Skip to content
Part 42 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Sati biyu, kwanaki sha hudu, wasu irin kwanaki da Sa’adatu batajin ko lokaci da kanshi zai iya goge mata su daga cikin kanta ballantana kuma ace itace zatayi wannan kokarin. Ta ina ma zata fara? Yanda Jabir ya zabtare shekarun shi ya maidasu dai-dai da nata yake biyewa duk wani abu da zatayi a kwanakin? Ko kuma yanda na minti daya bai taba nuna mata bambancin matsayin da yake tsakaninsu wani abu bane ba. Duk yanda zatayi tunanin tayi kauyanci baya damun shi, ko wani abincin yan gayun da bata tabaci ba ta gani, zaice suyi order ta gwada taji ya yake, da yawan lokaci kuma abubuwan suna zama asarar kudine ta bangarenta, shi zaici nashi, itace take kasawa, saboda hasashen da tayiwa dandanon ya bambanta da yanda taji shi akan harshenta.

A cikin kwanakin kuma, guda biyar Jabir ya diba babu wani abu daya gifta musu banda kokarin ganin ya gina shakuwa a tsakaninsu, idan ba fita hidimominshi yayi ba, to yana nan, suyi hira, suyi kallo, randa tayi zobo kuwa, darduma ya dauka yaje ya shimfida, tana durawa a robobi yana rufe robar, ya dauraye, ya goge ruwan jiki, sannan ya manna mata sticker a jiki, ga kuma kofin shi a gefe daya zubo kankaru a ciki

“Kinsan dole a dinga zubamun ladan aiki ko?”

Hakan kuwa ta dingayi, daya shanye zata kara zuba masa wani, idan kankarun sun narke ya tashi ya kara zubo wasu, har suka gama. Monday din da zata fara zuwa makarantar horarwar daya biya mata kuwa, shi da kanshi yaje ya sauketa, ajujuwan lokaci-lokaci ne, kaine kuma zaka zabi wanda yayi maka, saboda taji dadin baccin safe, saita dauki ajin goma zuwa sha biyu na rana, tasan lokacin har abin kari tayi, tana dawowa kuma saita dora abincin rana, yanzun bama koda yaushe takeyin girkin ba, saboda Jabir ya gane su fita yawo, suci abinci a wajen, saiya baiwa maigadi kudi, idan sunyo takeaway kuma wani lokacin ana hadowa dashi, idan ma basuyo masa nashi daban ba, to duk wani abu da zasu rage shi din ake baiwa.

To a ranar ne sun fita da daddare, suna zaune a wajen shan ice cream din da sukaje, itace ma ta zabi ice cream din wajen kala nawa, Jabir kuwa yoghurt ya dauka sai kuma waffle. Hira sukeyi jefi-jefi, wata mata da mijinta suka shigo wajen, da yaro rike a hannun matar, sai kuma wata mace da mijin yake rike da hannunta, ita kanta Sa’adatu sun burgeta matuka, yarinyar tasha kwalliya, ga kitson da akayi mata yasha duwatsu, sai jijjiga kan takeyi, alamar karar da duwatsun sukeyi yana sakata nishadi. Da ta kalli Jabir dan tace masa yarinyar tayi mata kyau, sai taga idanuwanshi akanta yake shima, fuskarshi dauke da wani yanayi da bata taba gani ba, lokacin da suka bacewa ganinsu kuwa numfashi ya sauke mai nauyi, yana juya kofin yoghurt din dake hannunshi

“Ina so Sa’adatu, yaro ko yarinya, ni banida zari, guda daya ma idan Allaah Ya bani zanyi godiya mai yawa, ba sai na samu da yawa ba, daya mai albarka wallahi zanyi godiya sosai…”

Ya karasa yana dago da kai ya saka idanuwanshi cikin nata, fatan dake cikin nashi ya daki zuciyarta matuka

“Zaka samu, In Shaa Allaah kaima zaka samu…”

