Skip to content
Part 29 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Gobe ko jibi yace, taji shi, rangadau, balle tace ko kunnuwanta ne suke son suyi wasa da kwakwalwarta

“Idan na dawo gobe ko jibi sai muyi magana, lokacin kin kara warwarewa”

Abinda yace kenan, babu kalma daya data manta, har yanayin fuskar shi da idanuwanshi lokacin da yayi maganar yana cikin kanta. Amman yau kwana shida kenan, wasu kwanaki yanzun da take zaune tana yanka cucumber din take ganinsu kamar basu faru ba, kamar basu zo sun wuce tare da wasu cikin kwanakin rayuwarta ba. Ta kuma daina dokin duba wayarta duk sanda zatayi kara da alamun shigowar sako. Haushin kanta ma takeji da take dauka tana da wani matsayin da zai turo mata ko da sakone ya fada mata uzurin da ya rike shi duk kwanakin nan batare daya ko kira yaji ya ta kara ji da jiki ba. Eh ya ta kara ji da jiki mana, ko da tace masa taji sauki ai batace ta warke ba. Data gama ta mike dan yunwar da takeji, hanjinta har nadewa yakeyi. Taci duk wani kayan kwadayi da take tunani har yanzun sun fara hau mata kai.

Shisa yau tana tashi taji babu abinda take marmari sai wake da shinkafa, ba garau-garau din da aka saba watsa musu ba, hadin yan gayu da take gani a waya. Data duba store din kaf, bata ga wake ba, saina gwangwani, harda wasu gwangwanaye data ga hoton masara a jiki, tana cewa a kasan ranta zata bude daya taci taji ita kuma masarar gwangwani ya take, haka ta bar store din tana jinjina al’amarin masu kudi. Wajen maigadi taje ta bashi dubu uku, tace ya hau abin hawa a ciki, ta kuma yi masa lissafin abubuwan da zai siyo mata. Dokin cin wake da shinkafar ne yasa ruwan shayi kawai ta sha me kauri da wainar kwai. Ga hanjinta nan yanata nadewa waje daya kuwa, ta dauka tunda gas ne yanzun, wake zai mata sauri wajen dahu, dan tana daga cikin mutanen dake da nauyin hannu wajen dafa wake, sai yayi mata sama da awa akan wuta kome zata zuba masa kuwa. Lokacin da suke gida bata zuba wake, saboda Amma zatace tana cinye musu dan gawayin ne, daga baya ma sai aka daina bata, sai dai wani ya dafa.

Ta zubawa maigadi a kular da yanzun ta ware da sunan tashi ce, ta dawo ta hada nata a wani filet, ta kawo cucumber, lettuce da sauran kayayyakin data yayyanka ta jera yanda yayi mata kyau a ido, sannan ta kawo soyayyen kifin data gyara ta zauna ta cire duk wata kaya da take jiki, ta barbada maginta, ta saka cokali, ta dauki filet din da robar yaji ta nufi falo inda ta ajiye akan kafet, gara tana kallo tana ci, sai yafi shiga, taje ta dauko wani lemon kwakwa na kwali da tunda ta dandana shi yayi mata dadi ta saka shi a gaba, yanzun sauran kwarori. Sai ruwa, ta dawo ta ajiye tana sake kallon wake da shinkafar kamar kar ta cakuda wani sashi ta ruguje kyawun da yayi, da hanzari ta nufi kicin din dan ta dauko kofi, ta dawo bata kai da zama ba aka kwankwasa gidan, zuciyarta taji ta buga, saboda tana da yakinin babu wanda zai kwankwasa mata gida a wannan lokacin idan ba Jabir ba.

Jikinta taji yayi wata irin amsawa, kamar duk wani doki na jiran shi da takeyi ne ya taso ya dawo mata a lokaci daya, a hankali ta taka zuwa kofar tana budewa, shine kuwa, kamshin da yake ya daki hancinta data ja numfashi, yana sanye da wani yadi ruwan toka mai laushin gaske. A littafin ance yan gayu nada kamshinsu, musamman maza irinsu Jabir, duk inda zasu shiga da anji kamshin ansan sune, amman yanzun haduwa ta nawa sukayi kenan da Jabir? Ita dai bata jin zata iya tantance wani kamshi guda daya da yakeyi. Kawai dai koya ya kusantoka koya giftaka zakaji sanyayyen kamshin da yakeyi, kamar ba guda daya bane, kamar ko yaushe yana cikin kamshine daban-daban.

