Tsaki ta ja, a karo na ba adadi, na yanzun yafi duka sauran tsayi da kuma fito da asalin takaicin daya cunkushe mata zuciya, tana duba takalminta daya tsinke, saboda duwatsin da yake hanyar, ga wani tudu da sauka, sunyi tafiya kenan ta kusan ta minti talatin daga inda mashina suka saukesu, amman ita banda fili bata ganin komai
“Yanzun haka zan taka duwatsun nan babu takalmi kome kike nufi?”
Ta tambaya kamar zata kaiwa Uwani duka saboda bacin rai
“Tun dazun kike mun masifa kamar bake kikace in rakoki ba, Asabe in kin fasa ne mu juya, amman ni ba ‘yarki bace da zaki sakani a gaba bayan duk kokarin da nake miki, kin dauka gari banza zan dauko kafata inzo nan dinne?”
Ganin Uwani ta fara harzuka itama, ta kuma san yanzun zasu iya kwasar yan kallo yasa Asabe shanye nata takaicin. Dakyar ta samu Alhaji Salihu ya barta fitowar nan, shima da kashedi kala-kala, duka akan Sa’adatu. Da to kawai tabi duka kashedin da ya dingayi mata. Da wani mai adaidaita sahun Uwani sukazo, tunda akaje Miltara, aka dauke hanya Asabe ta daina gane komai, bakin wani dan kauye ya sauke su
“Sai mun fito Balarabe…”
Cewar Uwani tana sa Asabe dauka sun karasane, sai taga sunbi wani dogon sirqaqo, suna bullawa wata hanya, kafin su tare masu mashin su hau, Uwanin ce ta kara gaya musu inda za’a kaisu. Kuma sai taga suna ta bin tudu da gangare, tafiya taki karewa, ga duwatsu, sai gurdewa takeyi. Yanzun haka da babu takalma a kafarta bata daina gurdewar ba, ta ma kuje karamin yatsan kafarta, tayi gum da bakinta ne saboda inta bude shi tabbas fadan da take kaucewa ne zasuyi da Uwani. Kuma data daga ido ta fara hango wasu bukkoki. Fatanta dai wahalarsu tazo karshe, Uwani tace mata sun iso. Aikuwa bukkokin suka nufa, ta sauke numfashi ganin Uwani taja burki a bakin daya daga cikin bukkokin tana fadin
“Ka dade Malam…”
Tana gyara tsayuwarta
“Uwani, ku shigo”
Aka amsa daga cikin bukkar, sai Uwani ta kalli Asabe tanayi mata alama data bi bayanta. Cikin bukkar suka shiga, inda take shimfide da tabarmin kaba, gefen Uwani ta zauna, tana kallon wani mutum dan tsurut dashi, bakikirin, ga kwalli yasha kamar wanda ya shafa shi da yatsa, kanshi babu gashi ko kadan, idan Asabe ba zatayi karyaba ma, sai tace tana hango kyallin hasken ranar daya hudo ta cikin bukkar a saman kanshi. Gaisawa sukayi da Uwani ya dora da
“Kwana biyu”
Sai Uwani tayi murmushi
“Hididinmu ne sukayi yawa…”
Wata dariya ya fashe da ita, saida Asabe ta tsorata, tana kara gyara zamanta kamar zata shige jikin Uwani, saboda batayi zaton jin sauti me karfi ya fito daga mutum mai kankantar shi ba
“Kin dai samu wasu da kike zuwa wajensu, saboda baki da bukatar da ta gagare su, ko yanzun inace kawarki kika rako? Bayan kun gama zagaye kananun Malaman da kikayi musayata dasu sun gagara biya muku bukata…”
Jikin Uwani ne yayi sanyi har zaka iya ganin hakan a yanda yanayinta ya sauya, gashi sai bude baki takeyi tana rufewa ta kasa dorar da komai
“Auren nan sai an daura shi, babu abinda zan iyayi muku sai satin bikin, ku tashi ku tafi”
Ganin yanda Uwani ta mike yasa Asaben ma tashi. Wannan karin ko tafiyar bataji saboda yanda ranta yake a dunguzume
“Uwani kinajin me yace, sai an daura auren nan, tsinanniyar yarinyar nan saita auri Tahir”
Dan kallonta Uwani tayi
“Bayace mu dawo satin bikin ba? Kibari a basu mamaki, da karamar bazawar ai gara gandareriyar budurwa”
Wannan magana, ita ta sanyaya ran Asabe, ita tayi mata jagora a kwanakin da suka dinga zuwa suna wucewa batare da ta rasa natsuwarta ba. Tana kallon Tahir, yanda yake zuwa gaisheta da sanyin jiki, da taraddadi shimfide a fuskarshi, har sai sunyi sallama ya mike yaji batayi masa maganar Sa’adatu ba take ganin natsuwa ta shige shi. In ba aikin sihiri ba, ya za’ace akan wannan yarinyar duk yabi ya susuce haka? Ko Alhaji Salihu kallon shi kawai takeyi, so takeyi ta samu ta kashe wutar Sa’adatu, saita koma kanshi.
