Skip to content
Part 2 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ko da ake cewa babu abinda lokaci baya tafiya dashi, Abida bata daya daga cikin mutanen da suka yarda da wannan zancen. A wajenta akwai abubuwan da basa taba wucewa, wannan abubuwan harda tsanar da Hajiya tayi mata, a cikin wannan abubuwan kuma harda halayen Asabe da kamar lokaci kara mata su yake. Lokacin dai wannan karin ya zo da sauyi kala-kala a gare su, ciki harda na muhalli saboda kadan da wannan yayi musu, iyali sun karu, duk da a cikin Bachirawa dai suka sake samu, mai daki hudune, sai wani karamin daki a soron gidan da ya zama mallakin Abdallah. Abdallah da bayan shi, sai da asabe ta kara haihuwar yarinya mace da aka sakawa Hadiza, suke kuma kira da Nana, ta sake samun wani cikin, tukunna Abida ma ta samu. Bayan daga ita har Habibu sun cire rai, sun dauka haihuwar ta tsaya mata daga kan Hafsatu.

Cikin daya tsokane idanuwan Asabe, ta daga hankalin ta har ta kasa boyewa a lokacin saboda kar Abida ta haifi namiji, musamman da ta haihu ta kuma samu ‘ya mace da aka sakawa Halimatu suke kiranta da Sadiya. Wata daya da kwana takwas tsakani Abida ta fara nakuda. Asabe ce tsaye akanta, abinda bata taba yi ba, duk wani ciwo sannu ce take rabata da Abida. Ba kamar Abida da zata dinga sintiri dakinta tana dubata ba. Kulawar duka yaran nata kuwa a karkashin Abida yake komawa kafin ta samu sauki ta koma yada maganar ba don Allah Abida tayi ba. Sai gashi itace rike da hannun Abida tana yi mata sannu, ko da ‘yar uwarta, Anty Khadi tazo. Asabe kin zama tayi, tace da ita za’a tafi asibiti. Babu wanda ya hanata binsu.

Kwana uku Abida tayi tana nakuda kamar ba zata rayu ba, sai gata rike da hannun Habibu bayan rokon da ta dingayi aka kira mata shi, tana kuka tana rokon shi ya yafe mata duk wani abu da ta taba yi masa ba dai-dai ba a tsayin zaman su. Tana yi yanayi, musamman da aka bashi takarda ya saka hannu dan sai anyi mata tiyata. Shi daga nesa yake jin labarin tiyata, a danginsu na kusa dana nesa babu wanda aka taba yiwa. Sai wata makociyar su a layin da suka taso, sai dai daga ita har abinda aka ciro din rasuwa sukayi. Karshe Hajiya da tazo ta koma lallashin shi, ko gani bayayi sosai lokacin da ya saka hannu. Kafin a shiga da ita dakin tiyata ta rike Hajiya tana kuka tana rokon ta yafe mata. Ta san Abida, ta kuma ganta a lokuttan da tayi ciwo, har wani ciwon ciki da ta taba yi satika biyu cir, taita suma. Amman bata rame irin yanda tayi a kwanakin nan ukku ba.

Saita tunawa Hajiyar da duk wata nakuda data taba yi, tana kara tuna mata yanda rayuwar mace take da tazara mai nisan gaske tsakaninta da ta namiji, daga darenta na farko zuwa wanda suke biyo bayan wannan, tsakanin kaiwa da komowa na aikin gida, da sauke hakkin namiji, har a dararen da dauriya ce kawai da son ganin farin cikin namijin da bukatar shi take danne tata. Kafin wani lokaci ciki, da laulayi bai cika hana da yawan mata kokartawa wajen gudanar da ayyukan gida ba. Taraddadi da firgicin da yake cikin tunanin nakuda da dandanata baya taba hanata bude kofar da wani cikin zai shiga, saboda tun daga rike da ko yar farko, tun a ranar da ta dandani wannan kaunar da take zuwa tare da mallakar halittar da komai nata zai tsaya dominta, halittar da zata iya sadaukarwa dukkan farin cikinta, take gane nakuda bakomai bace, saboda bayanta akwai wani farin ciki da ba zai taba misaltuwa ba.