Ta fadi tana kokarin danne harshenta da yake so ya furta masa cewar zai samu fiye da daya, saboda a wannan lokacin, yarjejeniyar su data taso mata take son turewa ta fada masa zai samu, zata kuma haifa masa, ko guda nawa yake so. Amman ai ko a yarjejeniyar daya yace, daya sukace shi da Aisha, kuma wannan kusancin da suka samu baya nufin hakan ya canza ai ko? Dayan dai? Kuma a bisa yarjejeniyar da sukayi. Yanda take kokarin mantawa baya nufin shi Jabir din ya manta ai, tunda kullum sai taji shi yana waya da matarshi, yana kuma fada mata tsananin kewarta da yayi. Ko mintina sha biyar basu kara ba, ya daiyi musu siyayya, a mota ma ba suyi wata magana ba har suka karasa gida. Ita kadai ta kara saka wani abu a cikinta, Jabir zuwa yayi ya kwanta.

Yanayin shine ya kashe mata jiki, yanayin shine kuma yasa tayi kokarin matsawa jikinshi ta kwanta ko zata sama mishi saukin da batada kalaman da zatayi amfani dasu, daya nemi al’amarin ya wuce kwanciya a kusa dashi, saita tsinci kanta da sallama masa, ta kumayi kokarin shanye hawayenta, ta aro jarumta ta yafa, washegari ta sake saka rigar jarumta wajen sake saukaka masa al’amura, bai fita ba, yana manne da ita, maganganun shi dai sunyi karanci a ranar, daya kaita makaranta ma gida ya sake komawa, sai dai baije daukarta ba, sakawa yayi direba ya dauko masa ita, batayi girko ba saboda Jabir din yace mata

“Nafi bukatar jinki a kusa dani Sa’adatu, abinci kowanne iri kike so sai muyi order”

Bata kumayi masa musu ba, sauran kwanakin da suka biyo bayan wannan din masu dadine a wajenta, masu kuma tsananin nauyi da firgici a wajen Jabir, saboda karfi da yaji ya kasa mallakar kanshi akan al’amuran Sa’adatu. Yanata fadawa zuciyarshi bambancin da yake tsakanin Aisha da Sa’adatu ne abinda yake fisgarshi, amman yasan yafi haka, shine kuma abinda yake tsoratashi, ita da kanta Sa’adatun ce, a matsayinta na mace, ta mallaki abubuwan da ko a mafarki bai taba tunanin zai gansu a tare da wata mace ba balle suja hankalin shi, asalima baisan akwaisu a tare da wata mace ba. Ko magana takeyi, ko dariya, akwai yanda take daga idanuwanta ta kalle shi, akwai kuma yanda take iya saka duk wani yanayi da takeji a cikin muryarta, gajiya, bacci, farin ciki, bacin rai, rudani, kowanne irin yanayi ne Sa’adatu zata saka shi a muryarta, zata kuma saka shi a duka jikinta.

Baisan yaya takeyin shi ba, zuwa yanzun dai yasan Allaah ne ya taimaki maza da yawa, ya kuma yi nufin basu da rabon wahala, shisa ya kammala Sa’adatu a lungun daya gani na gidansu, ya kuma sa ita da kanta bata fuskanci baiwar da Allaah yayi mata ba, mace irinta idan ta kauce hanya, zata halakar da maza da yawa, kuma ba zaiyiwa kanshi karya ba, idan akwai kaddara zai iya kasancewa cikin wadannan mazan, tunda gashi ya kwashe shekarunshi ya rataye a wani waje da baima san ina bane ba, duk abinda Sa’adatu zatayi motsa shi takeyi. Duk wata jarumta da zai tattaro, data sauke masa idanuwan nan nata sai yaji jarumtar ta murmushe tabi iska kamar tokar da aka kunnawa fanka. Kafin Aisha ta kirashi yake kiranta, sai dai idan tana wani abin taqi dauka, saboda yana so yaji cewar shi dinne, Jabir, mijin Aisha, yaron Hajiya Hasina, Jabir kafin Sa’adatu, kuma Jabir bayan Sa’adatu.