“Ga wannan, ki ba Tahir gudummuwa, wannan kuma nakine ko da zakiyi wata hidimar…”
Cewar Alhaji Salihu, hannu biyu tasa tana karbar kudin, hadi dayi masa godiya, saida ya fita, taga dubu talatin ne na Tahir din, sai dubu Ashirin nata. Ta bude jaka ta jefa abinta, ba zata ba Tahir kudi yaje ya mikawa Sa’adatu ba. Dasu zata kara taga wannan auren baije ko’ina ba
“Idan muka samu muka kashe wannan wutar, ga ‘yar wajen kanwata nan, yarinyace mai hankali yar babban gida, ba saiki hadasu da Tahir din ba?”
Uwani tayi mata tayi a hanyarsu ta komawa gidan Malam.
“Hakane, babu matsala ai, a dai gama da wannan din tukunna.”
Ta fadi a fili, a ranta kuma tana jinjinama Uwani, kallon bata da wayau takeyi mata, da hankalinta zata yarda ta hada Tahir da jinin Uwani? Tana neman kwato shi daga hannun Abida, sai kuma ta mikawa su Uwani da kaurin sunan da sukayi akan neman Malamai yasa har yanzun akwai Autarsu da shekara talatin da doriya kenan ko auren fari batayi ba, ga yaransu mata nan kuma duk sunki auruwa, kowa najin tsoro. Babu dar a zuciyarta da Malamin yace
“Dubu dari ne kudin aikinki, in dai kika kiyaye dokokin da zan saka miki, bukatarki zata biya”
Da kudin da Alhaji Salihu ya bata, da kuma na kayan data siyarwa Uwani ta hada ta ajiye masa. Roba biyu ya bata kanana, da ruwa a ciki, dan anan gabanshi ta dimha juya yan kananun robobin da basu nuna wata alama ta cewar na magani bane ba, yafi kama da ruwa
“Ki tabbatar ya sha daya ranar da aka daura auren, dayan kuma a zuba a bakin kofar gidan da zasu zauna”
Batason saka wani shakkune a ranta shisa batayi maganar maganin da Uwani ba. Ta tattaro duk wani fatanta ta dorashi akan Malamin da aikinshi. Da kanta ta kira Tahir tace tana son zuwa ganin gidan da zasu zauna, muryarshi har rawa takeyi lokacin daya amsata. Haka sukazo shi da abokinshi, da suka dauketa, saita sashi biyawa suka dauki Uwani, daman sun gama magana da Uwani. Shisa da suka isa saita tsaya a bakin kofa tana amsa wayar karya, sai da taga sun shiga cikin gidan tukunna ta ciro robar daga jakarta ta tsiyaye ruwan tas a bakin kofar. Ta shiga suka zazzagaya ko ina, suka kuma fito tare, Tahir din da abokinshi da taji ya kira da Bashir sune suka mayar dasu, aka sauke Uwani, ita kuma suka wuce da ita gida.
