Skip to content
Part 21 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Gani yake da Aisha tabar shi ya samu Hajja yayi mata magana, watakila abubuwa zasu fi tafiya da sauri, tun washegarin ranar da Sa’adatu ta tura mata sakon ta amince suka gama tattara duk wata takarda ta yarjejeniyar da suke da bukatar ta saka hannu akai, kusan ranar a zaune suka kwana suna sake jujjuya tsarin da sun jima da yin shi, ko akwai wata kwaskwarima da zasuyi wa al’amarin, kuma sun gamsu komai yana kan tsari yanda suke so

“Kabari ta saka hannu tukunna muyi wani motsi Jay”

Aisha tace masa ganin yanda ya kasa hakuri, sai dai bayaso ya furta mata a tsorace yake, tace masa matar wan Sa’adatun ce ta haihu, suna hidima ne sai bayan suna tukunna zata zo, wacce irin hidima ce? Ko ita ta haihu ba zata rasa awa daya da zata zo ta saka hannu ta koma ba, shi saiya aika ma a daukota, a kuma mayar da ita. Idan tayi wani tunanin daya canza mata ra’ayi kafin lokacin kuma fa? Kamar Aisha ta manta amincewar Sa’adatu ce hasken da suka gani a duhun da suke ciki, kamata yayi su kamata su rike gam karta kubuce musu. Ga lokaci ma kamar dan ya kara saka shi a taradaddi ya daina sauri. Shi ba mutum bane mai burika da yawa, zai iya kirga lokacin da ya dauki wani abu ya saka a ranshi da zummar samun wannan abin. Ya taso ne cikin gata, ya taso zagaye da tarin kauna, ya girma a inda kafin ma yaga abu ya furta yana so an mallaka masa shi.

Duk shekarar duniya sai an sake masa gabaki daya kayan sakawar shi, tun daga kan suttura, takalma harda agogon da ba damuwa yayi daya daura ba, kuma a cikin wadanda za’a kwashe din sai an samu sababbin da baiko yi amfani dasu ba. Bai taba sanin wata matsala ta rashin kudi ba, zai ce yana daya daga cikin mutanen da sukazo duniya da kafar dama, saboda babu abinda ya nema ya rasa. Akan Aisha ya fara sanin neman wani abu, akanta kuma ya fara sanin tashin hankalin ka nemi abu ka kusan rasawa, da buri kwara daya ya tashi, burin yaga ya tara zuri’a da yawa, ba don kaunar ‘yan uwanshi na da wani nakasu a zuciyar shi ba, yanajin kamar ya ta’allaka a wuyan shi ya haifi yara da yawa, ko dan kar jinin mahaifiyar shi ya kare daga kanshi

“Ina son yara…”

Ya cewa Aisha wani lokaci suna hira

“Nima haka”

Kai ya girgiza mata

“Ba daya ko biyu ba Tasha, ina son yara da yawa fa, bani da tsarin zama da mace fiye da daya, inajin idan kece zan hada da wata mace Allaah zai kamani da laifin rashin adalci saboda girman da kike dashi a zuciyata.”

Ba zai manta murmushin da tayi ba

“Allaah Ya bamu masu albarka, kaman guda nawa?”

Dan jim yayi kafin ya amsa

“Goma?”

Kallon da tayi masa a razane yasa shi yin dariya, itama dariyar tayi. Sai dai su duka sunyi tarayya a wannan soyayyar ta son ganin sun samu zuri’a mai yawa. Kamar yanda ya taso da burin nan hakama Aisha a nata bangaren, shi yana son ganin ya tara yarane ko dan mahaifiyar shi, Aisha na son ganin ta tara yarane saboda ta taso gidan da duk yanda ta juya sai taga muhimmanci da yara suke dashi a rayuwar iyayensu, sai kuma mahaifinta da baya gajiya da nuna mata duk wani farin ciki da zai samu a rayuwar shi inda bata ciki ita da ‘yan uwanta, wannan farin cikin daya zama ragge. Bai kuma yi wasa wajen labarta mata kuskuren da yayi a rayuwar shi ba, wani kuskure da duk kwanan duniya yake tashi cike da nadamar shi, su ukune kacal, daga ita sai kannenta maza guda biyu. Tana son yara da yawa saboda dalilai mabanbanta.