“Dan Allah ki yafe mun Hajiya…”

Abida ta sake fadi cike da rauni, wani irin nishin wahala na biyo bayan maganar, yana kuma saka hawaye cika idanuwan Hajiya. A ranar daya, ta kalli Abida a matsayinta na ‘ya mace ba matar danta ba

“Allah ya rabaku lafiya Abida kinji, kiyita addu’a”

Ko da suka fito, aka gunguota a keken guragu kamar ba da kafafuwanta ta tako asibitin ba, sai da wasu hawaye suka zubowa Habibu, musamman da suka hada ido tayi masa murmushin da ya hango karfin halin dake kwance a bayan shi. Ga Anty Khadi da take ta kuka har saida Hajiya tace mata

“Addu’a zakiyi mata, kuka ba mafita bane ba”

Asabe ta tabe baki, duk wannan bidirin da akeyi ko a jikinta. Awarar da ta fita ta siyo a bakin asibitin take ta dangwalawa da yajin da ke cikin ledar tana taunawa. Habibu ya bita da kallo yana jinjinawa irin zuciyar da take da ita. Damuwarta guda daya ce, kar ace Abida ta haifi namiji, banda wannan ta mutu ko tayi rai bashi da wani muhimmanci a wajenta. Da taga Habibun ma na kuka tabe baki tayi, sai kuma wani kishi daya turnuqeta yana kara rura mata wutar tsanar Abida. Da gaske har cikin zuciyarta ta dauka haihuwar Abdallah zai canza komai, ta dauka zata haska a zuciyar Habibu fiye da Abida. Duk da zatayi karya idan tace baya kamanta musu adalci, sai dai son zuciyarta da take bari yayi tasiri a kanta, ko idan kishi ya turnuqo ta. Amman in ba a yanayin rashin lafiya irin wannan ba, yana kokarin boye yanda Abida ce zabin shi a gabanta.

Kasa boye murnarta tayi lokacin da aka fito an cirowa Abida ‘ya mace.

“Alhamdulillah…”

Take fadi tana kara maimaitawa, hakoranta duka a waje, dukan su sun dauka jin cewa anyi aikin cikin nasara ne. Sai babu wanda ya kara bi takanta, har Hajiya kuwa wannan karin. Saboda wani abune da babu wanda ya taba hango faruwar shi ya faru lokacin da aka mikawa Hajiya yarinyar ta riketa a hannunta. Kauna, wata irin kauna da bata taba jinta akan jikokin nata na wajen Abida ba, duk da yanzun da suka fara tasawa, duk juma’ar duniya sai Abida ta shiryasu sunje wajenta, tun tana sharesu saboda kiyayyar Abida har yau da gobe tasa suka fara shiga ranta, musamman kyakkyawar tarbiyar da ko kin Abida bai rufe mata idanuwa daga kin ganin wannan ba. Har Abdallah da yake shalelenta, take kuma gatantawa, duk wasu yan kudadenta suke karewa a wajen shi, lokaci daya wannan yarinyar da bata rufa awa a duniya ba ta samu waje tayi mata zaune.

“Dame kayi mata huduba?”

Ta tsinci kanta da tambayar Habibu daya amsa da saurin shi

“Sa’adatu”

Hajiya ta jinjina kai tana gyara mata zama a hannunta

“Sa’adatu sa’ar mata, Allah ya rayaki cikin aminci.”

Ta karasa maganar da murmushi a fuskarta, har sai da Anty Khadi da kuma Asabe suka kalleta cike da mamaki. Shi kanshi Habibu kallon mamakin yake yiwa Hajiya. Ko da su Anty Talatu suka zo asibitin, suma mamaki sukeyi, saboda Hajiya na rike da yarinyar tana ta fara’a kamar ba ita ba, suka ma kasa samun damar da zasu kawo mata tsegumi ko su taso da maganar haihuwar macen da Abida ta karayi. Saboda makotansu Abidar da suketa zuwa dubata a asibiti, Hajiya ce take rigan kowa karbe addu’ar Allah ya rayar su da amin tana sake maimaitawa, harda hada musu da godiya. Wannan karin duk wata hidima da Habibu yakeyi bata daga kai ba, ko da Anty Talatu tayi magana kan kayan jariran daya jibgo haka Hajiya tace

“Kina da yawan magana Talatu, baki ga wahalar da yarinyar nan ta sha bane ba?”