Haka kawai da bikin ya rage kwanaki biyu sai takejin wani irin faduwar gaba mai tsanani, ranar daren daurin auren kuwa ko baccin kirki ta kasayi, tun asuba data tashi kuwa bata iya komawa bacci ba. Sai kallon agogo takeyi, wajen karfe tara saiga kiran Tahir kamar yanda ya saba
“Mama Na”
Ya kira yana dorawa da gaisuwa cikin muryarshi da taji dauke da nishadi yau
“Lafiya kalau”
Ta amsa tana kasa tambayarshi yanda yake
“Zamu biyo gidan anjima In Shaa Allah”
Ya katseta, daman ta bude baki tace masa ya biyone tana son ganin shi, saiya hutar da ita
“To shikenan. Sai anjima”
Bata jira yace komai ba ta fara sauke wayar daga kunnenta tana kuma yanke kiran. Sai taga tsakanin kiran da zuwan Tahir kamar an yini an sake kwana, a maimakon ‘yan awanni. Kamar ko yaushe saida ya kirata tayi masa izinin shiga cikin gidan tukunna taji kwankwasa kofar shi tare dayin sallama. Gabanta ya fadi, farar shadda ce a jikinshi sai daukar ido takeyi, anyi mata aikin ruwan toka, sai hularshi ma ruwan toka, kalar na kara fitowa da hasken fatarshi, sai dai akwai wata rama a cikin idanuwanshi da tafi kama data zullumi, haka ya tattare babbar rigarshi ya zauna a kasa wajen kafafuwanta, kamar zai kwantar da kanshi a cinyarta lokacin daya ke gaishe da ita
“Mama baki sake saka mana albarka ba”
Ya fadi a raunane yana sake sunkuyar da kanshi, saita mike
“Bari in kawo maka ruwa”
A kofi ta juye robar ruwan maganin, ta dauko wani ruwan daga fridge ta kara akai tana cika kofin sannan ta fito ta mika masa, ya karba
“Nagode…”
Ya furta yana kokarin kai ruwan bakinshi
“Allah yasa alkhairi…”
Cewar Asabe, tana katse mishi Bismillahr da zaiyi, sai murmushi ya subuce masa, a kunyace ya kafa kai ya sha ruwan, ashe kishi na damunshi bai sani ba, saida ya shanye kofin ruwan, har yana jin da zata karo masa ba zai rasa sauran waje ba
“Bani kadai bane Mama, na bar mutane a waje”
Ya fadi yana mikewa hadi dayi mata sallama
“Yanzun Bash ya gama fada kamar zai ari baki, wai da alama zaka tattara babbar rigarka ka hau mashin, dan ya kusan jan mota mu tafi”
Sadi, daya daga cikin abokansu ya fadi, dariya Tahir din yayi yana jan murfin motar ya rufe, hadi da kallon Bashir da yake mazaunin direba, ya hade gira ya basar kamar baiji abinda suke fada ba, shima farar shaddar ce a jikinshi, da aiki ruwan toka, sai dai hular kanshi tafi ta Tahir duhu, kuma shi baiyi babbar riga ba
“Kana babban abokin ango ba zakayi babbar riga ba”
Cewar Tahir
“Ko angon ne ba zanyi wata babbar riga ba balle abokin shi”
Baiyi mamaki ba sam, kuma yasan zai wahalar gaske Bashir din yayi babbar riga ko da bikin nashine, yana saka manyan kaya, amman yadi yafi yawa, zai iya kirga lokuttan da yaga Bashir da shadda
“Nifa zan tsoma shaddar nan a ruwa, me yasa zansa kaya kaman takarda?”
