Skip to content
Part 41 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Kwance yake, idanuwanshi a rufe, hannunshi rike dana Sa’adatu, ba kallonta yakeyi ba, ya dai san kuka takeyi har lokacin, ko yace hawayen da take ta kokarin ganin ta tsayar ta kasa, ga dakin yayi shiru, sai hanci da Sa’adatu take ja lokaci zuwa lokaci. So yake ya mike, ya taimaka mata, amman wani abu daya rasa ko menene ya rike shi. Babu yanda za’ayi binciken da sukayi akan Sa’adatu ya zama karya, saboda itama da bakinta ta tabbatar musu cewar ta taba aure, da wannan tunanin a ranshi yaje mata, sai komai yake nema ya karyata abinda ita da kanta ta tabbatar masa. Sai kuma shekarunta da nashi suke ta fado masa, musamman yawan nashi shekarun. Shi musulmi ne, haka Sa’adatu, akwai mata da yawa da akayiwa aure ake kuma kanyiwa aure da kananun shekaru, yau dai duk wannan ya bacewa Jabir.

Bayajin komai a yanzun da yake kwance sai rashin gaskiya, wani irin rashin gaskiya da yake ta daure shi ta wajaje da dama, musamman yarintar da Sa’adatu tayi masa, yarintar daya ture kasa da awanni biyu da suka wuce ya biyewa zuciyarshi. Hannunta ya kara matsewa cikin nashi yana fatan ta karanci hakurin da yakeso ya bata amman ya kasa furtawa. A hankali kuma ya saki hannun nata, yana lalubar kayan shi cikin duhun dakin ya suturta jikinshi ya sauka daga gadon zuwa bayi. Ruwa mai zafi ya hada sosai a kwamin wankan da yake cikin bayin. Kafin ya fito sai Aisha ta fado masa a rai, zuciyarshi tayi wata irin dokawa, tana son daukarshi ta watsa shi wani dare makamancin wannan, wani dare mai dumbin tarihi a tsakaninshi da Aishar, ya girgiza kanshi yana fitowa, ya bangaren Sa’adatu ya zauna gefen gadon.

“Sa’adatu…”

Ya kira a tausashe, taji shi, tunda ya sauka daga gadon tana jinshi, shisa ta rufe idanuwanta, abubuwa da yawane suka danneta, ciki harda wata irin kunya da batasan ya zatayi da ita ba, a gefe daya kuma tunanin Tahir ne da take tunanin ta gama binnewa yaketa yunkurin fitowa daga inda ta boye shi, aurenta ko akan wacce irin ka’ida akayi shi, aure ne, sunan shi da kuma zunubin da zata iya dauka a cikinshi dayane da kowanne aure, taje Islamiyya, ta sani, tunanin wani namijin da auren wani akanta yana cikin abubuwan da zasu zame mata barazana wajen karin taruwar zunubanta. Amman ya zatayi? Ya zatayi tunda Jabir yayi mata dalilin da ya tilasta mata wannan tunanin? Taya za’ayi ba zata hada abinda yayi mata da wanda ya gifta a tsakaninta da Tahir ba, Tahir din da yaje mata da tarin kauna, kulawa da kalamanshi da suka sakata sadaukar masa da kanta, suka kuma dasa mata jarumtar da batasan tana da ita ba sai a daren.

Duk wani zullumi da taradaddi, Tahir saida ya kawar mata dashi, ba zatace hawayenta basu zuba ba, amman sun zubone cike da kaunarshi, cike da farin cikin shine mutum na farko da tayiwa sadaukarwar nan, a lokacin bata taba hango cewa gari zai waye da yankewar zaman da suka fara a daren ba sam. Daya kare din kuma, ganin irin auren nan da sukayi da Jabir, tunaninta ma sai yayi nisa da wannan bigiren. Sai yan awannin da suka wuce, da Jabir yazo mata da bambanci mai yawa, yazo mata a mabukacin da yaci karo da abinda yake bukata, kuma da yanda yazo mata tayi amfani wajen yanke masa hukunci, bata tsinci tausayi ko daya a tare dashi ba balle wani lallami, sai yanzun? Zai kira sunanta kamar babu mai tausayinta sai shi?