“Ina wuni”

Ta furta tunda azahar tama wuce

“Sa’adatu”

Ya fadi a matsayin amsar gaisuwar yana shiga cikin dakin, hadi da mayar da kofar ya rufe, sai ta taka itama tana bin bayan shi, ta kuma zauna a kasan da tayi niyya. Kan kujera Jabir ya zauna yanajin kamar wani numfashi yake shaka na daban tunda ya daga hannu ya kwankwasa kofar, numfashin da ya samu wata tangarda da son ganinta, son jin ya take a kwanakin nan amman ya dinga dannewa. Yanzun kuma daya dora idanuwan shi akanta da idanuwantan nan, yanayinta da yake kwance wasu kananun notika a cikin kanshi sai yaji numfashin ya koma masa dai-dai. Abincin da yake ajiye yake kallo yana son gane menene da menene, yayi masa kyau a ido sosai, yaga shinkafa, ya kuma ga wake, amman shinkafar tayi masa duhu, batayi fari yanda ya saba gani ba, ba kuma tayi kalar da zaice akwai cefane a jiki ba, kamar dai tare da waken aka dafa idan hasashen shi dai-dai ne

“Abinci zakici? Sai yanzun zakici abinci?”

Ya jera mata tambayoyin a lokaci daya yana kuma dorawa da wata tambayar

“Wanne irin abinci ne wannan? Tare da waken kika dafa?”

Batasan lokacin da murmushi mai dan sauti ya kwace mata ba

“Garau-garau ne”

Ta tsinci kanta da fadi tana nazarin fuskar shi da take nuna kamar bai taba ganin an hada wake da shinkafa an dafasu waje daya ba, balle kuma ya taba jin wani abu waishi garau-garau

“Meye garau-garau?”

Ya tambaya da dukkan gaskiyar shi, yana raba idonshi da abincin ya sauke akanta, dariyarta take dannewa, itama kallon shi take taga ko wasa yake mata, ko kuma so yake ya raina mata hankali, amman babu komai akan fuskar shi sai abinda turawa suke kira da curiosity, da hakikanin gaskiyar shi baisani ba, kuma so yake ya sani, janyo robar yajin tayi ta bude, ta dan diba, ta saka a gefe ta juya wani sashi da komai da komai tana juya filet din saitin Jabir

“Sauko kaci kaji”

Saboda inda gaske baisan wake da shinkafa da mai da yaji ba, to shi yafi bukatar ya dandana wannan hadin, yau yasan me kudi da gayun shi suke katange shi daga samu. Sosai yake kallon abincin, na farko, yana daya daga cikin mutane masu bala’in zaben abinci, tunma yana yaro kuwa, ko shayi zai sha akwai yanayin yanda yake son komai, bakin shayi ko da hadin su madara, yana son ovaltine, bayason danginsu Milo, a cewar shi dandanon daban ne, shinkafa kuwa yanda duk za’a sarrafata baifi kala hudu yake ci a ciki ba, doya, yana son doya ita, yanda kuma duk za’a sarrafa masa ita zaici, in za’ayi sati ana sauya masa ita zaici, duka dai in za’ayi jimla abinda yake ci zai wahala ya haura kala goma. Sauran abubuwan kuwa a wajen Aisha yake ganin wasu, kuma yanda duk zatayi ta rokonshi ko dandanawa ne yayi bai taba gwadawa ba.

Kuma ko kasar ya bari, baya taba wuce wadannan cimar, amman yanzun Sa’adatu tana masa tayin wani abinci ma da bai taba gani ba a rayuwar shi, kuma da yake jikinshi na son nuna masa iyakar shi saiya sauko kan kafet din, mamakin kanshi na kamashi, musamman yanda ko a falo zaici abu sai Aisha ta janyo masa tebir gaban shi, ita takan zauna a kasa, shikuwa bayason cin abu a kasa, yafi son dai yaji shi daga sama. Gashi zaune kan kafafuwanshi daya lankwasa, hannun shi na kama cokalin ya kuma dibi abincin da yaketa tashin kamshin da baisan kona meye ba, yayi Bismillah yana kaiwa bakinshi. Dandano ne da bai tabaji ba, dandano daya gauraye duka bakin shi yana saka shi sake kai cokalin a karo na biyu kafin ma ya hadiye wanda ya diba, wannan karin kuwa baiyi kwauro ba kamar dazun, ya kusan cika cokalin. Daman daga nan gidan yake da niyyar tsayawa ya siyi pizza a hanya saboda tun abincin safe bai samu ya kara cin wani abu ba.