Sai jikin Anty Talatun yayi sanyi, ta kuma ja bakinta tayi shiru. Sun dai nuna halin nasu ranar suna akan nama, kamar ko da yaushe kuma su Anty Khadi basu tanka su ba. Su wannan karin farin cikin da suke ciki na ganin Abida ta fito lafiya ya danne komai, su da suka cire rai da rayuwarta, meye kuma wani nama? Sai dai kamar Hajiya, tunda suka koma gida, Abdallah ya kyalla ido ya ga Sa’adatu, sai yaki fita daga dakin, ya koma gefenta ya zauna. Da Asabe ta kwala masa kira yaje ya karbi abinci, daki ta jashi, a gidan har yan barka babu wanda bai juyo kukan yaron ba, babu kuma wanda bai fahimci dukan shi tayi ba, sai dai ba kowa bane ya gane dalilin shigar shi dakin Abida ne da take ta kokarin ganin ta yakice masa, amman ina ruwan yaro da baya fahimtar komai sai kyautatawa? Kuma kullum hakoran Abida a bude suke in dai zata ganshi, abinda duk zata bawa yaranta yana da kaso, idan yace

“Amma…”

Kamar yanda nata yaran suke kiranta zata amsa shi da

“Dan albarka”

Ko kuma

“Yaron kirki…”

Saboda natsuwa da sanyin yaron tana mata yanayi dana ‘yar uwar shi Nabila. Kuma fatan Abida bai wuce ganin duka yaran sun taso da kaunar juna ba, addu’arta Allah ya kare zukatan su yasa kar kishin da yake tsakaninta da Asabe ya taba alakarsu. Duk da yaranta ne manya a gidan, babu wanda ya san gobe. Tana ganin haukan iyayen da suke bari kishin su ya shafi yaransu, har a samu rabuwar kai, ya zamana kowa kyautatawar shi ta tsayane a wajen yan dakinsu. Idan kuma a cikin yaran kishiyar da kika dorawa karan tsana, fatanki idon mutane ya kauce kiyi musu mugunta, Allah ya nufa da samun arziki fa? Shikenan ke naki yaran basu da rabon dangwalar arzikin dan uwansu, babu wani taimako a tsakani saboda kin taya mahaifiyar shi wajen ganin hakan ya faru. Har kanki kika yiwa saboda sai wanda ya kai zuciya nesa ne zai dubeka a irin halayen da kika nuna masa suka kuma zauna masa a zuciya tun kuruciyar shi.

Ta yarda da cewa ba’a yiwa yaro mugunta, ko ba dan kishiya bama da yake da kusanci da naka yaran, kaddara kuma ta hadesu waje daya. Ko su Tahir da jifa-jifa suke zuwa gidan gaishe da Asabe yanzun, da fara’a take tarbarsu. Kuma da alama yaran suna samun kyakkyawar kulawa da tarbiya, dan basu taba kin gaisheta ba, musamman Tahir da ko tana cikin dakinta bata juyo su ba, daga inda yake saiya kwala mata kira ya gaishe da ita

“Amman su ina wuni”

Da ta taba ce masa

“Harda kai ai Tahir, ba su kadai ba”

Dariya kawai yayi, daga shi har ita kuma babu wanda ya kula Asabe da ta dinga sakin maganganu kan yanda Abida take shigewa yaranta. Duk wani kokari da takeyi na ta raba yaran da ita kuma ya ci tura. Kar a duba Abdallah ma da tayi dukan tayi zagin a banza. Sam bata ga  dalilin da yaranta zasu nanikewa Abida ba, bayan ita nata yaran suna baya-baya da ita. Ranar girkinta dai duk wani aiki da suke taya Abida, itama zasu tayata, sai dai babu mai shiga dakinta. Ta kasa gane cewa tsoronta da ta dasa musu ne dalili, jibgar da takeyi musu babu lefin tsaya balle na zaune ma wani dalilin ne, ga kuma zagi da kyara ko da Habibu ne ya aike su dakin nata. Ta tsani taga yaran suna shigewa Abida ko kadan,balle yanzun da har Abdallahn Abida take goyawa Sa’adatu duk idan ya bukaci hakan bata taba kuma hana shi tafiya da ita dakin Asabe ba, zuciyarta daya. Babu tunanin komai sai alkhairin da Asabe bata nufin duk wani abu daya shafeta dashi.

