Skip to content
Part 10 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ko a labarai, abubuwan rashin jin dadi duhun dare suke biyowa

A zahiri, mutanen da suke neman tsarin daga abubuwan da suke faruwa a cikin duhun dare da kuma wanda zasu iya faruwa sun ninka wanda suke neman kariya da rana, a cikin haske, hasken rana

Hasken da yanzun daya daki fuskarta ne, dumin shi ya ratsata take jin yaudarar da take cikin shi, da kuma radar da yakeyiwa mutane irinta na cewar sun tsira daga duk wani nau’i na abinki in dai suna cikin shi

Menene zai sameta da rana tsakiya haka? Balle kuma ayi maganar waye…

Takardar da take hannunta na dama take juyawa, takarda ce, falle daya, ko littafine gabaki dayan shi bai kamata yayi mata nauyin da takeji ba yanzun

“Ina zuwa…”

Yace mata bayan ya zame jikinshi daga nata, ya barta a kwance tana tunanin doguwar hanyar da a wani bigire cikin tafiyar ta yanke tsammanin zasu zo inda suke yau, ita har aka gama hotunan nan jiya, su Tahir suka fita daga gidan. Fa’iza ta kamata suka koma daki. Jinta takeyi sama-sama, hannunta kuwa ta kasa daina jin shatin na Tahir a cikinsu. A tsakanin nasihar da aka dingayi mata lokacin da akazo daukarta da kuma kukan da takeyi, zata tuna ta rike Abida, tayi mata rikon da duk kokarin su Anty Talatu da Amira suka kasa bambareta sai da Abida ta dafa kanta tace mata

“Kije su kaiki gidanki Sa’adatu, Allah yasa ki shiga a cikin sa’a, Allah kuma ya kareki daga duk wani sharri yasa muku albarka a zamanku…”

Tukunna ta saketa, ko da bata ga fuskar Abida ba, saboda tayi saurin juyawa, taji alamar rauni a muryarta, tana da karfin zuciya ta sani. Duk a cikin yaran nata, bikin Nabila ne kawai taga hawayenta, shima kusan duk wanda yake wajen sanda za’a dauki Nabila saida ta saka shi kuka saboda yanda ta rike Abida tana cewa ta yafe mata kamar wadda za’a kai kabari a maimakon gidan aure. Ta san yace mata ‘yan kaba ya kama haya, har ta dinga hasashen nisan ‘yan kaba saboda ta taba zuwa sau daya. Taso ta tambaye shi dalilin da zaisa ya tafi har ‘yan kaba, bayan ga unguwanni nan kurkusa da zai iya kama musu, sai bata tambaya ba.

Abu mai muhimmancin shine zata kasance tare dashi, bayan duk abubuwan da suka faru, a bakin Fa’iza take jin gidanta yayi kyau sosai, daki biyune da bandaki a tsakar gidan sai karamin kitchen. Gabaki daya mamakin kanta takeyi, yanda jikinta yake a mace, da kuma yanda take jin kamar ita da Tahir basu da rabon zama. Ita da take ganin bata da dalilin yin kuka in za’a kaita, sai dai tayi na ganin ido da gudun surutu, sai gashi har motar da aka dauketa a ciki ta tsaya, aka fito da ita kuka takeyi kamar numfashinta zai dauke, kuka takeyi da yasa ko hanya bata gani, kafarta kawai take dagawa tana barin Anty Talatu da take rike da ita yi mata jagora, ta sauke kafarta ta haggu kenan, taji wani abu ya tsirga mata, abinda kafin ma ta samu damar tantance meye taji an fisgota baya.

“Anty batayi addu’a ba…”

Ta tsinkayi muryar Nabila, kafin tace mata.

“Ki saka kafarki ta dama da neman tsari daga shaidan da kuma Bismillah, saiki karanta kursiyyu…”

A zuciyarta tayi abinda Nabilar ta umarceta dayi, saboda ta kasa motsa labbanta da sukayi mata wani irin nauyi, ga ciwon kai daya dirar mata lokaci daya. Duk wata gujumniya da akayi bayan nan bata fahimta sosai.

