Skip to content
Part 34 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Tana daya daga cikin mutanen da suka fi kowa dokin shigowar watan azumi, a baya saboda canjin abincin da akan samu ne. Ko babu komai ana iya yin azumi har a gama ba’ayi musu tuwo ba. Duk da ba soye-soye akeyi ba, anayin kosai kullum, da kunun tsamiyar Abida da tayi matukar kewa. Sannan idan an samu sarari za’ayi musu awara, dankalin hausa ko a dafa doya, kwan idan an samu akan soyane a rarraba kowa a saka masa a gefe tunda ba isa zaiyi ace a soya doyar ba, idan ma akwai kwan, mai fa? Duk da haka takan jita a sama idan azumi yazo, ga kuma kankara za’a siyo a hada kunun zaki ko zobo, ko yan lemukan ledar nan danginsu Tiara da Euro, da yawa suke hada wannan, dan ko su a tsakaninsu basu da kudi to tana basu a siyo a jika kowa ya sha.

Idan an idar da sallar asham kuma haka suke zama su duka a tsakar gida a dinga hira, kowa na dan taba abinda ya rage daga kayan buda bakin shi, idan angama abinci kuma wadanda basa iya cin komai lokacin Sahur sai su zuba suci a lokacin. Abubuwa sun canza sosai bayan rasuwar Habibu, amman wannan al’adar ko daya ba’a sauyata ba lokacin azumi, ko da suka zama basu da yawa a gidanma hakan suka cigaba dayi. Yau da ya rage saura kwana daya ko biyu a yanda ake saka rai a dauki azumin, bayan doki, Sa’adatu najin wani yanayi na kewa ne yanata dukan zuciyarta, musamman kewar Abida, bata cika barin zuciyarta na kaita wajen nan ba, saboda bata iya tsaida hawayenta duk idan hakan ya faru. Tasan tana kaunar Abida, bata taba sanin girman kaunar ba saida ta wayi gari babu Abida a filin duniyar gabaki daya.

Haka yinin ranar ya wuce mata da wani irin sanyin jiki, kuma kamar tasan za’a sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a ranar, tayi miyarta, dan haka saita dafa farar shinkafa, ta zubawa maigadi a wata babbar kula yanda zaici lokacin kuma yaci da sahur, harda lemo da ruwa ta hada masa. Data koma tayi isha’i, sai ta watsa ruwa, tana fitowa Fa’iza na kiranta a waya, ta dauka da fadin

“Matar Yayaa”

Sai dai taji sallamar Abdallah da bai jira ta amsa ba ya dora da

“Nine Sa’adatu, wayata ba caji, nace bari mu kiraki data Fa’iza, yanzun na dawo na samu mijinki ya cika mana gida da abin arziki…”

Kalmar “Mijinki” tayi mata wani iri, yanda takanji duk idan Fa’iza ta kira Jabir da mijinta.

“Na kirashi nayi masa godiya, Sa’adatu kayan da yawa, zanyi shekara ban siyi abinci ba, shisa nakejin kamar godiyar duk da nayi tayi kadan, Allaah Ya saka da alkhairi Ya kara zaunar daku lafiya”

Yanayin muryar Abdallah da yanda ta sauka sai taji yana neman karya mata da zuciya, harya ba Fa’iza banda Amin ta kasa cewa komai, da alama Abdallahn ficewa yayi ya barsu, Fa’iza ce take fada mata buhun shinkafa kanshi guda biyu ne, harda jarkar farin mai da ma manja, duk wani abu da ake tunani na kayan abinci, sai abinda ya manta. Ga kuma kwai da kayan shayi. Da yake tsohuwar wayarta Abdallah ta ba, shikuma saiya hada da tashi da kuma ta Fa’iza ya siyar ya dauko mata mai kyau da kudin, shisa suna yin sallama, ta dauki kayan tana turawa Sa’adatu ta whatsapp, ita kanta saida ta girgiza da ganin yawansu. Yaushe rabon data saka shi a idanuwanta? Tunda aka shiga kwanaki bakwai saitayi duk wani kokari da zata iya na danne zuciyarta wajen daina lissafin kwanakin da yayi bai tako inda take ba.

Ya dai tura mata wani gajeran sako yana tambayar lafiyarta da kuma in tana bukatar wani abu, ta mayar masa a gajarce itama. Yanzun kuma ga azumi yazo, zata sake maida hankalinta ne kan ibada, tasan tunani zai rage mata sosai, ta dai lalubo lambar shi ta tura masa sakon godiya da addu’ar karin budi da kuma arziki mai albarka. Bata tsammaci amsar shi ba, kamar yanda bai bata mamaki ba ta hanyar dawo mata da amsar. Tayi kwanciyarta, ta saita alarm a wayarta gudun makara tana duba komai ta tabbatar karar a karshe take, tukunna tayi addu’ar bacci, bata kuma wani jima ba, baccin ya dauketa.