Yace bayan sun karbo dinki, ya warware wandon tashi shaddar da suka sha guga
“Dan Allah karka wanke kayan nan, zaka rage musu kyalli”
Yau din kuwa tunda ya saka shaddar, yayi tsaki har Tahir ya bace kirga, baiko bi takanshi ba, yaga tunda akayi masa allurar sojojin nan zafin ranshi ya karu. In ba Bashir ba, waye yake tsoma sababbin kaya a ruwa dan suyi laushi? Walima ce abokan su suka shirya, yasu-yasu tunda babu wani abu bayan daurin aure, su dukkansu kuma masu son shagaline, harda Bashir din kuwa, harda sword-crossing a nashi bikin da saura sati shidda. Haka suka karasa wajen walimar, duk karadin hirar da sukeyi, Bashir kamar baya motar, duk kuwa da babu wanda bai saka shi a cikin hirar ba, harda Tahir, duk ya sharesu, har zagin da daya daga cikin abokansu yayi masa ma bai tanka ba
“Dan bakin halin tsiya…”
Cewar Sadi, yana ba Tahir dariya sosai, ya kamata su saba da tambotsan Bashir, sai dai Tahir yaja kujera baya da nufin ya zauna akai yaji duniyar ta juya masa, baisan tafiya yayi zai fadi ba sai da Bashir yayi masa wani irin riko kamar zai karya shi, ya kuma gyara kujerar da kafar shi ya zaunar da Tahir din akai
“Lafiyar ka kuwa?”
Ya juyo muryar Bashir
“Subhanallahi…”
Cewar wani da Tahir baisan waye ba, saboda sosai duniyar take juyawa masa, ga wani dumi da jikinshi ya dauka
“You are burning up Tahir…”
Bashir ya fadi yana daukar robar ruwa ya kwance ya mikamasa
“Duk yau bakaci komai ba, jiyama banajin kasa wani abin kirki a cikinka, idan ka fadi me kake so in cewa Sa’adatu? Malam ka sha ruwa kaci abinci, idan baka wartsake ba mu tafi asibiti, idan suma kakejin yi, kabari in mika mata kai, sai kaje kaita sumanka”
Duk da jirin da Tahir yake gani sai da murmushi ya kusan kwace masa, fada Bashir yakeyi tsakanin shi da Allah, amman zaka iyajin damuwa da tsoron da yake cikin muryarshi. Ko da kowa ya zauna ma, shi kanshi Tahir din ya danji natsuwa, yanajin yanda Bashir yake binshi da idanuwa kamar bai yarda ya koma dai-dai ba. Haka suka karasa yinin, inda duk zai cire kafarshi, nan Bashir yake mayar da tashi, yaki yarda su jera, gani yake kamar jiri zai sake daukar shi
“Kaga yanzun hankalina ya kwanta, na kawo mata kai lafiya”
Cewar Bashir daya bashi ledojin da suka tsaya kan hanya suka siya. Dariya kawai yayi yana kallon shi suna magana da ‘yan uwan Sa’adatu da zasu mayar gida. Ya kalli dakin daya san tana ciki tana jiranshi, ya sauke wani numfashi mai nauyin gaske, numfashin da yake rike dashi tunda aka tsayar da ranar aurensu, saboda gani yakeyi kamar ba zata zo ba, kamar kuma wani abu zai gifta ya hana auren, sai yanzun ya samu natsuwa, shisa da kowa ya fice, ya kullo gidan, sai daya sake sauke wani numfashi na daban. Ko daya shiga dakin, so yayi ace yana da damar da zai iya bude kirjinshi ya ciro zuciyar shi ya nunawa Sa’adatu tarin wajajen da ta samu a ciki.
A daren ya bude bakin shi, duk wasu kalamai sai sukayi masa kadan, shisa ya zabi wata hanya da zai jaddada mata soyyarshi, hanyar da ta kara hadesu waje daya, ya riketa a jikinshi yanajin dumi da kamshinta, ko da yaji saukar hawayenta, sumbatar gefen kanta yayi yana sake riketa, batare da yasan safiyar da suke tunkara zata jirkita kaddarar zamansu ba, kamar yanda a gefe daya Asabe ta kwanta da taraddadi kala-kala, ta kuma wayi gari da wani irin sanyi jiki da bata tabajin irin shi ba duk tsayin rayuwarta. Ta kira Tahir wayarshi a kashe, har azahar tana kiranshi amman wayar a kashe, so kawai takeyi taji halin da ake ciki, duk zuciyarta ta dungunzuma. Ruwan shayine kawai a cikinta, da tayi azahar nan falo ta dawo ta kwanta, bacci ne yake kokarin fisgarta tana kokawa dashi, lokacin daya dauketa kuma batajin tayi mintina goma, tayi wani juyi har saida ta fado daga kan kujera, ta hada zufa ta gaske, firgicin da take ciki ma saiya hana mata jin zafin fadowar da tayi.