Aisha itace zaren da yake kulle da wannan Jabir din, daya ganta yakejin ya dawo hayyacin shi, abinda yake damunshi ya kau. Amman idan ya sauke wayar kuma saiya tsinci kanshi dabaibaye da Sa’adatu da duk wani abu daya shafeta. Shisa yau daya kasance alhamis, daya sauketa a makaranta saiya wuce gidanshi, gidansu shida Aisha, so yake ya kwanta a gadonsu, ya shaki sauran kamshinta daya rage a cikin dakin ko zai saita abinda ya goce a cikin kanshi. Sai dai yayi mamakin kurar da gidan yayi, musamman falo, tv dinsu kamar anyi watanni ba’a kunna ba a maimakon satika, nan take kuwa ya fara kiran Hajiya Hasina, yasa a samo mishi wanda zasu zo su gyara gidan. Sako kawai yayiwa Sa’adatu cewar ta kira direba ya mayar da ita gida, kuma ta nemi abinda zataci karta jirashi, akwai abinda yakeyi.

Tsaye yayi, saboda sanin cewar Aisha bataso ayi mata irin wannan aikace-aikacen, ko da anyi ma saita kara maimaitawa, musamman bedroom dinsu, babu wanda ya taba shiga da sunan a gyara. Ko yau dinma ya girmama wannan ra’ayin nata, an gyara ko ina banda can din, shiya cire kaya ya zage ya gyara dakin, har zanin gado ya sake ya shimfida musu wani. Daya gama saiya kara watsa ruwa, cikinshi sai karar yunwa yakeyi tunda uku harda rabi da wasu yan mintinan a sama, yayi nufin zuwa gida, amman sai yayi tunanin kar yaje ya samu sun dafa abinda baiyi masa ba, ba kuma zai iya jira a kara dafa masa wani abinba a irin yunwar da yakeji. Shisa ya nufi daya daga cikin wajajen da suka saba cin abinci, ya cika cikinshi tukunna ya fito, ya tsaya yayi sallar la’asar, raka’ar karshe ma kawai ya samu.

Inda ya kwana bibbiyu baije ba ya tsinci kanshi da tafiya, duk dan ya kaucewa ganin Sa’adatu, ya shaki iska daban. Haka ya dinga yawo har bayan isha’i, dan karshema mai kawai ya dinga konawa cikin rashin sanin inda ya kamata ya nufa, kanshi na fada masa ya wuce ya koma gidanshi ya kwana shi kadai, amman zuciyarshi nace mishi don me? Daya karya kan motar ma, hannuwanshine a jiki, amman zuciyarshi ce tayi masa jagora har gidan Sa’adatu, haka yanayin kallon da tayi masa bayan ya mike, saiya taka ya karasa yana zagaya hannuwanshi a jikinta, suka sauke numfashi a tare

“Kiyi hakuri, abubuwane suka rikeni”

Ya samu kanshi da fadi, haka kuma ya dinga bare-baren jiki kamar yayi mata wani laifi, bayan babu abinda ta bude bakinta tace masa bayan tayin abinci da tayi masa. Sai dai idanuwanta din nan, da su taketa horashi, da su take fada masa bai kyauta ba daya barta ita kadai, tasirin da suke dashi akanshi kuma ya fahimci tasirine mai wani irin girma, tunda a daren ba kalamai kadai yayi amfani dasu wajen bata hakuri ba, harda jikin shi ya hada. Washegari kuwa Juma’a ce, Sa’adatu bata da makaranta, bacci suka sha da safen har wajen goma da rabi, da suka tashi kuma kowa ya watsa ruwa sai sukayi order din abinda zasuci, ita da kanta Sa’adatun ce tace masa ba zata iya shiga kicin ba, yunwar da takeji ba zata iya jira ba, dan kafin ma a kawo musu, saida ta hada shayi mai kauri ta sha. Bayan sun gama karyawa, Jabir ya hada kayanshi da suke gidan, masu dauda, ya kira akazo aka dauka, aka hada kuma dana Sa’adatu dan a wanko musu.