“Garau-garau”

Ya sake maimaitawa a cikin kanshi yana sake diba a karo na uku, Sa’adatu na kallon shi tana murmushi, hadi da neman tata yunwar ta rasa, lemon ta bude ta zuba masa a kofi tana dan tura masa, sai lokacin ya kalleta

“Ina ci..zan ci”

Kai ta jinjina masa tana mikewa, Allaah Ya taimaka tayi shi da dan yawa, daman da nufin har dare in tayi marmari saita kara, wani ta zubo, bata tsaya jera komai irin dazun ba, dan kifinma haka ta sakko shi gunduwa gunduwa tunda iya wanda zatacine ta gyara. Data dawo saita same shi ya ajiye cokalin a cikin abincin kamar yana jiranta

“Kaci wannan, ga wani na zubo”

Cewar Sa’adatu

“Na cinye wanda kika hadane, ki sake hadamun”

Zama tayi, saita tura masa robar yajin a gaban shi

“Ga yajin nan ai”

Da wani yanayi a fuskar shi yace

“Ki hadamun”

Batasan meye a yanayin yanda ya fadi kalmomin ba, ji tayi dai kamar ta zama kyandir, kalmomin nashi kuma wutace ya kara mata da in batayi maza ta matsa ba, narkewa zata fara yi. Shisa taja filet din, ta kuma sake saka yaji ta cakuda masa da yawa wannan karin

“Nagode”

Ya furta a hankali, so dai yake da gaske yaga ta fara narkewa, abincin ma nata duk dokin da take tayi da yunwar da takeji sai taji ya rage mata armashi, Jabir kuma ba kallonta yakeyi ba, hankalin shi nakan abincin da yayi masa wani irin dadi na ban mamaki

“Waye ya koya miki irin abincin nan?”

Yace yana sakata yin dariya

“Bawani abu bane mai wahala fa, wake da shinkafa ne da mai da yaji, kowa ma ya iya”

Yaji ta, amman bai gamsu ba, kowa fa tace, harda Aisha kenan? Itama ta iya? Ta iya abubuwa da yawa shi shaidane, ta kuma san abinci kala-kala, musamman na gargajiya da take so, idan batajin shiga kicin din takan saka su Nenne su nemo mata wadanda zasuzo har gida ayi mata ta biya, ko Sa’adatun ma ai irin hakan ne sanadin haduwarsu. Amman dai a shekarunsu shidda da aure, inda ta iya wannan, to da ko sau dayane yaga tayi. Har wani danwake ya taba ganin tayi, wani abu da ko kalarshi batayi masa kyau a ido ba, itama saida yace

“Me yasa zakici abu green haka? Kalar da kuka zuba batayi yawa ba?”

Ba zai manta ba har kwarewa tayi, kuma bayan ta dawo dai-dai ma data kalle shi saita kwashe da dariya kamar duk watan bataji wani abu daya sakata nishadi sama da abinda ya fada ba

“Kowa kikace fa, ni ban iya ba”

Yayi maganar yana daukar kofin data zuba masa lemo ya fara kurba, ya cinye wanda ta sake hada masa, kuma cikinshi dai ya cika, bakin shine bai koshi ba, ba zai biye masa ba, tunda yasan yana cikin mutanen da in sukayiwa cikinsu wannan mugun cikawar suke fama da matsalar narkewar abinci. Dariya Sa’adatu ta sakeyi

“Ba wahala da gaske, daka gyara wake ka zuba ya dahu fa saika wanke shinkafa ka juye, ka saka gishiri kadan, ka rufe, ka dinga dubawa harya dahu. Shikenan ka sauke, ka soya mai da albasa, ka soya kifi in kanaso, saika soya yanka su lettuce, timatir da albasa sai cucumber, wasu ma suna saka dafaffen kwai”

