Skip to content
Part 43 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Tun akan Tahir tasan tana da karfin hali, tana kuma da jarumtar jure kewa. Saboda idan akwai wani abu da tarayyarta da Tahir ta koya mata shine, tunda so da kewarshi bata kasheta ba, to batajin akwai wani namiji da zaiyi ajalinta. Duk da saita mirgina daga farkon gado zuwa karshen shi sama da sau ashirin, saboda yayi mata wani irin sabo da kanshi da take mamakin, tunda a ganinta duka kwanakin guda nawa ne? Tayi hakuri ta yakice Tahir ma duk shekarun da suka dauka suna tare? Wannan ma zata iya, dan bambancin ba mai yawa bane ba, Tahir zuciyarta da wani sashi na ruhinta ya kama, gangar jikinta na wasu yan awanni ne da washegarinsu kuma suka sameta da rudanin da ya wanke matasu kamar basu faru ba. Jabir kuma ba zatace ya samu zuciyarta ba, ya dai samu gangar jikin nata, ya kuma yi mata wani irin horo da yanzun take ji a jikinta da rashin shi, to duhun da taketa fama dashine dai bata san me ya hada tare da gangar jikin nata yayi gaba dashi ba.

Kawai dai a kwanaki bakwai din nan da take ta fadawa kanta bata kirgawa, tayi matukar kokari wajen saita kwakwalwarta, neman haihuwa ya shigo da Jabir da Aisha rayuwarta, ita kuma neman kudi ya shigar da ita tasu rayuwar, ta kuma tunawa kanta dararen da take shafe awanni a cikinsu tana kwance tana lissafa kudaden da bata dasu da kuma abinda zatayi inda ace tana dasu, ranakun da ta kalli abincin gidansu taji bawai zabi take dashi ba, dolene ma ta nemarwa kanta mafita, saboda tana son jin dadi, tana so ko bata saka abu mai tsada a jikinta ba, to taci abinda duk ranta yake so. Yanzun dan ta samu na yan watanni, taci abinda take so, ta zabi kayan da take so, ta kwanta a waje me kyau, ta tashi a waje me kyau, ga kuma kudi a asusun bankinta, ba kanta ba, har ‘yan uwanta sunsan cewa tana cikin wadata a yanzun, to baya nufin ta jingine muradinta.

Baya nufin Jabir ya rudata harta fara sauka daga hanya, sai takejin gara ma da Aisha ta dawo, dawowar da tayine ya farkar da ita, ya tasheta daga baccin da takeyi, ya tuna mata kayidadden lokaci take dashi a cikin wannan daular, tana kuma bukatar tara kudaden da zata cigaba da ko rabin irin wannan rayuwar ne bayan ta barta, dan yanda ta dandani ‘yancin jin dadi, bata fata ta koma ma kuncin talauci. Sosai ta dage da karatu, ta mayar da hankalinta kacokan akan abinda ake koya musu, tana kuma fahimta fiye da zatonta. A gefe daya kuma ta sake zagewa da sana’ar zobo da kunun ayarta. Kamar yanda duk lissafin da aka koya musu a makaranta bai kwace mata ba, hakama lissafin kwanakin da Jabir yake ta dauka bai nemeta ba, ko dan sakon da yakeyi mata, ya daiyo mata aike har sau biyu, kudi da abubuwan amfani, ita kuma ta murkushe muryar da ta taso tana ce mata ta tura masa da sakon godiya.

Duk cikin ribar yarjejeniyarsu ne, kuma ma yanzun baya kara kaurin layin da yake tsakaninsu ba? To akan me zata nemi dole sai taga ta rage shi? Kowa yayi harkar gabanshi kawai. Kuma kwanakin sai taga sunayi mata sauri, wani irin sauri da yau ta kasa yarda har an kwana goma sha biyar, kuma a cikin kwanakin ne tayi al’adarta, ranar da tazo mata dai wani abu ya tokare mata kahon zuciya, wani abu data danne ta hanashi yin tasirin da zata gane zuciyarta ce ta karye, saboda ta saka rai, ta saka ran akwai ciki a jikinta, da kuma bata gani ba wani sashi na zuciyarta ya karye, karyewar mai ciwon gaske. Saita danne kuncinta ta hanyar fadawa kanta ai a dadinta, da yanda lokaci yakeja batare da ta samu ciki ba, da yanda zata cigaba da tara kudaden da Jabir yake mata barinsu kamar wanda yake son wanke wani laifi da yayi mata dasu.