Sai ya tafi gida da nufin ya dauko wasu kayan, daya shiga kuma saiya kwanta akan gado ya dan huta, kwata-kwata baisan bacci ya dauke shi ba, kuma a cikin baccin da yayi tunanin mafarkine, kamshin Aisha ya cika masa hanci, haka ma sumbar da take manna mishi a ko ina labbanta ya samu a fuskar shi, saiya mika hannu ya rikota yana sauke numfashi

“Jay…”

Ta furta cikin kunnenshi, ya bude idanuwanshi, ya lumshe, ya sake budewa yana waresu a kanta, dariya tayi ta zame jikinta ta mike

“Suprise…”

Ta fadi tana sakeyin dariya ganin yanda Jabir yake ware mata idanuwa hadi da mikewa zaune akan gadon

“Tasha”

Ya kira, ta jinjina masa kai

“So nayi in maka bazata, daman sai dai ka dawo gida ka sameni yau, sai kuma na sameka a gidanma”

Zuciyarshi tayi wata irin bugawa tana sake bugawa da tunanin da ta dawo ta zauna jiranshi fa? Shikuma yana can gidan Sa’adatu, ko kiranshi tayi idan taga lokacin daya saba komawa gida ya wuce ba lallai ya zamana yana tare da wayar ba, sai yace mata me? Ina yaje ya kwana? Wajen Sa’adatu? Ya fara harhada kalaman ta ina? Yanzun ma jin makoshin shi kamar ansa zare da allura an kulle, sai yayi mata murmushi har hakoranshi suna bayyana, ya kuma mika hannayenshi, batayi musu ba ta saka nata a ciki, ya rike yana dan janta hadi da murza yatsunta

“Nayi kewarki”

Yace yana gyara zamanshi, ya kuma zaunar da ita a jikinshi hadi da rungumeta sosai, ya shaki kamshinta

“Sosai…”

Kalmar ta fito kamar an shake shi, saita kara narkewa a jikinshi

“Nima haka, duka banajin dadi, kuma nasan rashinkane a kusa dani”

Numfashi ya sauke, bai hanata ba da tace masa tana bukatar watsa ruwa, shima, ba kuma wai don ya wartsake daga baccin da ya tashi bane, bazatan dawowarta yake son daurayewa, ya kuma tattara nutsuwar shi waje daya, tunda Aishan tasan shi fiye da yanda yasan kanshi, alama dayace zata iya fahimtar da ita wani abu ya canza a tare dashi, wani abu da haka kawai yaji ya kamata ace ya binne shi a tsakaninsu, saboda baisan me sanin zai haifar musu ba. Ko bayan sunyi wankan ma sai suka zauna a dakin, ta kwanta a jikinshi suna hira, da ba juma’a bace a gida zaiyi azahar, yaja musu sallar suyi tare, dole ya sauya kaya ya fita, da yake akwai babban masallaci anan cikin unguwar tasu, ana idar da sallah kuma ya koma, ya samu Aisha harta shirya tana jiranshi

“Mu fita muci abinci ko?”