Daga Abdallahn har Sa’adatu tasha juyo kukansu, ko a jikinta, yanzun lamarin Asabe ma ya daina bata mata rai, sai dai mamaki da yake bata wasu ranakun. In dai dukane da take ganin da yaranta take yiwa, kuma mugunta ce, to ga wanda suke fito daga cikinta nan yanzun ma suna shan shi, musamman akanta. Abdallahn ma da yake dan gaban goshi, son da yake mata ya shafa masa kashin kaji. Sai ta kara maida hankalinta akan sana’arta da takeyi, wainar filawa yanzun harda safe, ga su aya, alawar madara, gullisuwa da takeyi. Saita hakura da siyar da gawayin tunda tana samun ciniki ba laifi, balle kwakumeti, yan unguwar har sari sukeyi a wajenta. Sosai bukatunsu suke fin karfin Habibu yanzun. Shisa ta kara dagewa da yin sana’ar dan ta taimaka masa. Jin dadin taimakon ne da saukin hidimar yara da yake samu daga bangarenta yasa shi yiwa Asabe magana kan itama ko zata fara wata sana’ar, tayi tsalle ta dire gefe tace ba zata iya wahala ba, haka kawai kullum tana gaban wuta, duk tayi baki.

Bai matsa mata ba, dan a daren har suka kwanta bata daina yi masa mita ba. Ya san sana’a a wajenta ba dole bace kamar yanda ta fada, nauyinta dana yara duka a wuyan shi ya rataya, kuma dai-dai karfin shi zaici gaba da saukewa. Ya dai dauka zatayi taya shi ganin asirin su ya cigaba da rufuwa kamar yanda Abida takeyi. Ranshi bai baci ba, saboda baya daga cikin maza

masu son kansu. Ko Abida dariya take bashi, ran girkinta ko bashi da kudin cefane yace tayi mai da yaji, zata saka kudinta tayi musu miya. Kuma harda Asabe da yaranta za’aci, amman ranar girkin Asabe, ko kudi yace in tana dasu ta ara mishi zatace masa bata dasu, wani lokacin saiya dawo ya shiga dakinta zata bashi hakuri kamar tayi masa wani laifi. Kishine yake damunta ya sani, kuma hakane, zata hana shi saboda tana jin ba zata bashi ya kashewa Asabe ba, amman da yake zuciyarta mai kyauce, idan ta kashe da kanta har Asaben ake mora.

Haka rayuwar taci gaba da tafiyar musu, ranaku da darare na wucewa suna hade watanni, shekaru na tafiya suna kuma nuna canjinsu a tare da komai na rayuwa, da alama dai haihuwa ta rufewa Asabe daga Nana, ko ita Abidar sai da Sa’adatu ta shekara uku tukunna ta sake haihuwar Jidda, alamu kuma suka nuna ita dince rabonta na karshe. Namiji kuwa Abdallah take kallo kamar nata tunda Allah bai tsara a cikin kwanta akwai namiji ba. Kusan duka yaran kowa aka kira zata dorar da wani abu akan halayen shi, banda Sa’adatu, komai nata daban ne kamar haihuwarta da tazo daban. Abinda zaka ga tana so to yasha bamban dana kowa, ga farin jinin mutane tana dashi, bawai dan tafi sauran kyau ba, ta dai biyo hasken fatar Habibu da kuma idanuwan nashi, amman a gidan kaf kowa ya fita hanci.