Kallonta yake, yanda ta dage da gaske tana koya masa abinda ba zai taba dafawa ba, shi in banda ruwan zafi meya iya dafawa? Ya yanka su timatir, shi zaije kusa da wuka

“In yanka su me? Salan in hada da yatsana in guntule ko? Ke bakisan hankalin sarrafa wuka mata kadai akayiwa ba”

Sosai take dariya, tana mamakin shine yake magana haka, daman haka yake da abin dariya? Amman daga nesa inka kalli fuskarshi zakaji tsoron ko gaishe dashi saboda yayi kama da mutane masu tsananin girman kai, irin jaruman cikin novel, masu miskilanci da shiru-shiru, wanda matansu ma ba kullum suke ganin hakoransu ba, balle kuma akai ga maganar wasa da dariya haka

“Ai shikenan tunda kin dauka wasa nakeyi, amman bafa wai ban iya komai ba, ina dafa ruwan zafi”

Ya karashe maganar kamar dafa ruwan zafin wani abune na alfahari. Kai kawai ta iya girgizawa tana dariya, yana kallonta, shima murmushi yakeyi. Yanajin yanda ashe akwai wata mace bayan Aisha, da zatasa shi jin irin abinda yakeji yanzun, nishadi, wani yanayi kamar bashi da nauyin komai a kanshi, kamar baya bukatar saiya tauna duk abinda zai fada, baya bukatar taga hankalin shi ko akasin hakan, a gabanta zai iya fadar komai, zai iya zama kanshi batare da hakan ya canza yanda take kallonshi ba. Abune daya taba faruwa akan Aisha kawai, shisa yayi zaton akanta zai kare, wannan yanayin

“Kayi kokari sosai, wanda ya iya dafa ruwan zafi ai ya iya mai wahalar”

Kafadu ya dan daga

“Inajin sarcasm din nan Sa’adatu, bai dameni bane, saboda ina alfahari da kaina”

Dariyar ta sakeyi tanajin wani nishadi data manta rabon da taji shi, suna zama a gida, suyi hira, suyi dariya, har wasu dararen ma sai taji hakarkarinta na zafi, daga Fa’iza har Abdallah gwanaye ne wajen hira da son nishadi, su uku kawai a gida idan ya dawo da daddare ta tabbata wani lokacin suna damun makota da rakadi da dariyarsu. Amman wannan ya fita daban, nishadin yau, tare sa Jabir, ba kuma dan shi bane, tanajin kamar tun Tahir, duk samarin da tayi, akwai wani kadaici da yake kasan ranta, ba kuma na kewar Tahir ba, kadaici ne da kowanne cikakken namiji ko budurwa da takai wani munzali take fama dashi, ko da kuwa ba kullum ba, a wasu ranaku, zataji tana son kasancewa da abokin tarayya, abokin hira, ba yan gidansu ko kawaye ba, abokin raba rayuwa tare, irin wannan kadaicin, shine yau Jabir ya tabo mata yana sata jin ko da na yaune kawai, ya cike mata wannan kadaicin.

“Ka koshi?”

Ta tambaya, ya daga mata kai

“Ki kwashe, kamshin na shiga hancina, bakina naso har yanzun”

Murmushi tayi tana jan filet dinshi ta hada da nata da itama rabi taci, tasan zata bukata anjima, kaso mai girma na yunwar da takejine ta rasa inda ta nufa. Hade fillatan tayi waje daya ta kife ta dauki wani kofin ta koma, Jabir yana nan zaune inda ta barshi, itama inda ta tashi ta zauna, ta dauki murfin robar yajin ta rufe, tana zubama kanta lemon itama ta fara kurba a hankali tana tunanin abinda zata fada da hirarsu zata cigaba, kar shirun nan dayayo sallama ya samu wajen zama

“Kinga banzo ba ko?”

Kirjinta ya buga, tana tuna ashe ta shaka da rashin zuwan nashi, ta mishi uzuri ta soke yafi a kirga, tayi fushi, ta kuma lallashi kanta, taji haushi, abubuwan da taji ma a kwanakin ba zasu lissafu, kawai duk ya shafe matasu yanzun da yazo, har yaci abincin data dafa, ya kuma sakata dariya. To meye yama yi saura a ranta a halin yanzun banda nishadi?