“Sa’adatu…ki tashi ga ruwan zafi can, zakiji dadi idan kika gasa jikinki”

Ganin ko motsawa batayi ba, yasa Jabir kama hannuwanta yana kokarin dagota

“Ka sakeni zan iya…”

Ta fadi da sauri, sakin nata yayi, saida ta nemi kayanta ta saka ta kasan bargon, tukunna ta sauka, idanuwanshi akanta harta nufi bandakin, saida yaga ta rufo tukunna ya tashi shima, ya fice daga dakin zuwa wani dan ya samu yayi wanka. Sanda ya dawo da fitilar wayarshi ya haska, Sa’adatu na kwance, sai shima ya kwanta yana matsawa ya rikota jikinshi, bata koyi motsin kirki ba, yana daijin tanata sauke ajiyar zuciya alamun kukan da tayi

“I’m sorry…”

Ya furta a hankali yana sumbatar kanta, hadi da shafa bayanta cike da lallashi, kalmomin kuma ya dinga maimaita mata har bacci ya dauketa. Kafin shima yayi baccin, da asuba kuwa ko da sukayi sallah baccin suka sake komawa, Jabir dai ya riga Sa’adatu tashi, har wanka yayi ya saka wani ya sake kaya, sai kuma ya fito da wani yadi, ya koma kan gadon ya zauna ya dauki wayarshi yana daddanawa, da yaji ta motsa sai yayi iya kokarin shi wajen ganin bai juya ya kalleta ba, ta dade kafin ta mike zaune, da ta ganshi a kusa da ita kuwa, yanda ta sauka daga gadon saida dariya ta kusan kubce masa.

“Kiyi wanka kizo mu fita muci abinci, yunwa nakeji tun dazun inata jiranki…”

Idan taji shi, to bata nuna wata alama ba, shi dai ya mike ya saka yadin shi a jiki, ya dauki links din da waya ya fita falo, mukullin motar shi dama wallet dinshi suna can. Bai san ko dan yanata duba agogo bane shisa yaga Sa’adatu ta dade. Kamshin turarukanta ya fara cika masa hanci, ya daga kai ya kalleta, bakar Abayace a jikinta mai fadi sosai, dan hannuwan ma manyane, baisan yanda ta daura dankwalin kanta ba, ya zauna yayi mishi kyau, sai ta nada mayafi ruwan toka, haka jakarta da dan flat din takalminta, kanta dai a kasa yake, mikewa Jabir yayi yana takawa har gabanta, yayi amfani da hannayen shi biyu, ya dago da fuskarta, idanuwanta a kumbure suke, daga saman fatar yayi wani ja, alamun kukan da tayi, sai tayi masa kyau, wani irin kyau da yasa shi son sumbatar idanuwan nata da yanzun ta rufe su tana kaucewa nashi da ya saka a ciki.

“Sa’adatu, ki kalleni please.”

Yanda ya karasa maganar ne, cike da tausasawa yasata bude idanuwan nata, kunya, kunya sosai ta lullubeta.

“Kinga kunyar nan…”

Jabir ya fadi yana dorawa da.

“Banason ta, dan Allaah ki taimakamun, karki ce zaki arota ki yafa a tsakaninmu, banaso…kinaji.”

Ta daga masa kai, saiya sumbaci goshinta yana dorawa da

“Good girl.”