Wajen shiga ranta, Abida bata mamaki, tunda ta shiga ran Hajiya, harta kasa boye hakan, to zata shiga ran kowa. Sau nawa zasuje gidan Hajiyar yanzun su dawo, kudin da Hajiya ta bata yafi na kowa yawa, zaka dai ga cewa sunci arzikin Sa’adatu ne, kome zata basu kuwa, saboda in sukaje su kadai haka zasu dawo batare da ta basu wani abu ba. Kamar yanda Hajiya take son Sa’adatu, a nata bangaren ma hakane, gani take ko iyayenta basa kaunarta kamar Hajiya. Sai kuma Abdallah, wani mutum na biyu da idan Sa’adatu zata rufe ido da rigima shi kadai yake iya lankwasata, kuma ra’ayi na kowa idan ya sha bamban da nata zata bude baki tayi magana. Banda Abdallah, sai an kai ruwa rana, rayuwaka sun baci ne zata sauya ra’ayi. Halayen Sa’adatu da ada Habibu yake tausar Abida akan cewa yarinta ce tana girma karuwa sukeyi.

Abida bata cika dukan yaro ba sai ya kaita makura, amman Sa’adatu na da kafiya, akanta tasan ta iya duka, sai dai dukan ma baya biyan bukata. Lokacin da aka sakata makarantar boko ta gwamnati inda duka ‘yan uwanta sukeyi. Ko sati a lokacin ba’a rufa ba, sun dawo tace

“Amma, daman makarantar su Asiya muke, kayan su sunfi namu kyau, kuma su a mota ake kaisu”

Asiya, yarinyar makocinsu da gidanshi yake daura da nasu, kuma gida daya a kan layin da yake da bene, saboda Alhaji Salihu ya taba rike mukamin kancila, da alama kuma ya kasance cikin yan siyasa masu dabara, dan yana kasuwanci, da ya sauka daga mulkin ma sai ya cigaba da buga siyasar da kuma kasuwancin. Yana da rufin asiri sosai, matar shi, Hajiya Karima, macece mai kirki, wadda rufin asirin mijin nta baisa ta kyamace su ba. Tana siyayya sosai a wajen Abida, wainar filawa bata wuce yan gidan, duk kuwa da in suna so zasu soya a gida. Haka zata bada kudi ayi mata alawar madara da yawa. Abida na aiken Sa’adatu gidan, ranar da ta aiketa ta kai mata alawar madara, da rana sunyi shinkafa ne da manja da yaji, sai ganye da aka yanka, ana zubawa Sa’adatu tace

“Me yasa ba’ayi mana da miya ba? Gidan Hajiya dazun da naje harda nama, kullum abincin su da nama.”

Ta karasa tana turo baki, in dai zata shiga gidan ta dawo to akwai wani abu da zata zo dashi wanda ya burgeta. Kuma ba Abida kadai zata fadawa ba, har da Habibu, yanda take nacin maganar talabijin din gidan Hajiya, Abida tasan shine dalilin da yasa Habibu ya kukuta ya siyo musu yar karama, yaso ya saka a dakin Abida, sai ya gujewa tashin hankalin Asabe ya barta a dakin shi, ranaku da lokuttan da babu makaranta zasu kamowa yaran wani shirin da akeyi a tashar talabijin din su kalla, duk da bai burge Sa’adatu ba, sai da tace,

“Mu babu katin irin na gidan Hajiya, kuma tasu batayin layi-layi, Amma tasu ta babbace sosai.”

Shisa ta daina aikenta gidan kwata-kwata. Saboda bata san da wanne kalamai kowanne yare zatayi amfani dashi ta fahimtar da Sa’adatu akwai bambanci a tsakanin mutane kamar irin na yatsun hannun su. Rayuwar gidan Hajiya daban da gidansu, karfin mahaifin su Asiya daban da Habibu, shi bayan hidimar su, gidan da suke ciki ma hayane. Duk wani kokari Abida tanayi akan Sa’adatu, amman tana kara girma hange-hangenta da son dai-daita rayuwarta da wanda suka fi karfinta tana karuwa. Ba kamar sauran ‘yan uwanta da suke cikin godiyar Allah da abinda suka samu ba. Lokacin da aka saka ranar Amira da wani Malaminsu da yazo bautar kasa a makarantar su, dan garin Bauchi, Habibu yaso ya hana shi, saboda yayi nisa, amman yaron yaki hakura, ya saka naci, har Kawun shi ya wanko kafa daga can Bauchin yazo ya samu Habibu. Abinda ya sashi saduda. Sai babban abokin shi Lawal ya dauki nauyin zuwa har garin Bauchi yayi bincike, kuma aka samu iyayen Aliyun da shi kanshi mutanen kirkine.