Yau din wainar filawa taji tana marmari, tana da sauran miya, saita tafasa taliya ta zubawa maigadi, itama taci kadan, saboda ta kwallafawa ranta cin wainar filawar, da grater tayi amfani wajen niqa kayan miyar da zata zuba a ciki dan batason suyi mata laushi, ta kuma zauna ta yanka koren tattasai, tumatir, albasa, cucumber da kuma kabeji, tayi yankan kabejin sirisiri, komai yayi mata kyau a ido. Ga manjan da take dashi me kyaune sosai. Saida tayi sallar azahar, tukunna ta fara soyawa, duka kwara goma tayi, ta ajiyewa kanta guda shida, ta bawa maigadi hudu, ta dawo ta baje a falon, harda kunun aya ta dauko dan taga alama wani lemon kwali ba zaiyi mata ba. Tunda taci kwara biyu takejin ai wannan shiddan tayi mata kadan

“Aikuwa sai in kara kwaba filawa in soya wata, me yayi zafi.”

Ta furta a fili, tana dangwalo yaji bayan ta hada da kayan hadin takai bakinta, wato abubuwa irin wannan idan akace abincin talakane bai samu kyakkyawan hadi bane ba, ko da wasa bata hasaso shigowar Jabir a wannan lokacin ba, batama san kofar a bude take ba bayan ta fita ta kaiwa maigadi wainar filawa, bata saka mukulli ba ashe, sai da ta ganshi yayiwa falon wata irin shigowa kamar an hankado shi. Ta daga kai suka hada idanuwa, sai yayi tsaye, baiyi mata sallama ba, wani abu da taji ya taso mata kuma yasa ta sauke idanuwanta taci gaba da kokarin cin wainar filawar da ganinshi ya dauke mata dandanonta gabaki daya. Dan saida ta dauki robar kunun ayarta tana kurba sannan wadda take neman shake mata wuya ta wuce, data mayar da hannunta a filet din kuma sai taketa wasa dashi a ciki.

Tanajin idanuwan Jabir a kanta, kallonta yakeyi yana mayar da numfashi, daurewar da kirjinshi yayi har cikin hakarkarinshi a kwanakinne yaji yanata warwarewa a hankali, dawowar Aisha ta bashi kwarin gwiwar nisanta kanshi da Sa’adatu, duk da a rana saiya karya kan motarshi sama da sau uku yana samu dakyar ya juya, wancen satin daya fita har bakin layin yazo, sau biyu, ya kuma kashe motar yayi zaune a ciki yana kallon layin kamar mai jiran ganin ta inda zata bullo, amman yasan ko wani waje zataje ai direba ne zaije ya dauketa, idan kuma ta gama abinda zatayi shine zai mayar da ita har cikin gida. Bayaso ya karasa ne komai ya sake kwance masa

“Wani abu yana damunka, ba zan matsa maka da tambaya ba, tunda da kanaso in sani ba sai na tambaya din ba Jay, kai me fadamun duk wani abu da kake tunanin ya kamata in sani ne…”

Aisha tace masa kwanaki biyar da suka wuce, saiya ware kwanaki uku, idan ma tana da aikin da zatayi to shine yake kaita, idan lokacin da ta gama yayi ta kirashi yaje ya dauketa, su zagaya duk wani waje da yake sakasu nishadi, kafin su dawo gida, tayi iya kokarinta wajen ganin ta saukaka masa damuwarshi ko da bata cire masa ita gabaki daya ba. Wani abu daya kula dashi, shine yawan ibadar Aishan daya karu, karfe uku da rabi take tashi, bata kuma komawa sai bayan asuba, ya sha tashi ya ganta tanata sallolinta, sai yaita kallonta harta koma bacci, sau dayane ma ya tsokaneta da fadin