A shekarar farko ta aurensu, wata na biyu, al’adarta tayi mata wasa, ko tace jikinta ne da yaga yanda hankalinta ya karkata kan samun ciki, sai data kara kwanaki shida, zatayi sallar asuba ta shiga bandaki taga jini, sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, ranta a cunkushe tayi sallar, da Jabir ya tambayeta meke damunta kuwa, hawayene suka zubo mata kafin ma ta buse bakinta, ya kuma hauta da fada a maimakon lallashi, me yasa zata damu, duka kwana nawa da auren? Shima sai ta hau fushi dashi, ya kuma shareta, da kanta ta sauko, sai lokacin ne yayi mata maganganu masu kwantar da hankali. Ba dan ta cire rai ba, amman ko da akayi shekara shiru bata daga hankalinta ba, saboda Jabir ya hadata da Adda Farhana, Yayar shi, da ta dinga mata dariyar damuwar da tayi, a lokacin take ce mata ko asibitu sukaje ma likita korosu zaiyi tunda auren bai shekara ba, ita saida tayi shekara uku da aure tukunna ta samu cikin farko.

Adda Farhana ce tace mata wasu matan ma har fiye da haka, kuma daga su har mijin lafiyarsu kalau, basu da wata matsala. Sai dai da aka fara dosar shekara biyu, duk watan da al’ada zata zo mata, Jabir ne yake wuni sukuku, damuwar shi ce ta dasa mata damuwa itama, lokacin ne kuma suka fara yawon asibiti, wasu watanni masu cike da fargaba, tashin hankali da rudani a wajensu. Watanni da Aisha zata kira na gwajin hakuri harda imaninsu, duk wani bayani da akayi musu bai gamsar dasu ba, hakan yasa suka shirya suka ketare kasar zuwa kasar waje, don sun raina kwarewar likitocinmu na nan. Su duka sun karfafi juna cewar maganin matsalar su yana wajen Nigeria, da sunje aka dubasu za’a samo musu mafita. Hakama makusantansu da suka bisu da addu’ar samun nasara. Sai dai bayan gwaje-gwaje da duk wani aune-aune da za’ayi musu, likitan yazo musu da wani bayani da ya dauki duk wata natsuwa da suka shiga kasar da ita ya watsar.

Wani bayani mai kama da almara, mai kuma kama da kamar a fim ne kawai hakan zai iya faruwa, babu wanda ya karanci wani abu mai daya hada layi da kimiyya a cikinsu. Jabir kasuwanci ya karanta, ita kuma fannin aikin jarida ne, tunda ko a lokacin tana aikine da gidan Radio Freedom, bangaren labarai. Amman a cikinsu babu wanda ya manta kalmar da likitan nan yayi amfani da ita a matsayin matsalar shi. Dan ya fara ne daga kan Jabir inda yace yana fama ne da abinda ake kira

“Oligozoospermia”

A likitance, kowanne dan adam, namiji akwai adadin kwayayen da yake dasu da abokiyar zaman shi zata iya daukar ciki, to wadannan kwayayen ne suka gaza, basu kai adadin daya kamata ba, duk da akwai yiwuwar zai iya haihuwa, amman cikin kaso dari, nashi ya rage da adadi mafi rinjaye, akwai kuma wasu hanyoyi da zai iya bi, sannan ba cuta bace da bata da magani. Inda matsalar take kasancewar Aisha yake aure, itama kuma tana da tata matsalar da ake kira

“Endometriosis”