*****

Yau kwana bakwai kenan da fara azumi, ita ranar azumin farko yayo mata aike, harda dubu hamsin din da ta dinga juyawa tana mamaki, saboda abinda ma da wahala tayi amfani dashi har azumin ya kare akwai a cikin kayan, fridge kuwa tun daga na kitchen har na dining a cike yake, lemukan duka store ta kaisu, sai ta dinga dibar kadan tana sakawa a fridge saboda sauran kayan wanda zasu iya lalacewa ne idan babu sanyi. Ana azumi ana ramewa, ita kam har wasu kumatu tayi saboda bata yiwa cikinta kwauro sam, lafiyayyen buda baki da sahur takeyi daga ita har maigadi kuwa. Sai dai haka kawai take tajin babu dadi, ba da zuwan Jabir ba, ta riga ta saba tun tasowarsu, duk kiyayyar da Hajiya take nunawa Abida, azumi na kwana biyu zuwa uku take hada duk wani abu da take da karfin yi suje suyiwa Hajiyar barka da shan ruwa.

Ba kuma gidan Hajiya ba, harma da Anty Khadi da duk wasu manya daya kamata. Haka kuma takanji yayyenta ma sunce sunje gidan surukan nasu. Kamar duk da auren nasu ita da Jabir ba aure bane kamar yanda kowa yake tunani, to ya kamata a dorar da tunanin mutane, ya kamata suyi abinda ya kamata. Taso ta share, sai dai waya goma zasuyi da Fa’iza sai ta kara mata godiyar kayan da Jabir din ya sai musu, ta kuma jaddada mata tayi kokarin ganin ta kyautata masa shima ta hanyar hidimtawa dangin shi. To ita ba kudi gareta da zatayi siyayya yanda yakeyi ba, idan ma tana da kudin me zata siya ta kai musu wanda basu dashi? Sosai takejin babu dadi da kuma wani irin rashin kyautawa da yake ta nukurkusarta.

Balle yanda azumin yaketa sauri, ranar da akayi azumi goma ne ta kasa jurewa, taga katin dubu ukune, ta kuma san babu wanda zai tura mata katin idan bashi ba, yau a maimakon godiya sai ta tura masa

“Ina taso in share na kasa”

Ta ma manta text ne ba WhatsApp ba, ta shiga turawa a rarrabe.

“Nasan aurenmu ba normal aure bane ba, amman mu kadai muka sani, azumi har anyi goma, ina so inje in gaishe da Hajja inyi mata barka da shan ruwa.”

Numfashin da take rike dashi ta sauke, ita bata iya nuku-nuku ba, kai tsaye takeyin magana in dai zatayi

“Kasa azo a kaini gobe bayan Magriba.”

Dorawa ta karayi da

“Idan kaga ya kamata inje din, in kuma babu damuwa shikenan.”

Taso ta yaudari kanta wajen basarwa, kamar bata jiran amsar shi, har hasken wayar ya dauke, ta sake dannawa, wata zufa-zufa takeji duk kuwa da akwai sanyin AC a dakin, sanyin da yanzun ta saba dashi sosai da sosai, har karawa takeyi idan zata kwanta saita shiga bargo, data rufa kuma sai taji yayi mata dai-dai yanda take so. Da hasken wayar ya dauke wannan karin, kafin ta danna ya kawo da kanshi, taji kirjinta ya buga, ta bude sakon tana dubawa, tana sake dubawa ko sauran kalmomin ne suka makale, amman ta dai fita ta koma

“Ok”

Kadai ta gani, sai taji ranta ya sosu matuka, saboda bai bawa zuwan nata muhimmanci bane kome da zai amsata da Ok, me hakan yake nufi, Ok zai aiko, ko kuma Ok tayi zamanta ba sai taje ba. Data dauki wayar tana son tambayar shi saita ma rasa ta inda zata fara, saboda da gaske ranta ya sosu, batajin kuma zata tura masa wani abu na hankali idan tace tayi masa magana a yanda kanta yayi nauyi, tana shirin ajiye wayar sakon shi ya sake shigowa

“Zai zo”

Ya sake fadi a takaice

“Hmmm”

Ta furta tana yin jifa da wayar. Haka ta karasa sauran daren kafin lokacin kwanciya tanajin bacin rai nata taso mata, saida tayi karatun Qur’ani ta samu salama, data kwanta kuma sai ta nemi dalilin da zaisa taji haushin Jabir din ta rasa. Ta dauki duka laifin ta dora akanta, aurensu a wajen shi aure ne na yarjejeniya, kome kuma zaiyi mata ganin damarshi ne, tunda bayan yayi din saiya tabbatar ya nuna mata cewa kyautatawa ce daya sa kanshi badan ita ko auren suna nufin wani abu na daban a wajen shi ba, laifinta ne da takan manta, takan saka rai kuma, shisa tsammaninta ya fara dagawa, tana neman fadawa duniyar magagin da duk wani mafarki da zatayi a cikinshi shirme ne, kuma ita zai dawo ya danne ita kadai. Ta kuwa dade bata samu tayi bacci ba tana ta tunane-tunane kala-kala.

