Sati biyu, kwanaki sha hudu, wasu irin kwanaki da Sa'adatu batajin ko lokaci da kanshi zai iya goge mata su daga cikin kanta ballantana kuma ace itace zatayi wannan kokarin. Ta ina ma zata fara? Yanda Jabir ya zabtare shekarun shi ya maidasu dai-dai da nata yake biyewa duk wani abu da zatayi a kwanakin? Ko kuma yanda na minti daya bai taba nuna mata bambancin matsayin da yake tsakaninsu wani abu bane ba. Duk yanda zatayi tunanin tayi kauyanci baya damun shi, ko wani abincin yan gayun da bata tabaci ba ta gani, zaice suyi order ta. . .
Ok
Jazakallahu khair for this amazing updates..
Shikenan tashar ta dawo zata cigaba daga inda ta tsaya