke Dan kwallin ta dogon gashin ta Yana bayyana ba . Lallen da ya kwanta bisa jar fatar ta yayi matukar tsuma shi jikin shi har kyarma yake ya Rungume ta Yana Bata hot kiss inda kamshin jikin ta yake sauka hancin shi ya Kuma gigicewa Yana sakin sambatu.

Bata Sha mamaki ba sai da taga yadda wassn ya Kare Domin kuwa Abinda Bai tab’a Yi Mata ba yayi a wanan Ranar don haka kudin da ta karba Kam ita kanta tayi mamaki Domin kuwa Dubu d’ari biyar ya Saka mata account ya Kuma Bata Dalar amurka a ambulan Yana ta mata magiya akan ta kwana Amma tace ba zata kwana ba saboda tana da Miji don haka karfe goma ya sauke ta a sauki venture ya wuce inda yake Jin wasila ta tsaya mishi a Rai ya kasaa Manta wannan dare nasu.

Ta shigo Gidan sagir Yana shirin Rufe kofar inda Sukayi ido Hudu da yaron Wanda take Jin ya Faye Saka ido Kuma tamkar Mai bibiyar ta Amma dai ta wuce zuwa d’aki Shima ya bita da wani irin kallo kafin ya Rufe kofar ya wuce zuwa D’akin shi Amma Kuma sai ya juyo zuwa D’akin Uwar tashi wasila wacce ta fito da Dalar amurka guda biyar tana kallon su sai kawai taga sagir ya shigo ya Kuma ga kudin a hannun ta don haka batayi yunkurin boye su ba.

“Mama Yaya Mai jikin?.

Ya tambaya ta gimtse fuska tana Fadin

“Da sauki.

“Amma mama naje gidan Anty mirja tace min Babu Wanda aka Kai Asibiti Amma Abban mu yace kince wai Anty murja aka kwantar Asibiti Kuma naje tace Baki zo ba.

“Shi ya turo ka kenan kazo ka tutsiye ni ko kuwa?

“A a ba shi ya turo ni ba mama kin fara sauyawa gaskiya Kuma Dubi fa kudin da suke hannun ki na amurka ne.

Gaban yayi masifar Sarawa Jin yaron Yana Fadin ta fara sauyawa.

“To yanzu me kake so ayi? Bai ce mata komai ba ya fito ya wuce D’akin shi Yana Jin zafin karyar da tayi har ya dawo ya fadawa Uban nasu yadda Anty murja ta fad’a mishi ya Kuma zo ya fadawa ishaq cewa Babu Wanda yake Asibiti da ya San ba haka abin yake ba da Bai zo ya tona Mata Asiri ba . Sagir ya jima Baiyi bacci ba Yana Bak’in cikin karyar da mahaifiyar tashi ta girba Wanda Hakan ya nuna Abinda tayi babu gaskiya a ciki.

Wasila tana Rik’e da kud’in ta ta kasa zama bare ta kwanta . Ta furgita matuka Gaya da jin sagir Yana tuhumar ta . Kuma yanzu da wane idon Zata dubi ishaq da ta gallawa karya? Ga Kuma girmen ta da zai zube a idon Anty murja da tayiwa karya.

Sai ya zama duk Wani karsashi da tazo dashi da kuma murnar Samun kudin Nan duk ta dushe sai tarin fargaba da Zullumi don ta tabbatar Da sai Anty murja ta fadawa Goggo wannan maganar.

Haka ta kwana cike da tsoro da shakka .

Washe gari sagir ya fito da Shirin Zuwa gareji inda ya Tara’s da wasila a Bakin murhun gawayi kurfoti tana Dora girki ya Duka Yana Gaishe ta inda yaga yadda ta koma.

Ya zuba Mata ido Yana kallon ta har ta juyo taga idon yaron akan ta.

Ta kadu matuka Gaya da ganin yaron ya kafe ta Ido kafin ya Mike jiki a sanyaye ya fice Bai ce mata ya tafi ba.

Sai a sannan take Jin Lallai tana da kalubale ta kowace fuska tunda ta zama Uwar su Kuma matar Wani dangin wasu duk Wanda ya San Halin da take ciki kuwa Dole ta fuskanci matsala Amma Kuma Bata fa Jin akwai Wanda ya Isa ya taka Mata Burki don zuciyar ta ta gama bushewa Bata Jin kamar zata bari.