Mafarkine tayi tasani, mafarki mai cike da matsanincin tashin hankali, gashi nan kirjinta sai dokawa yakeyi, amman kuma kwata-kwata ba zatace ga akan abinda tayi mafarkin ba, sai numfarfashi takeyi, ta mike ta karasa kitchen ta dauko ruwa ta sha, ta dawo falon. Ta dauki wasu mintina kafin ta samu natsuwa, saita dauki wayarta ta sake gwada lambar Tahir, amman a kashe take har lokacin. Jin kamar tsoronta na neman karuwa ya sata mikewa, lokacin kuma Sadiya ta fito daga daki, jikinta sanye da kayan makarantar Islamiyya, yanda bataje bikin ba haka ta hana Sadiya zuwa, itama kuma ko a fuska bata nuna ta damu ba, kusan rubutun shafe Abida daga zuciyarta da ta dinga bata, ya cire mata harda duka ‘yan uwanta, bata ganin kowa a yanzun sai Asabe, hakan kuma yafi mata
“Har la’asar tayi?”
Ta tambaya, Sadiya ta girgiza mata kai
“Uku da rabi, sallah kawai zanyi in saka hijabi…”
Kai ta jinjina, tayi nufin magana sai taji kamar anja wani abu a cikin kirjinta tare da numfashin data mayar, sai tayi kokarin jan wani, amman yana mata gardama, lokaci daya kafafuwanta suka fara rawa, kafin ma Sadiya data kwala mata kira a gigice ta karaso harta kai kasa, yanda taji kafafuwanta kamar basa jikinta, ga numfashinta da yake gargada sai wani irin tsoro yayi mata rumfa, wannan karin da taja numfashi tayi kokarin lankwasa harshenta ya kira sunan Allah, ko da kuwa rokar gafara ce, kamar tafi gajarta akan kalmar shahada, kuma zatafi sauri.
Ta manta da ikon komai ba a hannunta yake ba
Ta manta idan Allah ya yafe mata akwai hakkin mutane
Ta manta da labarin da take jira
A wannan lokacin, a wannan bigiren
Ta manta da Tahir balle kuma Sa’adatu
Ta manta da komai,
So takeyi ta kama Allah data jima da saki saboda son zuciyarta, ko kukan Sadiya baya karasawa kunnenta, data samu ta lankwasa harshenta da nufin neman daukin Ubangiji sai kara ta kubce mata, saboda firgicin da radadin da yake cikin fitar rai, mutuwa ta cika umarni akan Asabe, a jikin ‘yarta, tana barin duniyar da ta ciwa buri hartake kokarin canza kaddarar wasu a cikinta batare data tuna da lokacin da yake tafiya tare da fitar numfashinta ba. Idanuwanta a sama, suna bin ruhinta da kallo. A gefe kuma kukan Sadiya ne ya dauke dif, wani irin shiru ya ratsa dakin, shirun da giftawar mutuwa kadai kan haifar. Sadiya ba zatace bata san mutuwa ba, tana da wayau Habibu ya rasu, sai dai ko gawarshi sai bayan an hadata an tattarasu duka dan suyi masa addu’a ta ganshi a kwance, shine gawa ta farko data fara gani, sai kuma yanzun da take kallon Asabe.
Ba sai wani ya tabbatar mata ba, zuciyarta tayi luf, ta kuma bama gangar jikinta tabbacin gawar Asabe ce take rike da ita. Kamar daga wata duniya haka ta dinga juyo rurin waya, harta yanke ta kasa ko da kwakkwaran motsi, sai da aka jera kiran wajen sau goma, tukunna ta rarrafa tana dauko wayar akan kujera ta daga ta kara a kunne
“Mama…”
Muryar Abdallah ta daki kunnenta
“Mama…”
Ya sake kira
“Ta rasu!”