Biki sukayi dai-dai karfinsu, bayan sun hada karfi da karfe wajen kayan dakin shi da Abida. Amman a lokacin haka ta tsinkayi muryar Sa’adatu tana ce mata

“Kinsan Yaa Amira kicewa Abba ya sai miki irin kujerun hanyar makarantar mu, masu kyau ne.”

Da aka kawo kayan kuma, Amira tana dakinsu saboda kunyar da take ji, duk wani abu daya danganci bikin idan ana maganar shi nemarta zakayi ka rasa ta bar wajen. Sa’adatu ce ta wuni kumbure-kumbure, kujerun sam ba suyi mata kyau ba. Shisa da akace ma banda su za’aje kaita saboda nisa, abin bai wani damu Sa’adatu ba. Lokacin bikin Nabila kuwa, Sa’adatu ta gama aji uku na sakandire, zata shiga na hudu, a tsakanin hutun akayi. Kuma sai ta zama kamar wata babbar kawar Nabilar, yanda tayi tsaye akan sha’anin kamar wata babbar budurwa. Da yake hali yazo daya. Shima Sunusin da zata aura ba hayaniya gare shi ba, mahaifin shi dan kasuwa ne, suna da shagon saida robobi ne, kuma Sunusi a karkashin mahaifin nashi yake aiki. Kusan tun cikin hidimar bikin Amira suka hadu. Shekara wajen uku ya hada yana neman aurenta, hidima dai-dai karfin shi yana yi mata. Shisa ya danyi daraja a wajen Sa’adatu, dan har dan kunshin naman shi yakan kawowa Nabila lokaci zuwa lokaci.

“Kefa bai kamata kici ba, kinsani ai ko Yaa Nabi? Saboda ance ba kyau cin abin saurayi”

Sa’adatu kan fada idan taga nama ne, ko kayan zaki, duk da koma meye Nabila na shigowa zata karbe ledar. Ko kayan amfani ne, dangin su kayan kwalliya, wanda yayi mata zata dauke ta barwa Nabila abinda tayi niyya. Wasu ranakun kuma Nabila zata dauki turare ne a ciki tace tabar mata sauran. Ko maganar siyen kayan daki, sai da Abida ta mareta, zuwa tayi ta samu Habibu tana tsara masa abinda ta gani take so ya siyawa Nabilar. Shi kuma kamar ko da yaushe da Sa’adatu bata laifina wajen shi, soyayyar da kowa yake yi mata, shima ita yakeyi, kuma har yau halayenta a wajen shi kuruciya ne, zaice zata bari, duka nawa take. Sai yayi dariya yace

‘Sa’adatu rigima, to kiyi mun addu’a, Allah ya horemun”

Sai ta turo labbanta cikin shagwabar da ta saba

“Abba fa yunkurawa zakayi, ba wai addu’a ba”

Dariyar ya sakeyi, shisa Abida ta fita tana kuma kwala mata kira, da tayi mata fada sai ta juya idanuwa tana son fadar magana, saboda ita in dai zuciyarta ta shirya mata dai-dai, babu wani da ya isa yace mata ba haka bane ba ta saurara, idan ma fadane akeyi mata bata taba rasa kalaman kare kai. Bakinta dai ba zaiyi shiru bane sai dai ka kasheta. Marin da Abida tayi mata ma baisa tayi shiru ba, idanuwanta cike taf da hawaye take fadin

“Shikenan mu duk wani abin cigaba ko gayu sai dai mu gani a wajen wasu? Kuma ace…”

Bata karasa ba saboda Abdallah da ya kira sunanta, hawayen dake idanuwanta bana zafin marin da Abida tayi mata bane, na takaici ne da talaucinsu da lokaci yaki tafiya dashi.

“Zo nan”

Ba musu kuwa ta karasa inda yake tsaye, ganin ya hade girar sama da ta kasa, ya sata sake matso kwalla, bataso ya fara yi mata nasihar shi da bata karewa

“Ya mukayi dake akan yin shiru idan ana yi miki fada?”