Ko da wasu a cikin kwayayen nashi sunyi nasarar tsallakewa to zasu mutune a jikin Aisha, kuma a wajen likitan bayan ya yanke mata duk wani buri da take dashi ta hanyar sanar da ita cewar tata matsalar har zuwa yanzun bata da magani, saiya dora da fadin yanda take cikin mata masu sa’a da suke dauke da wannan lalurar, saboda bata duk wasu ciwuka da su suke fama dashi. Ko ciwon mara a lokacin al’ada na yini dayane takeyi, data sha magani kuma shikenan, zai wahala ta kwana dashi. Duka dai ko da matsalar Jabir ta kau, idan aka auna yiwuwar samun haihuwa a tsakaninsu to cikin kaso dari su kaso biyar ne, ko kasa da hakan. Ko da ake wani abin yafi karfin kuka, Aisha bata gama gamsuwa ba sai ranar, babu abinda yake cikin kanta sai tunanin yanda ta rako mata duniya, yanda take amsa sunan mace batare data cika macen ba, ashe nakasa kala-kala ce?

Irinta guda nawa ne a duniya? Masu yawo da nakasa batare data fito ta nuna a jikinsu ba?

“Allaah Ya baki yara nagari da zasu kyautata miki kema”

Addu’ar Mummynta kenan duk idan zatayi mata wani abu da taji dadi, ashe addu’ar ba’a ko daga ta daga inda tayi mata ita balle tayi sama har a amsa saboda tazo duniya da nakasa, nakasar rashin haihuwa. Tun a taxi din da zata mayar dasu hotel din da suka sauka Jabir yake kokarin rike hannunta tana ture shi, batason wani lallashi, bata kuma son jin komai daga bakin shi, saboda ba zai taba fahimta ba, ko yanzun za’a iya dora shi kan magani ko hanyar da zai samu lafiya, kuma daya samu idan ya kara aure zai haihu, zai ga yaran shi, ita kuma fa? Ko da bai samu lafiya ba tana jin likita na fada masa hanyoyin da zasu iya samun yara, sai dai a duka hanyoyin zata ganshi tare da wata ne, kwan nashi ba’a jikinta zai girma ba balle jinin ta dana abinda Jabir zai haifa ya gauraya.

Tun yana kokarin ganin ya lallasheta har ya dauki ido ya saka mata, haka suka tattara suka dawo, suna sauka filin jirgi tace masa gidansu zata wuce, yace mata to, sai su fara sauketa, kafin a kaishi gida, ta girgiza masa kai, ai tayi magana dasu za’a zo a dauketa, bai mata magana ba, alamar ranshi ya baci, tafiya kawai yayi ya bude mota ya shiga. Saida taji ta a jikin Mummynta tukunna ta fashe da kuka, kukane ta yini tana yi, ko da zazzabi ya rufeta ma bata daina shi ba. Lokacin da Daddynta ya dawo kuwa fada ya farayi kamar zai aro baki

“Ya za’a bar yarinya da ciwo haka”

Bai ma ji maganar Mummynta da take ce masa ta kira an dubata ba ya kama hannunta ya dagata suka tafi asibiti aka sake dubata tukunna suka dawo, ko da yaji matsalar karyatawa yayi. Da kanshi ya kira Jabir yace masa zai sake fita da ita wata kasar, Jabir yace masa

“Ba damuwa”

Bai kuma kirata ba, kusan kasashe biyar suka je tare da Daddynta amman magana daya ake fada musu, da suka dawo ma, shiya sake kiran Jabir yace yazo ya dauketa. Bai musa ba yazo, har cikin gidan ya shiga, zuwa lokacin kuma tasha jinin jikinta, dan bai kalleta ba, a watannin da sukayi suna yawon nan ko sau daya bai kirata ba, ita dai tana kiran shi in suka gaisa sai yayi shiru, itama tayi shiru

“Shikenan Tasha? Baki da wata matsala ko?”