Aikuwa baiyi mata musu ba, ya dai dinga zagaye yana son tuno wani waje da yake nasu shi da ita, wani waje da bai dauki Sa’adatu sunje ba, dakyar ya samu guda daya, yaji dadin yanda Aishan bata nemi dalilin da yasa ya dinga wannan zagayen dasu ba. Da sukaci abincin suka gama, saiya nufi gidansu Aishan dan yayiwa mahaifiyarta sannu da dawowa, sunma samu gidan da ‘yan uwan Aisha din, aka zauna anata hira har la’asar, daga nan suka wuce wajen Hajiya Hasina, ko da ya fita sallar Magriba, jikinshi yanata masa wani iri da tunanin Sa’adatu, ga wayarshi a mota ya barta, shisa suna komawa daga masallaci saiya tsaya ya dauki wayar, ya kuma samu tayi masa kira har biyu, ya nemi karfin gwiwar kiranta ya rasa, saiya tura mata sako gajeran sako kawai

“Aisha ta dawo”

Ya saka wayar a aljihun shi yana shigewa cikin gida. A bangaren Sa’adatu kuma tayi saurin daukar wayar da batafi mintina biyu da ajiyewa ba, wani irin kadaici da kewarshi ce suka dinga nukurkusarta, ta rasa abinda yakeyi mata dadi, duk wani abu da yake sakata farin ciki yau ta neme shi amman bataji ta dawo dai-dai ba, har kuwa da contract din yin zobo da kunun aya kowanne roba 100 da Badr ta samo mata na suna, dan ta lissafa, kudin suna da nauyi ba laifi, irin nauyin da ada zai sa tayi tsalle tayi juyi, nauyin da zai bayyanar da tattausan murmushi a fuskarta ko a yau dinma da ace Jabir na kusa da ita, ko kuma ace tasan me ya tsayar dashi, gashi ta kirashi har sau biyu bai daga ba tun wajen karfe shida, bai kuma biyo bayan kiran da sakon uzurinshi yanda ya sabayi mata a kwanakin nan ba sam.

Yanzun kuwa zuciyarta har tsallen murna tayi da sakon ya shigo, kafin ta koma tayi wani shiru cikin kirjinta, ta kusan mintina biyar, ko bayan hasken wayar data subuce mata daga hannu zuwa kan kujerar da take zaune ya dauke, sakon na mata yawo a cikin idanuwanta, ya kuma samu waje yayi mata zaune a cikin kai. Yawo yakeyi, kwakwalwarta nata nemar mata fassarar shi, data nutsu waje daya kuma saiya zamana fassarar ba guda daya bace ba, fassarorine masu yawa, kadan daga cikinsu sune

Aisha ta dawo

Matar shi ta dawo

Dalilin da yasa yake zaune da ita ya kare

Amfanin da take tunanin tana yi masa ta daina a yanzun

Abinda kuma duk take tunanin ya faru a satikan nan a cikin kanta ne kawai

A wajen shi, a bangaren shi babu wani abu daya canza

Ita din bakomai bace face yarjejeniyar data saka hannu akai

Wani irin abu da yafi hadari duhu ya lullubeta, kafin duka kirjinta ya fara zafi kamar ta kangashi jikin murhu, kawai dan an dan samu giccin wani abu daya sha bamban da yarjejeniyarsu baya nufin komai, wauta da sakarcinta ne ya hadu ya daga fatanta, watakila ma idan ta dauko takardar, tunda ba karantawa tayi ba, ta duba zata ga cewar yarjejeniyar tasu akwai wannan, akwai bashi hadin kai duk lokacin da zai nemeta, ai hakanma karin chances dinsune na samun abinda ya shigo da ita rayuwarsu. So take ta daina ganin bakin Jabir, bashida laifin komai, ita ta saki jikinta, itace kuma tunaninta yake rawa, nashi a tsaye yake, itace take tunanin ta dan samu muhimmancin da ba zai iya yakiceta gefe haka ba lokaci daya

Fatanta ne kawai

Kuma da alama in bata bi a hankali ba fatan nan zai zameta mata kogin da zata nutse a ciki

Gashi ko kusa bata iya ninkaya ba balle ta fito da kanta

Ta rufe idanuwanta, sai taji kamar tayi hakan ne a cikin idanuwan Jabir, sai kuma yau taga abinda ya razatana a cikinsu, abinda bata taba gani ba

Halaka…

<< Tsakaninmu 41Tsakaninmu 43 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 42”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×