Ya saki fuskarta ya juya yana barinta da mutuwar jiki, dakyar ta iya jan kafafuwanta tabi bayanshi, da tana bandaki taso ta fito ne tace masa yaje ya siyo musu koma menene ya dawo, sai dai tun fitar da sukayi Abuja, sai ta dinga tunanin fitar tana hasaso ranar da hakan zai sake faruwa da ita, sau nawa ma tanayin yunkurin kiran Direban da take da lambarshi tace ya kaita wani restaurant din dan ta zauna ta zabi abinci azo a jera a gabanta yanda masu kudi sukeyi, sai kuma ta nemi kwarin gwiwar zuwa irin wannan wajen ita kadai ta rasa. Shisa duk da ciwon da jikinta yake mata, saita kara shiga ruwan zafi, ta kuma gasa jikin sosai, data fito taji dadi, ta samu ta shirya. Saida Jabir ya bama maigadi kudi yace masa ya siyi wani abin da zaici sannan suka fita. Ya mika hannu yana kunna wakar data gauraye motar a hankali. Wakar turanci ce da tayi mata dadi, saboda irin wakokin nan ne marassa hayaniya, gashi Jabir na tukin a tsanake, ga kuma sanyin AC din motar da kamshinsu daya gauraye yana bada wani yanayi mai saukar da nutsuwa.

Da yayi parking din motar kuwa sai taji daman basu zo ba, daman wata tafiya ce mai dan nisa zasuyi. Haka suka fito suna shiga wajen tare, akwai tsirarun mutane, kuma kamar ba wannan bane zuwan Jabir wajen na farko, tunda wasu cikin ma’aikatan sunata gaishe dashi, haka kuma yanda yake tafiya tana biye dashi ya kara tabbatar mata ya saba zuwa, wata corner ce, suka zauna, kuma kamar akwai wata katanga tsakaninsu da sauran mutane, aka kawo musu Menu da jerin abubuwa birjik, idanuwan Sa’adatu ya sauka kan Coffee da shi kanshi ya kai wajen kala shida, sai taketa mamaki, dan tasha karantawa a littafi, kamar shan Coffee din wata alama ce ta gayu, ko kaiwa kololuwa a ajin wayewa, daga yanda zakaga jaruman, maza da mata sun tashi da safe sunce su Coffee kawai zasu sha, haka a fina-finan turawa ma, sai su shiga waje a basu shi adan kofi su kama gabansu.

Ta kuwa zaba dashi, bata san ya sauran yake ba, shisa ta zabi na saman kawai, shawarma, sai burger, batama ji duka abubuwan da Jabir ya zaba ba, ta daiji plantain a ciki, ita kuwa tana da ita a gida, me yasa zata fito waje taci? Basu jima sosai ba kuwa aka kawo musu komai aka jera a gabansu, Sa’adatu taja kofin coffee din gabanta, sak irin yan kofunan nan ne da take gani a fim, irin wanda aka bata abu a ciki da sukaje gidansu Jabir, dan karamin murmushi ya kwace mata, ta dauki shawarma din ta bude ta faraci a hankali tana jiran Coffee din ya dan sha iska, zuwa can ta dauka, tayi masa kyakkyawar zuka, gabaki daya yanayin fuskarta ya canza, wani irin daci da baiyi mata ba ya gauraye duka dandanon bakinta, Jabir na kula da ita.

“Ya akayi?”

Ya tambaya.

“Wani abune suka kawomun mai daci sosai.”

Ta amsa da dukkan gaskiyarta, dan dakyar ta hadiye, da badan karta bada kanta ba, tabbas dawo dashi zatayi, aiko maganin basir din da Abida takan matsa musu su sha idan ta jika, bai kai wannan rashin kan gado ba.

“Me kikace su kawo miki?”

Ya sake tambaya yana mika hannu ya karbi kofin daga hannunta

“Nifa Coffee na zaba”

Kaiwa Jabir yayi a bakinshi ya kurba ta hudar saman kofin

“Coffee ne ai.”

Yace mata, dan shi sikarin cikine ma yayi masa yawa

“Wannan ne Coffee din daman?”

Cewar Sa’adatu cike da tashin hankali, to akan me za’a dinga shan shi? Dariya Jabir yayi.

“Ke wanne iri kika saba sha?”