Wasu hawayen ne suka sake sauko mata, bakin nan kamar zai tabo bango saboda yanda take kara turo shi

“To ki share hawayen nan bana son su…kuma Allah za muyi fada sosai idan kina mun alkawari kina sabawa…”

Ya karasa yana mika mata bakar ledar da take hannun shi, ta karba da sauri

“Nagode”

Ta furta kasan makoshi tana barin wajen kar Asabe ta fito ta kare musu, kamar yanda ta saba idan taga ya bata abu. Shikuma sanin halin kanwar tashi yasa ko kudin makarantar shi, sai ya rage ya tara, kwai, kifi duk siyo mata yake. Sai ayi dai-daito ya dawo mata da kifin a ranakun da taqi kallon kason abincinta a zuwan anyi mai da yaji da bata kauna, musamman da manja. Ko kuma tuwo, tafi tsanar ayi musu tuwo, kowacce miyace ballantana ma kuka. Saboda tuwon dai iri dayane, na masara. Da yake yan kudinta inta adana, da wanda Hajiya takan bata, sai ta fita ta siyo taliya ta dafa, ko biredi ta sha shayi. Saida Abida ta rufe ido tace in ta kara gani saita mata dukan tashi kisha gishiri. Ita kuma da taci tuwo gara ta kwanta da yunwa da kuncin zuciya. Saboda ba ta ga dalilin da zaisa a hanata cin abinda take so ita da kudin ta ba. Da Abdallah ya fara zama wajen mai shayin da yake kasan unguwarsu, bayan Magriba zuwa tara na dare yana kama mishi ayyuka saboda ciniki yakeyi sosai. Sai ta samu sauki, saboda zai taho mata dashi a boye batare sa Abida ta sani ba, har kwai yake soyo mata idan ya samu sallama me kyau. Wani lokacin kuma indomie. Ta koma soron gidan ta zauna taci ita kadai dan kar wani ya sa mata rani.

Asiya kuwa da tun suna yara take burgeta. Sai rana tsaka aka sakota Islamiyar su Sa’adatu, ajinsu kuma tunda duk sa’anni ne, gwajin da akayi mata ta cancanta ta zauna aji hudun kamar su. Ai tun lokacin kuma sai Sa’adatu ta manne mata. Da yake zai wahala bata shiga ranka ba, itama Asiyar sai taji dadin hakan. Ko da Asiya ta fara sintirin zuwa gidansu, ran Abida bai so wannan kawance ba. Kirkin mahaifiyar Asiya ne yasa take sakar mata fuska, sai ta fara addu’ar Allah yasa Sa’adatu ta dauki kyawawan halayen da ta kula Asiya tana da su. Sai dai ita Sa’adatu ta kulla kawance ne da Asiya dan abinda suke dashi a gidansu, kamar duka kawayenta, in dai babu abinda zata mora a tare da kai, koya kake binta zatayi kokarin ganin ta yakice ka. Kamar kuma duka mutanen da suke rayuwarta banda Abida, soyayyarta takan rufe musu ido, yanayin salo da baiwar da Allah yayi mata, sai kaga kamar ita take juya mutanen da suke tare da ita cikin dan kaynkanin lokaci.

Ko wani dan abin kwalam akayi a gidansu Asiya, to ko nata kason ne saita raba shi da Sa’adatu. Haka wata kyautar kudi idan akayi mata. Kuma da yake su biyu kadai mata Allah ya bawa mahaifiyar su, babbar anyi mata aure. Sai wani lokacin idan zata siyawa Asiya dan takalmi sai ta hada harda Sa’adatu. Sosai Sa’adatun ta nace wajen koyon turanci a gurin Asiya da take makarantar kudi, daman ta jima tana son koyon turancin, sai dai makarantar gwamnati ba’a cika mayar da hankali wajen koyarwar ba. Ana kuma samun cigaba tunda in dai Sa’adatu zata sakawa zuciyarta yin abu, hankalinta baya kwanciya sai ta same shi. A cikin abubuwan da zuciyarta ta kissima mata kuwa harda samun rayuwar da ta sha bamban da wadda suke samu daga gidansu. Rayuwar hutu, saboda tana son jin dadi a rayuwarta, daga jikinta har bakinta yana son bambancin da bata taso a cikin shi ba.