Zai tambaya, in tace a’a to zaiyi mata sallama ya kashe wayar. Nasiha sosai Daddyn yayi musu ta hakuri da kuma daukar kaddara kafin suyi masa sallama cike da girmamawa. Ko da suka koma dinma haka Jabir ya cigaba da shareta, sai da ta same shi tana masa kuka tukunna ya sauke mata haukan da yake ji

“Ni bani da muhimmancin a wajenki ai, damuwarki taki ce ke kadai, shisa kika tafi gidanku, idan duniyar kike so mu zagaya ina da halin da zamuyi hakan Tasha, ke kinsani, sai kika sake nunawa Daddy ni din na gaza akanki, ba zan iya kula dake ba saiya taimakamun…”

Duk yanda taso ta bashi hakuri ranar abu yaci tura, basu taba wuce kwana biyu suna fada ba, amman satinsu biyu akan wannan abin, dakyar ta samu suka shirya. Sai lokacin kuma suka fara tattauna matsalar su, sai lokacin tayi kuka a gabanshi akan matsalar, ta bari duka wani rauni da karayarta ya bayyana. Ya sha gaya mata bashi da ra’ayin mata biyu, duk kuwa da hudu mahaifin shi yayi kafin rasuwar shi, kuma a cikin yayyen shi maza akwai masu mata biyu. Sai dai ko iya abinda ya kan fada kenan, a kalaman shi babu inda zatace yayi mata alkawarin zama da ita kadai har karshen rayuwar shi, yanzun ne dai take son yayi mata wannan alkawarin. Taji da bakin shi yace dan bata haihu baya nufin zai kara aure, zasu zauna a haka, zasu cigaba da addu’a wannan kaso biyar din ya faru akansu. Sai baice mata komai ba, saiya zabi ya riketa kawai a jikin shi yaja bakin shi ya rufe.

Shi ya samu Hajiya Hasina ya fada mata sakamakon gwajin da akayi musu, kamar ko yaushe damuwar shi ta Hajjya Hasina ce, hankalinta ya tashi matuka

“Yanzun kai sun doraka akan magani ne ko saika sake komawa?”

Kai ya girgiza mata

“Ina so in nutsu ne sai in sake komawa Hajja…”

Numfashi taja tana saukewa

“To gaskiya kazo ka koma da wuri, dan ka samu ka kara aure nima inga jininka kafin kasa ta rufe mun ido”

Da wani yanayi a muryar shi yace

“Ba zan kara aure ba Hajja, ba zanyiwa Tasha haka ba”

Bude baki Hajiya Hasina tayi Jabir yai saurin cigaba da magana

“Da nine, akace bana haihuwa gabaki daya, ku duka zaku gode mata idan ta zabi ta zauna dani, ku duka zaku ga bakinta idan ta nemi in saketa…dan Allaah Hajja, karki ce wani abu, karki sa inyi musu dake, ku bamu lokaci, yanzun ma muke fuskantar wannan matsalar…muna bukatar lokaci mu karbi al’amarin…”

Har a cikin idanuwanta yaga yanda take kokawa wajen danne zuciyarta. Amman ya sani, shine, ba wani ba, abinda yake so shi zai samu a wajenta. Kanshi ta shafa da yake yana zaune ne a kasa kan kafeta dai-dai wajen kafafuwanta, yanda yakeyi duk idan tana waje, ko akan kujera yake ta shigo falon kuwa, zai tashi ya koma kusan da kafafuwanta ya zauna, wani lokacin kuma ya dora kanshi a kafafuwanta ko gefensu kan kujerar. Ya kuwa sauke numfashi yana maraba da lallashin da takeyi masa, zuciyar shi da take wani irin zafi yaji ta sanyaya kadan. Ya jima a gidan kafin ya tafi, daya koma ma, basa komai a gidan shi da Aisha banda kwanciya, wuni suke a daki, abinci kuwa in suka siya har kofar gida ake kawo musu, Jabir ya fita ya karbo musu, akan gado nan suke ciki, sai kuma sallah.

