Skip to content
Part 44 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ya kamata ace murna takeyi, saboda yanda take ganin ana faduwa warwas duk lokacin da sakamakon jarabawar Jamb ya fito, yasa ta dinga jin tsoro, zuciyarta haka ta dinga bugawa, gashi daga kansu ne akace za’a fara amfani da Na’ura mai kwakwalwa wajen zana jarabawar, duk da a shekarar ta 2013 an bayar da zabine, sai daisu Sa’ad yace ita zasuyi. Hannunta har zufa ya dingayi da taga laptop din a gabanta, ga jami’an tsaron da aka baza sunata zagayasu suna mazurai. Tayi mamakin ganin tambayoyin, wasu ma da tazo bangaren Physics, kafin ta tsaya lissafawa sai taga tasan amsar. Duk da ance daman idan kaji dalibai na maganar wahalar jarabawa to shirin da sukayi mata ba mai yawa bane ba. Tasan abinda ta rubuta, tana kuma da yakinin samun sakamako mai kyau, tunda babu bangaren da tasha wahala. Kawai dai zuciyarta ce a cunkushe, shisa bata wata murna.

Asalima data koma gida lokaci zuwa lokaci idan ta juya, ko ta gyara jama sai tayi jinjina kai kawai irin na wanda ranshi ya kai koluluwa wajen baci. 

“Me yake damunki?”

Jabir ya tambayeta

“Marata ke murdamun”

Ta tuna amsar data bashi

“Ko muje asibiti?”

Ta girgiza masa kai tana fadin

“Inajin period ne zai iya zuwamun kowanne lokaci”

Kai kawai ya jinjina mata, wani yanayi mai nauyi na bayyana akan fuskarshi, yanayin da ya kara mata sanyin jikin da ya saukar mata tunda safe da ta farajin alamun period din. Idan yazo shine na uku tunda wani abu ya fara shiga tsakaninsu, ba kuma sai Jabir ya fada mata zuwan period din a kowanne wata yana tabashi fiye da yanda yake tabata ba, tunda baya iya boyuwa akan fuskarshi. Da sukayi sallama ya tafi, ta shiga bayi ta kama ruwa danyin alwalar sallar Magriba taga yazo, data gyara jikinta, ta fito saita dauki wayarta ta tura masa kalma daya

“Yazo”

Shima kuma ya maido mata amsa da kalma dayan

“Okay”

Basu sake magana ba, bata kuma kara saka shi a idanuwanta ba, daman tasan hakan zai faru, ta dai rasa dalilin da yasa wannan watan abin yayi mata ciwo fiye da hasashe, tunda bata da amfanin da zatayi masa, ba zaiko da tura mata sako yaji lafiyarta ba, tasan bata da hurumin da zata dinga tsammatar irin wannan abubuwan daga wajenshi, amman ta saitin da ta yiwa kanta ya fara kwacewa, koma tace neman saitin takeso tayi ta rasa, ciwo takeji bana wasa ba akan abubuwa da yawa, ciki kuwa har yanda yake dauke kafarshi duk idan bata da amfanin da zatayi masa haka, saita gama period din yake dawowa, sai dai haka ta lissafa kwanaki hudu, ranar na biyar din data dinga kallon kofa Jabir baizo ba. Takaicin kanta data saka abinci dashi ya kamata, haka washegari, wasa-wasa sai kwanakin suka dinga tafiya har satika uku, babu Jabir babu alamar shi.

Aiken da yayi mata na karshe, bayan kudin da aka bata a hannunta, wanda ya saka mata a cikin asusun bankinta ma masu dan nauyine, harta dinga tunanin ko yan kyautar tashi ce suka motsa. Kuma bata kawo wani abu a ranta ba har lokacin saida ta bude WhatsApp, ta tsinci kanta da lalubo lambar Jabir, sai taga ya canza display picture dinshi, ya saka hotonsu shida Aisha suna tsaye bakin wani waje da yayi kama da irin wajajen nan da akanje yawon bude ido a kasashen turai, yanda zuciyarta ta matse waje dayane yasa ta fita daga whatsaWhatsApp din gabaki daya, saita koma Instagram ma taga ko wasu nason Kunun aya, daga can ta tsaya kalle-kalle, a wajen kalle-kallen nan hoto irin wanda yake dp din Jabir yaja hankalinta, suna bin juna da kusan duka yan gidansu Jabir din, dama wasu a cikin danginshi, kuma kanwarshi ce ta saka, ba hoto daya ba, hotuna ne guda biyar, duka kala daban-daban nashi dana Aisha.