Ta girgiza masa kai

“Ni ban taba sha ba, yaune nace bari inyi abin ‘yan gayu, ashe wahala kawai kukeyi, bakina gabaki daya ya lalace, kaji tsautsayi”

Dariya yakeyi yana kallonta, ita bata boye-boye, komai kai tsaye takeyin shi

“To ai kuwa saiki shanye tunda kinsa an kawo miki”

Idanuwa ta ware masa

“Dan Allaah kace su kawomun wani abin, ko irin bubble tea din nan idan suna dashi, niko ma meye dai wanda bashida daci”

Saida ya gama dariyar shi tukunna ya kira waiter din, aka kawo mata bubble tea, sai dai har suka gama cin abincin yana dariya, musamman da ya cigaba da janta da hira, kuma yayi sa’a ta sake kamar ko da yaushe. Haka ya karayi musu takeaway na abubuwan ciye-ciye, ya biya suka koma gida, Jabir bai shiga cikin gidan ba, yace mata zaije ya dawo. Kar dai tayi girki, ta zauna ta huta, idan kuma tana marmarin wani abin tayi order a kawo mata. Haka ta shiga gida da nishadi na daban, da sukayi waya da Fa’iza tana fada mata ko kunun aya da zobo na nawa take so, take fada mata Jabir yana nan shisa ma.

“Ki dinga fadamun kona nawa akeso Sa’adatu sai in dingayi daga nan, kinsan maza irin Jabir suna bukatar kulawa, karki raba hankalinki biyu…”

Dariya kawai ta dingayi, haka Fa’iza taita bata shawarwari, wasu maganganun ma sunyi mata nauyi, musamman yanzun da Jabir ya sauya zaman nasu a jiya, tunda da gani takeyi ai duk wannan shawarwarin Fa’iza na bata bakinta ne, to yanzun kuma fa? Zata dauki wasu a cikinsu ne ta fara amfani dasu ko meya kamata tayi? Zuciyarta ta dinga bugawa, kuma kamar Jabir yasan tunanin da takeyi kenan ya zabi wannan lokacin ya kirata, muryarta har rawa take lokacin data amsa

“Yanzun nakejin an dade da fara siyar da Jamb, har an kusan rufewa, amman nayiwa Sa’ad magana sai muje café dinshi ayi miki komai, ki dai zauna cikin shiri dana shigo na dan watsa ruwa saimu wuce”

Muryarta can kasa ta amsashi, ta sauke wayar da wani yanayi da bashida suna a wajenta, Jamb, itace zatayi jamb? Jamb dai ta sharar fagen shiga makarantar gaba da sakandiri. Yaushe ma rabonta da tunanin makarantar? Tama gama yanke hukuncin abinda zata karanta? Ada tana da ra’ayoyi kala-kala, musamman da take bangaren science, sai daga baya kuma bangaren lafiya ya dinga fisgarta, idan kuma zata fadi gaskiya, bawai taimakon da suke bayarwa ga al’umma bane yake janta, irin kudin da ake magana suna samu, sannan da wahala ka karanci bangaren nan ka rasa aiki, ita kuma daman musababbin karatun kenan, saboda ya zame mata mafita, sai dai kuma ance kudaden da ake kashewa ba kanana bane ba, wannan ya sanyaya mata jiki matuka, Abdallah ma daya ya samu yin karatun? Shi da yake FCE.

To shi zai biya mata? Jabir din? Ta tambayi kanta tanajin zuciyarta na wani irin bugawa cikin yanayin da bata taba ba. Ko abubuwan da taketa harin zataci, ta kasa, saita sha kunun aya kawai. Ta daiyi kokarin turawa Fa’iza lambobin mutane da kuma adadin abubuwan da sukayi order, sai mai delivery dinta yaje ya karba ya kakkai musu daga can, tunda batasan sanda Jabir zai dawo ba, ko idan sun fita yaushe zasu shigo gidan. Tun azahar ta sakeyin wanka, wata abayar ta sake daukowa ta saka, zuciyarta nata bugawa, amman Jabir bai shigo gidan ba sai wajen uku da wani abu, tsakanin wankan shi da shiryawa saiga shi ana kiran la’asar, saida yaje yayi sallah ya dawo tukunna suka fita, kamar kowanne jamb center a lokuttan siyar da Jamb, layine dankam, dan dakyar ma Jabir ya samu wajen da yayi parking din motar shi.