“Kinga fuskarki kuwa?”

Fa’iza tace mata,

“Kaina kamar zai rabe biyu wallahi, ni kamar zazzabi ma nakeji.”

Fa’izar ce ta bata panadol extra, tana fada mata itama jiya saida ta hadiya, da safe ma haka saboda ciwon jikin da ya saka mata zazzabi. Haka ta sha, kwanciya taso yi, aka hanata, ana cewa isha’i ta kusa, ta tashi tayi alwala, tayi sallah a kara gyara mata kwalliyarta. Haka kuwa akayi din, aka kara feshe dakin da turaruka ga kuma na wuta da aka kunna. Ita kanta sai ta fara sauke ajiyar zuciya da bata da alaka da kukan da tayi. Kamshin daya karade dakin mai sanyi ya taimaka wajen sanyaya mata jikinta, wata kasala ta daban ta saukar mata. Amira ce tace babu wani siyen bakin da za’a tsaya yi tunda Fa’iza ce ita kadai, da kanta ta kira Tahir tace su taho, su za’a juya dasu. Sai Sa’adatu taji bugun zuciyarta daya daidaita ya kara hargitsewa, ta juyo Tahir yana musu sallama a tsakar gida, kafin wani irin shiru ya maye gurbin sawayensu.

Sai kuma alamar buga kofa, sannan takun tafiyar Tahir da zata rantse ta kara rantsewa zuciyarta ta fita daga kirjinta ta koma karkashin sawayen shi, har lokacin daya karaso dakin da sallama, akan zuciyarta yake tsaye da kafafuwan shi.

“Sa’adan Tahir…”

Ya kira da wani irin taushin muryar da yayiwa zuciyarta jagorar komawa mazauninta kafin ta narke ta zama ruwa, takalman shi ya cire yana shiga cikin dakin sosai, ya ajiye ledar da take hannun shi kan drawer din gefen gadon. Kafin ya zauna a gefen gadon yana sauke numfashi, ya mika hannu ya daga mayafin da aka rufeta dashi, kanta a duke yake, amman tanajin idanuwanshi na yawo a kanta.

“Kina da alwala?”

Kai ta daga mishi, saiya mike, tana jinshi yana ta kai kawo, kafin yazo yace mata ta tashi suyi sallah, suna idarwa ya juya ya dafa kanta da hannunshi na dama, tasan addu’ar da take sunna mai karfi yake karantawa, daya kama nata hannun ya dora a nashi kan, itama addu’ar ta maimaita tana jinta kamar akan iska. Shiya kama hijabin da batayi musu wajen barin shi ya cire mata ba, ya mike ya linke hijabin yana mayar da ita inda ya ganta, ya kuma dauko ledar daya shigo da ita. Kamshin naman kazar da yaji kayan hadi ya daki hancinta, sai dai yau duk soyayyarta da kaza ta neme shi ta rasa, da Tahir ya matsa mata, dakyar ta iya cin kadan a wanda yake rabawa da kashin yana ajiye mata tsokar, sai dai ta sha madarar daya cika mata kofin da yaje ya dauko a kitchen. Fiye da rabi tasha, tunda duk kokarin Fa’iza na ganin taci wani abu a yinin ranar yabi ruwa.

Shiya kama hannunta ya goge mata maikon da tissue din da aka nado cokullan wasu robobi guda biyu da batasan meye a ciki ba, dan ko budesu basuyi ba, sai kuma ya kama hannun nata kamar mai nazarin zanen lallen da suka sha, kafin ya daga hannun yana dora labbanshi akai ya sumbata hadi da sauke numfashi yana saka tsikar jikinta tashi.

“Kinga tun da na fito daga masallaci yau nake raina larabcin da nake yiwa Bash burgar inaji…bayan hamdala na kasa dora wasu kalmomi da zan kara amfani dasu wajen godewa Allah…”

Murmushi taji ya kwace mata

“To kayi da hausa mana.”

Kai ya girgiza a hankali.

“Ai mamaki nakeyi, yanzun dana ganki kuma hausar ma neman kwacemun takeyi.”