Dan bayanin da tayi yana nuna cewa basa kasar, dan ga Aisha nan ma tayi magana a comment section, kuma ita kanwar Jabir din na fada mata abinda take so a taho mata dashi a matsayin tsaraba, har tana dorawa da

“Kar soyayya tasa a manta ni kam”

Ta jinjina kai, ta kuma jinjinawa daukar da Jabir yayi mata, yanda taji wani abu da ba fatar idanuwanta ba na neman rufe mata idanuwan ruf yasata komawa WhatsApp babu shiri, ta kuma sake lalubo lambar Jabir, ko sallama batayi masa ba

“Baka kasar?”

Kawai ta tambaya, ta kumayi sa’a sakon na shiga sai gashi ya hau online din ya duba

“Munzo Turkey”

Wani abu mai kama da katuwar kwallo, ba guda daya bama, saboda taji daya a kirjinta, haka tajisu sun jera kamar bene zuwa makoshinta inda sukayi tsaye suka tokare, alamu suka nuna typing yakeyi, kamar bayani yake so yayi mata, sai dai kafin ya turo koma menene taje cikin settings, tana lalubo block option din da batajin ta taba amfani dashi tunda ta fara WhatsApp, ta kuma nemo lambar Jabir din ta ajiyeta a wajen, sai ta danji iskar da take shaka ta fara wuce mata. Ai bata da wani muhimmanci a wajenshi, bata da shi ko dan kankani da zai ware minti daya cikin lokacinshi yayi mata text ya fada mata zasu bar kasar shi da matarshi. Shisa ya bata kudi kenan, tunda taga alama bayan Miliyan biyar din da suka ambata mata shi da Aisha, bata kudin yin duk wata hidima na cikin yarjejeniyar, kawai dai daukarta yar adam, mai daraja da muhimmanci daya kamata a duba yau da gobe a dinga kamanta yi mata wasu abubuwan ne babu a ciki.

Saima da ta kwanta, data juya saita hango hannun Jabir zagaye da kugun Aisha, sai kuma dariyar da yakeyi da hakoranshi gabaki daya a waje, gani tayi ma kamar harda nacan ciki, wanda yake tauna abinci dasu, a wani hoton ma yanda ya dashe baki, har hakorin hankalinshi saida ya bayyana, tunda yana cikin farin ciki, yana tare da matarshi, ita kuma tana nan. Yanda duk ta dinga danne hawayenta sai da suka zubo, suka kuma cigaba da zama suna tayata hira har bacci ya dauketa. A maimakon kwanakin da suka cigaba da zuwa suna wucewa har zuwa yau su tafi da takaicinta, sai suketa kara masa yawa. Ga Jabir bata budeshi daga blocking din lambarshi da tayi ba, ta so ace harda takaicinshi duka ta hada tayi blocking din. Tana cin abinci tana mitar da batasan sanda ta koyeta ba cikin ranta, kuma duka akan Jabir. Ta gama ta tashi takai filet din kicin, ta koma daki, bata sake fitowa ba sai bayan tayi sallar la’asar, ta watsa ruwa ko zataji dadin jikinta, dan inta koma ta kwanta bacci zatayi, bata kuma son yin bacci da yammacin, tazo taita juye-juye da daddare.

Ta samu riga da wando ta saka a jikinta ta koma falo ta kwanta akan doguwar kujera tana danna wayarta, karatu ma takeyi, wani littafi na Rufaida Umar daya dauki hankalinta, mai suna Mukaddari, taji kamar ana kokarin bude kofa, hakan yasa ta tashi zaune tana dubawa, tabbas hannun kofar ake murdawa, ita kuma ta saka mukulli ta rufe, kuma mukullin yana jikin kofar, kafin tayi wani yunkuri an bubbuga kofar, tunaninta mutum daya ya bata, Jabir. Saboda babu wani wanda zaizo mata gida batare daya sanar da ita a waya ba, kuma masu zuwa karbar kunun ayarsu ko zobo har gida, a cikin yan uwanshi ma bakowa bane yake shigowa ciki, bakin gate suke tsayawa su kirata a waya ta fita ta mika musu. Shi kadaine yake zuwa mata batare daya kirata ba, saboda shi kadaine yakejin yana da wannan isar, idan ma kofar a bude take sai dai kawai ta daga ido taganshi, ko taji shi har cikin bedroom dinta.

