Kaman a rikice Alhaji Madu ya fito daga cikin ɗakin na sa ya nufi waje yana kiran sunan Man da Mane. Amma ina har sun gama aikin da ya basu sun bar gidan. Hakan yasa ya koma ciki da gudu ya ɗauki waya ya shiga neman layin su. Kira ɗaya Man ya ɗaga. Cikin rawar murya ya ce "Man yarinyar nan da na ce ku kashe ta, to ku kawo mini ita a raye, kar ku bari komai ya same ta, ko ƙwarzane kar ya taɓa ta". Man ya amsa da cewar yadda kace haka za'ayi you are excellence. . .