Yanda yayi maganar da dukkan zuciyarshi ne ya sakata dariya. Sakin hannunta yayi yana mikewa.

“Subhanallahi…”

Ta tsinci kanta da fadi zuciyarta na wata irin bugawa ganin kamar zai yanke jiki ya fadi, badon taimakon wardrobe din daya dafa ba, babu abinda zai hanashi faduwa, a hankali ya zauna gefen gado yana dafe kanshi, ai Sa’adatu ta manta da wata kunya ma, bata san ta dafashi tana jera masa sannu ba.

“Kinga tun dazun nakejin jiri fa, kuma nasan harda gujumniya da kuma rashin wadataccen bacci.”

Duk bayanin shi ba gamsar da ita yayi ba, fuskar shi take kallo tana son nemo gaskiyar abinda yake damunshi da kanta.

“Sa’adatu”

Ya kira yana riko hannayenta ya dan matsa.

“Gajiya ce kawai…”

Kai ta dan daga masa, amman zuciyarta taki samun natsuwa.

“Ka zauna, karka kara tashi, idan wani abinne ka fadamun in dauko maka.”Murmushi yayi.

“Idan kuma wani abin zanyi fa?”

Bata kawo komai a ranta ba tayi saurin amsawa da

“Sai inyi maka.”

Murmushin shi ya kara fadadawa.

“Ruwa nake son watsawa.”

Saita zame hannuwanta da yake rike dasu tana furta,

“Inalillahi…”

Dariya yayi mai sauti, ganin har tazara ta bayar a tsakaninsu ta hanyar matsawa. Wannan karin a hankali ya mike ya fice daga dakin. Saita koma kan gado ta zauna fuskarta dauke da murmushi. Ganin ya dade ya sa ta kwanta, daya shigo, wayar shi ya fara nema ya kunna fitilar jiki, sannan ya kashe kwan dakin.

“Ko zakiyi wankan ne kema?”

Kai ta girgiza kamar yana ganinta, sai da aka sa ta kara wanka kafin ta sake kaya a kawota. Ruwane mai dumi sosai, duk kuwa da turarukan da aka zuba a ciki. Taji dadin wankan, dan ta gasa jikinta da yake ciwo, da fitilar wayar yayi amfani yanata hidimar shi cikin dakin, saida ya hau kan gadon ta dayan bangaren tukunna ya mika mata wata riga.

“Ki tashi ki rage kayan jikinki…”

Da yaji ta karba, saiya kife wayar shi, duhu ya maye gurbin hasken, shiya bata kwarin gwiwar lalube ta sauke daga kan gadon ta sake kayanta zuwa rigar a cikin dakin, ta koma kan gadon, in dai Tahir ya saurara, tabbas zaiji bugun zuciyarta, dan ita tanajin shi cikin kunnuwanta. Sai ya kara tsananta lokacin daya matso yana rikota jikinshi.

“Alhamdulillah…”

Yake ta furtawa kasan numfashin shi har saida ta tsinci kanta da fara maimaitawa itama.

“Kiyi bacci yau, ki huce gajiya, shine abinda ya kamata, ni da zuciyata kiyi mana uzuri Sa’adan Tahir, ba zan iya wannan hakurin ba…”

Kalaman shi da suka samu waje suka zauna mata, suka zama akalarsu a wannan daren da ta dauka yana daya daga cikin dararen da ba babu wani abu da zai danne mata girman shi, shisa ta gyara kwanciya, Tahir kuma ya kara gyara mata kwanciya a jikinshi, yana furta mata kalaman da suka sakata lumshe idanuwanta, tanajin da su kadai ya gama biyanta duk wata jarumta data nuna masa. Karshen abinda taji kafin bacci mai nauyi ya dauketa shine addu’ar daya tofa musu. Kamar ya kamata ace ta gane safiyar lahadin zata girgiza duniyarta ne daga lokacin da ta bude idanuwa, taga alamar haske ta cikin labulen kofar dakin, kuma ta mike,

“Yaa Tahir…”

Da ta fadi na maye gurbin addu’ar tashi daga baccin daya kamata ta yi.”Yaa Tahir mun makara.”