Tayi hamdala, ta godewa Allaah, ta sake godewa Allaah da Yasa ta rufe kofar da mukulli, ya dawo kenan, shine ya kwaso kafafuwanshi yazo mata gida, to me zaice mata? Ita me zatace masa? Da kofarta a bude take ai daya gama da ita, tunda sai dai taganshi a tsakiyar falon, tun yana kwankwasawa a hankali harya fara kwankwasawa da karfi, ta tabe baki ta koma ta kwanta akan kujera tana daukar wayarta ta cigaba da karatun, duk da kalmomin sai hade mata sukeyi suna kuma yi mata wahalar fahimta saboda hankalinta nakan bugun kofar da Jabir yaketa famanyi, da ya daina, saita dauka tafiya yayi, saida wayarta ta fara ruri tukunna taga kiranta yakeyi, tana kallo har wayarta tsinke, ya sake kira, ta cigaba da kallon wayar harta sake tsinkewa, saiga sako ya biyo baya

“Inajin karar wayarki daga inda nake tsaye Sa’adatu”

Ta juya idanuwanta, sake kira yayi, saita daga ta kara a kunnenta

“Kinaji ina buga kofa”

Yayi maganar a hankali, amman tana iya juyo ranshi da yake a bace ta yanayin maganar tashi

“Inaji”

Ta amsa wani abu daya taso mata yanasa tajin cewa dai-dai take da duk wani rikicin Jabir, tanajin yanda yake sauke numfashi ta cikin wayar alamun ranshi a bace yake sosai, yanda yayi shiru, haka itama tayi shiru na tsayin mintina biyu, kafin taji alamar ya kashe wayar daga bangarenshi. Zuwa wasu mintinan kuma taji tashin motar shi.

“Ya daifi maka.”

Ta fadi tana juya kwanciyarta. Tana kuma komawa baya inda ta karanta bata gane ba, ta dasa karatunta. Washegari ma bayan mukulli harda dan abin kofar taja ta saka, bata ma zauna a falon ba, tayi yininta a cikin bedroom, sai dai tana ganin kiran Jabir har sau biyu taki daga wayarta, data yanke ma saita kashe layin yanda koya kirata ba zai samu ba. Kwanaki biyar ya jera yana zuwa tanakin bude kofa, haka kiranshi ma bata dagawa. Sai taji abinda yayi mata tsaye daga kirjinta zuwa wuya yana rage nauyi da duk zuwan da Jabir din zaiyi taki bude masa kofa, ta kumaki daga wayarshi, ko rantsuwa tayi ba zatayi kaffara ba, yanda ya kunsa mata takaici, itama ta kunsa masa, sai yaji idan akwai dadi. Yau ma ko da wasa bataji zuciyarta tayi mata sanyin da zata bude masa kofa ba idan yazo. Da marmarin tuwon shinkafa ta tashi, tana da komai na kayan miya, alayyahu kawai ta bayar aka siyo mata.

Tayi tuwonta da miyar ganye data sha naman rago. Ta saka tuwon a warmer, dan tayi ne har dare, idan ma ya rage da safe ta karaci, ta zubawa maigadi nashi, ta dauko hijabinta ta saka, tukunna ta dawo ta dauka taje ta kai masa, kamar ko da yaushe yanata mata godiya. Da yake ko a mafarki batayi tunanin Jabir zai iya ajiye motarshi a waje, ya shigo, ya samu waje ya zauna yana jiran wannan damar da zata fito ba, haka ta koma cikin gidan, kuma akace hankali ke gani ba ido ba, ko kadan bata kula yana tsaye a falon ba, ta mayar da kofar ta rufe tana saka mukulli. Data juyama hijabinta ta cire tana ninkewa, taji tsikar jikinta ta amsa, saboda kamshin Jabir da ya cika mata kofofin hanci, data daga kai, saita sauke idanuwanta cikin nashi, lokaci daya jikinta ya fara bari, zuciyarta ta fara wata irin bugawa har makoshinta yana bushewa.