ISHAQ Bai ce mata komai ba ya fice don Rabon da ta gaishe shi ba zai iya tunawa ba don Haka sai in shi yaso yace Mata kun tashi lafiya? In kuwa baice ba itama ba zata iya gaishe shi Ba in kaji tayi magana sai in Bata ga ya ce gashi ba yanzu ne zata tashi tana masifa tana maganganu da son ta keta shi.

Da fitar ishaq Bai Zame ko Ina ba sai gidan Anty murja wacce ta tarbe shi suna gaisawa tana Fadin
“Wai me yake faruwa ne ishaq? Jiya sagir yazo yana jajanta min Mai jiki da nace waye ba lafiyar sai yace kace mishi wasila tace Maka ni aka kwantar Asibiti.

“Yanzu ma Abinda Nazo ji kenan Anty don ni kaina na kwana cike da Rudani shin ko ba ke murjar take nufi ba?

“To ai bamu da wata murja sai ni kad’ai sai dai in a can cikin kawayen ta take da wata Amma Kawa ta Isa ayi Mata wannan sadaukarwar? To a can ta kwana ko kuwa? Ta tambaya tana Jiran Amsar shi.

“Bata kwana ba Amma dai sai goma ta dawo.

Ya Mike Yana yiwa murja sallama ya wuce ya bar ta cike da mamaki inda ta Mike tana Fadin

“Bari na Isa gidan nata naji wace murjar ce aka kwantar Asibiti?

Wayar wasila ce ke ta burari inda taga Alhajin naira ne yake Kiran ta Amma ta ki dauka don a Rude take matuka Gaya akan yaron can sagir da Kuma Shirun ishaq akan tambayar ta wace murja ta je Asibiti wurin ta?

Ta kasa cin Abincin da yake Gaban ta inda yusra ta dauko wayar tana Fadin,

“Mama yaushe kika siyi waya Mai shafa shafa?

Ta juyo da sauri ta fige wayar tana Fadin

“Lokacin da Uban ki yake bacci Bai farka ba .

Yusra tayi shiru tana cin Abincin ta ita da Zainab Bata Kuma magana ba don ta San in ta Kuma wata magana zata ji saukar Duka.

Anty murja tayi sallama ta shigo gaban wasila ya Fadi ta amsa tana Fadin

“Wai Anty murja Halan sun tayar Miki da Hankali ne ? ..

“To ai Dole hankali na ya tashi ance wai an kwantar dani Asibiti.

Ta fada tana kallon yadda wasila take Wani sheki da walwali.

“Ke kuwa wace irin daular kika samu ne haka kika danyace?

Wasila tayi murmushi tana Fadin

“Wani magani ne Ake siyarwa wurin Yar Sokoto Nima Gani nake kamar wata Haj

Suka gaisa murja na Fadin.

“Wai wace murjar ce Babu lafiya? ISHAQ yaje dazu Kuma juya ma sagir yazo.

“Wata ce fa nan a bayan layin mu nace zan Dubo a Asibiti Ashe har sun ishe ki da jaje.

“To ai Dole Nima Kuma na so na San wacece haka?

Wayar wasila ta Kuma daukar tsuwwa inda murja tabi wayar da Kallo Amma wasila Bata iya dauka ba inda akayi ta Kira Babu kakkautawa murja na Fadin.

“Wai ba Kira ne Ake a wayar Nan ba?

“Bana son amsa Kiran ne don ban San me za ace ba don ni tsoron amsa kiran bakuwar lamba nake tunda aka ce ana zuk’e jinin mutane.

“Amma dai wayar nan tayi kyau yanzu kaji kudi nawa kenan?

Cewar murja da take kallon wasila wacce take a tsarge don taga sai Binta da ido murja take tana kallon lass din da ke jikin ta da Kuma kunshin ta Wanda ya nuna tsadar shi.

“Ban San kudin ta ba Nima aro aka bani a gidan wannan murjar ta bayan layin mu jiya na Aro ta don na Kira ki don naji ance anzo gidan ki ance bake bace nazo wurin ki a Asibiti.

Yadda take Maganar ne ya nunawa Anty murja Wani Abu don taga sai kame kame take Kuma wannan Kiran da Ake Mata bayan gangami da Labari don haka jiki a sanyaye Anty murja ta Mike tana Fadin

“Bari na koma tunda dai naji kan Zancen Allah ya bamu Alheri.

Wasila ta biyo bayan ta tana mata Rakiya sukayi sallama tana jin Dadin rufuwar wannan Asirin.

<< Tana Kasa Tana Dabo 8Tana Kasa Tana Dabo 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×