Haka suka fita, ya kama hannunta ya rike suna ratsawa ta cikin mutane suka wuce, anma rufe gate din shiga wajen, sai dai suna ganin Jabir aka bude musu, tanajin wata na fadin

“Wannan dai rashin adalci ne, masu hanya sai zuwa suke suna shigewa, muna nan tun safe…”

Wata na karbewa da

“Allaah dai Ya isa”

Aka mayar da gate din aka rufe, Sa’adatu nata mamaki, wai itace yau da alfarmar nan, tazo waje irin wannan ta wuce hankali kwance, bayan ga talakawa can ‘yan uwanta a tsaitsaye, saima yanda taga an hau sama dasu bayan Jabir din ya kira Sa’ad, har da maltina da ruwa aka kawo musu, Office din ya dauki sanyin AC, ga kuma kamshin room freshener, haka wani matashi dan gayu da take tunanin shine Sa’ad din daga yanayin yanda suke gaisawa da Jabir, yanda ya gaisheta cike da girmamawa saida taji kunya

“To wanne course ma da wacce makaranta take so?”

Jabir ya kalleta, itama ta kalle shi

“Bari inje in karbo laptop daya sai inzo nan inyi mata…”

Cewar Sa’ad batare daya jira amsar tambayar da yayi ba, yana fita Sa’adatu ta kara kallon Jabir

“Wacce makaranta zan zaba?”

Ta tambayeshi

“Duk wadda kike so”

Ya amsa mata

“BUK akwai tsada sosai ko?”

Dan kallonta yayi

“Duk wadda kike so ki zaba, zan biya miki harki gama”

Kuma wannan din shine plan dinshi tun ranar da sukayi maganar makaranta a Abuja, alkawari ne kuma daya daukarwa kanshi, zai tabbatar ta samu ilimin daya ga soyayyar shi karara a cikin idanuwanta. Wani sanyi taji ya lullubeta, sanyi tare da wani abu daban kuma da yaketa kaiwa zuciyarta duka tunda Jabir ya rufe bakinshi. Tana daga cikin mutanen da sukayi sa’a sosai, waec dinta tayi kyau, lokacin tunanin inda kudin makarantar zasu fitone ya rage mata karsashin murnar jarabawar. A nutse Sa’ad yake mata tambayoyin duk da ake bukata, sai ta zabi BUK a zabinta na farko, ta kuma zabi Bachelor of Nursing Science, haka sauran makarantun ma duka abubuwan data zaba bangaren lafiya ne. Basu dauki lokaci ba aka gama musu komai, Sa’ad din yayi masa tayin ko zai biyawa Sa’adatu ajin da sukeyi na horarwa dan yana taimakawa dalibai wajen shiryawa jarabawar jamb din, musamman ma ita data zabi Nursing, kuma akwai lissafi a combination din nata, nan take kuwa Jabir ya biya komai, takardun kwara biyu ne aka fiddo mata, amman sai sukayi mata nauyi a hannunta, haka ta damketa suka fito, ko idanuwan mutane da surutunsu bataji ba har suka karasa motar Jabir.

Shine ma ya dawo da ita hayyacinta ta hanyar tambayarta

“Daman kina son Nursing ne? Ance akwai wahala fa”

Danshi ba karatu yakeso ba, me zai kaishi inda zai wahala, ko yan gidansu wadanda suka zabi courses da yake ganin masu wahala ne jinjina musu yakeyi

“Ina so”

Ta amsa a takaice, ya jinjina mata kai, yaci gaba da tukin yana barinta da tunanin da batasan takaimaiman akan me takeyin shi ba, abu daya zata dorar, kewar Abida da Habibu da suka taso mata lokaci daya, ko dan abinda ya kamata ace sune mutane na farko da zasuji ne ya sameta a yau?

Shikenan ko?

Haka kowacce nasara zatazo mata da famin rashin su…

<< Tsakaninmu 40Tsakaninmu 42 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 41”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×