“Indai nine fa Allaah Ya gama kama mikini, ba sai kin kara mika sunana ba”

Tayi dariya sosai tana sumbatar kumatunshi batare da tace komai ba, kamar yanda bata sake tayar mishi da maganar damuwar da yake ciki ba, damuwar da yaketa kokarin ganin ya raba kanshi da ita, ko da idan tana kusane, inta kaucewa ganinshi sai damuwar ta dawo. Shi aiya san ba wani abu bane sai tunanin Sa’adatu, sai son kasancewa da ita, da ace yana cikin maza masu yawan surutu a lokacin mu’amalar aure, to daya tuni asirinshi ya dade da tonuwa, saboda yanda tunanin Sa’adatu yayi masa kane-kane, sunanta zai iya subuce masa. Numfashin kirki baya iya fitarwa a kwanakin nan saboda wani abu daya daure masa zuciya, har hakarkarin shi yakeji yana amsawa duk idan yayi numfashi. Yau kam bai karya ba ya fita, daman da daddare saboda yanda Aisha taketa binshi da idanuwa ne yasa shi sakawa cikinshi burger guda daya da ruwan Lipton.

To a shago kuwa haka ya saka abincin da yayi order a gaba, amman ya kasa kaiwa bakinshi, saiya mayar ya rufe, ya kira daya cikin yaran shagon yace ya kwashe. Daya fita ya shiga motarshi kuwa, zuciyarshi batama tsaya neman shawararshi ba, ta karkato dasu har cikin gidan Sa’adatu, dayayi parking ya kashe motar kuwa, jikinshi har wani kyarma yakeyi, kamar yaron da aka kai hutu gidan kakarshi mafi soyuwa a gareshi, ji yake kamar ya shiga gidan da gudu, dakyar ya saita kanshi, amman irin yanda Sa’adatu ta daga ido ta kalleshi, ya tabbata da kanin gudun ya shiga gidan. Bai kuma ga laifinta ba sam data mayar da kanta ta saddar, me zatayi to? Me yake tsammanin zatayi bayan kwanakin da yayi batare daya waiwayeta ba, ai baya tsammanin zata taso ta rungume shi.

Daya karasa cikin dakin yaga abinci takeci, duk da baisan meye ba, ya daiyi masa kyau, kuma baiga alamar zai ciyu da cokali ba, saiya fara nufar kicin, ya wanke hannunshi, ya dawo ya zauna yana lankwashe kafafuwanshi a gabanta. Har lokacin kuma bata dago kai ta kalle shi ba

“Sa’adatu”

Ya kira a hankali, inda kuma zata iya tabbas saita saka iccen darbejiya ta zane jikinta da ya amsa kiran nashi, har wasu gashi da batasan akwaisu ba a bayan wuyanta suna mikewa

“Meye wannan?”

Ya tambaya, so yake yaji muryarta, ko ba zata kalle shi ba tayi masa magana

“Wainar filawa”

Ta amsa a hankali, ba jikinta ba, har bakinta saita gurje shi da dutsen goge kafa, tunda bata isa yayi abinda take so ba, yaki barin kalamai su kwace mata harta kula Jabir, yasan wainar filawa, Aisha nayi, bai tabaci ba, kuma yaga wadda takeyi din ba irin wannan bace ba, ba ja bace haka, farace 

“Ban tabaci ba, amman inajin yunwa”

Yayi maganar yana kai hannunshi ya gutsira, babu zafi, akwai dai dumi

“Ya zanyi?”