Ranar na uku ne sukaji ana buga kofar falon, sun san kowaye kuma na gidane, data kalli Jabir saiya kauda kai, dole ta sauko daga gadon, taje ta dauki abaya ta saka a jikinta tukunna ta fita. Yan gidansu Jabir ne, su dukansu, mazansu da mata, da wasu irin kulolin abinci da irin na saka abin sanyin nan, masu gaisheta da wadanda ya kamata ta gaisar duk aka kacame, da taje ta fadawa Jabir fitowa yayi yana mamaki. Yasan Hajiya Hasina ce ta fada musu, babu wanda yayi masa maganar a cikinsu, an zauna aka wuni ana shiririta, suka ci suka sha, Zaitun da take sana’ar hada lemuka da smoothie tazo musu dashi kala-kala. Hanyar suce ta nuna masa in yana bukatar su suna nan tare dashi, a shirye suke da su bashi duk wata gudummuwa da take karkashin ikonsu, kaunar da suke masa na daya daga cikin abubuwan da yake girmama samu a rayuwar shi.

Watanni shidda tsakani kuma, wani yammaci Ibrahim ya same shi

“Hajja ta hana mu tayar maka da maganar nan Jabir, yanzun ma bata sani ba, na kasa hakuri ne, idan nace maka bana kwana da abin nan ina tashi dashi karya nakeyi, baka so ka kara aure, naji wannan, duk da ba zan taba fahimta ba…”

Kallon shi Jabir yake tunda ya fara magana

“Muna da yara, ina da har guda biyar, nawa zan baka a ciki Jabir? Ko duka kake so? Idan nawa basuyi maka ba gidan duk wanda kaje ka dauko da babu wanda zai hana, sai shawara muke mun rasa ya zamu tunkare ka, watakila Allaah Ya tsara hakan ne, shisa ya bamu yara da yawa, saboda zaka dauki wasu a cikinsu”

Sosai Jabir yake kallon shi, yaransu nashi ne, haihuwar su kawai sukayi, amman ko su da suke yayyen shi baisan zaiso wasu halittu sama da soyayyar da yake musu ba sai da yaransu suka fara rugowa suna fadawa jikin shi, sai da suka fara daukar waya suna kiran shi, sai da yarinyar Ibrahim Muhibba tace masa

“I love you Uncle”

Ya duba zuciyar shi yajita cike fam da wani yanayi da ba zai misaltu ba, kamar duk inda ya duba kaunar yarinyar ce, kafin su fara haihuwa sun sani, ba gidajensu yake zuwa ba sai da wani dalili, amman tunda suka fara tara yara, yasan lokuttan da basa da makaranta, duk karshen wata akwai rana daya da yake warewa ya kwashe su suje yawo. Kuma yasan duk wanda yace zai dauka a ciki, jakar kaya kawai za’a miko masa

“Yaranku nawa ne har abada Hamma, ko baka zo ba, nasan duk yaran da nace zan dauka ba zaku hanani ba, hakan kawai wata garkuwa ce a wajena, amman idan na dauko a yanzun, zanji kamar na yanke duk wani fatane, kamar har abada ni ba zan samu nawa ba…bansan ko kagane abinda nake nufi ba…”

Numfashi Ibrahim ya sauke yana kallon shi, kafin ya jinjina masa kai a hankali

“Muna nan, kasani ko? Kome kake bukata”

Murmushi yayi, ko yanzun din murmushin ne ya sake kwace masa, saboda zaiso ganin fuskokinsu randa zasu rike gudan jinin shi a hannuwansu

Sa’adatu

Sa’adatu kawai yake jira

<< Tsakaninmu 20Tsakaninmu 22 >>

1 thought on “Tsakaninmu 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×