Washegari tana gama baccin safenta, saita wuce kitchen kawai, ta riga ta yanke shawara dambun shinkafa zatayi, saboda ta duba, ita ba abincin yan gayu ta iya ba, amman na gargajiya kam duk wanda sukeyi a gida bata da matsala dashi. Tana kuma da zogalen da Fa’iza ta bata, itama da yawa aka kawo mata ta shanya a inuwa ya bushe. Ranar gani tayi me zatayi da wani zogale, kamar karta karbo, ashe zaiyi mata rana. A blender ta barza shinkafar iya wadda take so. Ta ajiye shi a gefe, ta cigaba da hidimarta, kazar da tun asuba ta fito da guda biyu kuwa ta saki, ta dora, sai ta yanke shawarar daka citta, tafarnuwa, da masoro kadan ta zuba ta kuma yanka albasa wadatacciya, duk wannan kayan kamshin da take dasu saita kyale, yau yanda Abida takeyin girki haka zata kamanta, komai a gargajiyance.

Zuwa azahar ta rage aikin sosai, ta wanke hannunta ta wuce tayi sallah. Ta idar tana zaune kiran Fa’iza ya shigo, daman sunyi magana, tace mata zataje gidansu Jabir din, zobo takeso tayi mata mai dadi

“Yayanki zaizo ya kawo miki idan anyi la’asar.”

Dadi taji sosai

“Me zan bashi ya kawo miki?”

Ta tambaya, yar dariya Fa’iza tayi

“Idan nace miki muna da komai zaki yarda Sa’adatu? Komai nake nufi, harda nama da kifi…”

Murmushi Sa’adatu tayi cike da farin ciki, haka sukayi sallama, data koma kitchen din sai taji da wani irin kuzari na daban takeyin aikin. Zuwa la’asar kuwa ta gama miyarta da taketa kamshi, ga suyar kajin tayi kyau saita kara haska miyar da fashi biyu tayiwa kayan miyar saboda bataso suyi mata laushi. Dambun ne kawai ya rage, wajen biyar saura Abdallah yazo, da wata irin murna ta saka hijabinta, shima yanata mata murmushi, kullum ya ganta sai yaga ta kara kyau, kwanciyar hankali ta bayyana a jikinta. Da gaskiyar kowa da aka dinga cewa ya bi auren na Sa’adatu da fatan alkhairi, yayi hakan, yana ma kanyi, duk da wani abu a kasan zuciyar shi a tsorace yake sosai. Musamman irin hidimar da Jabir din yaketa fama yi dasu. Addu’ar dai da itace mafita akan komai ya kara dagewa dayi.

Yanda duk taso ya shiga kiyawa yayi, tana ganin kunyar nan da kawaicin da yake sa mutane da yawa suna dauka Abida ta haifeshi ya bayyana karara da tace ya shiga ciki, kamar ma ta kore shi, yayi mata sallama yana cewa akwai uzurin da yake gabanshi, ta dinga dariya, ta san babu wani uzuri. Haka haihuwar Nabila da aka matsa masa, itace ma jagora wajen janshi cikin gidan dan yaga babyn da yace a dauko masa kofar gida akaqi, saika rantse akan wuta yake zaune ba kujera ba, da yaji muryar mijinta ya shigo kuwa babu wanda baiyi dariya ba, har shi mijin ganin irin zufar da Abdallah yakeyi saboda kunya kamar marar gaskiya. Shi a dole suruki ya ganshi ya shiga cikin gidanshi, kunyar nan kuwa har Fa’iza tana ganin yana nunawa ita lokaci zuwa lokaci.

Data koma cikin gida da ledar kuwa ta dinga mamaki ganin wasu robobin yan gayu da Fa’iza ta zuba zobon a ciki, irin robobin nan da zaka gani a manhajar Instagram yan gayu na tallah dasu. Ba kuma zobo bane kawai, harda kunun ayar da yasa yawunta tsinkewa. Ta je ta samar musu waje cikin fridge din. Kafin Magriba ta gama komai, ta dauko kuloli ta saka, ta kuma jera a wani kwando, harda farfesun kifi tayi. Ta dibarwa maigadi ta mika masa tayi alwala, da kunun ayar Fa’iza ta fara ana kiran sallah, sanyin da yayi da gardin ya sata lumshe idanuwa, tana kuma cewa a ranta saita tambayi Fa’iza ta fada mata ko dame-dame ta hada kunun ayar, ta kurkure bakinta, amman harta tashi sallah ta sallame taje ta sake kurkurewa dan bata daina jin gardin kunun a bakinta ba.