Ya tambayeta, saita tsinci kanta da karbe wadda ya gutsiro din, ya nado masa yankakkun kayan hadi, ta kuma dangwala yaji ta saka masa a hannunshi, sannan ta mike, dan cikinta ya cunkushe kuma, wainar filawar ta fice mata daga rai. Kicin ta nufa ta wanke hannunta, bata koma falon ba, dakinta ta shige, tabar Jabir a zaune yana cin wainar filawar da tayi masa dadi, saida ya cinye sauran duka, ya kuma shanye sauran kunun ayar data rage. Shima yaje kicin din ya wanke hannu, saiya nufi dakin nata, ya murza kofar yaji a kulle, ya kwankwasa amman tayi kamar bataji ba

“Ba zaki budemun ba Sa’adatu”

Ya fadi cikin wata irin murya data sa bugun zuciyarta karuwa, ta kuma sa jikinta barin son tashi taje ta bude masa kofar, sai da ta janyo filo ta danne kunnenta dashi, dan ta daina juyo maganar shi, ta daiji ya kara kwankwasawa sau wajen biyar, kafin taji shiru. Ta sauke filon, batayi mintina uku ba a tsakani taji tashin motar shi, sai kuma wai idanuwanta suka cika da wasu hawaye, kirjinta ya dauki dumi

“Da kin bude kinji me zaice miki”

Wani sashi na zuciyarta ya fada mata, taji kamar ta tashi taje ta same shi kafin ya fice daga gidan tace ya dawo, sai dai jikinta yayi mata nauyin daya sa ta kasa tashi. Ta bar hawayenta sun zubo, sun kuma dade suna zuba har bacci ya dauketa, bata farka ba sai wajen shida saura, har kanta wannan karin yayi mata nauyi. Tayi alwala ta rama la’asar data wuceta, ta kumayi zamanta akan dardumar har aka kira Magriba, da ta idar saita shiga kicin tana da biredi saboda mai kwakwa data siya jiya a hanyar dawowarta, babbane kuma, saita fere dankalin turawa ta soya, tayi wainar kwai, har maigadi shayin ta bashi shima. Ta dawo taci sosai dan yunwa taji tanaji sosai, haka ta kwanta, baccinta rabi da rabi saboda yanda mafarkin Jabir ya addabeta.

Washegari ma tun kafin takwas ta farka daga baccin bayan asuban data koma, ta gama hada abin karinsu, tayi yan aikace-aikacenta, ta koma daki tayi wanka, saita samu wata rigar bacci marar nauyi ta saka ta haye gado abinta, kallo ma takeyi, wani series, legend of the seeker da taji anata hirar shi a makaranta, to wani dan ajin yanata turawa mutane, sai ta bada wayarta itama ya tura mata. Kuma yana yi mata dadi sosai, batasan lokacin da bacci ya dauketa ba, cikin baccin ne kuma taji wani abu mai dumin gaske yayi mata rumfa, dumin da ko a cikin baccin tasan bana bargo bane ba, a hankali ta bude idanuwanta, kamshin turarukan Jabir nasa ta wartsakewa lokaci daya, kafin tayi yunkurin motsi ya sake riketa yanda hakan zaiyi mata wahala. Yanda kuma duk taso ta kwace saita kasa saboda yasa karfi a rikon, cikin kunnenta, da muryarshi da a irin wannan yanayin ne kawai take sauka haka yake fada mata

“Nayi kewarki, yanzun ma da kike rike a hannuna kewarki nakeyi Sa’adatu”

Haka ya dinga maimaita mata, yana kuma sassauta rikon da yayi mata, saboda yaga baya bukatar yasaka mata karfi, da duk yanda ya maimaita yayi kewarta da yanda kalamanshi suke kashe masa jikinta, saiya maye gurbin kalaman da abinda yasan zaifisu tasiri. Har saida ita da kanta ta amsa shi da

“Nima haka?”

Cikin wata murya da inda hankalinshi baya kanta ba zaiji ba

“Kema me?”