Ta sake fadi ganin da gaske haskene take gani na wayewar gari, daya bude idanuwa shima, tashi yayi. Ya kalleta, yana sa wani irin sanyi ratsata kamar an zuba mata ruwan kankara, yanayine da bata tabajin irinshi ba. Saboda kallo ne yakeyi mata kamar bai santa ba, kallonta yakeyi kamar yana tantamar abinda takeyi a daki daya, gado daya tare dashi, kafin ya sauka daga gadon kamar wanda aka zaburar. Ya fice daga dakin cikin hanzari, jikinta takeji yayi mata nauyi. Ta manta wani abu mai girma ya faru da ita, saida ta sako kafafuwanta daga kan gadon ta mike tsaye. Sanda ta kara kokartawa ta mike ta fita daga dakin, bata ga Tahir ba. Saita shiga kitchen, ta jinjina flask din data gani a kasa, ta kuwa yi sa’a taji shi da ruwa a ciki, dan Tahir ya dafa musu ruwan zafin daren jiya.

Data fito daga bayin,taji dama-dama. Ta wuce daki tayi sallah, data dauki wayarta, ta duba sai taga takwas da kwata, tunda take makara sallah, bata taba makara irin haka ba, kuma harda Tahir da yake zama alarm dinta ma a lokutta da yawa, komawa tayi ta kwanta tana mamakin inda yaje, tunda ai da kunya ace masallaci ya fita yin sallah a wannan lokacin. Da yake akwai gajiya da kuma bashin bacci akanta, bata san sanda ya dauketa ba, cike da wasu hargitsattsun mafarkai, da har a cikin baccin fatan farkawa takeyi dan ta guje musu, amman ta kasa. A cikin mafarkan ne tayi wani inda ta gansu tsaye ita da Tahir, yayi taku biyu baya, ta bude baki, kafin ta furta wani abu ya fada wani katon rami da takeson ce masa yana bayanshi, kafin ma tayi ihu wata iska ta taso tana yin baya da ita, ta fada wani ramin da batasan da shi ba, zurfin shi na shanye sautin muryarta.

“Tashi”

Taji an fadi hadi da girgizata, ta kuwa bude hadi da fisgar numfashi kamar a lokacin ne ta fada ramin. Tahir ta gani tsaye a kanta, yanayin fuskarshi yasa duk wani bacci barinta, lokaci daya taji ta wartsake.

“Yaa Tahir”

Ta kira tana samun natsuwar godewa Allah da yake a gabanta, ba’a cikin ramin data gani a mafarkinta ba.

“Tashi…”

Ya sake maimaitawa muryarshi na fitowa daga can kasan makoshi, sai kuwa ta tashi, da kanshi ya zagaya ya dauko mata hijabinta yana mika mata. Mamakin yanayin shine yasa ta karbi hijabin ta saka a jikinta, saiya saka hannu a aljihun jallabiyar da take jikinshi ya zaro takarda ya mika mata, haka kawai taji zuciyarta tayi kundumbala a cikin kirjinta kafin ta zauna mata a jirgice.

“Takardar meye?”

Tayi mamakin kanta data iya kwato azancin yi masa wannan maganar a yanayin daya dirar mata lokaci daya.

“Ki karba.”

Har yanzun, muryar shi daga kasan makoshi take fitowa, cikin wani irin sanyi da taji ya lullubeta kamar bargo.

“Ki karba Sa’adatu…”

Sanyin muryar, da yanayinshi duka taji bataso, har inda za’a bata zabi tsakanin saurarenshi da komawa baccin da bata jima da gama godewa Allah daya kawo mata karshen shi ba, zata zabi komawa baccin.

“Yaa Tahir…”

Hannunta ya kamo ya saka mata takardar a ciki yana kuma dagota ta mike tsaye, dube-dube yakeyi yaga wayarta a ajiye, ya dauko itama ya saka mata a hannu kafin ya fara janta.

“Yaa Tahir…”

Ta sake kira duk wasu kalamai na bace mata, janta yayi har suka fita daga dakin kafin ya saketa yana kallonta da wannan yanayin da yake kara mata firgici da rudanin da take ciki.