Data idar, buda baki tayi, tana cin plantain din data soya da kunun ayar. Tana gamawa ta bar sauran a robar anan kan tebir a falo ta koma daki, a gaggauce ta watsa ruwa ta fito. Doguwar rigar Abaya ta dauko sabuwa dal, baka, sai wata hijabi karama ce sai dai ta sauko, dan anyi mata wani irin design ne, rubi biyuce, bula mai haske. Ta dan shafa mai sai hoda a fuskar, ta saka man lebe, ta feshe jikinta da turare, takalmi ta duba, ta kuma yi sa’a akwai kalar hijabin nata. Ta dauki wata yar bakar jaka ta saka wayarta, saita dibi kudi, dan ta yanke shawara zata sa a tsaya ta siyi tufa a hanya ta hada harda ita takai, tunda cikin kayan marmari dai shine abinda masu kudi sukafi darajtawa, sai kuwa inibi idan ta samu. Wannan tasan yafi tufar tsada, shisa ta kara dibar kudin.

Ta fita falo ta nufi wajen fridge ta fara fito da robobin tana jerawa a wani karamin kwandon, ta shiga kitchen ta dauko dayan kenan ta fito bakon kamshi ya daki hancinta, ko kafin ta daga kai tasan Jabir ne, ta kuma so ta basar saita kasa, daure fuskar da tayi niyya ma saita kasa saboda ganin murmushin da yakeyi mata, jikinshi sanye da yadi ruwan toka, ta kula duka kayanshi masu laushi ne, ko kananan kuwa, haka take ganin shi dasu har takan so ta taba taji ko laushin nasu zaiyi dai-dai da yanda take hasashe cikin kanta, ya saka hular data kara masa kwarjini

“Ina wuni”

Ta tsinci kanta da furtawa

“Sa’adatu, kin sha ruwa lafiya?”

Kai ta jinjina masa

“Alhamdulillah, kaifa?”

Ya dan daga mata kai yana dorawa da

“Sai dai inajin kishi har yanzun”

Bata san sanda bakinta ya furta

“Zaka sha kunun aya? Yayi dadi sosai”

Kallonta yayi yana maimaita

“Kunun Aya?”

Kamar bai gane me take nufi ba, ta ajiye kwandon hannunta ta rabashi ta wuce ta dauko sauran wanda tasha tana kwance robar ta mika masa, ya karba, ya kai bakin shi ya kurba kadan kamar mai tsoron jin dandanon da zai daga masa hankali, sai ya kara, wannan karin yana shanye fiye da rabin da yake cikin robar, kafin ya sauke numfashi yana karasa shanyewa

“Da dadi”

Ya fadi yana kallonta tare da dorawa da

“Ina sha”

Wajen fridge taje ta dauko masa roba daya cikin biyun data rage dan tasha ta kawo masa

“Direban baizo ba”

Ta fadi bayan ya karba saboda bataso suyi dare

“Tare zamuje”

Ya fadi kamar hakan ba wani babban abu bane ba, mamakin shi bai saketa ba ta dauki kwandon da yake gabanta, yakai hannu ya karba, sai ta wuce ta dauko dayan tana bin bayanshi har waje. Ta ja gidan, bata wani saka mukulli ba ta wuce. A gidan baya suka ajiye komai, ta bude gaba ta shiga, shikuma ya zagaya. A cikin motar ya ajiye kunun ayar da harya sha rabi, suna fita titi tace masa

“Dan Allaah ka tsaya dani in siyi apple da inibi”

Kai kawai ya jinjina mata, saboda duka yau din a bazata tazo masa, suna zuwa gida gaishe da Hajiya Hasina shida Aisha, haka sauran surukan gidan, kawai baiyi tunanin ya kamata Sa’adatu taje ta gaishe da ita ba saida tayi masa magana yau. Kamar yanda tace ne, aurensu su kadai suka san ma’anar shi, amman a wajen su Hajiya Hasina aurene kamar kowanne aure, to zuwan Sa’adatu ta gaishe dasu kuma abune da ya kamata ace yayi tun yan satika bayan auren. Shisa yaga suje taren zaifi ace sawa yayi aka kaita. Kawai ganin kwandunan ne abinda ya bashi mamaki, yasa shi tunanin komeye a cikin kulolin, ga kuma wannan kunun ayar da ya tabbatar Hajiya Hasinan zata so sosai. Shiya fita ya siyo mata apple din mai yawa da kuma inibin kamar yanda ta bukata, ya bude baya ya saka ledar.

Yaja mota suna hawa titin da zai hadasu da gidan nasu…

<< Tsakaninmu 33Tsakaninmu 35 >>

3 thoughts on “Tsakaninmu 34”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×