Karya takeyi, datace ta shiryawa rikicin Jabir, abinda ma duk kuwa ya tunzurata ya bata karfin gwiwar blocking dinshi a whatsapp, jarumtar ya jera kwanaki har biyar yana buga mata kofa tanakin budewa, tabbas ya yaudareta, yaudara mai girma, saboda yanzun da take tsaye a gaban Jabir, da tazarar taku wajen biyar a tsakaninsu, ta kuma ga abinda yake cikin idanuwanshi, sai taji tanaso ta zama gari, ta baje a wajen, tabi tiles, inda halima ta silale zuwa dakin da zai zamana akwai kofa a tsakaninsu, ko dan ta gujewa hukuncin da zai iya dauka akanta

“Zo nan…”

Ya furta a hankali, ta girgiza masa kai, idanuwanta na cika da hawaye

“Karki fara, karki sake kiyimun kuka Sa’adatu”

Jabir ya fadi muryarshi cike da kashedi, waiya gama rubutu, rubutu mai tsayi, duk kuwa yanda bayason dogon rubutu a whatsapp, duk idan ka duba zaka samu amsoshin shi gajerune, kalmomin da basa haura goma a lokaci daya, amman ranar saboda yanda tayi masa tambayar yasa shi jin bai kyauta ba, ya tsaya yayi mata bayanin ‘yar uwar Aisha ce, yarinyar kanwar mahaifinta ta haihu, kuma acan Turkey din suke zaune da mijinta, tun watan haihuwar take tsare-tsaren zuwan, ta kumayi tafiya irin wannan kashi nawa tana rokonshi suje tare yana kiyawa, to wannan karin shima akwai abinda yake so ya duba a kasar daya shafi kasuwancin shi, sai kawai yabari ta tsara musu tafiyar. Kuma yaje ma ya tura mata sako ya fada mata, baisan meya dauke masa hankali ba, tunda yake dinma bai zauna ba sam, abubuwa sai sukayi masa yawa, dan lokacin suka diba din shi saiya nemi yayi masa kadan.

Amman ai tana ranshi, ko dan yanda yayi kewar komai nata, ciki kuwa harda girke-girkenta da bai taba sanin akwaisu ba saida ta shigo rayuwarshi, saida ya gama ya tura mata yaga yayi tick daya, dp dinta ma yayi fari, daya duba saiya ga blocking dinshi tayi, yafi mintina talatin zaune a inda yake, wayar na rike a hannunshi, mamaki yaki sakinshi, shifa, akayi blocking, kuma ma Sa’adatu, wannan yar tatsitsiyar yarinyar har tana da karfin halin da zatayi blocking dinshi, da mamakin nashi ya kau kuma sai bacin rai ya maye gurbinshi, bacin ran da Aisha ta nemi jin dalilinshi ya zame musu fada, saboda yana neman inda zai huce kadan a cikin haushin Sa’adatu. Daya bude WhatsApp saiya kara komawa ya duba yana jinjina kai. Shisa suna dawowa, wanka kawai yayi, ya sake kaya, ya dauki mukullin mota ya fito yayi gidan, so yake ya riketa ya matse, saita fada masa inda ta samu karfin halin yin blocking dinshi, amman saita kara masa wani mamakin, da bacin ran daya dinga buga kofar taki budewa.

“Inajinka”

Wannan kalma tayi masa zafi, bayajin daga tasowarshi, da kuma yawan kannen da yake dasu, ba wanda suka hada mahaifi ba kawai, harda wanda ake rike dasu a gidan, akwai wata rana da ya taba dukan wani, duk da hakan na faruwa a tsakanin kannen nashi da sauran yan gidan da suke sama dasu. Ba kuma laifi bane basayi masa, kawai bayajin yana bukatar saiya hada da duka tukunna zasu san sunyi masa laifi, amman a ranar, a karo na farko da yaji yana so ya zane wani, ya zane Sa’adatu. Ko yau daya baro gida tun karfe sha daya, ya kuma ajiye motarshi a waje ya shigo gidan, a wajen maigadi ya karbi kujerar roba, ya koma gefen gidan ya zauna yana tafasa, saima da rana ta same shi a inda yake din, ya dauki kujera ya sake waje, rigimar da yakeji ma ta hana zafin da yake dukanshi yayi wani tasirin kirki, ji yayi kamar yayi awa goma a zaune kafin yaga fitowar Sa’adatu, tana wucewa ya mike yayi wuf yaje ya shige gidan, yana tsayen ma jiran shigowarta yakeyi.