Idan har iyayenta basu da halin sama mata, ita ba zata kwanta ta rungumi kaddara ba. Zata nemawa kanta mafita ne. A yanzun dai iya wannan take dashi, inda mafitar zata fito ne bata sani ba. Ana kuma haka, wani yammacin Asabar da ba zata manta ba, anyi musu hutun islamiyya, tana zaune a wajen dan karamin kicin dinsu, tana tsince hancin waken da duk wankin da tayi masa wani bai fita ba, ranta kal za’ayi musu alale, kuma Asiya tace za’ayi musu farfesun kifi da dare, tana da yakinin akwai kasonta, saita hada da alalen. Taji sallama ta mutum biyu, amman kunnenta sai ya ware mata muryar shi taji ta daban, daban din da ta sakata daga idanuwa bayan ta amsa dan ta ga su waye. Ta kuwa sauke su cikin na Tahir da jikin shi yake sanye da wandon bula, sai riga mai dogon hannu, fara kal da ita, ta haska fuskar shi da take cike da kwarjini, yayi mata murmushin da yasa take son tuna inda ta san shi.

Makarantar kwana aka kaisu suna gama aji uku, to da suka gama sakandire dinma, shi saiya samu gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ba kamar Yayan shi Aminu ba da yake nan Jami’ar Bayero. Ganin shi da Aminu yasa ta gane shi, Tahir ne, Tahir din Asabe. Ba zata tuna ranar karshe data ganshi ba. Sai dai taji labarin zuwan shi a wajen su Nana

“Su Hamma Tahir sunzo, baki ga atamfar da suka kawowa Mama ba”

Ko kuma wani turare da suka kawowa su Nanan, turaren da in dai zasu kawo to akwai nasu Sa’adatu a ciki. Asabe ce take hanawa, da duk wani abu ma da zasu kawo da sunan a basu. Bata ga dalilin da zaisa ta bayar ba, bayan ga Abdallah nan ya tare a wajen su, bata haifi yaranta dan Abida da nata ‘ya’yan ba.

“Sannu da aiki”

Ya fadi, sai murmushi ya subuce mata, har dimfil din da yake kowanne gefe da gefe na kuncinta ya bayyana, ta juya idanuwan da halittarta ce kafin ta gaishe dasu, Aminu ya amsa yana wucewa, Tahir kuma ya tsinci kafafuwan shi da tokarewa suka tsaya a gabanta

“Wake kike gyarawa?”

Ya fadi, ta daga masa kai, ba samari bane basa tsayar da ita, kawai bata taba ganin wanda ya burgeta bane a cikinsu, saboda labarin Haris, wan Asiya da yake kasar waje karatu ya cika mata kunnuwa, ta gama hasaso shi ta hanyar hada duk wani abu me kyau da yake jikin kaf ‘yan gidan su data taba gani, ta lika masa. Ta kuma hango kanta dashi tare da mafitar da take nema. Sai gashi wani abu da bai taba faruwa ba ya faru da ita yau, kunya, kunyar nan da take gani tare da ‘yan uwanta, musamman Nabila, kunyar nan da take takaici saboda bata ga dalilinta ba, itace tayi mata dirar mikiya yau

“Ubanka ka tsaya yi anan kuma?”

Asabe da ta dago labule ta fadi, tana saka kunya kama Tahir din, da sassarfa ya wuce, ta daga ido da nufin bin bayan shi da kallo, sai ta sauke su akan Asabe da take zabga mata harara. A ranta tana jan duk wata addu’a da zata iya tunawa da nufin neman gina katanga tsakanin ahalinta dana Asabe.

Sai dai kaddara ta riga fata

Kaddarar da zata karya zukata da yawa

Wata irin kaddara da inda za’a haskawa Asabe ita babu abinda zai hana jiri tikata da kasa…

<< Tsakaninmu 1Tsakaninmu 3 >>

3 thoughts on “Tsakaninmu 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×