“Bana son ganinki ne Sa’adatu, ki tafi gida.”

Cikin rawar murya tace,

“In tafi gida?”

Kai ya jinjina mata.

“Sakinki nayi”

Tasan idanuwanta akanshi suke lokacin da kalaman suka dira kunnuwanta, ta daina ganin shine, ya bace mata a cikin hasken da taga ya gilma mata, kafin duk wani abu da yake samar da tunanina tare da ita ya tsaya cak, kanta kamar an zuba ruwa an wanko shi haka take jinshi. Taji kafafuwanta sun motsane saboda takalmin da bata dashi, ta kuma tabbatar da tafiya takeyi lokacin data fita daga gidan, tsakuwoyin data taka suka ratsa tafin kafafuwanta. Sai kuma hasken rana daya daki fuskarta, ya sata daga kai kafin ta sauke cikin hanzari, saita kalli hannunta da takejin yayi mata nauyi kamar wadda take dauke da dutse ba fallen takarda ba, taci gaba da tafiya ta kuma sake tsayawa cikin fitar hayyaci, kafin ta dinga jin wani sauti na kaiwa kunnenta, hakan ya faru fiye da sau biyar kafin ta gane daga wayar hannunta yake fitowa, dagawa tayi ta kara a kunnenta.

“Kanwata…”

Muryar Abdallah ta daki kunnenta, sai taji wata sheshheka ta taso daga kasan zuciyarta, numfashinta yana wani irin sama, amman ko kusa bata jin alamar kuka

“Sa’adatu”

Abdallah ya kira cikin tashin hankali, da alama yaji yanda take fisgar numfashi.

“Lafiya? Menene? Meya faru?”

Ya jera mata tambayoyin lokaci daya yana jin wani abu yana kaiwa zuciyarshi duka. Yanda duk ya dinga addu’a, da sadaka na neman Allah ya tabbatar da auren idan alkhairi ne, saboda yanda yaga Sa’adatu ta dauki son duniya ta dorawa Tahir, zuciyarshi taki natsuwa. A masallaci ma da yaji Amin din jama’a tayi amsa kuwwa na shaidar an kulle Sa’adatu da Tahir waje daya sai yaji wani yanayi kamar na rashin natsuwa ya sake saukar masa. Lokacin da za’a tafi da ita yana kan layin tsaye, har motocin suka wuce.

“Allah ka karemun Kanwata ka tabbatar mata da alkhairin da yake cikin wannan auren.”

Ya tsinci kanshi da furtawa a hankali, tun da aka tsayar da lokacin auren, duk wani kira da yayiwa Asabe bata daga ba, Nana ma tace masa bata daga kiranta, da alama fushi ta dauka dasu, da alama kuma auren bai kwanta mata ba har yanzun. Ya san wacece Asabe, ya san ta dinga wankar kafa tana zuwa gidan Tahir din kamar yanda suka sami labari Hajiya na yiwa Abida kafin a auro Asaben, ba wahala zaiyi mata ba. Ko sallar asubar ranar ma, mugun mafarkin da yayi akan auren Sa’adatun ne abinda ya tashe shi, yayi tunanin duniya kuma ya kasa tuna abinda ya faru a mafarkin, ya dai san ba mai kyau bane ba. Shisa ya jima zaune a masallaci yana yi mata addu’a, kusan shine na karshen fita ma. Shi baima so zamansu a Kano ba, dan dai nan din akayi posting din Tahir, yaso a tura shi nesa, yanda ganinsu zaiyiwa Asabe wahala.

Kamata yayi ace ya tafi wajen aiki tunda lahadi ce, babu makaranta, amman jikinshi yayi masa nauyi sosai, saiya koma daki ya kwanta, lokaci zuwa lokaci yake duba agogo, saida yaga sha daya da rabi tayi tukunna ya fara neman lambar Sa’adatu, ko daya jera mata kira hudu bata daga ba, saiya kasa hakura, so yake yaji tana lafiya ko zai samu natsuwa. Koko da kosan da Abida ta saka shi dauka ma, dakyar ya iyacin kosai biyu, ya ajiye, duk komai baya masa dadi.