Data shigo, sai yaga kamar fuskarta ta kara haske, kuma a maimakon tarin bacin ranta da yake tare dashi, sai kewarta ta taso masa tayi masa wani irin duka da yake neman kore bacin ran, musamman yanda idanuwanta suka haska da kyallin hawaye, ko da yace taje ma bayajin idan ta tako din ba zai rungumeta ba, shisa ma yace kar tayi masa kuka, dan hawayenta na zubowa zata karasa tsinka masa zaren da yake rike da bacin ranta, hawayen natane kuwa suka zubo, ya karasa ya damko hannunta, saita tafi gabaki daya tayi kasa, tana rike kafafuwanshi

“Dan Allaah… kaji dan Allaah…”

Take fadi a rarrabe tana jan numfashi, dan duka alamunshi sun nuna dukan tsiya yake shirin nada mata, ita kuwa yanzun yanda jikinta ya manta duka, ina zata iya? Ko da canma baso takeyi a taba lafiyar jikinta ba, balle kuma yanzun

“Ai kaine, kaine ka fara tafiya baka fadamun ba…”

Ta cigaba hawaye wani nabin wani, saiya saki hannun nata yana kallon ikon Allaah, yanda take hawaye kamar wadda ya daka

“Kuma sai kazo, nima shine na rama”

Ya jinjina kai

“Saboda na zama sa’anki right? Ni Sa’adatu…”

Kai ta girgiza masa da sauri

“A’a wallahi, nice dai, ni…ba kai ba ni”

Ta karasa tana kama kafafuwan nashi ta mike, hawaye basu daina zubo mata ba, ita waye ma yace taki bude masa kofar

“Ba zan kara ba.”

Kallonta yakeyi, gabaki daya ta rikice

“Ga tsoro ga karfin hali.”

Ya fadi a zuciyarshi, yasa hannuwanshi duka biyun ya tallafi fuskarta data jike da hawaye, yana saka idanuwanshi cikin nata

“Ba’a taba blocking dina ba.”

Ya furta a hankali

“Zan budeka…..”

Ta fadi muryarta na rawa.

“Ba’a taba ba Sa’adatu.. ba’a taba rufemun kofa ba…”

Dan ko fada sukayi da Aisha, sai dai idan shine yayi fushi ya bar mata dakin, amman ita idan ta gwada binta yakeyi su cigaba daga inda suka tsaya, balle ace ta rufe masa kofa, ai bazai ma iya hasaso tashin hankalin da zai faru ba.

“Ba zan kara ba.”

Tayi maganar cike da tabbatarwa, da kuma wani irin rauni daya sakashi rankwafawa yana sumbatar idonta, ya koma ya sumbaci dayan, yanajin sanyin hawayenta akan labbanshi, daya dago sai yayi amfani da hannuwanshi wajen goge mata fuskar cikin wani yanayi dayake neman saka tsayuwa gagararta, duka haushin shi da takeji yabi iska

“Kayi hakuri”

Baice komai ba, fuskar yake goge mata, yakai daj yatsa yana dauke kwallar datake neman sake zubo mata hadi da dan girgiza mata kai, bayason kuka sam, musamman nata da yake sakashi jin abubuwa mabanbanta

“Ka hakura?”

Kai ya daga

“Idan ban hakura ba ya zanyi dake?”

Sai dai yayi mata fada, saboda yarintarta, badai yayi fada da ita ba, yanda take ta tsiyayar hawayen nan, wani nabin wani tunma kafin yayi mata fadan, ina zata iya fada dashi? Ai bata da karfin gwiwar mayar masa da magana yana gab da ita haka

“Kije ki budeni a whatsapp kuma”

Yanayin yanda yayi maganar yasa dariya kwacewa Sa’adatu, daya harareta saita kwace fuskarta daga hannuwanshi tana boyeta a cikin kirjinshi, ya kuwa zagaya hannuwanshi ya rungumeta

Wani abu na dukan zuciyarshi

<< Tsakaninmu 43Tsakaninmu 45 >>

1 thought on “Tsakaninmu 44”

  1. Ummulkhair Abdullah

    Tunda na fara karanta littafin nan na kasa ajiye shi sai da kai karshe yanzu! Ina jiran cigaban ta kan na yi comment properly
    Amma Nagode sosai da wannan rubutun, na ji dadin sa sosai sosai sosai

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×