“Akwai abubuwan dana tsayayi ne. Kinga yau juma’a ko?…”

Kai ta daga masa

“Kafin nan, kina da wani I.D card?”

Da mamaki take kallonshi

“I.D card?”

Ta tambaya cike da mamaki, ita da ba ma’aikaciya ba mai zai hadata da I.D card? Wannan karin shine ya daga mata kai, saita girgiza masa nata

“Kowanne iri fa”

Ganin ta sake girgiza masa kai yasa shi fadin

“Ko irin na zabe”

Kai ta jinjina, wannan tana dashi, kuma ba zata manta ba, Tahir ne ya sakata a gaba saida taje tayi, dan ranar farko ko awa batayi ba ta dawo gida saboda layi, da yake sunzo nan kasan unguwarsu anata yiwa mutane, dashi ma tayi amfani wajen bude bankinta.

“Ina da wannan”

Numfashi ya sauke, dan ya fara tunanin mafita idan bata dashi, da sai dai ya karbi karamin hotonta ayi mata na kamfanin shinkafarsu a matsayin daya daga cikin ma’aikata

“Idan yana gida kiyi waya a kawo miki, zamuje Abuja ranar lahadi, amman sai da yamma, wajen karfe uku da rabi haka, ki shirya, kaya biyu ko uku zaki dauka”

Kallonshi takeyi kamar wani yare yakeyi mata ba hausa ba, zasuje Abuja? Ita dashi? Ita dashi da Aisha? Natsuwa tayi tana kallon bakinshi da yaja ya rufe kamar ba zai mata wani karin bayani ba, ita kuma batasan ta inda zata tambaye shi ba. Mikewa ma taga yayi

“Ki kira fa su kawo miki karki manta, ko in turo a kaiki ki dauko?”

Kai ta daga masa da sauri

“Eh dan Allaah, a kaini”

Ya danyi murmushi

“Tam. Saiki shirya gobe idan Allaah Ya kaimu zan aiko akaiki”

Fara’ar dake fuskarta sai taki boyuwa, tanata murmushi ta mike itama. Sai lokacin ma yaga doguwar rigace ta abaya a jikinta, sai hula da ta saka, jin da yayi yana so ya rike ko da hannunta ne yasa shi fara tafiya

“Nagode…”

Cewar Sa’adatu da murmushi ya kasa kwacewa, bai amsa ba ya saka takalmin shi ya fice daga gidan, ita kuma ta kulle kofar, saita wuce daki kawai ta kwanta a gado, ta janyo wayarta da nufin kiran Fa’iza, sai kuma ta fasa, gara tayi mata bazata. Littafin data fara karantawa jiya da daddare ya kuma ja hankalinta ta bude, Zanen dutse sunan shi na Aisha Shafi’i, daman tana ganin sunan taji wani sanyi, dan ta karanta Waye shi, labarin ba karamin tsaya mata yayi ba, tayita so ta kara samun wani littafin na marubuciyar sai dai bata san hanyar da zata biba, karatun ta cigaba dayi, tana gaba tanajin kamar itace Jidda, kamar kuma Madaki ne Jabir. Bambancin da yake tsakanin su hudun ba mai yawa bane ba. A madadin auren hadin da akayi musu, ita nasu na yarjejeniya ne.

Sai kuma a madadin ka’idar da Madaki yake tunanin zai dibarwa Jidda kafin ya saukake ma kanshi aurenta, ita hannu ta rattaba a takarda tana yarda da wannan kayaddajjen lokacin da kanta, sai kuma Jidda ta zama daga cikin mata masu sa’a, Madaki bashi da mata, kuma zuciyarshi saita haska masa ita, saiya sota, wani irin so da ya dinga ratsata yana sakata yin fata kala-kala. Lokacin da ta ajiye littafin kafin ma ta kai karshe batasan siririyar kwalla ta kwace mata ba, sai da taji zubowarta da duminta

Inama, Inama
Ace ta zama Jidda, Jabir ya zama Madaki
Tayi duk wani kokarin da zata iya yasota
Amman kuma ai a tsakaninsu akwai Aisha
Fatane kawai da ta kowacce fuska alamu suka nuna zai tsaya a fata kawai
Wata kaddarar sai dai a littafi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 28Tsakaninmu 30 >>

5 thoughts on “Tsakaninmu 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×