Sadiya ta amsa shi, muryarta na komawa cikin kunnenta kamar ba tata ba, ta kuma sauke wayar daga kunnenta tana sake rarrafawa ta koma ta daga kan Asabe ta dora akan cinyarta, wannan karin rurin da wayar ta sake dauka bai karasa kunnenta ba, idanuwanta na kafe akan idanuwan Asabe da suke kallon sama. Lissafin komai ya kwace mata, shisa bata san mintina ta dauka zaune da Asabe ko awanni ba, ta daiji ana kokarin janyeta daga jikin gawar Asaben, bata kuma ga dalilin da zaisa ayi mata haka ba
“Nasani, ta rasu, nagani, a gabana ta rasu ai…ku kyaleni in zauna da ita…ku kyaleni”
Take fadi tana kaima hannayen dake kokarin janyeta duka
“Sadiya…”
Ta juyo muryar Abdallah, data daga kai, bata ganin shi sosai saboda hawayen da suka taru cikin idanuwanta
“Tashi, zo, saketa, zo…”
Ta kasa motsawa, bata daiyi musu ba daya kama hannuwanta yana mikar da ita, a gigice take jinta harya taji an sake riketa
“Ikon Allah…rai bakon duniya”
Taji an fadi, kafin wani irin duhu ya lullube mata komai. Ba kuma ita kadai ta suma ba, mutuwar Asabe har abokan zamanta da zasu kirga sau nawa suka taba hangenta daga nesa sai da mutuwar ta basu tsoro. Abida kuwa tare da Abdallah suka taho dama, ita tayiwa Asabe wanka, idanuwanta sunki rufuwa saboda sun rigada sun bushe, da ita da uwargidan Asaben suka karasa hadata. Lokacin da su Abdallah suka shigo daukarta, sai Abida ta mike
“Shikenan ko? Mutuwa ta dauke mana Habibu a tare, aure saiya sake raba zamanmu, yanzun mutuwa ta sake yanke komai… jama’a shikenan fa… Inalillahi wa ina ilaihi rajiun… Shikenan ko?”
Ta karasa tambayar a hankali, Abdallah saiya kauda kai, wani abu na dukan zuciyarshi. Jinshi yake kamar yana yawo a wani mugun mafarki, yanajin har ya koma ga Mahallicinshi idan aka kira ranar Lahadi sai gabanshi ya fadi, idan ranar Lahadi ta sake zagayo ta riske shi sai natsuwar shi ta girgiza da taraddadin abinda zatazo masa dashi. Lokacin da suka sauke Asabe cikin kabarinta, ya dibi kasa ya fara zubawa, nauyin kanshi ne ya karu, abubuwan da suke faruwa dashi yau yakejin sunfi karfin ace shi kadai zai dauka, har aka rufeta ya kasa wani kwakkwaran motsi, daya daga kafarshi sai yaji kamar daga can nesa ana
“La hawla wala quwwata illa billah…ku taimaka mu rike shi…”
So yake ya juya yaga wa za’a rike, amman jikinshi yayi masa nauyi, sosai, wani irin nauyi na ban mamaki, saiya rufe idonshi, ya dan huta ko yaya ne
Yau dai ya ganta
Labarin gobe kuma abarwa Allah…
HasbunAllahu wa ni’imal wakeel 😠Allah ka rabamu da muguwar zuciya, asabe anyi tafiyar zomo kasuwa. Allah ya yafe miki kurakuran ki ya gafarta wa iyayenki
Allah ka yaye mana son zuciya
Allah ya kara mana imani.
Dagaske na tsorata
Ke Duniya ina zaki damu rayuwa baki da tabbas ya Allah ikon iya tanƙwara zukatan mu ka tsaremu da sharrin zuciya
Gsky babin nan ya taɓa ni ya tuna min da nima ina zaman jiran tawa mutuwar Allah kasa mu cika da kyau da imani