“Alhamdulillah…”

Ya furta cikin zuciyarshi da ta daga wayar, sai kuma ya ji tana fitar da numfashi kamar wadda aka shake.

“Sa’adatu?”

Ya sake kira jin bata amsa tambayoyin da ya jera mata ba, sai kokawa da takeyi da numfashinta, idan kuma kunnen shi yaji masa dai-dai, karar mota yaji ko machine, bai gama tantancewa ba ya sakejin karar abin hawa da ta saka shi fita daga dakin ya zira takalman shi, wayar na manne da kunnenshi har lokacin ya fita daga gidan.

“Kina ina yanzun? Kina jina? Kanwata karar abin hawa nakeji, kiyi mun magana dan Allah, kina ina? Me yake faruwa? Gani nan na fito nima, kiyi mun magana…”

Ya karasa muryarshi na sauka kasa saboda tashin hankali, ko dai Asabe ce taje gidan ta korota? Ko tayi musu wani abin?

“Sa’adatu…”

A tsakanin wannan numfarfashin da takeyi ne ta kwato.

“Nima ban sani ba.”

Nashi numfashin ne yake son yin anko da nata wajen fita.

“Kina ina?”

Ya tambaya a hankali.

“Waje…akwai titi…akwai makaranta.”

Kai yake jinjinawa kamar tana ganinshi.

“Ki matsa daga wajen titin, kina jina? Ki matsa, ki tsaya a wajen karkije ko ina, gani nan zuwa.”

Gani yake kamar mai mashin din da ya hau baya sauri, kamar ya karba yayi tukin da kanshi. Makarantu biyu ne ya kula dasu a unguwar duka akan titi, lokacin da Tahir yasa shi nemo mai fenti sukaje akayi, saiya tsaya a ta farkon ya zaro dari biyar daga aljihun shi yana mikawa mai mashin din yayi gaba, dan ba ciniki sukayi ba. Dube-dube yake yana son hangota, a hankali yake takawa yana kuma dubawa bai ga ko alamarta ba, saiya kara sauri dan ya tabbatar tana dayan wajen, kuma akwai yar tafiya. Tun daga tsallake ya hangota a tsaye, Allah ne ya kareshi, baiko duba ba ya afkawa titin cike da son cimmata, shisa bai damu da mai adaidaita sahun daya watsa masa zagi ba.

“Sa’adatu…”

Ya furta yana karasawa ya kama hannunta, duka fuskarta yake ganin tayi masa wani irin fayau, idanuwanta sunyi haske kamar wadda ta tashi ciwo.

“Menene? Me kikeyi anan?”

Idanuwan kuwa ta saka cikin nashi.

“Yaa Tahir yace ya sakeni.”

Ta jera kalaman kamar tana fadawa kantane fiye da yanda take fada masa, kafin ta mika masa takardar hannunta.”Ya bani wannan.”

Karba yayi yana tantamar natsuwar Sa’adatu, saiya warware ninkin takardar mai dauke da rubutu layi daya, ya karanta, saiya sake karantawa, yasan Hausa ce yake karantawa, amman da wani yare daban kalmomin suke karasawa cikin kanshi, ma’anarsu na masa wahalar fahimta, saiya kara karantawa, ya kalli Sa’adatu da take kallonshi, lokaci daya ma’anar kalmomin suka dake shi, wani jiri ya kawo masa mamaya, sai ya riko hannun Sa’adatu yana dumtsawa.

“Inalillahi wa ina ilaihi rajiun.”

Ya furta a cikin zuciyar shi cike da sallamawa da mika kai ga Ubangiji, cike kuma da neman karfin tsayuwa da kafafuwan shi.

Saboda faduwa bata shi bace a wannan bigiren

Sa’adatu ce zata fadi, idan ya dagata, saiya dora kafafuwanta akan nashi su tsaya tare harta sake koyon tsayawa da nata…

<< Tsakaninmu 9Tsakaninmu 11 >>

1 thought on “Tsakaninmu 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×