Ya fadi hannuwanshi na isa inda kalamanshi suka kasa

“Kewarka…nayi kewarka”

Ta fadi, hawayen da batasan dalilinsu ba suna sauko mata, duk wani birbishin haushin shi da takeji ne yabi ya goge mata. Bayan ya tafi saita tsinci kanta da tambayar shikenan ko? Sai kuma randa bukatarshi ta sake kawo shi, sai ya bata mamaki, washegari ma sai gashi da rana, bai kuma saurari maganar da takeyi masa ba lokacin daya damki hannunta yana fara janta

“Girki, girki nakeyi…”

Tace, dan sunanshi har yanzun nauyin fada yakeyi mata a fili, bata kuma san abinda ya kamata ta kira shi ba

“Ruwan shinkafa na dora…”

Ya mika hannu ya kashe gas din, yana sauke mata kallon daya narkar da duk wani musu da taso tayi masa. Kwanaki masu bin kwanaki Jabir ya shafe yana kawo mata kwanan da bayayi mata shi da daddare duk rana, ita din ba mai iya danne komai bace ba, shisa yau tana kwance a jikinshi tace masa

“Matarka batasan kana zuwa nan ba ko? Shisa baka taba kwana ba tunda ta dawo”

Tambayar ta dake shi, duk da karshenta ta bawa kanta amsa ne, amman bai saba anayi masa tambaya kai tsaye haka ba, ko yace tuhuma, shiru yayi, itama sai batace masa komai ba, sun kusan mintina sha biyar a haka kafin a hankali ya zame jikinshi, ta kuma san tafiya zaiyi, tunda saida sukayi wanka ma tukunna suka koma bacci, suka kuma sake tashi, tama rigashi tashi. 

“Tafiya?”

Ta bukata, ya jinjina mata kai, da gaske ne da akace yau da gobe bata bar komai ba, idan mutum ya tsaya ya kula, zaisan cewa ranakun shiga ukunshi suna farawa ne daga lokacin da zuciyarshi ta kekashe ta daina tuhumarshi kan wani zunubi da yake aikatawa kullum, alamun yana bukatar ya tuba da gaggawa ya koma ga Allaah don Ubangiji Ya saki al’amuranshi kenan. To kusan a wajenshi hakane, ranar farkon nan daya koma gida ba karamin dadi yaji ba da bai samu Aisha ba a gidan, kafin ta koma kuma wanka sabi hudu yayiwa jikinshi da shower gel kala daban-daban, sannan ya kara sabawa da sabulun Aisha, duka wai wajen kokarinshi na ganin ya wanke duk wani tambarin da Sa’adatu ta bari a fatarshi, duk wata alama da idan Aisha ta kalleshi zata iya ganewa.

Amman yanayi mata sannu da zuwa ta karasa ta rungume shi ta gefe, ta sake shi da murmushi a fuskarta

“Wannan ne Jay dina”

Ta fadi tana wucewa ta barshi a falon, rashin gaskiyarshi na kashe masa jiki, washegari kuwa saiya aro alhini ya yafa a fuskarshi, ya kuma shagwabe mata cikin yanayin da yake sakata ajiye komai ta koma hidimar tattalin shi, zuwa yanzun kuma ya saba ya kalli tsakiyar idanuwanta batare da taji ko da digon rashin gaskiya ba, saboda yana fadawa kanshi ai duka cikin yarjejeniyar suke dagashi har Sa’adatu, kuma abinda yayi dalilin auren ne yake kokarin ganin ya tabbatar, harma da suka sake waya da Likitan shi yace masa zai nemeshi da kanshi idan bukatar hakan ta taso, kuma wannan dalilin saiya gamsar dashi, har yanzun yanajin babu wani abu da yakeyi da bai kamata ba.

Sai kawai Sa’adatu ta jefeshi da wannan tambayar? Akan wanne dalili, kayanshi ya mayar, ya kuma fice daga dakin hadi da rufe mata kofar batare da ya sake cewa komai ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 42Tsakaninmu 44 >>

1 thought on “Tsakaninmu 43”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×